Showing 72001 words to 75000 words out of 150731 words
wani azabtarwa da wahala dakika sani aduniyan nan Ya Marwan yasha shi dama wanda yafi haka, ko punishment za'a mana Ya Marwan baya bari amana, za amai nashi, amai nawa, sanan amai na Abdallah, kinsan kacha?" gyada kai Mum tayi tausayin yaran nawani irin shiganta tun kafin ma tagama jin labarin yace "dashi ake dukan ya Marwan, Ya Marwan dana zuciya ga taurin kai, he was small then amma we are his life, daki tabamu gwara kin kasheshi gashi har an sanmu, da sanyin safiya za'a fitar dashi waje tun irin karfe biyar dinan acire mai kaya abarshi da boxer adinga watsa mai ruwan sanyi harda Ice aciki ana dukanshi mercilessly kuma ogansu kesa amai haka because yaki yarda muyi training din guns da ake so afara mana, sanan munki yima kowa magana dudda ana mana magana da larabci dan ansan bamujin hausa amma munki mu amsa, and kullum attempting guduwa muke sabida tunanin kanwar mu Rahma, koyaya take oho, Ya Marwan yakusa mutuwa sabida azaban wahala, saida mukaga zasu kashe Ya Marwan dakeda wani irin taurin zuciya mara misali yasa muka fashemai da kuka muka sakashi agaba dan mu kadaine weak point dinshi mukace ya yarda zamu dinga yin abinda sukace, koma miye zamuyi yadena bari ana dukanshi dan kasheshi zasuyi sanan ya yarda" ahankali Omari ya sauke ajiyan zuciya yadan goge hawayen daya zubomai yace "mun wahala, mun wahala, munga rayuwa da bazata faduba wani abun saika gani da idonka zaka yarda, wani hisabin alahira kadai za'a iyayi, idan yaro yana rashin lafiya suka bashi magani baya responding to treatment kasheshi sukeyi, ahaka mutumin yasamu a makaranta wanda na aminin shine dasuke siyan yara tare har muka gama body guards kusan 6 ke kaimu, har University yatura mu, private university abokinshi, Ya Marwan ya karanci computer engineering, nikuma na karanci economics sai Abdallah daya karanci accounting, ko mutum daya ba'a bari muyi magana dashi, security dasuka saka mana yawuce tunanin ki" shiru yayi ya goge hawayen daya zubomai yana girgiza kai yakasa cigaba wa, Abdallah yace "fashi, arm robbering, da kidnapping babu wanda basu koya mana, babu wanda bamuyiba base on his order, haka mukeyi kullum muna neman hanya dazamu gudu muje wurin kanwarmu Rahma, ko munyi yunkurin guduwa saisun kamamu dan sun samana trackers ajiki, da kyar da taimakon wani mutumi wani ma'aikacin gidan, daya daga cikin kuku dake girki dake son Ya Marwan sosai yabar mishi kitchen a bude bai rufeba, shiga Ya Marwan yayi asabe batare da kowa ya ganshi ba, duka gas din ya ciccire pipe dake bama top din gas, ya ijiye pipe din akasa hakan yasa gas din yadinga fita yabar kitchen din da sauri yazaya ta bayan window kitchen din dayake a kulle yaje ya kunna ma wata rigar shi wuta ya ijiye jikin windon kafin yabar wajen da sauri yay ihu yaje wajen guards din gate yana cemusu fire da sauri sukai wajen sukaja rigan wutan suna kokarin kashewa dayan kuma yabude window dan yaga ko akwai wuta a kitchen din aiko wurin yabada wani irin buuuu, wuta ci kawai take hakan yasa da manya da yara duk suka fito kowa yana neman hanyan fita wasu guard na binsu gudun karsu gudu, bude musu gate Ya Marwan yayi kowa na gudu ana fita ya bude jakarshi yacire spherical bomb ya kyasta ma bakin wuta da lighter ya wurgama guards din dake shirin binsu aiko da sauri suka