Showing 45001 words to 48000 words out of 150731 words
hakan yasa ta dago kai ta kalleshi dauke kai yayi yawuce ciki yana kallon kofan dakin Nadeera kaman ya bude ya ganta haka yakeji, bude kofar dakinshi yayi ya shiga yay bedroom dinshi direct kafin ya shiga bayi ya sakinma kanshi ruwa ya mikar da hannayen shi ya dafa bango yana tunani, ko duka duniyan nan ya mallaka zai iya bayarwa inhar zaigano inda princess take d biggest problem in trying to track down her location according to abinda commissioner yace is because bata tare da waya da an iya anyi tracking down location dinta sharp sharp, gashi bai samu yaga inda koda hanyar gidansu ba balle yabada any clue dazaisa agano inda take easily, inda ace yasan sace princess wanan mugun zaiyi daya shanye koma me yake damun shi aranan yahakura, gashinan duk binta dinan dayayi ne yaja wani banza chan ya aureta, runtse ido yayi da karfi ya daki bango yana cikin zafin rai yana fata dakuma rokon Allah akan karya bashi daman tabamai princess harsai angano inda take tadawo gida araba dan iskan aurenta dayayi. Yabata kusan one hour abayi tunanin yanda zaiga princess yake sanan ya kashe shower yabude kofa yafito daga bayin Mum yagani zaune abakin gado hakan yasa ya dauke kai yay gaban wardrobe wani goggagen shadda gizna brown ya ciro ya shiga sakawa ahankali Mum tace "a ina ka kwana jiya Alhaji?" ko kallonta baiyiba saima karasa zira riganshi yayi yay gaban madubi yadau mai yana shafawa tasowa tayi tazo wajen tana binshi da kallo tace "ina kaje Alhaji, a ina ka kwana?" ko kallonta baiyiba danji yayi yanxu koson ganinta bayayi daukan turaren shi mai shegen dadi yayi zai fesa Mum ta fizge cikin fushi ta jefar akasa yafashe tace "nizaka maida mahaukaciya nace ina kaje?" wani irin mugun kallo yamata kafin yay controlling kanshi yace "naje neman abin sona, yata Nadeera, my princess, the apple of my eye, My love" cikin wani irin kunan rai Mum tace "Alhaji wai dan Allah lafiyan ka lau kuwa kokuma you are posses ne nakira malamai ama ruqiya, this isn't you" wani kallon rainin wayo yamata kafin ya dauko wani sabon turare zai fesa takara fizgewa cikin kunan rai tace "Alhaji talk to me wai menama ne? Dan Allah kabar wanan wasan dakake min i know you are joking ko dakace zaka auri Nadeera, nasan nama laifuffuka da dama, jiya nakasa bacci tunanin abubuwan danake ma nayi and nai concluding maybe zakai punishing dina ne you want me to realize my mistakes shine kake cewa u wanna marry princess, Alhaji yanzu kamin bayanin auren dakace kamata da gangster din dakace musan yanda zamuyi mu kwatota because i know wasa kakemin da xancen sonta kake xaka aureta ko Alhajina?" wani irin kallo yamata from head to toe kafin yaja tsaki yace "ina ganin too much business da tafiye tafiye yafara affecting yanda kike tunani ko Hajara, now bari namiki bayani daki daki kiji ki fahimta, zauna kiga" ya wani irin ingiza Mum kan gado ta zauna ya tsaya agabanta ya nuna kanshi yace "ni dai ni dinan uban yayan ki Muhsin da Ahmadu Alhaji Naseer Aluminum Son yarmu Nadeera nake, dazaran an ganta kinajina? Zan shigar da kara kotu zan raba auren inje masallaci a aura mini ita mubar muku kasar Spain zamu, jibi Hajara inama Princess so dakoke dakina budurwa ban miki irinshi ba, ke ina gaya miki princess yar baiwa ce, wato Allah yay hallita ne awurin nan, tafimini ke sau miliyan kan miliyan, Allah yay kira, yay zubi awajen nan, yatace idan na aureta sai yanda nayi da ita dama gata dajin magana very innocent girl wlh ba