Showing 114001 words to 117000 words out of 150731 words

Chapter 39 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

798

motar, saida suka fara ajiyeshi a tsohon gidansu na bwari kafin su wuce gida. Suna isa gida suka taradda Nadeera sai barci takeyi a palour remote na hannunta. Part dinsu suka wuce suka hado kayansu kafin su dawo nata su hada mata nata, Saida suka gama hadawa sannan suka zauna booking tickets dinsu Marwan yafara tura musu ta email sanan suka tasheta tare da mika mata hijab dinta binsu tai da kallo Omari yace "wear your hijab" karba tayi tasaka ba musu tana gama sawa Abdallah ya mika mata takalmin ta "wear it" ahankali ta zura, Abdallah ya ja hannunta suka fita daga gidan bude mata mota yayi yasata aciki Omari yakoma ya rufo gidan ya shiga cikin motar suka bar gidan. "where are we going to?" tai tambayar ahankali tana kallon Ya Omari dake driving, juyowa Abdallah yayi yace mata "we are living nigeria to eg.." batama bari ya karasa ba tace "toh ina ya Marwan? Taya zamu bar nigeria bayan he is still in cell?" Tana kaiwa nan tafashe da kuka sosai Omari ne yakira sunanta. "Rahma dont worry he is fine kinji i assure you" kuka tacigaba dayi har suka isa airport bata bar kuka ba. Ahaka sukayi boarding idonta duk a kumbure jirgin su yadaga sama.

Around 6:30 pm na yamma jirginsu ya sauka a garin egyp, wata babban mota tazo ta daukesu daga airport din takaisu wani babban gida...


2days later.
Marwan yadawo gida ya hada important document daya kamata ya hada duk ya hada, ya nemi masu siyan gidan sunzo sun siya yahada kudin yaraba gida uku kashi daya yakai gidan marayu, daya prison, daya kuma hospital, The following day yaje har gidansu na daji daya barma kamal abokin Abdallah da baban shi ya gaidasu yamusu sallama sukamai fatan alheri.

Bayan 5days, he is almost done da koma. Mota ya dauka yaje office na commissioner don yin mishi sallama, luckily for him he meet Abba there.. Sosai Abba ya wani irin rame kaman mai wani cuta, ahakan ma yanxun ya fara jin sauki sosai dan abun yadena mai zafi, sai dai ya dawo shuru shuru, sai kwamissiona ya matsa mai zaici abinci tunani yamai yawa, kullum yana office tare da commissioner, baima damu da company shi ko aikin shiba. Ya kiran numb din mummy don ya bata hakuri taki dauka daga baya number din ma ya daina shigan mishi kwata kwata, yadawo abin tausayi, yakira number su Ahmad da Muhsin su nasu kwata kwata bama ya shiga kaman sun chanza layi, duk inda yasan suna zuwa na gidan kwallo da filin sport amma bai gansu ba, to a ina suke, idan yafara kuka saiyafi hours yanayi, ya dawo so lonely bayida kowa, tunanin princess yatasa shi gaba zai iya bada komi daya mallaka dan kawai yaga princess koda daga nesane. Within this 5day da abunnan ya faru har wani duhu yayi na musamman ya rame ya yamushe, ya lalace kaman wanda yay shekara baida lafiya.


