Showing 123001 words to 126000 words out of 150731 words
kaninki" "to" tace tafita daga falon, ko 2min batai da fitaba kwamissiona ya shigo yana murmushi zama yay kusa da Abban yajawo tray abincin yadau goran ruwa yana kokarin budewa batare daya kalli fuskan Abban ba yace "ga Fateema nan idan tama zan baka ita friend you need a woman, life cannot go on like this, d best of us shine wanda yagane kuskuren shi yay admitting sanan yay asking Allah for forgiveness, dan Adam ajizi ne, no body is above mistake, sanan babu wanda yafi karfin jarabawan Allah, zan baka auren Fateema she's 24 yanzu, kanason ta? Zaka aureta?"
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi*
*masu fitarmin da novel waje kuda Allah*
*3107021073 first bank aisha Muhammad zaki turo 300 access fee saiki turamin evidence ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting, you can also send MTN card through my watsapp number 07012181461*
_BOYAYYEN MUTUN_
*A22*
Kallon kwamissiona yake da mugun mamaki yama kasa magana, kunenshi da gangan jikinshi sun kasa yarda da abinda sukaji shi kwamissiona yace zaibama Fateema? Fateema dai da yanzun nan tabar dakin nan? Dago kai kwamissiona yayi ya kalleshi yay murmushi ya dafamai kafada yace "am serious o, just take it as wani kyauta ne Allah yakeson yama nayin nadama akan abubuwan dakayi, so dan haka nabaka y'ata kafin takoma kano school next week Sunday sai adaura auren ko, duk yanda zaka yi sai kayi tunda matar kace, zaka Iya kamamata gida akanon kokuma dukma yanda zaka yi nidai nabaka ita" sosai Abba kewani irin kallonshi ahankali bakinshi narawa sosai yace "f..fr...friend, Fateema yarinya ce, namata tsuf..." hannu kwamissiona yasa akan bakinshi yace "yes yarinya ce, karasa Nadeera wani yariga ya aureta sonake ka hakura da Nadeera gabaki daya, dan tunanin matar wani kadai karama zunubi yake, take Fateema as compensation, babu xancen taima kadan ko kaimata tsufa, yo nima ina yar wata nake aure amaryata ita she's 22 ma, gatanan kaje ka shirya nabaka, u need a woman, Dr yafadamana matsalan ka, kana bukatan aure, u are morethan a friend to me, kadawo jini na, I can do anything for you sabida nasan kokai waye, kome yafaru nasan kaddara ne because deep down u are good, very good kind hearted man, ka tuna abinda kama mahaifiyata kafin tarasu you paid for her surgery ka kaimin ita makk..." da sauri shima Abba yarufe mai baki hawaye yacika idanunshi sosai yace "friend thank you, am speechless banmasan mezan cemaba, banda kaman ka, amma anya zan amshi auren nan kuwa munma yarinyar nan adalci kuwa jibeni fa sa'an ubanta" ya nuna kanshi, dan dariya kwamissiona yayi yace "ai kafini yarinta, kafini kama ma da yaro, haihuwan kafa biyu kacal a duniya niko yanzu yarana goma sha daya idan kahada da dayan da yar Shila ta haifamin, kata kata da hada hadan yara dukya maidani tsoho kaikofa kalleka kaman wan Muhsin" da sauri Abba ya washe baki yace "Allah nawan? Kodai ba'a kakemin yanzu nai kama da saurayi dan talatin?" "sosai ma, jibifa dan gumunka mai kyau dayan Fulani mugama kaman furfura guda biyar gareka" washe baki Abba yayi sosai yana wani irin shafa gemunshi yana bubbuga kafa yana murmushi, murmushi shima kwamissiona yayi smile din dayagani akan fuskarshi saiyaji hankalin shi ya kwanta ahankali yace "yanzu sauko muci abinci kasha magani ka da Dr yabaka, ka kwantar da hankalin ka, yaranka su Muhsin zamusan yanda zamuyi mu nemo maka su ka roki gafaran su dana mahaifiyar su ku daidai ta komi yay daidai duk ahadu adawo daya" hawaye Abba ya share da sauri dayaji yana neman zubomai yace "thank you friend" zama sukayi sukaci abincin Abba is happy koba komi zaiyi aure amma duk second sai ranshi yay flashing a Nadeera, sai bayan Isha kwamissiona yakara turomai fateema ta tattara kwanukan dasukaci abincin dare sai kallonta yake tana sanye da doguwan rigan atampa kanta daure da dankwali, doguwa ce gata fara saidai princess tadan fita kiba sosai dan ita bada da kiba but she's booby, harta fita binta yake da kallo kafin ya sauke ajiyan zuciya not knowing what exactly yake feeling, shigowa kwamissiona yayi suka fita ya maidashi gida yacemai yafara shiri ran jumma'at bayan sallan jumma'at za'a daura auren.
