Showing 108001 words to 111000 words out of 207756 words

Chapter 37 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

626

duk macen data amsa sunanta *MACE* zaki sameta jaruma sannan duk tsanani bata raki. Mai haƙuri, mai juriya, mai tiƙe sirri, mai bama mijinta farin ciki, mai mantawa da duk wani ɓacin rai bayan ya fuskanceta koda a baya ya cutar da ita, mai kula da tarbiyyar ƴaƴanta dama duk wanda zai kasance a ƙarƙashinta koda ma'aikacin gidanta ne. Karkiyi sakaci da yima mijinki addu'a idan yay miki alkairi koda na murmushi ne, karkuma kiji shakkar bashi shawara ko sauke fushinsa koda bazai fahimceki a lokacin ba koya saurareki. Domin mata dayawa tsoron baza'a fahimcesu ko baza'a ɗauka shawarsu ba kesa watsar da miji idan yana cikin wani hali koda sun fahimci hakan. Wannan ba dai-dai bane ba. Bashi shawara koda baya ganin kimarki, wlhy Ameenatu wataran da kansa zaizo miki da damuwarsa domin yasan a wajenkine kawai zai samu mafita. kuma inhar kikaima miji shawara ta farko ya dace akanta ya kuma fita a damuwa, shima bazai ƙara yarda ya ganki cikin ƙunci bai ƙoƙari ganin ya fiddaki ba koda ace shine ya sakaki sai ya damu ya dawo yana lallashinki da son maye gurbin ɓacin ranki da farin ciki......_
Ƙwallane suka cika mata ido, dan kuwa tabbas taga haka, ta kuma yarda da batun Anne. Dan tana ƙyautata zaton canjinsa nada alaƙa da abinda ya faru ranar. Fatanta ALLAH dai yasa ya ɗore.



(Uhm su Meeno aiki ya fara ci za'a mallake ɗan gimbiya Su'adah🤥😏🤕🚶🏻).

____________★★★★_____________

             Su Lubnah sun sauka a ɗakin kusa da ita, sai dai saɓanin wancan lokaci ɗaki guda aka haɗesu yanzu. Sosai Raudha ta sake kame kanta da ga garesu, dan taci alwashin zata kiyaye gargaɗin Maah. Sai dai bazata sake bada fuska gasu Muneera suci zarafinta ba duk da kuwa sun girmeta.
         To Alhmdllhi, tattarasu datai ta watsar ya taimaka mata matuƙa wajen saka shakkarta a zukatansu. Dan bama ta yarda ta fito inda suke balle su ganta. Ɗakinta kuwa da sun so dinga binta har ciki suyi mata cin kashi, gargaɗin da Ramadhan yay musu ya sakasu kame kansu dan sun san halinsa. Idan ransa ya ɓaci ya kama mutum ya ɓalla ya ɓalla banza babu mai ce masa baiyi dai-dai ba.