Gaisawa yayi da commissioner yace "Nazo in maka sallama ne in shaa Allah gobe i will be on my way back to my fatherland, thanks for all your care and hospitality we really appreciate, Allah ya bar kauna" Murmushi commissioner yayi yace "its okey, Allah ya kiyaye hanya. My regards to sauran siblings dinka" Godiya yama commissioner ya juya zai fita daga office batare dayama Abba second look ba, har zai fita daga office din sai kuma ya juyo ya kalli Abba daya kuramai jajayen idanunshi yana numfashi da sauri da sauri, sosai yaji tsohon yawani irin bashi tausayin, koma komi ya raini Rahma, kuma yaci darajan Rahma namai kallon mahaifi, ahankali yace "Abba am sorry for All the pains i have coursed you, kayi hakuri kayafe mun, Sannan i really appreciate dukka kokarin dakayi in other to bring my lil sister, my wife Rahma up, babu abunda zan iya cewa sai dai ince Allah ya biyaka, am really sorry and thank you so much Allah ya biyaka, sanan Allah yabaka lafiya" ko dago kai Abba baiyi ba sabida wani irin zafi da zuciyarshi ke mishi, he just wanna cry and cry and cry, he called princess wife, shikenan yarabani da Princess?. Kallon commissioner yayi ganin yanda Abba ke dafa kirji yace "please can you help me with his phone number saboda once in a while indunga kiranshi muna gaisawa" murmushi commissioner yayo tare da bashi number din Abba, yana gama amsa ya musu sallama yafita daga office din. Kuka Abba ya fashe dashi yana dafa kirjinshi yace "shikenan princess, shikenan ya kwacemin y'ata, why why why Nasiru maisa kai mistake dinan, mesa nai yunkurin yin abinda Allah ya hana, nai yunkurin yima yata fyade Allah bai bani iko ba karahema ya jarabceni da sonta sanan yahanani ita, yakuma rabani da ita, I know this is my punishment Ya Allah, Ya Allah natuba wlh, Amma bakomai haka Allah ya kaddara, i loved her with all my heart, no problem thats my destiny, I've accepted that, Ya Allah wherever my princess is please make her happy, let her be happy dats all I want now.." yafashe dawani irin heart melting kukan dayasa kwamissiona share kwalla da sauri ya rungume Abba yana patting bayanshi dan Allah look so pathetic.
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *masu fitarmin da novel su da Allah*

*3107021073 first bank aisha Muhammad zaki turo 300 access fee saiki turomin evidence ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting, you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461*

*A18*

*Eygpt*

Bayan 2 weeks

Ko kadan batajin dadin garin, babu second din dazai wuce da bazata tai tunanin Ya Marwan ba, kome zatayi shi yake Fado mata, da kyar ta iya ta shirya kaman yanda Ya Abdallah ya umurceta, black doguwan riga kawai tasaka ta yafa black vail akai tafito daga dakin tana tafiya ahankali harta sauko kasa, murmushi Abdallah dake zaune afalo yana jiranta yayi yace "yauwa my shagwababbiya sis oya muje, kitso za'ama gashin nan sanan zansa amiki wani milk body scrub da akeyi agarin nan na gyaran jiki, sai amiki red cultural henna ai kinaso ko?" dan guntun hawayen daya zubo mata ta share batare data bashi amsa ba da sauri ya rungumo kafadarta yace "chill jor, wlh karkimin kuka kindaisan nan ba Nigeria bane ba ko hakanan kija akamani Malama, oya shish and lets go" murguda mai baki tayi tare da ture hanunshi daga kafadarta tai hanyar mota da sauri kaman zata tashi sama, murmushi yayi ahankali yace "yarinya yau zakiga mijinki muga karshen kuka" da sauri yakarasa wajen motan ganin yanda ta tsaya tana jiranshi, dariya yayi ciki ciki ganin yanda tai kini kini da rai kaman ta saki kuka, ya bude mata kofa ta shiga ya zagaya ya bude dayan bangaren ya shiga yatada motar yaja motar suka bar gidan.

