Showing 48001 words to 51000 words out of 150731 words

Chapter 17 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

786

home tafito tana murmushi aka bude kofa wani babban Alhaji dayasa kayan yan Nigeria malum malum dawani balarabe dayasa farin jallabiya da rawani ne suka fito, tunda yafito yake kallon su Marwan har hada ido sukayi da Marwan daya kafesu da ido shima yakasa dena kallon yaran, Ameera ce ta nunasu ganin yanda yake kallonsu tace "wayan chan marayu ne maman su tamutu tabar kanwar su mace jaririya watan ta biyu yanzu, muje office Alhaji wanan karan adopting kazoyi ko siya kazoyi? Dan gaskiya kudi yakaru" wucewa sukayi sukai ciki office dinta Alhajin na kallon yaran.
Motherless home din abinda gwamnatin garin basu saniba shine suna sayar da yara kuma wanan Alhajin suke saida mawa duk bayan wata biyar yake zuwa saya, nan Alhaji ya nuna yana sonsu mazan yabiya miliyoyi akansu ya shiga mota shida abokin shi balarabe yacema Ameera da daddare insunyi bacci zai turo adauke su gyadamai kai tayi tana murmushi dan tunda yake siya bai taba biyanta irin kudin wanan karan ba, aranan da daddare duk suna bacci shidai Marwan sama sama yake bacci dan tun ranan dasuka fara dira gidan marayun yaji hankalin shi bai natsu ba baya iya bacci saisa bini bini yake tashi ya kalli kaninshi sanan yakara kwanciya yana rungume Rahma da kyau, lekowa Ameera tayi dakin tawani irin huro wani hoda, strange wari dayaji yasa yabude ido yana kokarin laluban touch light yaduba Rahma dasu Abdallah amma kafin ya farga kawai yay passing out, shigowa wasu kattai sukayi suka kama Marwan, Abdallah da Omari suka fita dasu aka sakasu awani bus a sussume akabar motherless home din dasu. Wani irin ihu Rahma dake kan gado ta sandara da sauri Ameera data taushe hanci ta shigo ta dauketa tana jinjigata tafito sanan ta saki hanci tace "sorry baby anbiyani da kyaune saisa na saida brothers dinki kema karki damu in kinada luck wani zaizo yasiyeki in baki dashi haka zaki girma ahannuna yarinya".
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *idan kika karanta baki biyaba keda Allah*


*AP*

Ahankali yake bude idanunshi dasukai nauyi sosai, duhu yagani sosai yadan kalli dan bulewan da haske ke shigowa inda yake da kyar ya daga kanshi ya leka yaga ruwa kaman a jirgin ruwa suke, dafe kanshi yayi yana kokarin tashi tsaye da kyar ya iya bude baki yace "Rahma, Rahma" kafin ahankali yakara sumewa sabida wani irin dimm da kanshi da kunnuwan shi sukayi bai kara farkawa ba sai bayan kwana biyu, ahankali ya bude idanunshi yana kallon inda yake, akasa kan simenti ya ganshi kwance awani daki ya kafe silin din da fanka ke juyawa da kallo, da kyar kanshi na zafi ya juya gefenshi Abdallah da Omari yagani a wurin suma asusumen warwas, afirgice yatashi yana neman Rahma bakinshi na kiran "Rahma, Rahma" idanunshi ne suka sauka kan window dakin hango manyan maza yayi rike da bingida sunsa bakaken kaya sun zagaye wasu yara da akalla zasu kai shekaru sha biyar haka ansa musu bindiga kananu a hannu ana gwada musu yanda ake amfani dashi, daga yanayin garin kadai da yaren dayaji sunayima yaran yagane nan ba kasarsu bace ahankali cikin yaren larabci yace "Ina muke? Ina Rahma". Wanan kenan.

Ba karamin ciwo Rahma tadinga yiba bayan tafiyan su Marwan, wasu irin kuraje suka feso mata kona kyanda ne oho anadai kula da ita daidai gwargwado ana bata madara ana mata wanka ana kuma bata magani amma ciwo yakici yaki cinyewa ahaka har sati hudu.