     Bayan kwanaki uku da zuwansu data kama monday bayan sallar isha'i Raudha na ɗakinta kwance a gado cikin dauriyar ciwon mara data ɗan fara ji sama-sama telephone na ɗakinta tai tsuwwa alamar kira. Ɗagawa tai da tunain Mama Ladi ce ko Mama Tambaya ko Kuku. Dan sune kawai ke kiran layin idan tayi baƙi ko suna sonjin abinda zata ci ko take buƙata.
       “Assalamu alaikum”.
Ta faɗa a nutse cikin sanyin muryarta data sanyaya sakamakon ciwon da takeji na ɗan taso mata musamman ƙafafunta, tunda tazo gidan batai period ba. dama yakan mata haka wata biyu uku wani lokacin kafin yazo. Ramadhan dake acan falonsa na ƙasa ya ɗan lumshe ido yana sake lafewa jikin kukerar da yake zaune. Sai dai idonsa na kan COS dake daga ɗan gefensa.
        “Wa'alaikassalam”.
Ya bata amsar da ta ɗan sata zabura tana cire kan wayar a kunnenta ta kalla da mamaki. Sai dai maganar da taji kamar yana sake yi ya katse mata tu'ajibbin nata ta sake maida wayar a kunnenta.
        “Ki sameni a downstairs”.
Wani irin kakkauran numfashi Raudha ta fisgo daga ƙirjinta ta fesar, sai kuma tai tagumi tana jujjuya abun a ranta dan ji take kamar mai mafarki. (Itako mi zata masa yanzun? Yau fa tsahon kwana uku bata gansa ba ma. Kai ko motsinsa bataji ba). Rashin mai tayata zancen ya sata miƙewa kawai. hijjab fari ta ɗauka ta saka a jikinta har ƙasa, sai ta ɗan ƙara turare kawai a jikinta saboda tunawa da shawarwarin Bilkisu.
     Sanin downstairs na fadarsa yake nufi ya sata nufar can kai tsaye, dan tunda take dashi bata taɓa ganinsa a falukan da zai kawoka sashen nata ba. Ta can yake shiga tacan yake fita. Inba dare ba bazaka taba ganinsa ko'a falon upstairs ɗin ba ma sai dai na downstairs din. Itako sau biyu kacal ta taɓa zuwansa.
         Tun kafin ta gama sakkowa ta ƙare masa kallo shi da COS, kayan data gani a jikinsa jallabiya baƙa da adon golden ya sata tabbatar da ba yanzun ya dawo ba. Koma bai fita a gidan yau ɗinba ma oho masa. Duk da a nutse take tafiya hakan bai hana flat shoes ɗinta ɗan bada sautin ƙarar da ta saka Ramadhan duban stairs ɗin ba ta wutsiyar idanu.  Ganin sanye take cikin kayan mutunci ya sashi ɗan furzar da numfashi ya maida hankalinsa ga sakama takardun da COS ya kawo masa hannu.
        Da sauri cos ya mike tsaye domin girmamawa a gareta, ya ɗan risinar da kansa yana faɗin, “Barka da fitowa ranki ya daɗe”.
      Raudha da taji abin gingiringin ta haɗe yawu da ƙyar tana aro jarumta ta yanama kanta. A tausashe ta ce, “Barkan ka ya ƙoƙari?”.
        “Alhmdllh Ranki ya daɗe”.
Cos ya sake faɗa cike da girmamawa. Ramadhan dabai ɗago ba duk da yana saurarensu yay mata nuni da kujerar gefensa da hannu kafin ya ɗan dago ya dubi cos bayan Raudha takai zaune zuciyarta sai faman gudu take a ƙirjinta.
         “Barka da dare”.
Ta faɗa yanda take da tabbacin shi kaɗai zai iya jin gaisuwar tata. Bai amsa ba, bai kuma daina abinda yake ba har tsahon minti guda da wasu sakkani. Ya miƙama cos file ɗin da ya gama dubawar sannan ya dubi Raudha data fidda rai da zaton zai amsa matan.