Wani ubansu spa ya kaita, har office din manager ya kaita yabiya kudi mai yawa, da harshen larabci yay maganan dan bayason taji yace "a gayarata gyra bana wasa ba dan yau mijinta zai dawo, duk wani abu daya kamata kimata kiyi sanan amata kitso da lalle, ko kudin bai isaba zan tafi yanzu dazaran an gama mata saiki kirani nazo" murmushi manager tayi tace "shikenan angama sir, zamu mata presidential first class gyara" juyowa yayi ya kalleta yanda har lokacin idanunta ke cike da ruwa tana kallonsu, wayarshi yaciro daga aljihu ya mika mata wayarshi yace "gashi ki rike incase, zanje nadawo insun gama zanso na nadaukeki, bye" hannu ta dagamai yajuya yafita daga spa, manager kuma ta kaita wani room of one aka fara mata gyaran gashi aka wanke gashin dawani irin ruwan turare da ita kanta jitayi kaman ta suma sabida tsabagen dadin kamshin aka wanke gashin tass dayay kaman an tsomashi a ruwan turare akai drying sanan aka fara mata kitso yan manya amma masu kyau bana wasaba, aka fara mata wani irin jan lalle da bata taba ganin irinshi a Nigeria ba, saida aka gama kitson tass sanan aka karike lallen aka wanke mata sai kallon hannuwan nata take yanda suka mata kyau kaman ta lashe, wani abu aka gunguro aka shigo dashi dakin wayansu gorunan fruit juice kusan uku aka bude aka bata akasa ta sanye hakanan ta sanye tana lashe baki dan wlh dadi sosai sai wani nono da aka bata shima tasha mamaki ta dinga yi tace "shi spa dinnan har fruit juice suke bayarwa" saida suka bata magungunan dake sa mace dadi dakuma kara ni'ima da jukuwa ta sanye duka sanan suka fara mata gyaran fata bayan sunyi steaming Hq, sosai suke mata gyaran jikin tun daga yatsun kafa har fuska dan kayama akasa ta cire aka bata wani white towel ta daura, aka mata waxing, scrubbing wata tsiya ce duk saida aka mata, aka mata sauna bath, aka mata tsuggunno nawani turare mai kamshi, gyara aka mata irin wanda akema amarya dan Abdallah yabiya su da kyau saisa sukai mata mai kyau suma, aka gasa mata jiki da turare wanda zatai watanni tana kamshin, ita kanta saita fara son jikin nata sabida yanda tayi, fatarta nada tushi amma saiya kara wani extraordinary taushi kaman newborn baby, saida aka gama komi sanan aka kawo mata wani abu kaman pepper soup kaman miya akasa taci taci dan da dadi ba laifi sanan akasa tai bacci akan wani machine dake massaging jiki ahankali aka kashe wutan dakin aka rufo mata kofa, sai bayan asr ta tashi aka sake mata wani wankan turare aka turara ta sanan aka barta tai salla sanan aka cigaba ita kanta jitayi tana wani irin cikowa ta kasa mamaki tayi me akeyi mata haka takeji wani irin sai bayan magrib suka gama komi tsaf, data kalli kanta amadubi saida tasaki baki tana kallon kanta dan wani irin glowing take da shining bana wasaba ga kanta wani irin kamshi yakeyi ba kadan ba, kitson ya mata kyau sosai goshinta sai shining yake irin na sabon kitson nan, light makeup aka mata dan Abdallah ya turo text a mata sanan aka kawo mata wani new doguwan riga irin nasu tasaka black da fari bakaramin kyau tayiba kaman wata balarabiya, Isha tayi kasancewan tanada alwala kowani motsi zatayi wani irin daddaddan kamshi take da ita kanta so take ta dinga shinshina kanta, shigowa dakin akayi hakan yasa ta dago kanta balarabiyar tace "your brother is here" tashi tayi tabi bayan matan suka fito kafeta da ido Abdallah yayi wani irin dadi na lullube shi yana wasa kanshi aranshi yace "wlh Ya Marwan zaka ganene, sainasa kazama bindin lil sis, ha'a kai thank you Instagram a Instagram naga anama mata gyara idan zasuyi aure ai haka duk week zan dinga kawota ana mata" wani irin taune lips dinshi yayi yana rolling eyes dinshi still looking at her yace "wow wlh I tried jibi sis Ya Marwan sunanka sorry, you're a goner, ai wlh zaka dawo zanin daurawan lil sis ne dan kaji" yay wani irin murmushi "wai wat is it? I look funny bari ma naje a goge makeup din" da sauri yariko hanunta yana hararanta yace "ke dalla chan kinsan nawa nabiya? Let's go jor, kuma kome Ya Marwan yabaki tare zamu raba" da sauri tana kallonshi tace "Ya Marwan?" da sauri yadan sosa kai yana daure fuska yace "eh mana once an sakeshi ba lawyer my yace next month za'a sakeshi ba, muje ya Omari yahada dinner and d food is yummy" yaja hanunta dan bayaso takara jefomai wata tambaya, suka fito yay wajen motanshi yabude ta shiga ya zaga ta dayan bangaren ya shiga kafin ma yatada motar wayarshi tahau kara da sauri ya ciro daga aljihu screen din ya kalla ganin sweetest bro yasa yay picking yana satan kallon Nadeera dayaga ta lumshe ido kaman mai shirin yin bacci dudda ba bacci takeji ba dan tasha bacci sosai a spa, baima bari yay magana ba yace "Boss chill mana wlh saima nafasa kawo ta atoh" kawo ta dataji Abdallah ya ambata yasa tabude idanunta tajuyo ta kalleshi, dan murmushi Abdallah yayi yana lakatan hancinta ahankali yace "we're coming to" katse wayar yayi ya maida aljihu ahankali tace "waye Ya Abdallah?" batare daya kalleta ba yana kunna mota yace "Ya Omari ne yawani dameni wai wani irin saloon ne ake kaiwa har dare haka" mayar da kanta tayi jikin kujera tace "wai haka spa din garin nan ake bama mutum kayan dadi? Sau daya nataba raka Mum spa kuma ai banga an bamu kayan dadi kaman nan ba" da sauri Abdallah while driving yace "Allah Rahma baby? Haka suka baki kayan dadi? Yanzu ai kome kika samu tare zamu dinga rabawa ko my shagwabatu?" hararanshi tayi yacigaba da tuki yana wani irin jin nishadi har suka kai anguwan su, yay horn mai gadinsu ya bude ya shiga da motar ciki yay parking suka fito suka jero tana tafiya ahankali ya kalleta yace "wat is it Rahma?" dan yatsine fuska tayi tace "am feeling somehow" bude kofa yay ya shiga tana biye dashi itama tana tafiya ahankali Ya Omari kadai suka gani a falon yana aiki da system akan dining ya kafesu da ido yana kallon su kafin ma ta gaidashi yace "kun dawo sis?" murmushi tamai mai kara mata kyau tace "eh Ya Omari, ina yini" kannemai ido Abdallah yayi hakan yasa Omari yace "fine je sama kihuta, shower ki sauko kasa kiyi dinner" kaman zatai kuka sabida kuncin datakeji tace "am not hungry naci abinci achan, I just want to sleep" murmushi yamata yace "shikenan sweetheart gud night" ahankali chan kasa tace "yea gud night" tai hanyar stairs tafara hawa kaman mara jini har saida takai karshe sanan Abdallah yace "Rahma look ur bracelet" da sauri ta juyo tace "Ya Abdal..." kasa karasa maganan tayi sabida ganin Ya Marwan da tayi zaune a tsakiyar falon kan kujera hanunshi rike da remote yana kokarin chanza channel, tundaga kafarshi ta shiga kallonshi yana sanye cikin wani hadadden white hermes sandals dayama farar kafarshi mugun kyau, ga white fararen farcenshi dake nan agayre, yasanya black 3quater na maza daya wucemai gwuiwa da kadan sai wani sky blue V-neck t-shirt daya kamashi sosai ya fito da cikan wide chest dinshi dakuma manyan muscles dinshi da jijiyoyi suka fiffito, hanunshi daure da wristwatch black, gashin kanshi nawani irin kyalli sunyi curls sosai sai uban kamshi yake yakara wani irin kyau da haske kodan ta dade bata ganshi bane oho, shi kanshi he's dying to go and hug her but he just wanna see her reaction, yanaso yagane kotafara sonshi, he missed her so much, he missed everything about her, her smile, her cry, her warm breath, her touch, her smell, the way she talk, how cigaba da danna remote din yayi yana chanza channel while trying to control his breath.

