Showing 177001 words to 180000 words out of 207756 words
Miya faru da shi?. Waɗan nan sune jerarrun tambayoyin dake mata yawo bisa kai. Sai dai ta kasa furtasu ga kowa.
Anne da tasan lokacin barcin Raudhan ya gota cikin sanyin murya tace, “Ameenatu kije ki kwanta kinga kema fama kike da jikinki. Tunda Alhmdllhi da alama komai ya dai-daita barci ne ya ɗaukesa. Kamar Raudha zatace a'a sai kuma tay yunkurin mikewa domin bin umarnin Anne. Caraf taji an ruƙo mata hannu, bama ita kaɗai ba kowa a ɗakin sai da ya kalli hanun Ramadhan ɗin, kafin ya firta. “Ameenatu ruwa! Bani ruwa na sha inajin ƙishi”.
A hankali yake maganar amma hakan bai hanasu jinsa ba. Raudha duk kunya ta isheta. Amma saita daure ta dauka goran ruwan dake kusa da Anne, a sanyaye tace, “Ga ruwan to buɗe idonka”.
Bakinsa kawai ya buɗe mata yana ɗan girgiza kansa, kamar zata sake magana sai kuma Bappi ya dakatar da ita ta hanyar ɗago kan Ramadhan ɗin yanda zata iya zuba masa ruwan batare da ya cutar da shi ba. Duk da kunyar da takeji haka ta daure ta ɗora masa gorar a baki. Sai ko gashi yana zuƙarsa da yawa harya shanye. A hankali ta janye goran shi kuma ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonta. “ALLAH yayi miki albarka”. Ya faɗa a hankali tare da maida idanunsa ya lumshe.
Kusan atare duk suka amsa da amin tare da sauke ajiyar zuciya. banda Raudha datai kasa da kanta ta amsa a kan laɓɓa. Bappi ne ya basu umarnin zuwa su kwanta, shi kuma zai kwana da Ramadhan ɗin sugani ko zuwa asuba zai dawo hayyacinsa su samu ya koma can government house kafin a farga. Dan sun tabbatar fitar ɓadda kamar daya sabayice yayo yau ɗin ma.
Badan Raudha taso ba ta mike. Koda suka isa ɗaki Anne wanka ta sakatayi, ta bata tea tasha kamar yanda ta saba turketa a duk dare kafin ta sakata kwanciyar dole. Sai dai ta lumshe idanune kawai badan barcin ba. Amma ita kanta tasan idan tace zatai barci a irin wannan halin yaudarar kanta zatai kawai...
A ɓangaren su gimbiya Su'adah kam kowa tunda baiga Ramadhan ba sai hankalinsa ya karkata akan Addah Asma'a da suka samu a kasa wanwar. Ruwa aka bata tasha, aka kuma dagata zuwa kujera sannan suka shiga mata sannu. Bayan numfashinta yaɗan daidaita Gambiya Su'adah ta sallemsu su duka falon ya rage daga ita sai Adda Asmah da Aynah.
“Adda inaga kuje gida zanzo da safe na sameku, dan zamanku yanzu anan akwai matsala zai iya fargar da jama'ar gidan wani abu. Su kuma ku barni dasu game da Ramadhan zanma tufƙar hanci”.
Addah Asmah da ba fahimtar komai takeba a yanzu gudun kar gimbiya Su'adah ta ɗagota ta jinjina mata kai ko maganin da suka kawo ɗin bata samu bata ba suka fice cikin taraddadin da ƙaulani. Numfashi gimbiya Su'adah saukewa, kafin ta nufi sashen su Anne. Sai dai tana tu karowa taji sautin karatun Raudha da Pa. Wani irin kunci da duhu zuciyarta ta sake shiga najin tsantsar tsanar Raudha da batasan yaya akai tazo gidanba ya riketa. Tunanin ko dama tare da Ramadhan sukazo ya sata juyawa ta fasa shiga baki ɗaya ta koma sashenta tana haɗiyar zuciyarta data cika kirjinta fam kamar zata fashe.
★_★★____________★★_★
Da asubar fari Bappi ya fita raka Ramadhan government house, kamar yanda ya fita ta barauniyar hanya yanzun ma tanan yabi da taimakon odilan nashi da shi kaɗai dama yasan da fitar. Tunda yaga bai dawo akan lokaci ba hankalinsa yake a tashe. Shi kansa yasan irin waɗannan fitar da shugaban ƙasar keyi akwai haɗari a cikinta. Sai dai shi ko'a jikinsa. Ko'an nuna masa illar fitar ɓadda kamar baya nuna damuwa ko hango wata matsala. Amma har cikin rai odilan ɗin nasa na tsoron randa wani zai farga a cikin gidan ko waje.