dare yajamu muka fita daga gidan da gudu munabin dajin, da kyar muka sabe muna gudu adajin nan some guards na binmu ana harbin mu, Ya Marwan kawai yafadi ya sume ashe an harbeshi agefen ciki, rudewa mukayi muka rirrikeshi nida ya Omari muna gudu har mukakai titi, wani mutumi ya tai makemu ya tsaya ya kwashemu yakaimu asibitin ana treating Ya Marwan muka fadin mai komi yafadinma polisawan akai tracking gidan gwamnati, akadau hotunan yaya Marwan anata watsawa a media banda mu, bayan komi yalafa gov. tabiyamana kudin jirgi ta maidamu kasar mu Egypt, direct gidan marayun nan mukaje muka tarar da Ameera mukace mata ina sister mu ganin tana neman maidamu wawaye mukai reporting to police station da kyar tai confessing tace anyi adopting dinta and mutanen yan Nigeria ne sukai adopting dinta, sosai ranmu barin ma Ya Marwan da kaman ya kasheta ya baci, akai kaita prison, da kyar muka samo wanan file din dat contain actual profile dinmu da ranan damuka zo, gwanati tai transferring yaran zuwa wani gidan marayun aka rushe wanan aka kama ma'aikatan dan duk dasa bakinsu, bayan kwana biyu muka wuce bank inda Abee ya biyoma Ya Marwan gadonshi da iyayen shi suka barmai dan ko kwandala bai tabamai ba, yaje karbo bayan dogon bincike aka bashi kudin shi kudin dayawan gaske rasa yanda zama muyi da kudin mukayi, ya zuba dayawa a account sanan muka fara shirin dawowa Nigeria dan daukan fansa, a tunanin mu wayan nan politicians din dasuka sayemu susuka sayi Rahma saisa mukace saisun fito mana da kanwar mu and they will pay darely, aboyayyen Mutum ya Marwan yadawo sabida akwai hotunan Shia media, nan muka gida wanan gidan atsakiyar dajin nan, muka fara fita operation muka addabi politician hartakai ga su kansu tsoron fita daga gidansu suke, d worse part is basusan waye Ya Marwan ba, ya Marwan yay planing accident din mutumin nan na asibiti dan shine mutumin daya siyemu bayan yama ya Marwan wayanan tabon jikin nan nashi, mun daukoshi yace bashi ya dauke Rahma ba, shi maza yake siya baya siyan mata, zuciya ya debi ya Marwan yakusa kasheshi da kyar muka ceceshi muka maidashi gida yan uwanshi suka ganshi aka kaishi asibiti shine Ya Marwan yabishi har asibitin da aka kwantar dashi danya kasheshi aranan ne kuma Yahadu da Nadeera data chanza komi nashi, yarasa sukuni, baya iya fita operation, yadinga zazzabi, mu kanmu munyi mamakin shi ashe destiny ne, Allah yaga zukatan mu, Allah yadawo da kanwar mu da tun kafin ahaifeta Abee yafada agida inhar Momma mace tahaifa to yabama Marwan ita, ya aureta, unknowingly Allah dakanshi ya kaddara auren su, auren da yayishine danya taimaka yay saving dinta daga mahaifinta, ashe itace Rahma mu, ashe sister muce, oh Alhamdulillah, Allah nagode mun godema, am so happy, am a happy brother today I can't wait ta tashi nabata brotherly hug omg" ya share hawayen daya zubomai ya rungume Omari dake gefenshi, sosai Mum takafe Marwan dashi kadaine sanye da mask da ido, ahankali tace "can I see your face Marwan?".
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *karki karanta in baki biyaba, in kina son novel dinan, zaki turo 300 kota card kota bank sai nai adding dinki a group din danake posting kullum*
_Acc no 3107021073 first bank aisha Muhammad_
*Kokuma zakiyi chatting dina up ta watsapp number na 07012181461 saiki turamin evidence of payment*.