Wani irin nishi tayi heart dinta na beating very fast tana kallonshi ko kyafta ido batayi, gani take kaman bashi bane mafarki takeyi, hawaye ya cika idanunta sosai, cikin rawan murya tace "Ya...Mar..." kasa karasa kiran sunan tayi tawani irin taho da gudu tana saukowa daga stairs din kaman zata fadi tsabagen sauri tana kallonshi, shima kasa daurewa yayi saida ya juyo da kanshi ya kalleta yanda take saukowa da gudu jiyayi yana fizgarshi ahankali ya mike tsaye ya kafe ta da ido wani irin sanyi na shigan shi kaman yaune yafara ganinta, dawani irin gudu tazo wajen tana kuka sosai ta tsaya agabanshi ta daura hannu a ido tana kuka sosai kaman wata karaman yarinya tana murza idanun. Hada hannu Abdallah yayi kaman mai addu'a shi kadai yana kallonsu yana magananan xuci yace "hug him lil sis, hug him sisto na, wayyo Allah na give ya Marwan the hug of his Life, hug him hug him jor, wayyo hug him tight baby sis" kaman taji me yace ahankali ta zare hannun daga fuskarta ta kalleshi shima ita yake ma wani irin cool look batare dayay uttering any word ba, wani irin fashewa tai da kuka mai kara jikinta na rawa kafin ta taho dawani irin gudu tai wani irin jumping tafada jikinshi ta kankameshi ta daure kafafunta ta bayanshi tasa kanta awuyanshi hannayenta abayanshi tana kuka sosai, wani irin ihu Abdallah yayi aranshi yace "I don die, wai wai wai ya ilahi! lil sis don't kill Ya Marwan dinmu fa ewoo, dis kind hug aii..." hanunshi dayaji an fizga yasa yadago kai Ya Omari ne yadure fuska yajashi yabude kofa suka fita daga shashin sukai hanyar shahinsu kaman zaiyi kuka yace "me haka Ya Omari inacikin kallon show ni gaskiya kumin aure nima i want my woman to hug me dat way" jan kunenshi Omari yayi hakan yasa yafashe da kukan karya yace "wayyo Allah Ya Omari kunennafa kaifa mugu ne wlh ka sakenmin kunne to" "baza asaka ba wuce muje kayi bacci, naughty fellow."