       “Kina lafiya?”.
Ya faɗa shima a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa. Ɗan ɗagowa Raudha tayi tana amsa masa a tunaninta har yanzu idonsa akan takardun yake. Ido suka haɗa, tai ƙoƙarin janye nata ya hana ta hanyar cafko yatsun hanunta da take ɗan murzawa a hankali alamar a takure take. A dolenta ta ɗan ware idanunta cikin nashi, shi kuma yay amfani da damar wajen kashe mata ido ɗaya cike da salon da ya nema birkita mata lissafi. Sai dai kafin ta dawo hayyacinta ya ɗauka envelope ɗin saman table ɗin gabansa ya aza mata bisa cinya.
         “Ki duba a cikinsu ki zaɓi guards biyu da zasu dinga kasancewa da ke”.
    Tamkar mai koyon magana ko mai tsoron buɗe laɓɓa tace, “Amma....”
        “Shiiii!!”
Ya faɗa a hankali yana ɗaura pen ɗin hanunsa saman lips ɗinsa tausasa kalar pink. Dole ta haɗiye yawu a hankali dan har yanzu idonsa na cikin nata tace, “Thanks”.
        Wani tattausan murmushi yay mata yana wani lumsha idanu da janye yatsun hanunsa dake murza nata ya maida hankali ga cos da yay ƙasa da kansa tamkar hankalinsa nakan takardar da yake dubawa. Sai dai kuma a munafunce yake satar kallon wannan soyayya ta Mr president da first lady. Sai da ya ga Ramadhan zai juyi ne yay saurin maida dukkan hankalinsa ga takardun sosai.
       Oho daga Ramadhan har Raudha basu san yanayi ba. Dan tuni Raudha ta zaro hotunan cikin envelope ɗin tana dubawa. Ƴammata ne cikin shigar uniform na aiki, wasu kuma suit na mata. Dukansu bazasufi shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai talatin ba. Sai da ta duba duk hotunan guda biyar sannan ta zaɓa na mutum biyu dake sanye da baby hijjab alamar musulmai ne, maybe ma yarenta ne duka.
        Kamar mai jin tsoron maganar yanzun ma tace, “Waɗan nan sunyi”.
     Kai kawai Ramadhan ya jinjina mata batare da ya ɗago ba.  Dan rabin hankalinsa na ga abinda yake dubawa a file ɗin hanunsa. Kusan mintuna uku sannan ya ɗan duba cos da alamar ɓacin rai a fuskarsa... “Jafar! Abinda ke rubuce anan kuwa gaskiya ne? Ko idona ne?”.
           “Tabbas gaskiya ne ranka ya daɗe. Dan duka mutane goma sha ukun nan daka gani akwai kwangilolin ayyuka a kansu, wasun su sun fara basu ƙarasa ba, wasuma ko niyyar farawar basuyi ba. Kuma munada tabbacin kuɗaɗen aikin sun fita a bitalmani harda saka hanun shugaban ƙasa mai sauka. Waɗan nan sune evidences na fitar kuɗaɗen duka”.
     Yay maganar da miƙa masa wani file ɗin. Sosai Raudha ta ɗago tana kallonsu yanzun kam, dan zancen nasu haka kawai ya ɗauka hankalinta. Ta ɗan kafama Ramadhan daya dafe kansa bayan duba takardun idanunta.
       “Cos!!”.
Ya faɗa a kausashe.
       “Yes your excellency!”. 
   “Ina buƙatar a tura ma dukansu takardar gayyata, ku zauna da su kai da minister Abubakar Gandu Ku tattauna dasu domin bibiyar gaskiyar lamarin. Bayan kun tabbatar da gaskiyarsu ku basu kwanaki biyu kacal su dawo da kuɗaɗen kafin mu miƙa sunansu ga hukuma”.