Ranan karaman salla!
Sosai ranan taji sauki danba zazzabi kurajen jikinta sun soma warkewa tana kwance kan gadonta na yara abangaren yara jarirai irinta tana kallon toys din dake juyawa tanadan mika hannu yanda jarirai sukayi kaman zata kamo toys din, an mata dan gayu danyau salla, baki akayi dan dama yawanci ran salla ana zuwa ana kyauta ana bada taimako.

Mum ce dataci doguwan riga hanunta rike dana Ahmad dake 7years yana rike da minti mai tsinke anmai gayu sosai yanasha, sai shikuma Abba dake rike da hanun Muhsin dan shekara 10 sai kallon jariraan wajen yake dan agarin Abba ke aiki dawani kampani na aluminum, envelope ne dayawa a hanun Abba yana ajiyewa akowani gadon jariri daya duba shida mum da yaran nasu, tsala ihu tayi hakan yasa Muhsin da Abba ke rike dashi ya fizge hanunshi yay gadon dayaji jaririya tai kuka ya tsaya yana kallonta, Ahmad ma fizge hanunshi yayi yaje wajen yana kallon jaririyan, ahankali Muhsin ya mika hanunshi yana dariya saikuma ta mika mita sweet dinshi yace "cute baby zakisha sweet dina?" tureshi Ahmad yayi cikin shagwaba yace "no nawa zata sha" dambe suka fara hakan yasa Ameera da Mum da Dad sukazo wajen dan raba yaran suna dariya, daukota Ameera tayi daga gado tana jijjigata tana nunama su Muhsin ita tace cikin harshen turenci "her name is baby R, mamanta ta rasu she don't have anybody" da sauri Muhsin yakama rigan Abba dake kokarin daukan waya yace "Abba i like this fine baby" kafin Abba yay magana Mum ta mika hanunta ta karbi jaririyan dataji ta burgeta yarinyar ga gashi kaman me tanason mace sosai dama gashi a haihuwan Ahmad aka cire mata mahaifa, kiss tamata a goshi Ahmad yay ihu yace "Mum zan dauketa" tsugunnawa tayi ta sakama Ahmad ita a hannu yanata dariya Muhsin shima yace shima aka bashi Ameera nata dariya, kallom jaririyan Abba yayi yaji shima yama wani irin sonta sosai yanda yaketa kallonta baya magana yasa Mum ta karbeta daga hanun Muhsin ta mikama Abba, ahankali Abba ya dauketa yana kallonta a kunne mum tamai whispering "lets adopt her Alhajina kaga our children like her nima haka wlh i really really love the cute little girl muyi jahadi lada zamu samu kagama batada lpy gata marainiya anan bazata samu isheshen care ba" ga mamakin ta saitaga Abba ya kalli yarinyar dahar tai bacci ajikinshi yace "okay wife" nan fa sukai magana aka musu papers yabada address din gidanshi dana kampanin dayake aiki da duk dai wani information da aka tambaya suka daukota da tarkacenta suka taho gidansu bayan sun kaita asibiti an dubata sosai an rubuta magunguna suka siya, bayan sati biyu Abba yahada mata hadadden suna nagani nafada ya gayyaci yan wurin aikinshi ya radama yarinyar baby R suna Nadeera.
Bayan shekara daya Abba ya tara kudin dayake bukata yafara shiri yakoma gida Nigeria da iyalinshi dakeji da Nadeera da yanzu tana tafiya tanacin abinci yarinyar bulbul da ita ga gashi kaman me ga kyau gatada shiga rai.


