Showing 42001 words to 45000 words out of 207756 words

Chapter 15 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

661

kallon mahaukata. Yo inba mahautaba taya zasuce Taura da kansa, mutum lamba na biyu a masu kuɗin africa, na ɗaya a NAYA yazo nan domin su kawai.
    Shidai Doctor Shamsu rasama yanda zaiyi yay, sai dai cikin ikon ALLAH yana tunanin miye mafita sai ga Bappi ya kirashi. Cikin rawar jiki ya ɗauka, ya kora masa bayanin halin da ake ciki. Murmushi kawai yayi da cewa, “Karka damu ina zuwa”.
    Idanu Dr Shamsu ya ɗan kwalalo da hangame baki na mamaki, sai dai kafinma yace wani abu Bappi ya yanke wayar.



      Bappi ya ajiye wayar yana duban Ramadhan dake gefensa yana shan furar da Bappin kesha shima, tun wayar farko da yayi Anne ta tambayi lafiya ya mata bayani, amma duk da Ramadhan ɗin na'a wajen ko tari baiyiba, furarsa kawai yake sha yana sarrafa lap-top ɗinsa kamarma baya a wajen.
          “Ramadhan!”.
Bappi ya kirashi a hankali.
     Ɗago nutsatstsiyar fuskarsa yayi mai ƙarancin hayaniya yana kallon Bappin, kafin yace wani abu Bappi ya taresa da faɗin, “Tashi muje ka kaini TK hospital”.
        Tuni ɗan sakewar fuskar tasa ya ɓace, sai dai kuma babu damar yin gardama, dan shima Bappin ya tsuke tasa fuskar. Cikin marairaicewa ya maida dubansa ga Anne tamkar zai fasa kuka.
      “Ni miye nawa kake kallona. Koni nace ka kainin?”.
    Ɓata fuska ya sakeyi da janye idanunsa, batare da yace komaiba ya kashe lap-top ɗin ya miƙe, jacket ɗinsa baƙa mai ƙyalli dake ajiye saman kujerar gefensa ya ɗauka ya ɗora saman baƙin wandonsa da baƙar t-shirt, yanda t-shirt ɗin ta kama jikinsane yasa ƙyawunsa da yanayinsa na mutum mai tu'ammali da motsa jiki ya bayyana. Sosai sumar nan tasha gyara yau sai ƙyalli takeyi. Ɗan corridor ɗin dake hanyar bedrooms ɗin Anne ya nufa, ya buɗe wani ƙaramar drawer na glass da aka saka domin ado kawai ya ciri key batare daya duba na wace mota ya ɗauka ba. Dan duk keys ɗin motocin da suke amfani dashi anan sashen nanne wajen ajiyarsu.
     “Furar fa!?”.
Anne ta tambaya lokacin da Ramadhan ɗin ke ɗaukar p-cap ɗinsa zai ɗora saman kai, dan yasan Bappi sai yayi magana akan gashinsa.
       Hular ya gyara ta rufe masa fuska sosai, ciki-ciki yace, “Na ƙoshi”.
    A yanda yay maganar Anne tasan a ƙufule yake, dama yaya lafiyar giwa. Tunda akai masa zancen mulkin nan da aure ƴar sauran fara'ar fuskar tasa ta ɓace ɓat duk da shi ba mutumne miskili ba, maganarce dai sai ya zaɓa da wanda yay niyyar yi saboda jin kansa da yay gado gurin uwa. Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan daga gaisuwa babu ruwansa da kowa a gidan. Gashi kuma Ramadhan yayi mugun tsanar driving a rayuwarsa, ita da Bappi ne kawai ke shigar masa hanci akan ya tuƙasu ko yanaso ko bayaso. Amma daya tuƙa mota ya gwammaci ma ya hau mashin, shiyyasa mashina ɗinsa kusan uku a gidan.
      Duk da yanda yaga bayan motar daya ɗakkoma key tayi ƙura haushi ya hanashi komawa ya canjo key. Sai Alu ya ƙwalama kira akan yazo ya fidda masa ita daga runfa. Lokacin da Bappi ke fitowa cikin jallabiya dan bai canja kayaba hula kawai ya sanyo saboda yamma ce garin yayi luf da alamar hadari. Ramadhan dake amsar motar a hannun Alu ya miƙa hannu ya buɗema Bappin gefensa, dan yasan in har shine zai tuƙasa a mota baya zama baya.
     Koda Bappi ya shigo komai baice masa ba ya ɗaura belt tamkar yanda Ramadhan ɗin ke ƙoƙarin saka nashi, dan shi ƙa'idarsa indai zaiyi tuƙi baya ƙin saka belt ɗin, dan mutum ne mai tsananin son bin doka koda ace sauran ƴan ƙasa na mata riƙon sakainar kashi.
         
