Showing 144001 words to 147000 words out of 150731 words

Chapter 49 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

805

Muhsin yabashi address din office dinshi sanan yawuce Ahmad yajasu sai gida.

Sosai suka tarairayan mahaifiyan su koda yaushe suna tare da ita hakan yasa taji sauki sosai ta warware tai lumu tai kyau kaman baitaba.
Ahankali wata irin cool warm soyayya ke shiga tsakanin Muhsin da Firdausi, Mum da Ahmad bakaramin dadi sukajiba.

Da kyar Dr Ali yasamu Muhsin da Ahmad suka yardan mai suka bashi daman zuwa ganin Mum dinsu dan yariga yanuna musu son Mum dinsu yake. Koda yatari Mum da zancen fir taki, tacemai ita tagama aure, kaman zaiyi kuka yace ta taimaka ta karbeshi tunda matarshi ta rasu baitaba ganin wacce yake tsananin so ba sai ita, yana bala'in sonta, kin amincewa Mum tayi daga bayama tashi tayi tabar falon tawuce dakinta tabarshi nan, yadade a zaune kafin yamike idanunshi sunyi ja yafice dan wani irin jarababben sonta Allah ya dauramai, a yanda su Muhsin suka ganshi yasa suka bashi hakuri yatafi.

Ahankali ahankali suke lallaba maman tasu suna nunamata mahimmancin auren, besides Dr na mugun sonta da kyar suka shawo kan Mum ta yarda nan akasa ranan aure sati biyu yay ma Mum kaya daidai karfinshi amma nagani nafada dan Mum ta fishi kudi nesa ba kusa ba, shikuma Dr ne kawai a asibiti yake aiki, ranan aka daura aure inda ya tare gidan Mum danta rokeshi alfarma ya barta agidanta. Zama suke da amana da tsantsan soyayya, sosai yakeson Mum, sanan yarike su Muhsin kaman yayanshi nan suka dawo one happy family.


**

_Eygpt_ .

Lips dinta dataji ana lashewa yasa ta bude ido ahankali ta saukesu akan Marwan dake sanye cikin wani fine white jallabiya, lumshe ido tayi da sauri hakan yasa yace "ki bude ido ki kalleni Sugarlips" yanda yafadi maganan ataushashe yasa ta bude ido ahankali ta kallai, murmushin shi mai kyau ya sakin mata yace "come and shower, I got something for you" yanda tai wani irin yaushi ko kadan batada karfi yasa yadan lakaci hancinta yace "are you tired?" dan turomai baki tayi hakan yasa yay murmushi yace "sorry Rahma na, nagajiyar dake ko?" yay maganan yana kamo hanunta yana rikewa, ahankali yakai hanun bakinshi yamusu kiss yana kallonta kafin ahankali murya chan kasa yace "Allah yamiki albarka Sugarlips, I love you so much" ahankali ta kama hanunshi tarike gam itama tana kallonshi, she just wanna cuddle him su zauna ahaka bataki har karshen rayuwaba, kiss tamai akan fararen hannayen shi kafin ta rungume hanun akirjinta tana kallonshi wani irin sonshi na shiganta, murya chan kasa irin na wacce ta mugun gajin nan tace "I love you too MaskMan" da sauri ya daura kanshi kan nata har tanajin saukan breath dinshi kan fuskanta, yana mata wani irin kallon so, ahankali yace "mekika ce?" wani irin murmushi tayi ta saukar da idanunta kasa chan kasan makoshin ta tace "I love you MaskMan" yakai kusan 1min yana kallonta kafin ahankali ya sakinma lips dinta wani irin lightkiss yana mata wani irin kallo yay sigh din relief sanan yace "am the happiest Man on earth yau, I love you so so much MaskMan wife" dan murmushi tayi ta kalleshi shima ita ya kalla ya kafe lips dinta da kallo ganin akwai alamun magana ahankali yace "talk to me Sugarlips" dan murmushi tayi tai wrapping legs dinta a back dinshi ta yanda ta kwanto kanta, tana kallon kwayan idanunshi tace "ina sonka Boyayyen Mutun" ahankali yawani irin fadawa gefenta ya dagata ya daurata akan jikinshi ya rungumeta sosai yana janyo filo yana daura kanshi yace "I was once BOYAYYEN MUTUN because of you wife, nai alot of things, cikinsu harda kwatoma wani balarabe diamonds dinshi dawani igbo man yay scamming dinshi ya kwace, i took d diamonds na kaimai he gave me alot of money nahada danawa na bude company mu anan eygpt while muna Nigeria my manager was here taking care handling the business, I was the maskman because of you Sugarlips, the first time we met.." yay shiru yana tunani yana wani irin kallonta, ahankali tace" the first time we met saida saida naje police station, I was so scared, nakasa mantaka, every every minute kake flashing mind dina, I never knew kaine zaka dawo savior dina, I never knew cewa we are related, I never knew..." da sauri yace "you never knew that wanan yatsun nawa kika farasha a duniyan nan" ya nuna mata yatsan yana wani irin murmushi yace "yarinya yatsu na was d first nono dakika farasha, kika dinga muah muah muah kaman zaki hadiyemin yatsa" kaman zatai kuka ta yatsine hanci tana kallon hanun tace "ewww nine nasha wanan hanun?" gyadamata kai yayi yana dariya sosai yace "is too late yarinya kin sha kin sha har kikai bacci kinasha dats to tell you how good it taste laaaa" ta turo mata harshe, tsayawa tayi chak tana kallonshi dan wlh he look so cute, yanda ta kafeshi da kallo yasa ya shiga kissing dinta for some minutes ahankali yasaki lips din yace "zomuje kiyi wanka Sugarlips, we're all alone a gidan nan su Omari are not coming back today, nakaiki yawo?" gyadamai kai tayi ahankali hakan yasa ya dagata yana wani irin kallon jikinta, long eye lash dinshi taja tace "a'ah stop" dariya yayi yabude bayi ya shiga da ita, saida ya wankota yafito da ita ta shirya tasaka wani doguwan rigan atampa sanan tai salla, tana idarwa yakawo mata abinci ya shiga feeding dinta, ahankali takeci hartaci iya cinta ta ture yay murmushi yafita da tray outside.