***
Da gudu Ahmad dake gefenshi ya tsugunna ya dago kanshi Abba ma da Mum arude duk sukayo wajen suka tsugunna da sauri Abba ya karbeshi daga hanun Ahmad yana kiran sunanshi "Son, Son Muhsin" dago kai yayi ya kalli Ahmad da idanunshi sunyi jajir yace "kawomin ruwa Ahmad" da sauri Ahmad yatashi yafita daga dakin dan dauko ruwa, fashewa Mum tai da kuka tana kallon Muhsin dako numfashi bayayi kanshi akan cinyar Abba dake ta tofamai addu'a, shigowa Ahmad yay da sauri rike da bottle water da sauri ya bude Abba ya karba ya yayyafa mai a fuska yana kiran sunanshi "Muhsin, Son" ko motsi baiyiba hakan yasa Mum tafashe da kuka sosai tana salati tace "innalillahi Alhaji danmu maiya samai" dago kai Abba yayi da idanunshi dasukai ja ya kalli Ahmad yace "get key ka kunna mota kazo Son" gyada kai yayi yafita da sauri afalo yadau keyn motar yabude kofa yay tsakar gida, kunna motan yayi yadawo dakin dashi da Abba suka fita da Muhsin asume Mum biye dasu tana kuka tana goge fuska da handky suka sashi a mota, dawani irin gudu Ahmad kejan motan Abba har lokacin yana rike da Muhsin yanamai addu'a aka harsuka kai asibitin yay parking kafin kace me nurses sun turo gado Abba da Ahmad sun daurashi akai anyi ciki dashi likitoci na kanshi ana bashi taimako da kyar sukaci nasaran farfado dashi nan aka gungurashi zuwa wani daki Mum tabisu, magani aka rubuta ma Abba da allurai da drip akace yaje yasiyo binshi Ahmad yayi suka fita daga dakin akabar liktan dake duba pulse dinshi da Mum dake zaune ta bakin gadon dayake kwance, kallon Mum din likitan yayi yanda tai tagumi tana kallonshi yace "karki damufa hajiya zaiji sauki bari idan sun dawo zanzo na sakamai magungunan" gyadamai kai Mum tayi batare data iya magana ba yajuya yafita daga dakin, wani irin bude ido yayi dasukai jajir yana kallon sama hakan yasa Mum sauka daga gadon da sauri tai wurin kanshi tana shafamai fuska tareda kiran sunanshi tace "Muhsin my boy menene katashi mekema ciwo? Gani nan look at me Son" kallon Mum yayi da rinanun idanunshi kanshi najuyawa ahankali cikin zafin ciwo yafara sambatu yace "Mum Abba..Abba..Abba ya nemi Nadeera bayan haka ya aurar da ita sanan kuma yana cewa yana sonta, Mummm bakinmin alkawari zaki auramin Nadeera idan ta girma ba? Mum i really really love Nadeera tuntuni ita nake jira tagama nursing school, Mum bazan iya rayuwa ba Nadeera ba, I love her, i love her mum, i love her, Mum zan mutu inban sameta ba, zuciyata zuciyata Mum my heart" yadafa zuciyarshi, shafa kanshi Mum tayi cikin tsananin tashin hankali ta jijjigashi tareda kiran sunanshi tace "Muhsin," ko jinta bayayi saima sambatun dayake yi ba kakkautawa ana haka su Abba da Ahmad tareda Dr suka shigo dakin da sauri Dr yay kanshi allura yamai kusan uku hakan yasa yakoma bacci, kasa rike kukan dake cinta sosai Mum tayi tana kallon Muhsin da sauri tafice daga dakin Ahmad yabi bayanta zama tayi a reception tana goge hawayen datake yi da handky da sauri Ahmad ya zauna kusa da ita dudda yana mugun fushi da ita amma yanda take kukan nan really break his heart ahankali yace "don't worry Mum he will be fine kidena kukan hakanan" gyadamai kai tayi tareda resting head dinta a shoulder dinshi tana kara share idanunta da handky saiga Abba da Dr sun fito daga dakin dago kai sukayi suna kallon su, godiya Abba yama Dr yazo inda suke batare daya kalli Mum ba ya kalli Ahmad daya dauke kai kaman bai ganshi ba yace "kai jeka zauna da wanka inya tashi ka kirani a waya zanje masallacin asibitin akwai wani salla da akace nayi na addu'a a wanan lokacin, na addu'a ne kan princess dita ta bayyana, bari naje" bai jira amsan suba yawuce yafice daga asibitin Mum tabishi da kallo tana buga tagumi tana kiran Allah danshi kadai zai magance mata wanan matsalan.