irinki ba dakika nunama duniya kinfi karfina, bari kiji kin riga kin shani na warke raras, auren Princess zanyi ke bakiga yanda muka dace bane jibifa sunayen mu Naseer da Nadeera wayyo Allah na" yay maganan yana wani irin shafa kirji yana kallon sama yana wani irin murmushi daya bayyana fine set of teeth dinshi, salati kawai Mum take aranta dan gani take kaman tabin hankali Abba yasamu, kallonshi tayi tace "Alhajina kodai tsufa ne yafara kamaka muje asibiti ne?" wani irin ihu Abba yamata kaman zai daketa yace "ni kike cema tsoho? Kibari mufara aure nida princess ta haifamin twins kafin kice nai tsufa, kinma tunamin lemme call commissioner yace dama nabashi yau da gobe lemme call him inji how far about princess dina, in sha Allah sai an ganta in sha Allahu saikinga aurena da princess, banyi baccin dareba jiya Allah naketa kaima kukana da yardan ubangijin al'arshi princess zata bayyana zakiga aurena da Princess hajara, agaban ki direba sai tuka mota yakaimu airport mu barmuku garin, nama mata order Lamborghini duk randa tadawo shi zan bata as gift i really really miss my baby girl" cikin Wani irin mugun kishi da gushewan tunani Mum tace "in sha Allah, da yardan Allah baza aganta ba, indai niyyarka kenan da yardan ubangiji bazaka sake saka princess a idanun nan nakaba in sha Allah kagama ganin Princess aduniyan n..." wani irin mugun mari Abba ya dauke ta dashi dayasa tasaki wani irin wawan ihu dan ya mugun shiganta, Muhsin da Ahmad dasuka shigo dan gaida Mum sukaji ihun ta shigowa dakin sukayi da gudu, tsayawa sukayi suna kallon Mum data dafe kuncin ta tana kuka sosai tana kallon Abba, ga Abba tsaye akanta yana huci kaman zaki yana ganin su ya nunasu da yatsa kafin ya nuna Mum yace "kuma maman ku magana tafita daga idona, ta kiyaye ni inhar tanason aurenta and you Muhsin" yanuna Muhsin da idanunshi sukai jajir yana sanye da black suit hanunshi rike da necktie yace "yes, yes, yes, I know kunsan komi by now kunga komi kunga komi ta CCTV footage, dat is why kuka tsaneni haka ko gaisuwa bani samu daga wurin ku kuma nagode da hakan bakomi yasani aikata hakan ba uwarku ce tajamin ita tajefani halaka amma yanzu nasan maganin matsalata, Muhsin start with divorce proceedings wanan dan daban daya dauke Nadeera shiyasa akazo har gida shekaran jiya aka daukeni yasa nabashi aure Nadeera aka daura auren akan sadaki 200k, yanzu kwamisona yace nabashi yau da gobe Nadeera zata fito, once sun ganota tadawo gida zamu maka dan shegiyan dan ta'addan a kotu mu raba auren nasu na aureta, kufada ma mahaifiyar ku tun wuri tai karatun ta natsu dan wlh aurena da princess babu fashi, and duk randa tasake maganan banza akan Princess dita wlh abakin aurenta, i can fight the whole world for my babygirl inhar war ne am ready kota gabas kota kudu kota yamma kota arewa zanyi fighting, me and my princess mutu karaba takalmin chicken" kuri Muhsin yayi yana kallon mahaifin nashi tun yana gane meyake cewa haryaji zuciyarshi ta tsaya chak ko kadan baya ganin kowa sai duhu, daga Abba dake ta bambamim bala'i dabayaji yanadai ganin bakinshi na motsi sai Mum dake zaune kan gado da Ahmad dake kallon Abba yanaji kaman ya tsireshi basu lura da Muhsin ba kawai karan fadin abu sukaji da sauri kowananesu ya kalli inda yaji karan atare dukan su sukace "Muhsin" gabaki daya idanunshi sun kafe yana kallon sama baya numfashi ko digi.
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *inkin karanta baki biyaba keda Allah*
*Maman Abd Shakur*
*22 Years Ago*!!