A taura house kam koda aka wayi gari babu wanda ya tada zancen. Musamman daga sashen Anne. Ita kanta gimbiya Su'adah tana son ma Pa magana tanajin tsoron a yanda ya tashi yau fuska kamar hadarin gabas. Amma har cikin rai tana buƙatar jin halin da yaronta ke ciki. Ta kira wayarsa amma ba'a ɗaga ba, ta rasa inda zata tsoma ranta ta huta har baƙi dai suka fara isowa irin su Safina da tawagar ƴaƴanta. Sai daga masarautar Bina kuma.
Zuwa Azhar gidan ya fara ɗaukar baƙi sosai. Hakan ne ya tilasta Gimbiya Su'adah fasa fita gidan Addah Asmah dan tun jiya da suka bar gidan bataji daga garesu ba. Ta kira duk wayoyinsu a kashe. Ta aika Muneera ta dawo ta sanar mata Aynah da Addah basa gida wai tun safe suka fita baƙi ma daketa isowa babu wanda ya samesu a gidan sai ma'aitan gidan keta saukesu. Wannan zance ya sake tada hankalin gimbiya Su'adah matuƙa dan haka ta kira fulani da suke shirin tahowa da yamma ta sanar mata. Duk da fulani tasan komai sai ta ɓoye mata akan ta kwantar da hankalinta zata bincika. Amma tasan Addah Asmahn bazataje wani waje ba daban. A sanyaye tace to.
Fulani ta sauke wayar tana taɓe baki. Dan yanzu sun ƙudiri aniyar daina faɗa gimbiya Su'adah komai akan shirinsu. A ganinsu sakacintane ya lalata komai a daren jiya kokuma akwai abinda take son gujemawa. Itako fulani burinta da alwashinta sai ta nunama Anne ba itace kaɗai keda iko da Ramadhan ba, yayinda Addah Asmah ke nuna itama shine burin nata. Sai dai acan kasan rai ba haka bane. Baƙar hassadar ƴar uwartace kawai ke cinta akan ta fita komai na rayuwa. A ganinta mallakar Ramadhan matsayin mijin ƴarta, zaisa abinda Gimbiya Su'adah ke takama da tinƙaho da shi ya dawo tafin hanunta ƙarƙashin ikonta.
Faruwar komai a jiya yasa Aynah kwana kuka akan bazata iya haƙuri da Ramadhan ba a yanzu. Ita duk ma yanda za'ai ayi ƙoƙarin gyara matsalar nan da suka tabbatar komai ya watse. Wannan shine dalilinsu na tafiya gidan boka bayan tun dare sun kirashi yanata faɗa akan abinda tunkan su sanar masa yace musu ya sani tunda aljanin daya turama Ramadhan yaci ubansa hanun Raudha da Pa da ayar ALLAH. Tun tafiyar da sukai da asubahin nan suna can har yanzu anata sake tsumo Aynah da shaiɗanci kala-kala akan Ramadhan kawai....
To bara muga wazaiyi winning anan kuma🚶🏻🤕.
*_____________________________*
Ƙarfe biyar na yamma dai-dai tawagar shugaban ƙasa Ramadhan ta iso Taura house bisa rakkiyar jami'an tsaro da wasu na jikinsa. Kamar wancan hutun tako ina anguwar ta zama ƙarƙashin mulkin mallakar jami'an tsaro ne. Sauƙin ma dama can anguwar manyace bawai hayaniya ko yawan shigi da fici ake samu ba. Sai dai abin ya shafi masu tururuwar zuwa biki. Dan duk waɗanda suka iso yau dasunci karo da jami'an tsaron nan sai tsoro ya kamasu duk da sunsan yanzu Taura house yana da wani sabon girma bayan wanda kowa yasan gidan da shi.
Babu wanda yaga Ramadhan, domin motar da yake ciki har jikin ƙofar falon Bappi ta baya aka kaita, yana fita kuma ya shige ciki abinsa.
Raudha na bedroom ɗin Anne kwance ta gama ƙwallar shan kunu da Annen ta tsareta tayi Bilkisu ta shigo ɗakin da sallama. Wayar ta dake hanunta tana game ta ajiye, dan dama game ɗin kawai takeyi amma hankalinta naga mijinta da tunanin miyake ciki yanzun? Yana ina? Jikinsa da sauƙi ko babu?.
“Sai a daina mana shagwaɓa ga boss nan ya iso”. Bilkisu daba sanin abinda ya faru da Ramadhan ɗin tai jiya ba ta faɗa tana dariya bayan takai zaune kusa da Raudha. Murmushi kawai Raudha tayi da faɗin, “Kai aunty ni shagwaɓar mi nayi?”.