_Bayan yadawo gida_
kwamissiona yakira Phaty falonshi, a natse cike da lallamin d'a yamata bayani ya lallabata amatsayinshi na mahaifinta, Phaty dama yarinya ce mai hakuri, ga biyayya da bin iyayenta ba, kuma ko a school dama bata kula samari hakan yasa batama mahaifinta musu ba, dudda tai abun yamata wani irin wired a kunne cewa ita da tsoho but bazata taba iya yima Abban ta musu ba, dan tun suna yara Abba yasha basu labari yanda abokin nashi ya taimakeshi a rayuwa, ya kula da mahifiyar shi kakansu kafin tarasu, shiya kaita hajji, hakan yasa ta amince, tace shikenan ta yarda, bakaramin addu'a kwamissiona yamata wanda saida tai kuka sabida tsananin farin ciki yanda mahaifinta ke mata addu'a, nan yama maman su uwargidan shi bayani yabada makudan kudi yace gashi tayi abinda yakamata nan aka fara gyaran amarya faty amaryan Abba, koda ranta yabijiro mata da tsoho zata aura saita cema kanta babanta takemawa biyayya and Allah yabata lada ta dage sosai tana addu'a tana tashi sallan dare. Ko akwatinan ta daga kasan waje Abba yay order aka hada mishi komi ubansu kaya saiti 12,yabama Adamu driver da matayenshi suka kai gidansu.
Da kyar kwamissiona yasamu yasami Muhsin awaya gaisuwa sukai na mutunci cike da girmamawa yama Muhsin bayanin komi da condition baban nasu, sanan ya rokan ma Abba gafara a wurin Muhsin yace bakomi Allah sanya alheri sanan yahada Abba da Muhsin din, sosai Abba ya shiga yima Muhsin kuka awaya duk yanda Muhsin yakejin haushin shi saida zuciyarshi ta karaya, yasan deep down mahaifinshi mutumin kirkine, sanan komi mukaddari ne, and ance tsakanin d'a da iyaye sai Allah kasa jurewa yayi yace "Abba please kadena kuka is okay nayafe ma okay" kasa gasgata abinda Abba yaji yayi ahankali yace "please stop crying don't worry zanzo jibi before d wedding, Allah ya yafemana gabaki daya I really miss my Abba too, I love you so much Abba na" da sauri Abba yace "I love you too my Muhsin, Ya Mumy ku, ina Ahmadudu?" ahankali yace "Mum na gida gani ga Ahmad gashinan" yabama Ahmad da da kyar ya karbi wayan da kyar Abba ya shawo kanshi da kyar Ahmad ya yafemai yacemai insun kai gida sukirashi yayi magana da maman su, sukai sallama dukansu dadi sukaji ganin Allah ya amshi addu'an su Abban su ya shiryu yay nadama. Koda sukakai Mum kin yarda tayi su kira Abba but she's happy yanda suka shirya ya nemi yafiyan su.
Ranan Thursday suka dira a Nigeria, Abba yakusa Suman dadi, jiyayi kaman zai mutu rungumesu yayi, his children are his life, yanda yake musu kuka yasa su suka shiga lallashin shi suka tafi gida da kanshi ya shiga gyara musu gadonsu a shashin su yana wani irin farin ciki, tashi sukayi suka hadu sukai aikin tare inka gansu gwanin ban sha'awa that's family. Mukasance masu yafiya da manta baya, wayansu abun suna faruwa ne dan akoyi darasi, wasu abubuwan suna faruwa ne dan Allah ya bayyana wani al'amari, wani abin kuma zallan kaddara ne kawai. Ranan atare dasu Abba ya kwana a shashin su dan sunce gobe da karfe daya nadare zasu koma kasancewan duk sun sami aiki a Canadan a chan suke aiki.