_Egypt Cairo_
*AO*
Wata matace data dan manyanta fara haka tana sanye da doguwan riga baka har kasa tana gudu sosai kana ganinta kaga balarabiya da tsohon ciki agabanta haihuwa yau ko gobe, tana gudu agalabaice dan batada ragowan karfi gefenta kuma wani farin yarone balarabe dabazai wuce 12 years ba yana goye da wani namiji abayanshi da bazai wuce 6 years ba, yarike hanun wanda bazai wuce 8years ba duk suna gudu suna waigen baya, baya mai cikin tayi zata fadi agalabaice hakan yasa babban cikin yaran yay ihu yace "Umm" ya saki wanda ya rike yataro ta da sauri amma harta sume hakan yasa ya saukar dana bayanshi daya fashe da kuka kasa cikin harshen larabci ya kalli dan kimanin shekara takwas dake gefenshi yace "yi wasa da Abdallah" cikin kuka ya daga Abdallah dake kallon maman nasu yana jijjigashi yana wasa da hanunshi shikuma babban ya shimfidar da maman tasu da kyar akasa dajin wajen idanunshi sunyi jajir ya janye dan handbag din hanun maman tasu ya bude dan goran ruwa yaciro yabude da sauri ya yayyafa mata a fuska hakan yasa ta farfado dawani irin azababben ciwon mara da ciwon baya sosai, wani irin nishin azaba tayi tana cije baki ta kama hanun yaron tarike gam tana numfashi, arude cikin harshen larabci yaron yace "Umm menene, meke miki ciwo?" kasa magana tayi saima juyawa idanunta suka fara tanaso takara suma, da sauri wanda ke rike da Abdallah ya zo wajen ya tsugunna shima yana share hawaye ya dafa babban yana kallon maman tasu data rufe idanu cikin kuka sosai yace "meke damun Momma Ya Marwan?" rungumeshi yayi tareda karban Abdallah dake kuka sosai yana sharemai hawaye ya kwantar da Abdallah a jikinshi yana sharema Omari hawaye shima, girgiza mai kai yayi cikin murya datai rauni sosai yace "don't cry" gyadamai kai Omari yayi sanan ya sakeshi, sake yayyafa ma Maman nasu ruwa yay a fuska hakan yasa ta bude ido wani irin nishi tayi tai juyi cikin azaba sukaga jini nabin kafanta takara yin kara takara sumewa, kiran sunanta sukayi amma shiru hakan yasa ya mike tsaye, goya Abdallah yayi abaya ya kalli Omari yace "stay with Umm lemme call help" da gudu yajuya yafara bin dajin nan yana gudu da Abdallah dake kuka abayanshi yay kusan gudun 8min sanan yakai bakin titi duk wacce yagani saiya tsayar da ita yace dan Allah ataimaka musu maman su zata haihu amma ba'a kulashi ba, da kyar yasamu wata yar tsohuwa dattijuwar balarabiya ta tsaya itama dan yanda taga Abdallah na kukane ga wannashi yay zuru zuru saisa suka bata tausayi tambayarshi tayi menene yace mata maman su nada ciki jini nabin kafarta kuma sai suma take, shiru tsohuwan tayi saikuma tace nakuda ce su kaita asibiti, cikin tsananin tashin hankali yace tayakuri basu da kudin kaita asibitin ne da kyar tsohuwan ta yarda ta biyoshi masifa ma tadinga mai ahanyar dajin wai wajen yay nisa kodai yan cinkai ne, rantse rantsr ya dinga mata kafin da kyar ta yarda tabisu koda suka kai sun tarar Omari na kuka sosai Maman tasu asume jini yay mala mala akasan wajen, daga Omari yayi yana sharemai hawaye ya rungume shi yana kallon maman tasu dake nan kaman mara rai, Tsugunnawa tsohuwar tayi akanta tace "subhannallah metayi ta galabaita haka jini ya tsinke mata?" ahankali yace "gudu mukayi" girgiza kai tayi tace "assha ku matsa daga tachan inga mezan iya mata Allah bani sa'a" jan hanun Omari yayi yana rike da Abdallah suka koma chan daga dan nesa basa ganin su, rungume Abdallah yayi yana bubbuga bayanshi danyay