*Maman Abd Shakur*
*AZ*
Shiru yayi yana kallon Mum he has so much respect for the woman sabida yanda yaga tanason Rahma saisa bazai iya mata gardama ba, ahankali yasa hannu ya tuge mask din ya ijiye akan table idanunshi akasa, wani irin kallo Mum takemai tana mamakin kyau haka ko wata macen albarka tana ganin su Abdallah kyawawa ashe shi wanan kankat ne, bakinta har rawa yake tace "masha Allah, kunga haka fa Allah ke abinshi dama nataba ganin news din a aljazeera an rushe motherless home dinan sabida suna saida yara, oh Allah kasa mugama da duniya lafiya, kunga yanzu hankalina yakara natsuwa wlh na natsu sosai Allah yakawo wayanda suka fimu iko da Nadeera naga yanda Abba zaiyi" tadanyi tsaki kafin ta dago ta kallesu ta hade hannayen ta tace "kuyafe mana, kuyafema baban su shirin shedan ce nasan yay babban laifi, amma kuyafe mana, to ya akayi Nadeera batai kama dakuba naga dukkun fita hasken fata?" murmushi Abdallah yayi yace "da Abee take kama fatarshi ta dauko mu farin momma ne" murmushi Mum tayi tace "ikon Allah amma am so happy kaman an ciremin wani stone azuciyata nakeji wlh, to yanzu tayaya zamu sanar da Princess? How is she going to take and accept wanan babban labari haka?" ta kalli Marwan tace "tayaya zamu sanar da ita Marwan?" dan dago kai yayi ya kalli Mum kafin ya mayarda kanshi kasa anatse yace "dazaran taji sauki" tashi yayi ahankali daga kan table din yace "bari nadubo ta" yawuce sama batare daya jira amsan Mum ba, ahankali ya bude kofan dakin ganin ta bude ido yasa yarufe kofa da sauri yay cikin dakin yana tafiya ahankali yana wani irin kallonta, daga kwance datake take mika hannu agajiye tana kokarin janyo doguwan riganta dake gefe tana rike cikinta dan mugun ciwo yake mata bana wasaba, hanunshi dataga yariga nata ya dauko rigan yasa tawani irin ja numfashi cikin tsoro tareda kulle idanunta tanajin mayen kamshin dayake yi kaman ya juye turare ajikinshi, zama yay ta bakin gadon tareda sa hannu ya dagota zaune, nishi tayi cikin ciwo kaman zatai kuka tace "cikina" da sauri yasa hannu ya juyo da fuskarta tareda hura mata iska a fuska hakan yasa ta bude ido ahankali hawaye na taruwa a idonta, bakinta har rawa yake kirjinta na bugawa tace "p..please zan shiga bathroom" gyada mata kai yayi yanajin kaman karta dena mai magana, rigan yadaga yasa mata awuya da sauri tana kara rike bargon jikinta ta zura hanunta daya kafin ta karbi dayan hannu ahankali ta saka kirjinta na bugawa tajashi kasa, tashi daga kan gadon yayi ya mika mata hannu ahankali yace "come" dan kallonshi tayi da sauri ta dukar da kai dan kwarjinin shi yamata yawa ta mikamai hanunta dake rawa ya dagata sama ahankali yanabin inda ta tashi da kallo itama wajen takebi da kallo da sauri ta fizge hanunta daga nashi a mugun tsorace dudda uban ciwon dake cinta ta tsaya agaban gadon tana kokarin yaye bedsheet din tace "please am sorry I was sleeping saisa bansan yaz..." hanunshi dataji akan waist dinta yawani irin rungumota ta baya yasa takarsa karashe maganan hawaye nason zubo mata, daura kanshi yayi agefen wuyanta murya chan kasa yace "you are on your period ko I guess?" gyadamai kai tayi atsorace wani irin sanyi na shigan ta, dan juyo da ita yayi tai facing dinshi wani irin kallon dayake mata daya bambamta dana kullum yasa tasake saukar da kanta kasa da sauri matseta yayi ajikinshi yana taba wuyanta ganin har yanzu jikinta da dan sauran zafi amma ba kaman na dazuba dayake kaman wuta, bakinshi yakai saitin kunenta dan lashe kunen yayi slowly da sauri tai yunkurin janye kunen sabida yanda taji tsirr, ahankali yace "wat do you