_Friday_
Bayan sallan juma'a aka daura aure Abba da Fateema akan sadaki dubu Dari biyu inda Muhsin ne yabiya mai kudin sadakin, murmushi Abba yadingayi ganin yaran sun manta da komi bamasa son yana musu maganan, komi yariga yafaru hakane rayuwan dan Mum tana matanshi dama ba dole bane zata zama matarshi har karshen rayuwa ba cewan Ahmad ajiya da daddare, da kanshi ya kaisu airport da daddare suka wuce kaman zaiyi kuka.
Sosai Fateema tasha fada wajen iyayenta, dakuma addu'a dasuka mata nayi musu biyaya inda nan ake sanar da ita ranan Sunday zata koma gidan ta a kano sabida school, ana watsewa mum tahada mata wani ruwan magani taje tayo wanka tadawo tai salla tai bacci abinta.
_Ran Sunday_
Karfe takwas tama Abba a gidan inda Adamu yatukoshi acikin bakar jeep dinshi, bakaramin kyau yayiba yasanya farin shadda gizna sai kamshi yake hade da malum malum yay kyau bana wasaba, kasa shiga gidan yayi ya kira kwamissiona ya sanar dashi yana cikin mota, murmushi kwamissiona yayi yace "malam saifa ka shigo namaka wa'azi ni yanzu sirikin kane" dan dariya Abba yayi irinta manya yace "haba mana friend am shy can't come in" daidai lokacin ya hango kwamissiona na fitowa rike da waya a kunenshi yana murmushi yana kallonshi, murmushi ma Abban yayi yabude kofan bayan yafito musabaha yayi kwamissiona yace "karfe nawane flight din naku to kano?" "agogo Abba ya kalla yace "10:55" "gashi yanzu to 9 bari na shiga nakawo maka matarka karkiyi missing flight" adan kunyace Abba yadan juyar dakai, dariya sosai kwamissiona yayi yay cikin gidan dakin matarshi ya shiga inda Fateema ke zaune an shiryata cikin wani hadadden bakin doguwan riga an mata makeup tai kyau sosai idanunta sun kumbura alamun taci kuka zama kusa da ita kwamissiona yayi ya rumgumota, fadawa jikinshi tayi sosai tafashe da kuka Ahankali yake shafa bayanta yana murmushi yace "duk yaron dayama iyayen shi biyayya baya tabewa, Alhaji Naseer mutum ne mai kirki nagari nakuma tabbata zai rikemin ke amana, kaman yarda ya haifa, nazaban miki shine sabida nasan waye shi, nakuma San tarbiyan dana baki, ki zauna da mijinki lafiya kinji fateema, kimai biyayya kome yakeso ki mishi ki tarairayi mijinki kisani aljannar ki na karka shin kafarshi, yanda kikamin biyayya kikaji magana ta batare da kinyi gardamaba, yanda kika farantamin dinan fateema ubangiji Allah ya faranta miki haka ranan gobe kiyama" fashewa tayi da kuka tanajin dadi taga babanta namata addu'a haka, ahankali yama forehead dinta kiss yace "Allah yamiki albarka ki dage da karatu kinji ki kare mutuncin auren ki banda magana da mazan school, oya tashi muje naraka ki zaku tafi Kanon" dagota yayi daga jikinshi, mamansu kuma da kanwata da amaryan kwamissiona suka saka mata wani hadadden alkyabba kwamissiona yadau wani bangles din gold yakamo hanunta ahankali ya saka mata su guda hudu yana goge mata hawayen datake yi kafin yakara kissing forehead dinta yarike mata hannu ya kalli su Maman su yace "afito mata da jakan makarantan ta inda books dinta suke" yarike ta yafita daga dakin har zuwa tsakar gida kafeta da ido Abba yayi bayako kyaftawa