bacci shikuma Omari ya daura kanshi akan kafadarshi ya rikeshi duk sunyi zuru zuru gawata uwar yunwa dake cinsu tun asuba suke gudu gashi har yamma tayi da kyar Abdallah yay bacci dan yunwa yakeji, sunkai kusan awa uku zaune sanan matan tazo inda suke rike da dan kwalin Maman su tana share hanunta dake da jini sosai idanunta sunyi wani iri tace "kuzo Maman ku na kiran ku" da sauri Omari ya mike tsaye shima tashi yayi rike da Abdallah dayay bacci gabanshi na faduwa sosai yarike kanin nashi sukai wajen, akwance sukaga Maman nasu inda suka barta ga jaririyan data haifa acikin wani mayafin ta baki an nannadeta, dago kai maman nasu tayi da kyar ta kallesu da gudu Omari na kuka ya tsugunna agabanta ya daura kanshi akan hanunta yana kuka, murmushi tayi ta shafa kanshi kafin ta daga hanunta ahankali ta mikama Marwan dake tsaye goye da Abdallah dake bacci abaya, ahankali yataka kafa yawani irin tsugunna agabanta idanunshi sunyi ja yana kallon fuskar Maman tasu yanda tai fari sosai tai wani irin haske kaman mara jini, dago jaririyan tayi ta mikamai hakan yasa ya sauko da Abdallah ya mikama Omari shi ya karbi yarinyan yana kallon fuskanta very cute baby girl ga gashi kanta bakin kirin har goshi tana bacci, dayan hanunshi ta kama hakan yasa ya kalleta ahankali ta mikama Omari hannu hakan yasa ya riketa shima yana kallonta cikin kuka murmushi tamusu da kyar cikin harshen larabci tace "Marwan" dago kai yayi ya kalleta yama kasa magana tsabagen yanda yakeji ahankali tace "ga sister kunan nasa mata suna Rahma da babban ku kafin ya rasu yace inhar nahaifi mace sunan dazamu samata kenan, Marwan ka kula da kaninka kaji, duk runtsi duk wahala karka sake ka rabu dasu ko ka nisan cesu, Omari" takira sunanshi tana kallon fuskarshi asanyaye, daga mata kai yayi cikin kuka yakasa magana, ahankali tace "kubi yayan ku kaji, kome yace shizakuyi, karku saba mai ko sau daya, kuhada kanku kuso junanku, farin cikin dayan ku ya zamto na dukan ku, bakin cikin dayan ku ya zamto na dukan ku, karku sake ku koma gida dan zasu kashe ku kaman yanda suka kashe mahaifin ku, Marwan" takira shi ahankali tanadan nishi, cikin wani irin raunanniyar murya yace "Umm" ahankali ta daga hanunta dake rawa ta mika zata daura akan kan jaririyan dake hanunshi takasa sabida yanda hanunta ke rawa hakan yasa ya kamo hanunta ya daura akan yarinya murmushi tayi wasu hawaye suka gangaro ta gefen idanunta da kyar ta iya magana tace "ina so bayan na rasu kutafi motherless home achan za'a kula daku zasu tayaku rainon Rahma kanajina" gyada mata kai yayi daidai lokacin Abdallah yatashi da kuka sauka yayi daga jikin Omari yafada jikin maman tasu yace "Momma are you sick?" cikin kuka, rungumeshi tayi sosai tafashe da kuka sosai danya karya mata zuciya, hannu tamikama Omari dake kuka shima harda majina yafada jikinta ta rungume su biyu tana lallashin su tana kallon Marwan da idanunshi sukai jajir yana kallonsu, dagasu tayi ta kalli Marwan tana murmushi takamo hanunshi da kyar hawaye nafita ta gefen idanunta tace "my strong brave boy, the only Man damuke dashi, haka nakeson ka da jarumta, karkai kuka okay dan aduniyan nan kaikadai ne gatan kaninka, inaso ka rage zuciyan nan naka, wanan hot temper dinan ka rageshi kaji Marwan, ga kanwarku nan ka kulanmin da ita, mace ce ka tsaremin ita ka kare mutuncin ta, katuna abinda Abban ku yafada akan idan har mace na haifa? Gyada mata kai yayi ahankali, tai murmushi