***
Ahankali take bude idanunta tashi tayi da sauri ganin gari ya waye tana sosa ido sosai, kaman daga sama taji ance "by this time kike tashi agida ko?" ahankali ta juyo dakai yana zaune akan kujera yana aiki da MacBook ya sanya normal hoodie maroon ajikinshi da dogon black trouser wanan karan baisa face mask da safan hannu ba, bakaramin kyau yayiba kaman wata mace ga giranshi acike baki sidik da manyan gashin idonshi da gashin kanshi dake wani irin shining da sauri ta dauke kai a tsorace ta sauko daga gadon ahankali ta zauna tana kalle kalle ko zata ga hijabin ta amma batagani ba gashi dan gown dinta iya gwuiwa, ahankali ta mike tsaye tadan juya tana waigen shi kafin ahankali ta tashi harda dan gudunta ta bude kofa ta shige dan karya ganta, murmushi yayi ya ijiye MacBook din yatashi daga kan kujera yabude kofa ya fice daga dakin daidai lokacin Omari da Abdallah sun fito suna magana shiru duk sukayi suka tsaya chak suna kallon yayan nasu ganinshi ba facemask wani irin juyi Abdallah yayi ya kannema Omari dake kallonshi kasa kasa ido kafin ya juyo ya kalli Ya Marwan din daya tsaya ya zuba hannu a aljihun hoodie yana kallonsu yana kokarin karanto abu akan fuskokin su kafin ahankali yadan hararesu yace "what?" girgiza mishi kai duk sukayi sun kasa magana kafin su tako kaman wasu marasa gaskiya suna kallonshi sukai staircase suna waigenshi suna murmushi kasa kasa, biyosu yayi hakan yasa suka sauka da wani irin gudu suna ihu Omari yace "Abdallah Ya Marwan yasoma gane karatun damuke mai fa" Abdallah dake dariya yace "i see, iyye yayan mun baaa" sukai wani irin tafi shida Omari, tsaki yadanyi ya zauna kan kujera yana duba agogon hanunshi yanadan karkada kafa, kallonshi sukayi kafin su je da gudu su fada kanshi suka danneshi sunamai chakulkuli, dariya ya shiga yi dake karamai kyau yana turesu da kyar suka barshi ya mike tsaye yana hararan su yawuce kitchen da sauri, hijabinta da abubuwan su da jakan shi daya bari a kitchen din ya dauko yafito yay sama da sauri kaman wanda bayaso su ganshi bude kofan dakin yayi ya shiga akan dadduma yaganta tana zaune akan dadduma, tana ganinshi ta daura kanta akan kafafunta ta kankame kanta kaman wacce taga dodo, ajiye abubuwan yayi akan kujera kafin ahankali yazo inda take, zama yayi agefenta batare dayay making any sound ba da sauri ta dago kai ta yunkura zata gudu ya kamota, zaunar da ita yayi tareda sata ajikinshi ya rungumeta tsamtsam ya saukar da ajiyan zuciya yana sauraran yanda heart dinta ke beating fast fast jikinta na rawa, dagota yayi daga jikinshi da sauri ta kawad dakai ahankali yasa hannu ya yaye hijabin ya cire ya ijiye akan gado, fashewa tayi da kuka mara kara, wani irin bin jikinta yayi da kallo tasaka wani open neck gown navy blue daya amshi fatarta ya bayyana cikanta sosai babu hula akanta kalabanta na lilo a kirjinta sai cool kamshi take fitarwa, ahankali ya mika hanunshi ya shafo gefen kumatunta dakeda taushi sosai kaman na jaririya kafin ya juyo da fuskarta ta fuskance shi murya chan kasa yace "Hey! Look up" dago manyan idanunta tayi ta kalleshi tana sauke ajiyan zuciya hawaye na gangaro wa, yanda yakafeta dawasu irin idanu yasa tace "g..gu..d m..morning" wasu irin hawaye sukai rolling down her cheek, gyada mata kai yayi batare dayay magana ba idanunshi akan kwayar idonta kaman maison karanto wani abu, ahankali ya mika duka hannayen shi ya daura akan shoulder dinta ya kullesu ta baya batare daya sakin mata nauyi ba, wani irin kallo yamata yanabin bakinta dake rawa sosai nason yin kuka da kallo murya chan kasa yace "why are you crying for me now?" girgiza mai kai tayi da sauri tana share hawayen tana marmar da idanu, ahankali tace "ka kaini gurin Mummy na