Dawowa ciki yayi ya mika mata hanunshi tashi tayi takama nashi tarike ahankali ya dauko blindfold yace "saina rufe miki ido tukunna" murmushi tayi tadafa hanunshi ta rike yabude musu kofan suka fito yana rike da shoulder nata har suka hau stairs suka sauka kasa ahankali tace "har yanzu Zauj" bakinshi yakai saitin kunenta yace "saura kadan Sugarlips" fito da ita tsakar gida yayi ya tsayar da ita gaban wani hadadden Jeep na Cherokee black bakaramin haduwa motar tayi ba, an makala ma motar wani flower ajiki pink, ahankali ya mata whispering a
"are you ready?" gyadamai kai tayi cikeda murna hakan yasa yazare mata blind fold din daga idanunta tareda kamo hanunta ya sakamata hadadden car key aciki, kallon key tayi sanan ta kalli motar, tasake kallon key ta kalli motar sanan ta kalleshi murmushi yamata ya nuna mata motar yace "is your car Sugarlips" sake kallon car din tayi unbelievably kafin ta kalleshi, yanda yake mata wani irin cool smile, wani irin fashewa tai da kuka tai tsalle tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka sosai tama kasa magana, dariya yayi yacirota daga jikinshi yakai hannu yana share mata hawayen yace "stop crying luv today is a happy day, save wanan kukan na anjima when I screw and knock you down like a mortal combat" murmushi tayi cikin kuka tadan nusheshi agefen ciki tana kallonshi tace "bad Zauj kawai, I love you so much Zauj" ta sanya kanta a kirjinshi tana kulle hanunta ta bayanshi, rungumeta yay back yana wani irin jin dadi harcikin ranshi yace "muje ki shiga car dinki akwai one more surprise" da sauri ta dago kai ta kalleshi tace "another one again" ahankali yace "yes wife, muje kiga" hanunta yaja yakaita wurin motar ya bude motar, bude baki tayi tace "wow! Zauj bantaba ganin irin motar" ganin kallon motan take tawani bubbude ido yasa yabude motar ya zaunar da ita mazaunin driver ya zagaya ya shigo ya zauna adayan side din, hanunshi ya mika ta baya ya dauko mata wani big kwali da akai wrapping da hadadden wrapping sheet ya mika mata da sauri ta karba tana kallon shi kaman taga wani film, ahankali yace "open it" gyadamai kai tayi kafin tafara budewa tabude wrapping sheet din tass sanan ta bude kwalin, wani babban hoto taciro na wata kyaykyawan balarabiya, ciro hoton tayi ahankali ta kafeshi da ido tanajin wani iri sosai ta dago kai ta kalleshi, shima kallonta yake, bakinta nadan rawa tace "wh...who is she?".