               ★
  
   Tunda motar ta shigo Doctor Shamsu ya fahimci su bappi ne, sai ya zare jikinsa da ga wajen hayaniyar ya nufesu. Shine ya buɗema Bappi ƙofa ya fito, zai risina domin gaisheshi Bappi ya hana ta hanyar riƙo hannunsa. Cikin kunya da girmamawa Dr. Shamsu ya yarda suka gaisa, kafin yace, “Ranka ya daɗe sun riga sun tara mutane, ina ganin muje daga ciki sai na shigo da su”.
      Bappi baiƙi hakan ba, dan daga inda yake yana hango yanda M. Dauda da abokinsa ke zazzaga masifa ga mutane da securitys ɗin asibitin zagaye da su. Wasu na musu kallon mahaukata wasu na dariya, wasu najin daɗin abinda sukeyi na yaɓa magana ga Alhaji Hameed Taura.
      Ramadhan da baida niyyar fitowaba sai ya kwantar da kujera ma abinsa ya lumshe idanu tare da ƙara ƙarfin a.c dan garin yay luf-luf dayin dumm alamar hadarine, sai ɗan zafin ya bada yanayin jinsa a cikin jiki kawai.
        
      Da ƙyar Dr. Shamsu ya lallaɓa su M. Dauda zuwa office ɗinsa. Sai dai duk wani iya shegen da suka shigo da shi suna cin karo da fuskar kamala ta dattijon arziƙi Alhaji Hameed Harith Taura ya gudu. Cikin ɗan rawar jiki suka zube a ƙasa tun daga ƙofar office ɗin. Ɗan murmushi yay musu yana girgiza kansa. “A'a haba kutashi ku ƙaraso Please”.
      “Ranka ya daɗe nan ma ya isa”.
Suka faɗa cikin haɗa baki.
   “Bazai yuwu ku zauna anan ba, kuyi haƙuri ku ƙaraso.”
         Dole suka miƙe domin cika umarninsa. Bayan sun zauna Bappi ya tura musu ruwa da lemon da Dr. Shamsu ya ajiye masa. Suna ƙwaɗayin sha sunajin kunya, dan haka suka dai daure da ƙyar suka haɗe yawunsu na ƙwaɗayi. Hannu Alhaji Hameed ya miƙa musu, nan ma suka shiga nannoƙewa sai da yay da gaske suka yarda suka bashi nasu hannayen suka gaisa. A zukatansu sai yaba laushin hannun wannan tsoho suke, koda yake gidan kuɗine fa da kansa.
         “Alhmdllhi Doctor ya kirani yaymin bayanin komai game da zuwanku nan, kuyi haƙuri ba'a hanaku shiga gareta bane dan baku isaba, kawai dai saboda tsaro ake taka tsantsan, gashi kuma bamu da tabbacin abinda kuka faɗa ɗin...”
      “Wlhy ranka ya daɗe ni mahaifinta ne, ama ɗauka hotona a nuna mata”. M. Dauda ya faɗa cikin zillo yana katse Bappi.
     Murmushi Bappi yayi, dan shima dai yaga yanayin jini, sai dai taba data cinye M. Dauda ɗinne ya ɓadda ainahin kamanin nasa da Raudha.
     “Ai bama sai ankai ga nan ba. Yanzu bara muje ɗakin kawai”.
    Kafin ma Bappi ya miƙe su har sun fice, ya ɗan girgiza kansa yana murmushi dan dariya suke bashi. Suna abune tamkar wasu firgitattu...........✍


https://arewabooks.com/chapter?id=629a77b967809ad6daab2109






*_Chapter 13_*


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*



Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/8, 6:03 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_Episode 17_*