dudda baya iya hango fuskarta sabida alkyabban but bakaramin kyau tamai ba gani yayi kaman princess ake tahomai da ita sosai heart dinshi ke beating fast fast har suka karaso wajen murmushi Abba yayi yana kallon kwamissiona a kunyace, ahankali kwamissiona yakamo hanun Abba sanan yakamo hanun Fateema yasaka ana Abba da sauri Abba yarike hanun gam ahankali kwamissiona yace "gatanan, ga matarka nan friend Allah baku zaman lpy, and fateema kibi mijinki kinji Allah baku zaman lpy" bude musu bayan motan yayi yace "ku shiga" ahankali Abba yafara shigar da ita kafin shima ya shiga daidai lokacin kuma aka fito da trolley ta da books dinta ke ciki kasancewa akwatunan ta da kayan dakin anriga anje and jerasu a Kanon sawa akai a booth, Adamu ya kunna motar yaja Abba na dagama kwamissiona hannu har sukabar gidan dan juyo dakai yayi yadan saci kallonta ganin yanda take kuka sosai amma mara kara yasa yaji duk ba dadi, ahankali yakamo hanunta yasa acikin nashi yarike gam yanadan matsawa batare dayay magana ba ahaka har sukakai airport din suka shiga jirgi tana kusa dashi har lokacin kanta akasa har jirgin yadaga kuka take mara kara, ahankali ya daura hannunshi kan nata data ijiye akan cinyanta dayasha lalle ya shiga shafa bayan hanun ahankali murya chan kasa yace "am sorry My Fateema Zarah, nine namiki laifi" da sauri ta girgiza mai kai, shiru yayi yana kallonta kafin yarike hanunta kam yakamo kanta ahankali yadaura kan kafadarshi yana shafa bayanta, lamo tayi a tsorace tana numfashi fast fast ahaka har jirginsu ya sauka suka fito yana rike da ita kaman yasami yar jaririya suka shiga wani babban jeep driver yajasu har zuwa GRA, wani babban gida suka shiga akai parking a big compound ahankali Abba yace "munzo gidanmu My Zarah" bude kofa yayi yafito yafito da ita yana rike da hanunta yafito da ita har lokacin kanta n kasa cikin hulan alkyabban yay cikin gidan da ita hakanan yakejin wani irin farin ciki kodan auren dayayi ne oho komadai me Alhamdulillah, hadadde ne gidan duplex dudda ya hana kwamissiona yin komi amma saida ya zuba mata hadadaddun furnitures upstairs sukayi inda akwai dakuna hudu amma yakaita wani babban daki dan ko kadan bayason yakara gwada rayuwan dayay da mumy dan yaga side effects dinshi first thing first no more raba daki, da dayake da dakinshi na mum ma daban duk yanadaga cikin abubuwan dake jawo matsala so no more yanzu, dakinshi daya da matanshi bazai kara raba daki da mataba, dakin ya shigar da ita hadadden dakine mai makeken gado, zaunar da ita yayi abakin gadon ahankali ya tsugunna agabanta yasa hannu ya yaye hulan alkyabbanta yana wani irin kallonta dan bakaramin kyau makeup din da aka mata yayi mataba, runtse idonta tayi gam hawaye na gangaro mata gabaki daya tsoro ma takeji dukta takure, ahankali yakira sunanta "My Zarah" bude idanunta tayi a tsorace ta kalleshi hawaye na zuba, murmushi yamata yakai hannu ya share hawayen yace "please kidena kuka okay" gyadamai kai tayi hakan yasa yamike ya zauna a gefenta yasa hannu ya kwanto da ita jikinshi ya rungumeta sosai yana shafa bayanta ya chusa hancinshi a wuyanta.