        “Okay sir!”.
     Ɗan murmushi Raudha ta saki daya ƙawata fuskarta, cike da ƙarfin halin danne ciwon marar dake tsinkulinta, sai hakan yay dai-dai da ɗagowar Ramadhan suka haɗa idanu. Harara ya sakar mata yana sake tsuke fuska. Sai kawai murmushin ya sake suɓuce mata batare data shirya hakan ba. Idanu ya ɗan ƙanƙance ɓacin ransa na sake bayyana a fuskarsa, tai saurin girgiza masa kanta da kama kunuwanta dake cikin hijjab alamar “Am sorry”.
       Baya ya ɗanyi da jikinsa yana lumshe idanu da furzar da huci. Hakan da yay ya saka Raudha cikin dauriya tace, “Ranka ya daɗe idan babu damuwa nace wani abu dan ALLAH?”.
         Babu shiri ya buɗe idanunsa dan baiyi zaton jin hakan daga gareta ba. Ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “Dan ALLAH abokina”
       Tai maganar cike da marairaicewa. Sai yanayin yay kama da wadda shaƙuwa ke tsakaninsu sosai take masa shagwaɓa. Harga ALLAH sai da zuciyar Ramadhan ta motsa. Domin shima dai mutum ne tamkar kowa, sannan zuciya gare a ƙirji ba kuma dutse bane....
    Kafin ya gama dawowa hayyacinsa ta ce, “Ranka ya daɗe maimakon a damu da zancen su dawo da kuɗin kuma su sake faɗawa hanun ɓata gari kafin su koma a bital mali, mizai hana a zaman da zakuyi dasu, mizai hana ku tilastasu ƙarasa aikin da suka fara, waɗanda basu faraba su fara kawai. Idan da buƙatar ƙarin wani abu da zai inganta aikin fiye da farko ko zai kammalashi sai ku daɗa musu. Koba komai hakan zai sa talakawa su tabbatar aiki kukazo yi da gaske......”
     Yanda ya kafeta da idanu ya sata haɗiyar yawu da ƙyar. Cikin ɗan shakku da ganin zaƙewarta ya sata faɗin, “Ban faɗi haka dan ganin gazawar maganarku ba. Sai dan kawai a nawa hasashen shari'a da su tamkar zaman ɓata wani yanki na lokutankune masu muhimmanci ga alƙawran da akaima talakawa. Dan fallasasu zai ɗauke hankulanku ne kacokan ya maida can, aikin da kukai burin yi lokacinsa yayta tafiya. Bai kuma zama lallai su da suka basu kwangilar ba su yarda su tozarta kai tsaye tunda maybe akwai ƴan uwansu ko abokansu a ciki da makamantan hakan. Ƙila kuma dalilin hakan da zaku musu su shiryu su koma mutanen kirki wajen gyara halayyarsu har na ƙasa dasu masu tasowa suyi koyi idan kun ɗorasu akan irin wannnan matsayin. Idan na shiga hurmin daba nawa ba a gafarceni ranka ya daɗe”.
         “Raf! Raf! Raf!”. Cos ya fara sakin tafi bakinsa a washe da murmushi.
      “Oh my god uwa garemu. Ranki ya daɗe wannan shawara ce mai daraja data warware kowanne irin tarnaƙi cikin sauƙi ai. ALLAH ya kara girma da nisan kwana masu albarka.”
        A ɗarare Raudha tai murmushin yaƙe. Dan bata da tabbacin mai gayya mai aikin shi ya amshi zancen kamar yanda taga cos ya nuna jin daɗinsa kai tsaye ba.
      Cos da ya sha jinin jikinsa ga yanayin shugaban ƙasar shima yay saurin dakatawa yana faɗin,  “Ranka ya daɗe m....”
     Hannu shugaban ƙasa Ramadhan ya ɗaga masa yana buɗe idanunsa da furzar da iska mai nauyi...........✍
      