“Ai ba abun jayayya bane bara na lissafa miki yanzu kuwa ɗaya bayan ɗaya ta Brothe......”
Ta kasa karasawa saboda wanda ya shigo ɗakin. Da farko tsoro taji sosai ita kanta Bilkisun, sai dai yanda taga yanayinsa kamar a sanyaye ya sata ɗan sassautawa ta gaisheshi zata mike. Sai dai Raudha tai saurin riƙo hanunta idanunta na cika da ƙwalla. Sosai yanzu tsoronsa takeji, tsoro mai tsanani dan ita kaɗai tasan azabar da taci a hanunsa har sau biyu da bazata taɓa iya mantawa ba.
Raunanannun idanunsa ya sauke akan hannayen da Raudhan ta sarƙe. Sai yaji wani irin tausayinta mai tsanani yana dirar masa daga tsakkiyar kai har tafin kafa. Da ido yayma Bilkisu alamar ta fita. Dan haka tai saurin son zame hanunta cikin dabara tana faɗin, “Aunty Raudha bara na dawo tanan sai Yaya ya zauna nan”.
Sam Raudha bata yarda ba, saita ƙara ƙwaɓe fuska zatai kuka. Bilkisu da ita kanta tausayinta takeji tunda batasan ko yayan nasu bai dawo cikin hankalinsaba har yanzu ta zame hanunta ta gudu. Sosai jikin Raudha ya fara rawa ganin ya maida ƙofar ya kulle harda key. Babu shiri ta miƙe a kan gadon tana ƙoƙarin sakkowa. Sosai tayi ƙiba, tako'ina komai yayi zam, damma doguwar rigar jallabiyace a jikin nata baƙa. A hankali ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannayensa duka a ƙirjinsa, sai kuma ya sake buɗesu ya zuba mata. Yanda take rawar jiki yasa ko'ina nata ke motsawa, ga rigar mai santsi ce, sai hakan ya ƙara taimakawa wajen motsawar jikin nata.
Murmushin takaici da tausayin kansu ya saki. Baiga laifinta ba, dan yasan dolene taji irin wannan tsoron nasa. Ya ɗan furzar na numfashi tare da warware hannayensa daga ƙirji ya fara takowa gareta cike da nutsuwarsa da kasalar yanayin rashin jin daɗi da yake a ciki........✍
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: - Nawa aka tura?
Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*WANNAN SHINE BAYANAN*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/12, 10:50 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_Episode 63-64_*
...........Ƙasa takai durƙushe cikin rawar jiki. Ta haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo. “Ya Ramadhan dan girman ALLAH kayi haƙuri, na tuba kar kayi zan iya mutuwa yau. Wlhy wajen har yanzu yana ciwo”.
Kasa jurewa yay, sai da ƙwalla suka taru masa a ido. Matarsa ta sunna ke tsoronsa saboda yaje gareta tamkar karen farauta. Ya kusanceta tamar babu zuciya a ƙirjinsa. Maimakon abinda Raudha tai tunanin sai taga saɓanin hakan. Dan shima gabanta yakai durƙushe. Ya ɗora duka hannayensa kan nata ya riƙe. “I'm vary sorry Ameenatu ki gafarceni dan ALLAH”.
Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai tsananin rauni da rawa. Da sauri Raudha ta buɗe idanunta dake rufe, danjin furucinsa da sautin muryarsa. Sosai ƙirjinta ya buga ganin hawaye a fuskar mijinta. Sai ta sake fashewa da kuka tana girgiza masa kanta. “Dan ALLAH Ya Ramadhan kabar kuka”.
Hanunsa dake cikin nata ya riko, ya jawota ta faɗa jikinsa, sai kawai suka saki kukan a tare abin tausayi. Tsahon mintuna uku suna a haka. Kafin Raudha ta ɗago tana share hawayenta tana magana. “Kaga dan ALLAH kabar kukan Abokina. Kaga nima na daina. Kuma ni ban taɓa rikekaba dama na yafe maka. Kai harma wanda zakamin a gaba na yafe maka Ya Ramadhan. Dan ALLAH ka daina kuka kar wani ya shigo, idan wani ya ganka a haka bazan yafema kaina ba”. Ta ƙare maganar tana kai hannayenta saman fuskarsa ta shiga share masa nasa hawayen.
Murmushi yay mata, wani irin kaunarta na ratsashi. Ya riƙo hannayen nata da take share hawayensa ya sumbata. Idanunta ta lumshe a hankali, saƙonsa na ratsa mata jini da ɓargo. Ciki disashiyar muryarsa yace, “Ustazah!”.