............★Raudha na zaune yau an cire ƙafar tata a jikin ƙarfen dan kumburin ya sauka sosai, maimakon tayi ramar ciwo sai ta ƙara haske da ƙyau saboda samun canjin waje, ga abinci mai ƙyau ga a.c.
     Idanu taɗan waro saboda mamakin ganin mahaifin nasu, cikin rawan baki tace, “Abbanmu!”.
    Wannan kawai ta isa amsa ga bappi, dan cike da zumuɗi shima M. Dauda ya nufa gadon yana ware hannuwa wai zai ringume Raudha irin na turawa kar Bappi ya rainasu yaga su ƴan ƙauyene basu iya tattalin ƴaƴa ba. Sai dai kuma tunkan ya ƙaraso Raudha tai saurin ɗaukar filo ta tareshi tana faɗin, “Abbanmu lafiya?”.
     Sosai dariya ta nema kufcema Bappi, yay ƙoƙarin kauda kansa yanayi ƙasa-ƙasa. Dan M. Gambo ya matsa da sauri ya ɗirkama M. Dauda dundu a baya. “M. Dauda ka nutsu mana miye haka zaka zubar mana da mutunci”.
      Harararsa M. Dauda yayi, cikin yin ƙasa da murya yace, “Kai baka gane ba, idan ba'ayi hakan ba ai sai attajirin nan ya ɗauka bama kula da ƴaƴanmu, kasan su haka sukema ƴaƴansu kamar larabawa da turawa. Ko so kake yay tunanin dan munga sun raɓesune muka fara son su”.
     “Eh kumafa hakane kayi gaskiya, sai dai kasan Raudhatu ustaziya ce bazata yarda ba fa, karma kaja ta bamu kunyar datafi wadda muke gudu”.
     Duk zancen nasu sarai Bappi najinsu duk da a hankali sukeyi, dan shi ALLAH ya bashi ƙarfin ji, zama a iya cewa a wajensa Ramadhan ya gado ƙarfin ji, ko yaya kai magana kusa da su sai sunjika da izinin ALLAH, dan haka yay saurin katsesu dan karsu kasheshi da dariya. Ya gyara tsaiwarsa dayin gyaran murya yana faɗin, “Ya kamata ku dubata sai muje muyi sallar magrib, na kuma san masaukinku......”
     Kafinma ya kai ƙarshe M Gambo ya katsesa da faɗin, “Ai bamu da wani masauki yallaɓai, dan shi M. Dauda ya rabu da gyatumar tata shiyyasa ta taho nan ita da yaran wajen tata gyatumar. Dama yanzu haka munzo biko ne da duba jikin Raudhatun”.
        Raudha dake jin tamkar ta fasa ihu dan takaicinsu ta kauda kanta gefe idanunta na tara ƙwalla. Tana son mahaifinta, tana kuma fatan ya nutsu ya bar duk abinda yakeyi na ashsha, sannan sam bata baƙin cikin nunasa matsayin uba dan bata da kamarsa..
     Bappi yay saurin dakatar dasu, “Ok ok babu damuwa muje muyi sallan first dai yanzu, sai musan abunyi kamar zaifi”.
    Badan sun so ba suka bisa. Dan gaba ɗayansu idonsu nakan Haɗaɗɗun kulolin abincin dake gefen gadon Raudhan. Sai haɗiyar yawu suke tunkan suga abinda ke a ciki.