need for the period, tell me" idanunta alumshe batare data bude suba tace "sa..sanitary pad and drugs" gyada mata kai yayi ya maida kanshi kan wuyanta ya tura hanunshi a aljihun bayan wandonshi yaciro wayarshi ya kawo ta gabanta ya daddanna ya shiga inda zai taypa ma Abdallah message ya mika mata murya chan kasa yace "write it down" gyadamai kai tayi hanunta na rawa ta karba sabida wani irin shafa mata ciki dayake yi gashi ya matseta da kyar ta iya ta rubuta sunan pad da magungunan datake amfani dashi duk lokacin mp agida, idanunshi akan screen din ta mikamai ahankali ya karba ya hada da hanunta yarike ya rubuta get it now sanan yay sending message din ya mayard da wayan aljihun shi yana wani irin juyo da ita tareda daukan ta yana kallon fuskarta data lumshe ido tana ajiyan zuciya da sauri da sauri kaman zai mata wani abu ya shigar da ita bathroom ya zaunar da ita kafin ya tsugunna yariko hanunta ahankali yace "Rahma" da sauri ta bude idanunta tadan kallai irin Rahma kuma ganin kallon dayake mata yasa ta saukar da kanta kasa tana marmar da ido ahankali yace "namiki wankan cuz u are not strong?" da sauri ta girgiza mai kai tasa hannu tana goge hawayen dake zubo mata, ahankali ya mike tsaye yajuya ya tsaya wajen kofa yace "15 minutes nabaki" fita yayi ya rufo mata kofan gadon yaje ya cire bedsheet din yakai shi ya ijiye akan kujeran dake tsakiyan closet wani hadadden zanin gado yaciro ya shimfida ya gyara ko ina dudda dakin ba datti kuwa dakin yahau kamshi, knocking kofan akayi Ya bude Abdallah ne rike da babban ledan wani pharmacy, karba yayi yaja kunen Abdallah dake mai murmushi yajuya yabar wajen yakoma kasa wurin Mum, shikuma yakoma daki yarufo kofan.
Bude kofan yayi ya ijiye mata pad din akan kujeran dake tsakiyar closet din yafita ya ijiye maganin akan gado ya zauna yana jiranta, tadade tana wanka da ruwan zafi, sosai taji dadin jikinta barinma fuskarta dataji ya sake mata sosai, taji da dinshi bakaman da daya daddaure mataba, dauro towel tayi tafito tana tafiya ahankali, pad din data hango kan kujera yasa taji hankalin ta ya kwanta sosai, shiryawa tayi tsaf tasaka wata atampa da aka mata riga da sket blue da pink ne atampa aiko tai kyau ta daura dankwali babu komi a fuskarta but tayi kyau bana wasa ba looking so simple and sweet, ahankali ta bude kofa da sauri ya daga kai yana kallon kofan fitowa tayi tana jan gaban dan kwalinta danya rufe mata kirjinta dasuka taso ta gaban rigan sosai da kyau, kafeta yayi da ido hakan yasa ta tsaya kyam takasa shigowa falon sai wasa take da yatsun ta, ahankali yabude hanunshi yana wani irin kallonta cikin sauki dawani irin so yace "come" dago kai tayi adan tsorace ta kalleshi da sauri ta dauke kai sabida wani irin kallon dayake mata kaman zai hadiyeta, ahankali tafara tafiya harta karasa gaban kujeran takasa fadawa kanshi kaman yanda yake nufi gefenshi tayi zata zauna yawani irin fizgota tafado jikinshi harsaida tai kara tace "wayyo" sassauta riko dayamata yayi tareda gyara ta ajikinshi, murya chan kasa yace "sorry" zare dan kwalin kanta yayi ya ijiye gefe yanabin gashin ta da kallo kafin ya saukar da idanunshi kan kirjinta dasuka ciko kaman zasu fito daga rigan, wani irin ajiyan zuciya ya sauke yadan lumshe ido yana sauraran yanda kirjinta ke bugawa ahankali yace "I have a surprise for you, kinason kiga surprise din?" yay maganan yana dago habarta ta kallai yanda ya tsareta da ido yasa ta gyadamai kai ahankali, murmushi yayi yace "okay" ya shafa inda ya kumbura a fuskanta abin namai ciwo kafin ya kalleta kwayar idanunta yace "meke miki ciwo