Please kuyakuri nai tafiyane, nan da 2 or 3 pages ma zan gama novel din gaba daya.
I love you all❤
[10/23, 3:47 PM] Aishat Muhammad: _BOYAYYEN MUTUN_






*Bayan wata daya*


_CANADA_

Karfe 8 na dare jirginsu ya sauka a Canada, ahankali Marwan yafito rike da hanun Nadeera dan jikinta yay zafi sosai, tun acikin jirgi takejin zazzabi sai running temperature take, tana sanye cikin wani armless gown white data daura black kimono akai ta kulle igiyan ta gaba, tun a jirgi ta warware rolling gyalen datayi ta daura gyalen kawai akan hadadden kiston dake kanta, bayansu kuma Abdallah ne da Omari suna hira abinsu, Muhsin da Abdallah ne sukazo daukan su, Nadeera na hangosu ta fizge hanunta daga na Ya Marwan taje da gudu taikan Ya Muhsin harda kukanta zata fada jikinshi tama manta da zazzabin datake, dan hararanta Muhsin yayi cike dawani irin tsananin kewanta yace "ke bakisan kin girma ba" makemai kafada tayi ta rungumeshi ahankali tasaki wani irin kuka tace "Ya Muhsin I miss you so much" shafa kanta yayi ya cirota daga jikinshi yana murmushi yazare handkerchief ya share mata ido yace "stop crying, I miss my lil sis aswell" sakinshi tayi ahankali tafada jikin Ya Ahmad daya kafeta da ido shima cikin tsananin so while Muhsin cikeda murna da fara'a yay hugging su Marwan, ihu Ahmad yayi yace "zaki karyani ke dis tuluka wayyo Ya Muhsin kaganta ko" sakinshi tayi tana dariya tace "ina Mummyna" mikama su Marwan hannu yayi suna gaisawa cike da mutunci, tai wajen Ya Muhsin dake tsaye kusa da Marwan tana murmushi tace "ina Mummyna yayanmu?" ahankali yace "tana gida waiting for you, let's go Bro" yay maganan yana kallon Marwan dakedan satan kallon Nadeera, gyadamai kai yayi duk suka tafi tana gefen Ya Muhsin, motoci biyu suka zo dashi suka shishiga Marwan da Muhsin ne agaba Muhsin na driving yanata hira da Marwan sai ita abaya, Ahmad kuma dasu Omari a motarsu suka bar airport din, kaman ba ita bace mai zazzabi ba dazu a jirgi har suka kai babban katafaren gidan nasu surutu takema Ya Muhsin dabaya replying dinta sosai, batadamu ba dan dama batun yauba tasan baida magana ba shi, wani remote Muhsin ya danna gate din yabude Mum ta hango tsaye taci gayu cikin shiga ta alfarma tasa wani irin hadadden black jallabiya da stones dinshi keta sheki tana murmushi tabi motocin da kallo batada burin daya wuce taga Nadeera, wani irin ihu Nadeera tayi tun kafin suyi parking. "Yeeee Mummyyy na" tawani zabura zata bude kofan taji an chapke hanunta karaf da sauri ta dagokai Ya Marwan ne dake gaba yadan leko da kanshi, hararanta Muhsin yayi yace "aida kin fita kin karye" kaman zatai kuka tana kallon Ya Marwan din dake mata wani irin kallo kaman ya cinye ta tace "wajen Mummy fa zani" ahankali yana wani irin kallon ta yace "kibari muyi parking first" turomai baki tayi yabi bakin da kallo Ya Muhsin na karasa parking ta fizge hanunta daga nashi tabude motar tafita dawani irin shegen gudu tana dumfaran Mummy data bude mata hannu. "Mummy, Mummy, Mummy na Oyoyo" wani irin fadawa jikin Mum din tayi ta cusa kanta a wuyan Mummy sai kuka, tsayawa sukayi mazan gabaki daya bayan sun karaso wajen suna kallonsu, Muhsin da Ahmad murmushi sukayi sanin yanda Mum tai kewan Princess, sosai take kuka Mum na lallashinta tana mata magana a kunne tana bubbuga bayanta, Ahmad ne yawani zo wajen yace "dalla chan malama aiba ke kadai bace bakuwan ba ko, saiki bari taji da bakinmu" sakin Mum tayi ahankali tana pmurgudamai baki tana share hawayen, dan murmushi Mum tayi tana goge karamin kwallan da Nadeera tasata ta kalli su Marwan tace "Bismillan ku, maraba, maraba, ku shigo please" Atare duk suka shiga babban falon suka zazzauna Nadeera na rungume da Mum a gefe kaman zata hadiyeta, atare duk suka gaidata bayan an zauna, Mum sai murmushi take musu tace "sassanunku da zuwa, wai kunsha hanya" yan aikinta ne suka fara sintiri a falon ana gabatar musu da drinks da sauran su tace "please kusha ruwa ga Alhaji nan fitowa yanzu nan yadawo daga clinic, he will join us yanzun nan" murmushi Nadeera tana wani irin kallonta dan gani tayi Mum tamafi da kyau, rungumeta tayi tsam tsam a jikinta, murmushi sosai Mum tayi ta shafa kanta tacirota daga jikinta tace "Kinga have something first Princess" daukan juice tayi ta tsiyaya mata a glasscup takai mata baki da sauri tasha harda rike hanun Mum tana gama sha takara maida kanta jikin Mum ta rungumeta, hararanta Ahmad yayi ya kalli Marwan dake sipping juice ahankali kusa da Muhsin yace "Ya Marwan kaganta ko nitake murguda ma baki" dan murmushi Marwan yayi kanshi akasa, dan hararan Ahmad Mum tayi tace "kaga Ahmad banda shairi fa, bari akawo abinci let's have dinner daga saimu kaikuje kuyi wanka ayi salla a kwanta ahuta, Gwen" ta kwalama Gwen kira, da sauri Gwen tafito