please" wani irin kallo yay mata hakan yasa tafara yunkurin tashi atsorace hannunta ya jawo hakan yasa tafado jikinshi tafashe da kuka sosai a tsorace, ahankali yace "shiiii" shiru tayi tana kallonshi, hanunta yakama yana shafa nails dinta yace "ba kince tana Dubai ba" gyadamai kai tayi tana goge hawaye da bayan dayan hanunta dabai kamaba ta ijiye cikin wani irin muryan tsoro tace "tadawo yanzu" sakin hanunta yayi ya kalleta, gyadamai kai tasake yi muryanta narawa sosai tace "i..ca..can feel it, please zanje wurin Mumy na please" tafashe mai da kuka sosai harda shesheka dandan Mum kawai takeso tagani, fizgota yayi tafado jikinshi ya daka mata tsawa. "shut up" atsorace tsabagen frigita tasa hannu ta kama lips dinta gam tana kallonshi, shiru yayi yana kallonta kafin yasa hannu ya janye hanunta daga bakinta yana kallonta ya sauke idanunshi akan lips dinta dake rawa sosai ajiyan zuciya ya sauke, ahankali ya daura hannunshi akan waist dinta ya kulle yawani matso da ita gaba har saida kirjinshi da nata ya hade ajiyan zuciya suka sauke atare kafin ahankali yana kallon kwayar idanunta yace "you want to talk your Mum?" gyadamai kai tayi kaman wata marainiya, aljihun wandonshi shi ya nunamata da baki yace "give me my phone" dan kallonshi tayi kafin ta kalli aljihun nashi ahankali jikinta na rawa tadan duka ta mika hannunta zata tura cikin aljihunshi hakan yabashi daman ganin kirjinta sosai kasancewar open neck riga ne ajikinta wani irin abu yaji dayasa tsigan jikinshi mikewa duka ya lumshe ido da sauri, ciro wayar tayi IPhone ta mikamai bakinta na rawa tace "ga..gashi" bude idanunshi dahar sun chanza kala yayi ya daura su akanta kawad dakai tayi da sauri tana mikamai wayar, murya chan kasa yace "sa number ta" da sauri ta kalleshi murmushi tayi sosai daya lobar da dimple dinta hakan yasa ya lumshe ido da sauri, cikin murna tace "Number Mummy na zansa?" gyadamai kai yayi batare dayay magana ba da sauri ta bude wayan babu password hoton Omari tagani da Abdallah a Screensaver batasan suwaye ba, dialog taje ta saka number Mum hanunta har rawa yake sake dago kai tayi suka hada ido yana wani irin kallonta ahankali cikin tsananin farin ciki tace "in kira?" dan fuzar da iska yayi awahale yace "yes" wani irin jujjuyar dakai tayi tai dailing number tana murmushi sosai daya bayyana teeth dinta tana addu'a Allah yasa tadawo dan number Nigeria ta ta haddace kusan ringing hudu sanan taji an daga wani irin tashi tayi daga jikinshi tai tsalle tahau kan gado tama kasa magana tsabagen murna yawani irin bita da kallo yarinyar nakara shiga ranshi wani irin sanyi na shigan shi, daga ta dayan bangaren Mum na gefen Muhsin dake bacci a asibitin tace "Hello" kallon screen din wayan tayi tana mamaki dabataji magana ba hakan yasa tasake maidawa kunenta tace "helloo waye i can't hear you" ihun dadi Nadeera tayi harda daga kafa tawani irin yin jumping ta tashi ta zauna daga bakin gadon tace "Mumy na" ko acikin barci duk inda taji muryan Nadeera zata gane hakan yasa Mum ta mike tsaye ta dafe kirjinta dayawani irin buga dum ahankali tace "Princess kece?" gyada mata kai tayi ahankali kaman tana gabanta kafin ta wani irin tabe baki ashagwaban ce tace "Mumy na i miss you so much" tafashe ma Mum da kuka sosai, share hawaye Mum tayi tana kara kallon dakin da Muhsin dake bacci kafin da sauri ta shige bayin dakin gudun kar Abba yadawo ta kullo kofan ta jingina da bango ahankali tace "My Princess" kasa magana tayi sabida kuka, sake share hawaye Mum tayi tai murmushi tace "stop crying Mummy's girl" gyada ma Mum kai tayi tana share hawaye cikin muryan kuka tace "Mum i have alot of things to tell you kizo ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login