tace "Masha Allah, karka manta da hakan, Omari karku manta kota girma bata yardaba ku fada mata abinda iyayenta sukace ce kuma suke so, inaso ku kula da junanku kuso junan ku, ku hada kanku ku dawo daya, karku sake ku raba kanku, ku tuna kuku dinan kune ku, kuna gatan kanku, Allah ya muku albarka ya tsaremin ku, ya karemin ku, ya kulanmin da ku, i love you so much yarana" sosai Abdallah da Omari ke kuka ahankali ta zare hanunta daga kan macen idanunta na kukkulewa ta mika hanunta tanaso ta shafa kan Abdallah wani irin jini ya balle mata paaa da sauri tsohuwar da matsar dasu Abdallah tana salati ta tsugunna tana cema Marwan ya matsa tashi tsaye yayi yana kallon maman nasu rike da jaririyan su Omari da Abdallah suka wani irin rungumeshi suna kuka sosai suna kallon maman nasu da jikinta ke rawa, kafe maman nasu yayi da ido ko kyaftawa bayayi tun yana ganin alamun numfashi ajikinta har yadena gani ya lumshe ido zuciyarshi na wani irin rawa ya tsugunna ahankali ya kankame kaninshi yana sauke ajiyan zuciya da sauri da sauri, mayafinta tsohuwar ta cire ta lullube ta tajuyo ta kalli yaran dataji sun bata tausayi sosai tace "bari naje nakira jama'a amata sutura" fita tayi tabarsu awajen daidai lokacin jaririyan ta tsala ihu tashi yayi ya shiga jijjigata yana kallon fuskarta sai ihu takeyi gasu Omari na kuka suma hakan yasa ya sakamata yatsarshi abaki ta dinga tsotsa tana bacci hawaye yacika idanunshi ahaka bacci yasake dauke ta gaba daya ya zare yatsar yasake rungumeta yana kallon gawan Umm dake lullube.
Ba'a wani jimaba tsohuwar tadawo da mutane kusan 20 mata da maza da jarkokin ruwa a hannun su nan dai aka kebance wajen mata suka mata wanka ana gamawa aka shiryata suka sallaceta aka kaita makwancinta Abdallah Omari sai kuka suke yana lallashin su, tsohuwar da mutanen ne suka tasasu agaba suna tambaya basu da yan uwa da kyar ya iya girgiza kai yace "basu dashi kuma baban su yarasu" hakan yasa tsohuwan tace to azo aje akaisu motherless home kaman yanda mahaifiyar su tafada kodan wanan jaririyan nan akula da ita achan, cikin mutanen wani dayazo da machine ya kwashe su aka kaisu motherless home din dake garin nan fa aka karbesu ga yara da dama agidan, aka karbi jaririyan da ya yarda ya bayar da kyar aka mata wanka aka bata madara aka saka mata kaya za'a kwantar da ita akan gadon jarirai ya karbeta ya rungumeta tsam hakan yasa suka barshi da ita, Abdallah dake zazzabi sosai aka bashi magani aka basu abinci sukaci banda shi daketa kallon yarinyar su Omari na gamawa sukai bacci akan gadajen su shiko yana zaune da jaririyan yana kallonta yanda take bacci abinta.
Ahaka rayuwan tacigaba ana kula dasu sosai a motherless home din, ma'aikatan wajen nada kirki har an sansu dan kullun tare zaka gansu su uku wuri daya babbban yadau jaririyan da ayanzu har yama iya mata wanka yaro dan 12 years yanama jaririya wanka yabata abinci ya shiryata yariketa, basa wasa da sauran yaran koda yaushe suna tare a manne suna jikin wansu.
Jaririyan na kimanin wata biyu wata rana suna zaune a compound din motherless home din suna zaune a simenti a karkashin bishiya yana rike da Rahma da idanunshi biyu tana rike da yatsarshi gam tana kallon sama, Abdallah yay bacci ya daura kanshi akafarshi shikuma Omari ya jingina da bayanshi yana wasa da duwatsu yaga an bude gate din gidan wasu manyan motoci hudu sun shigo an rufe gate din, wacce ake kira da Ameera dake in charge of the motherless