Mum tace "akawo abinci nan, afalo zamuci" gyadamata kai tayi tawuce kitchen da sauri, kamshin turarenshi da Mum taji yasa ta daga kai hada ido sukayi da Dr yana sanye cikin hadadden farin jallabiya dayar farin glass akan idanunshi, idanunshi da hankalin shi duka akan matar tashi da ayanzu baida abinda yakeso a duniyan nan kaman ita, murmushi suka sakin ma juna atare sanan yafara saukowa daga stairs din ahankali cikin tafiyarshi na wanda ya mayyanta, anatse akuma tsanake yana kallon bakin dasu Muhsin dake shan drinks ana jera abinci akan hadadden rug din falon, duk basu lura dashibama banda Mum, ahankali yakarasa saukowa daga stairs din cikin muryanshi dake nuna kamilin magidanci yamusu sallama. "Assalamu Alaykum" atare dukansu suka dago kai suka kalli direction din da aka musu sallama, tashi tsaye Marwan yayi da Omari atare suna wani irin kallon Dr da shima ya tsaya yana kallon su ko motsi yakasa, kallonsu kowa yayi cike da mamaki tashi lafiya suka tashi tsaye, ahankali bakin Marwan na rawa sosai yana kallon mutumin ya daga hannunshi ya nunashi zuciyarshi nawani irin gudu da kyar ya iya yace "A...Abee!".



*kuma kunsanni I type regularly saida idan da abinda yahanani typing, kuyakuri nai tafiya ne bana gida, but everything yazoma karshe, thank you*❤
[10/23, 3:47 PM] Aishat Muhammad: _BOYAYYEN MUTUN_



_Alhamdulillah am back, yau inna fara saina dire muku shi, thanks for your patient._