Idanun ta buɗe a hankali tana kallonsa. Ya kafeta da nashi dake cikin yanayin shauƙi da bege. *_“I love you!. Am serious I love you more than you can ever comprehend. Kinada muhimmanci a duniyata. Ina miki irin son da bayan mahaifiyata da Anne ban taɓa yima wata mace a duniya ba sai ke. Bazance miki ban taɓa so ba, sai dai inajin naki daban. Ga Ramadhan nan Ameenatu, Ramadhan B. Hameed Taura ya mallaka miki kansa da duk abinda yake nasa sai yanda kikai da shi, dan ALLAH karkici amana, karkiyi butulci, karkiyi amfani da wannan soyayya da dama ki cutar da shi......”_*
Gaba ɗaya jikin Raudha rawa yakeyi, gaba daya ya kashe mata jiki, ya sakata cikin taradadadi da kaulani. Ta fashe masa da wani irin sassanyan kuka mai tsuma zuciya.
“Nima ina sonka Ya Ramadhan, ina ƙaunarka da iya gaskiyata. Insha ALLAH bazan taɓa cutar da ko dabban Taura family ba balle kai. Har abada ko wanda zai ci amanarka bazan barsaba ma balle ni kaina. Ina fatan ko mutuwa ta ɗaukemu rana ɗaya, lokaci ɗaya, mu zama maƙwaftan juna a kabari sannan mu kasance ma'aurata a aljanna.....”
Fuskarta ya kamo cikin tafukan hanunsa ya haɗe goshinsu, sai kuma ya manna lips nashi akan nata tare da rungumeta a jikinsa.
Da sauri Anne da Bappi dake tsaye jikin window suna kallonsu suka ɗauke kansu. Anne tasa hannu ta share hawayen da suke saukar mata a fuska na ɗunbin tausayin waɗan nan ma'aurata. Tun fitowar Ramadhan daga falon Bappi Anne ta biyosa da shirin dakatar da shi, dan ta ɗauki aniyar saita wanashi akan Raudha. Biyota Bappi yay da hanzari shima da zummar dakatar da ita, sai dai tana ƙoƙarin gitta window ɗin ɗakin nata dake tabayan sashen Bappin ta tsinkayi roƙon da Raudha kema Ramadhan. Cak ta tsaya, a kuma dai-dai nan Bappi ma ya iso, ganin taja birki shima yaja ya kai dubansa ga abinda take kallo. Wannan yasa komai dake wakana a kan idonsu ne akuma kan kunnuwansu. Hannunta Bappi ya kama suka bar wajen.
“I need you Please”.
Ya faɗa murya a sarƙe lokacin da yake janye lips nasa daga kan nata. kai ta shiga jujjuya masa cikin tashin hankali, har hawaye sun sake cika mata idanu.
“Please Ya Ramadhan forgive me wlhy akwai ciwo”.
Da ƙyar ya iya rumtse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, dan tabbas bukatarta yake mai tsanani, bakuma zaiso cutar da ita ba. Amma dole ya samawa kansa mafita ba kuma a ɗakin Annensa ba, dan akwai kunya a raka baƙo ya ruga...
“Shike nan naji, amma muje zan duba naga ɓarnar da nayi dan ALLAH”. Yay maganar a wani irin marairaicewa kamar bashi ba. Zatai magana itama ya girgiza mata kai tare da ɗora hanunsa kan lips nata alamar kartace komai. Dole tai shiru, ga tsoro ga fargaba. Haka ya kamata ya miƙar, batare daya bata damar cewa komai ba ya kama hanunta suka fito. Addu'a take a ranta ALLAH yasa babu kowa a falon, duk da tasan dai ta inda zasu ratsa ɗin ba falon da kowa ke iya shigowa bane sai iya ahalin gidan kawai.
Ta ɗanji sanyi da basu haɗu da kowa ba, sai dai mai aikin Anne dake ƙoƙarin shirya abincin dare a dining. Koda suka fito kam kasa tai da kanta tana gaida Ramadhan ɗin. Hannu kawai ya iya ɗaga mata suka wuce, dan yasan inhar yay magana kai tsaye za'a gane yanayin da yake ciki. Ko'ina ƙal yake a sashen nasa. Sai ma kamshi na musamman dake tashi dan Bilkisu da Basma ne sukai bautar gyaransa. Suna shigowa cikin ɗar-ɗar Raudha tace zanyi fitsari dan ALLAH. Sakar mata hannu yay kawai batare da yace komaiba. Sai ma ƙoƙarin rage babbar rigar shaddar jikinsa yake.
Babu wani fitsari da zatayi, tayi hakane