     Suna fita doctor na shigowa. Hakan yasa Raudha roƙonsa aron waya dan gara ta kira Mommy ita kam bazata iya da halin Abba ba. Shima Dr Shamsu ya gamsu da hakan, dan haka babu musu ya bata ta saka number Mommyn, cikin sa'a kuwa bugu ɗaya aka ɗaga. Wani daɗi ya kama Asabe saboda jin muryar Raudhan Alhmdllhi, duk da dai da safe sunzo asibitin dubata ita da Aunty Hannah ma.
      “Mommy dan ALLAH kizo asibiti wlhy Abba ne yazo shida baba Gambo”
     Zumbur Asabe ta miƙe har tana neman yadda zani. Shi dauda ɗinne yazo Bingo harma asibitin da kike?”.
     “Wlhy kuwa mommy gasu ma tare da baba alhaji (Bappi take kira haka). Yanzu ya jasu suka tafi massallaci”.
     “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Ashe kuwa zanci kaza kazan ubansu a garin nan. Ni yanzu babbar matsalata baza'a barni shiga asibitin ba....”
        “Mommy dan ALLAH ki kwantar da hankalinki banga abin faɗa anan ba. Kizo asibitin Doctor zai shigo dake yace. Amma mommy dan ALLAH karki tayasa kuyi rikici Please”.
    Tai maganar tamkar zatai kuka. “To” kawai asaben tace mata ta yanke wayar, badan tasan zata iya bin maganar Raudha ɗin ba.

*_BINA STATE PLACE_*

           “Ranka ya daɗe bakace komai ba”.
   Fulani ta faɗa a hankali cike da ƙasaita tana duban mai-martaba dake kishingiɗe a tsakkiyar falon hutawarsa da ko iyalan nasa ba kowacce keda ikon shigarsaba sai Fulani kawai.
       Bai motsa ba, sai dai ya saki wani murmushin ƙasaita irin na manya, masu kuma ji da girman mulki. Kafin ya ɗago idanunsa ya ɗan dubeta ya ɗauke kansa.
      “Wai miyasa ku mata a koda yaushe baku da hangen nesa ne? Yanzu banda dai son neman magana miya kawo zancen haɗa Aina'u da Ramadhan aure? bayan kunji Alhaji Hameed ya zaɓa masa mata...”
        “Humm mai-martaba kenan, ni a ganina ai hakan ba wani abu bane, ƙara danƙon zumincine, ka tuna fa Ramadhan shine jikanka na farko namiji a gidan nan, da ace shi ɗin ɗane da namiji ya haifa ba mace ba shine kamarfa magajinka a yanzun, amma sam yaron nan baya son zama cikinmu, akoda yaushe sai dangin ubansa saboda Firdausi ta gama shanyesa su kaɗai yake gani ita da mijinta, amma idan muka haɗashi aure da Aina'u ta tayamu yaƙin jawosa jikinmu ai muma ka.......”
        “Ya isa dan ALLAH. Yanzu nan Wasila bana hanaki irin wannan zancen ba? Yanzu miye abin asiri dan Ramadhan yafi buƙatar ya rayu a gidan su?. Karfa ki manta can ɗin shine adonsa, kuma shine tunƙahonsa, to bana son ƙara ji, hakama maganar haɗasa da Aina'u inhar ba sune suka sasanta junansu ba bana buƙatar sake jinta. Dan har abada Alhaji Hameed bazai saka doka na karya masaba koda akan ƴaƴana ne balle jikansa da yake da iko da shi tamkar yanda yake da iko akan mahaifinsa. Kuyi masa fatan alkairi kawai ku tsaya matsayinku”.
       Fulani ta taune lip ɗinta da ƙarfi da haƙora kamar zata hudashi, sai dai sanin halin mijin nata yasata sakin ɗan murmushin yaƙe da cewa, “To shikenan ranka ya daɗe, yanda kace ai haka za'ayi insha ALLAH anbar zancen. Dama can rashin zama nayi nazarine akan batun shiyyasa ban fahintaba.”
        “Haka nakeso ki kasance. ALLAH yayi muku albarka baki ɗaya”.
     Da ƙyar fulani ta daure ta amsa tana haɗiyar zuciya. A ranta ko abubuwa masu yawa take kitsawa gameda kowacce shegiyar yarinyace zata aure mata jika sama taka.

(Hummm Fulani kina kaka inaga gimbiya Su'adah uwar miji. To maji yaya za'a kwashe to😜🏃).