Shima Dr wani irin Marwan din yake at the same time yana kallon Omari da Abdallah wanda shi kadaine bai ganeshi ba yanadai kallonshine kaman yanda yaga yayyinshi na kallonshi, sosai kirjinshi ke wani irin racing, hannu yasa yacire glasses din idanunshi ya goge kwalla yasake maidawa idanunshi yana kallonsu still yakasa koda kwakwaran motsi, ahankali Marwan yatako yana wani irin kallonshi muryanshi na rawa sosai kaman zaiyi kuka yace "Abee, kaine or mafarki nake? Abeeee" yaja sunan sosai cikin wani irin yanayi na mamaki, ahankali Dr yabude hanunshi yana kallon Marwan yace "Marwann" da gudu Marwan yafada jikinshi ya kankameshi yace "Abee, Abee kaine, how did you survive? Nida Omari and Umm we all saw when they shot you, Abee na kaine" Abee da Marwan keta cewa dakuma yanda Dr yakira sunan Marwan yasa kowa ya shiga mamaki barin ma Abdallah da Nadeera, ahankali Marwan ya sakeshi jin yanda Abee yake kuka, hannu yasa ya zare glasses din idanunshi yacire ya sharemai ido sanan ya mayar mai da glasses din yana murmushi, murmushi Abee yamai yana kokarin hana kanshi hawayen yafara takawa ahankali Marwan na biye dashi ya tsaya agaban Omari dake tsaye yana kallonshi shima, ahankali yadaga hanunshi dake rawa sosai ya daura akan kafadar Omari ahankali yace "O...mar" gyadamai kai Omari yayi hawaye na gangarowa daga idanunshi kafin yafada jikin Abee da sauri yasaki kuka shima 22yrs rabonsu da iyayen su, rabonsu da mahaifin su, duk dauriyanshi kasawa yayi saida yasaki kuka, ahankali Nadeera dake kallonsu ta kalli Mum da idanunta suka ciko da kwalla tace "Mummy na dama sunsan new Dad ne?" shiru Mum tayi tana kallonta, ahankali yasaki Omari yana kallon Abdallah daya kafeshi da ido bayako kyaftawa feeling somehow yace "Abdallah" kallon Marwan Abdallah yawani irin yi irin waye wanan kuma, ahankali Marwan yace "your biological father, Abee" kallonshi Abdallah yasakeyi, itama Nadeera kafe mutumin tayi da ido jin abinda Marwan yace, ahankali ya rungumo Abdallah yace "My son, mai sunan babana, baka ganeniba ko, you were small dasuka harbeni suka tafi dani, I miss my children so much" yajuyo ya kalli Mum yace "Habibty come, they're our children, wayanda naketa baki labari, i tot I've loosed them, I thought sun kashemin suma, Habibty come" ahankali Mum ta taso tana murmushi tana goge kwallan datakeyi, sakin Abdallah yayi yariko hanunta ya nuna mata Marwan yace "he's Marwan, I called him Tufah because he's my sweet boy, he's my only brother's child, Marwan is everything to me, shi kadai nake gani naga Yayana" ya nuna mata Omari yace "he's Omar, shine my first Son, sai Abdallah" ya nuna mata Abdallah da idanunshi sukai ja yace "he's my Abdallah, he's d last although natafi nabar Mum dinsu da ciki and I always say inhar ta haifi mace abama Marwan ya aura, is a promise I made for mahaifinshi kafin yarasu cewa zan kara hada kanmu, da zumunci mu, inhar nahaifi mace zan bama Marwan" shiru yayi tears yay rolling down his cheeks, ahankali Mum ta sharemai ta matse hanunshi alamun is okay, gyadamata kai yayi kafin ahankali ya kalli yaran yace "ina Momman ku? Banganku tareba? Maiya sameta? Ina cikin dana barta dashi? Ta haihu? A ina kukasan Habibty?" bayanshi Mum ta shiga tama su Muhsin da Marwan alamun suyi shiru, ahankali ta juyo dashi yay facing kujeran da Nadeera ke zaune akai kuka take uncontrollably tunda tagane asalin baban su ne take kallonshi, sosai gabanshi yawani irin fadi daya hada ido da Nadeera dan tunda ya shigo falon sai yanzu ma yalura da ita, kallon Mum yayi zaiyi magana Mum ta girgizamai kai tace "meet your 22 year old daughter, Rahma. Matar Marwan" bakinshi na rawa sosai ya kalleta yace "Ra...Rahma...My daughter?" ya nuna kanshi, gyadamai kai Mum tayi cike da tausayinshi, kafin ta kalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login