Sosai take kuka a wuyanshi hawayen ta na gangarawa kirjinshi tana rungume dashi kaman za'a kwace mata shi tace "Ya Marwan am so sorry, am sorry is all my fault, I shouldn't have done wat I did da yanzu bakai going through all this trauma ba, am sorry..." ahankali ya ciro fuskarta daga jikinshi yana wani irin kallonta sabida kyan datamai gawani irin hadadden kamshi datake dat is driving him crazy kaman yahadiye ta, kasa magana yayi saima sauke ajiyan zuciya daya dinga yi yama forehead dinta deep kiss yana kallon long eyelash dinta, murya chan kasa yakira sunanta kaman wani mara lafiya. "Sugarlips" hanunta tai wrapping around his neck da kyau tana kara daure kafarta gam abayanshi dan yanda yakirata jitayi tana neman sakinshi tafadi kasa, ahankali itama kalleshi da idanunta dake cike da hawaye tace "Ummmm" yanda tai da baki saida yasaki ajiyan zuciyan dabai shirya yakafe lips dinta da ido, dawata irin shakakkiyar murya dat is so down yace "I missed you so much wife" murmushi tamai adan kunyace dan yanda yake wani irin kallonta da yanda yake shafa bayanta yasa tafara kokarin sauka kasa sabida jikinta yafara wani yam yam, riketa yayi gam yana make mata kafada alamun bazai saketa ba kaman wani yaro, yana wani irin kallonta yacigaba da shafa bayanta gently tana kara rikeshi har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login