___★____★___

         *_BINGO CITY_*

   
     Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Asabe da M. Dauda lokacin da akai kici-ɓus. Dan kuwa dai doctor Shamsu da kansa ya shigo da Aunty Hannah da Asabe, shigowarsu babu jimawa kuma Bappi da su M. Dauda suka dawo ɗakin domin yin sallama da Raudha.
       Asabe ce ta fara janye idanunta tana jan tsaki, hakan yasa M. Dauda da jikinsa ke tsuma da sabuwar ƙaunarta matsowa kusa da ita cikin ɗan rawar jiki. “Haba Asabe nine fa Dauda ɗinki, dan ALLAH karkiyi fushi dani wlhy sharrin shaiɗanne”.
        Hannunsa dake neman taɓata ta buge tana faɗin “Kaine sheɗan ɗin kanka ai macuci kaw......”
      “Mommy Please!!.....”
Raudha ta faɗa tana fashewa da kuka dan tasan komai zai iya faruwa akan iyayenta na raba hali. Asabe zata sake magana Bappi daya fahimci su ɗinne iyayen Raudha ɗin yay saurin dakatar da ita.
            “Inaga nan ba wajen magana bane, kamar zaifi muyi haƙuri muje daga waje ko masaukinku ko? Ko kuma mu bari zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.....”
       “A'a dan ALLAH ranka ya daɗe gara ayita yau ta ƙare, idan ta bar nan bazata sake yarda na gantaba, zama ta iya sace Aminar daga nan ɗin itama”.
     Harara Asabe ta balla masa, sai dai riƙe hannunta da aunty Hannah tayi ya sata yin shiru ta haɗiye abinda taso faɗa.



     A tare suk rankaya gidansu Asabe, sai dai Bappi motar Dr Shamsu yabi yace Ramadhan ya koma gida, dan sanda suka fito barci ya samesa yanayi a cikin mota, ya sanshi da barcin wuri, dan shi ƙa'idarsa da tara na dare tayi to ya kwanta kuma. Sai dai kwana biyun nan daya tsinta kansa a NAYA hakan bai kasanceba, shiyyasa daya ɗan kaɗaice sai ya kama barci saboda tsabar buƙatarsa da yake yi.
      Rikicewa sosai Hajiyar Birni tayi da ganin Alhaji Hameed Harith Taura har cikin gidanta. Mutumin da bata taɓa tunanin koda ganin motar hawansa ba a hanya balle shi kansa. Babban abinda zai birgeka da shi babu wani damuwa ko tsantsamin gidan tare da shi, hasalima da aka kawo ruwa shine ya fara sha tare da godiya.
     Su M. Dauda dai an nutsu saboda hararar da Hajiyar Birni ke antaya musu tamkar ƙwayar idonta zai fito.

       “Kuyi haƙuri da lattin zuwan gareku matsayin wanda ƴarku tai kasadar bama kariya. Da farko dai naso ace sai ta samu lafiya zanzo da kaina na kawota gareku nai muku godiya na kuma baku haƙuri. Sai dai an samu akasin hakan a dalilin zuwan waɗan nan bayin ALLAH da ayanzu na fahimci shine mhaifin *Raudhat*. Duk da dai na haɗu da ita mahaifiyarta a aaibiti tun randa abun ya faru, hakama ku da bansan matsayinku garetaba har yanzun. Zanyi amfani da wannan damar domin neman afuwarku, ku gafarceni, da nasan Raudhat zatayi wannan kasadar domin ni tabbas zan dakatar da ita, sai dai masu iya mafana kance ƙaddara ta riga fata, sai muce ALLAH ya bata lafiya ya albarkaci rayuwarta. Ku kuma kuyi haƙuri ku koma tare dan na fahimci baƙwa tare da juna, kuma Raudhat batajin daɗin hakan”.
          Kafin kowa yace wani abu hajiyar birni ta amshe zancen cikin washe baki. “Ai muke da godiya ranka ya daɗe, ALLAH ya saka da alkairi bisa kulawar daka nuna akan Raudha, dan bamu taɓa zaton hakan ba. ALLAH ya kara lafiya da nisan kwana. Suko babu sauran aure a tsakaninsu dan saki uku ne yallaɓai......”
        M. Dauda yay wata zabura tare da fashewa da kuka. “Ni wlhy ina son matata kuma a bincika ba'a cikin hayyacina na saketaba ranka ya daɗe...”
       “Eh wlhy wani malami yace asiri Larai ta maka ai”. M. Gambo ya amshe zancen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login