*_Humm su Ustazah kai ya fara buɗewa fa, an fara samun kan😹😹😜🚶🏻_*

    

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/27, 8:50 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*

https://arewabooks.com/chapter?id=62b6073efa0b02c20d2ac11e



*_Episode 37_*


..........“Vary interesting”. ya faɗa a hankali, batare da ya basu damar maganaba ya cigaba da faɗin, “Inaga zamubi exactly idea ɗin nata, sai ka shirya muku zama a tura musu invitation ok”.
        “Yes ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara lafiya da shekaru masu albarka.”
      Raudha ce kawai ta amsa da amin tana sauke ajiyar zuciya kusan sau uku a jere. Harga ALLAH tayi matuƙar yin ƙarfin hali ne kawai wajen faɗa. Ba komai ya sata kawo hakan ba sai tunawa da su tsohon shugaban ƙasa. Dan tabbas zasu iya bin kowacce hanya domin ganin anƙi hukunta su waɗan nan ƴan kwangilar, sannan yanda suke ɗane da shi a tarko fara fiddo manufarsa kai tsaye ga duniya cutarwa ce garesa. Dan ta tabbatar bazasu ƙyalesa ba yay aikin shekara biyun da suka ƙudiri aniyar bashi damar yi ɗin. (Duk da tasan su basu isa hana zartar da ƙaddarar da babu wani hannu daya ƙirƙiri rubutata a doron duniya).....
        Hotunan dake saman cinyarta da ya ɗauka ya sata dawowa a hayyacinta. Bayan ya duba waɗanda ta zaɓa batare da yace mata komai ba ya mikama cos.
      “Okay sir an gama insha ALLAH. Za'a kaima Chairman ɗin zuwa safiya zasu fara aikinsu.”.
     Kai kawai shugaban ƙasa ya jinjina masa tare da tura masa sausan files ɗin dake ajiye saman centre table ɗin. “Babu yuwuwar zan duba waɗan nan ɗin a yanzun. Inaga ma ƙarasa a office idan ALLAH ya kaimu, idan na fito ina buƙar fara ganawa da vice president”.
       “Okay ranka ya daɗe, ALLAH ya huta gajiya ya ƙara lafiya. A huta lafiya ranki ya daɗe”.
Cos ya faɗa cikin rissinar da kai alamar respect sannan ya mike da takardun daya tattare ɗin ya tura a bag ɗin da ya shigo da su. Raudha na ganin ya fice itama ta yunƙura da nufin miƙewa dan mararta ta takura mata dauriyarta neman fara ƙarewa takeyi. Jitai an cafko mata hannu.
         Da ƙarfi ta rumtse idanu dan harga ALLAH wannan sabon salon nashi na harmutsata. Abune da shi kaɗai ya fara mata su a rayuwa....
       “Nace na gama da ke ne?”.
   A hankali ta girgiza kanta tana faɗin,  “Kayi haƙuri” ta koma ta zauna tana ƙoƙarin cire yatsun hanunta a nashi. Gaba ɗaya yanda yake murzasu ɗin harmutsa mata jinin jiki yake yi. Sakinta yay shima, ya koma jikin kujerar ya lafe yana ɗan furzar da iskar bakinsa. Sai dai yanda maƙogwaronsa ke kai kawo zai baka tabbacin magana yake da zuciyarsa. Dan harda ɗan matse idanu yayi lokacin da yake tura lip nashi a baki yana ɗan ciza. Sai kuma ya buɗe idanun a kanta da alamun kore tu anin dake bijiro masa ya ɗan tsuke fuska
             
          Takardun da ke gefensa ya ɗauka ya miƙa mata, “Komai ya kammala akan school naki. Akwai sabon driver da zai dinga kaiki yana maido ki.”
      Hannu biyu tasa ta amsa tanajin kamar ta tashi taita tsallen daɗi. Amma sai ta daure ta shiga masa godiya da addu'a cikin dauriyar danne ciwon da ke taso mata.
     Gyaran murya ya ɗanyi cikin kausasa harshe ya cigaba da faɗin, “Barinki kije makaranta bashike nufin zaki iya duk abinda ranki ya so ba. Ki kama kanki dan a yanzu kinada banbanci da baya. Akwai aure a kanki banason shigar banza. Sannan ki sani ke matar shugaban ƙasa ce, komai naki a yanzu abin tallatawa ne ga mutane koda bai kai ya kawo ba. Ya rage naki ki riƙe wannan darajan ko kiyi sakaci da shi komai zai iya faruwa. A waɗan nan takardun akwai na bank a ciki, ki cika komai kiyi musu singing za'a maidasu can. Karatu nada muhimmanci a gareki matuƙa a wannan gaɓar, saboda ƙarancin shekarunki da matsayin da kike kai a yanzu, ya rage naki ki maida hankali kiyi abinda ya kaiki kokiyi wasa da damarki.”
      Ganin yanda yake magana serious ya sata sake nutsuwa itama. “Insha ALLAH zaka sameni mai kiyayewa. Bazan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login