yanzu?" marmar tai da ido tana shirin kuka ya girgiza mata kai yace "don't cry for me, crying queen" jawota yayi sosai yana gyara kwanciya tareda daure hannayen shi abayanta yana kallonta yace "tell me meke miki ciwo yanzu?" ahankali tace "my stomach" lumshe ido yayi da sauri dan yanda tai maganan chan kasa kaman wacce muryanta ya shake yasa yaji ya shiga wani irin yanayi bukata ahankali yabude idonshi dasuka dan chanza kala ya daura akanta tareda kamo lips dinta nakasa batare dayay sucking ba yace "I will make it stop, zai dena miki ciwo kinji" gyadamai kai tayi ahankali tanason ta fizge lips dinta ya shiga kissing dinta da sauri da sauri wani irin ajiyan zuciya ta sauke kaman zata sume itadai ta banu, ahankali yakai hanunshi bayan riganta yana kokarin zage zip dinta tafashe mai da kuka dan kwanciya kawai take so tayi tahuta sosai cikinta ke mata ciwo, da kyar ya saketa tareda matseta ajikinshi yana sauke ajiyan zuciya yace "don't cry for me please" yasa hannu yana share mata hawayen datake yi, dagata yayi shima yatashi shima yakaita ya zaunar da ita abakin gado yana kokarin saita kanshi ya dauko magungunan ta yabata yana murmushi yanda yaga dukta takure waje daya yace "lemme bring your surprise for you matsoraciya" dukowa yayi yama lips dinta kiss ya dago yana murmushi da sauri tasake sunnar da kai kasa, ahankali ya dago yafita daga dakin yana waigenta.
Ya rufo mata kofan yay kasa yatarar da Mum dasu Abdallah nata mata hira dago kai duk sukayi suna kallonshi ahankali yace "ta tashi Mum lemme take you to her" tashi Mum tayi tana murmushi ta nunamai jakanta tace "ga abubuwan ta nanma nakawo mata" wurin jakan yayi yaja yahau kan stairs Mum biye dashi tana kallon ko'ina ya tsaya gaban kofan dakinshi ya bude yana kallonta har lokacin tana zaune inda ya barta tana wasa da yatsun ta yaja jakan ya shiga ciki Mum ma ta shigo tana murmushi tana kallonta ita kanta tai kewan yar tata ahankali tace "Princess" dawani irin sauri Nadeera ta dago kanta ta kalli hanyar kofan jin kaman muryan mum dinta, ganin Mum dinta yasa tawani irin mike tsaye tana kallon Mum da mugun mamaki, dawani irin gudun bala'i dan tama manta da rashin lafiyanta tawani irin yin tsalle tafada jikin Mum ta kankame ta tasaki kuka sosai kaman wacce bataga mum nakusan shekara dayaba, tsayawa yayi chak yana kallonta daga ita har Mummy datake neman tafadar waka cikin kuka tadago kanta a shagwabe tace "Mummy na kece?" gyada mata kai Mum tayi hakan yasa takara mayar da kanta jikinta ta kankameta tana sauke ajiyan zuciya tana kuka sosai tace "kinzo kitafi danine Mummy?" dagota mum tayi tasa handy dinta dake hanunta ta share mata fuskanta ahankali gudun karta kama mata ciwon fuskanta tace "is okay dena kukan, keda bakida lafiya kinji Princess zomuje mu zauna" gyada mata kai tayi Mum taja hanunta suka shiga dakin suka zauna akan kujera, da sauri tasake fadawa jikin Mum tawani irin rungumeta ta kankameta sosai, murmushi Mum tayi itama tai hugging dinta back, ahankali ya juya zai fita daga dakin yadan zuyo ahankali daidai itama ta juyo da kanta hada ido sukayi da sauri ta lumshe ido tana rirrike Mum tana murguda mai baki, dan murmushi yayi yabude kofa yafita daga dakin yarufo musu kofan yana sake murmushi dan abunda tamai ya bala'in bashi dariya da sha'awa dakin su Omari yawuce yana murmushi shi kadai kaman an mai kyauta.
Ahankali Mum taciro ta daga jikinta tana taba inda ya kumbura a fuskanta tace "kinsha magani kuwa?" gyadama Mum kai tayi ahankali, kaman Mum zatai kuka tace "mai yake miki ciwo yanzu princess?" a shagwabe tace "marana ke ciwo sosai