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *masu fitarmin da novel kuda Allah*
*karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi*
*3107021073 first bank aisha Muhammad zaki turo 300 access fee saiki turo evidence ta watsapp number na 07012181461, you can also send MTN card ta watsapp number na kaman haka 07012181461*
_BOYAYYEN MUTUN_
*A23*
Yana shakkan wani irin kamshi mai dadi datake yi, sosai jikinta ya shiga rawa hakan yasa yasaketa ahankali ya sanya hanunshi akan kafadarta ya warware daurin alkyabban ta gaba ya cire ya janyeshi daga jikinta yana wani irin kallonta wani irin abu na fizganshi ahankali ya mikar da ita tsaye yay pointing kofan bathroom yace "jeki dauro alwala kizo Zarah" gyadamai kai tayi tawuce yabi bayanta da kallo bata wani jimaba tafito daga bayin kana ganinta kasan duk afirgice take, murmushi yamata dan bayason ya takura ta yafison tasaki dashi yatashi yaje ya dauro nashi alwalan sanan yafito ya tsaya gaban wardrobe yabude dayake an jera mata kaya yaciro mata hijabi yadawo gabanta ya tsaya ya warware ya Sakamata yana murmushi yace "yauwa Zarah na, oya tashi muyi salla kaman yanda annabin mu ya koyar ko?" tashi tayi yajasu nafila raka'a biyu kafin ya juyo ya kama goshinta yay addu'a sanan ya matso kusa da ita nishi tafara da sauri da sauri tana kallonshi ahankali ya kama hanunta yanata shafa lallen da aka mata batare daya kalleta ba yana kallon lallen yace "waya miki wanan lallen zarah na?" adan tsorace tana kokarin danne kukan datake ji tace "maryam me la...lle" dagokai yayi ya kafeta da ido jin yanda muryanta ke rawa, kafeta da ido yayi yana mata kallon kurulla dan baitaba kallo hakaba, da sauri ta saukar da kanta kasa, kakkyawa ce itama masha Allah gatada dogon hanci ga manyan idanu, ga pink lips dinta kaman na princess, lips din ya kafe da ido kafin ahankali ya mika hanunshi ya daura akan lips din yana shafawa ya hadiye wani abu murya chan kasan makoshi yakirata. "Zarah look at me please yar kirki" dago kanta tayi da idanunta dasuka cika da hawaye sosai ta kalleshi ahankali yajawota jikinshi ya rungumeta ajikinshi ya lumshe ido murya chan yace "karfe nawa ne lectures dinki gobe?" "t..ten" tafada bakinta narawa, dan shafo bayanta yayi kaman wanda ya rungume jaririya yace "Ok banda magana da maza kinji" gyadamai kai tayi da sauri gabanta na faduwa kamshin dayakeyi na shiga hancinta sosai ahankali yakara tausasa voice dinshi yace "kidena jin tsoro na ki saki jikinki dani am your best friend, your life companion, abokin ki, your hubby kinji Zarah na" gyadamai kai tayi yay murmushi yace "yauwa dats good, yanzu tell me mezakici namana order" murya chan kasa dake rawa tace "z..zan..zanyi girki" da sauri Abba ya dagota yadan harareta ya lakaci hancinta yace "kin taba ganin inda amarya ta shiga Kitchen Zarah?" girgiza mai kai tayi tana wasa da yatsa, wuyanta yabi da kallo zuwa kirjinta yace "bari naje na aika daganan zan wuce mosque sallan zuhur feel free ok" gyadamai kai tayi ahankali ya kama habarta da sauri ta kallai murmushi ya sakin mata yama forehead dinta kiss kafin yay shiru ya tsaya yana kallon yanda jikinta ke rawa dagowa yay yana kallonta murmushi yamata yace "natafi" gyadamai kai tayi batare data bari sun hada idoba yajuya yafita wani irin farin ciki na lullube shi. Fashewa tayi da kuka da kyar ta lallaba kanta ta tashi taje bayi tai wanka a gurguje tafito ta shirya cikin wani riga da skirt na atampa daya mata kyau sosai tahau kan dadduma tai sallan azahar sanan ta linke takoma gefe ta zauna batare data cire hijabin ba, dan kawai tasaki jiki yasa Abba bai dawo gidan ba yabama gateman take away yakai mata yazo yay knocking yana kwala sallama tafito ta amsa bai sake dawowa gidan ba sai bayan sallan Isha wuraren tara da rabi, Kulle kofan falon yayi ya shigo rike dawani manya manyan ledojin kaji biyu dan yabama mai gadi na ukun yafara hawa stairs, ahankali yabude kofan dakin da sallama wani kamshi mai dadi ya budemai hanci, zaune yaganta kan dadduma sanye da hijabi tana bacci ta jingina da gado bamataji shigowan shiba dan baccin ya shigeta shigowa yay dakin ya maida kofan yarife ahankali ya shigo ya tsaya chak yana kallonta yanda take baccin kaman