Showing 57001 words to 60000 words out of 207756 words
fitsari lokacin da taji hanunsa a gefen fuskarta, tanaso ta ɗago ta kasa, sai rumtse idanu da tai da ƙarfi jin ya tura yatsunsa biyu ta cikin hijjab ɗin ya saƙala igiyar a kunnenta, kafin ta farfaɗo ya ja facemask ɗin zuwa ɗayan gefen haggunta ya saƙalo nan ma.
(Ya rabbi) ta iya ambata a ranta. Bata iya motsawaba duk da rawar da jikinta ke mata sai da taji alamar ya juya sannan ta iya binsa da kallo.
Yanada tsayi gwargwado, sannan ga jikinsa a murje kasancewar yana cin ƙarfe ga kuma jin daɗin rayuwa. Jin kansa da ƙasaita da mutane d yawa ke fassarawa da girman kai suna ƙara masa wani ƙyau da girma a idon mutanen. Musamman masu son kawo masa wargi duk da ƙananun shekarunsa kuwa. Duk da kasancewarsa ba miskiliba bashi da yawan fara'a. Bakuma dan baya yin dariyar bane, a'a kawai sai ya zaɓa wanda yaso yake iya ganin haƙoransa.
Tunda suka fara sakkowa. steps ɗin jirgin hasken camaras keta walainiya a kansu, dan su Bappi duk sun sauka har suna ƙoƙarin shiga motocin dake jere da aka kawo dansu. Sake ruɗewa Raudha tayi duk da ya zartata da step ɗaya, dan yana gaba ne tana biye da shi.
Ƴan jarida nason ji daga garesa amma securitys sun musu zobe. ganin yanda wani keta son kutso kai yasa Ramadhan ɗan dakatawa ya ɗagama securitys ɗin hannu. Dole suka ɗan janye hannayensu suka bama ƴan jaridar dama suna antaya musu harara.
“Ranka ya daɗe gaka a jiharka ta Bino domin zuwa tushenka ka jefaa ƙuri'a. Ko zamu iya sanin ya kakeji a wannan ranar kuwa?”.
Wani ɗan murmushi ya saki dakai hannu ya shafi gashin daya zagaye bakinsa, “Inajina tamkar kai, kamar kuma kowa, domin banda banbanci da kowa”.
“Amma ranka ya daɗe duk wani mai irin matsayin da kake kai na ɗan takara a yanzun musan hankalinsa nakan zaiyi nasa ko bazaiyiba. Miyasa kai kakejin kanka kamar kowa irina?”.
“Saboda nayi imanin ALLAH shine ke bada mulki ga wanda yaso, a kuma lokacin da yaso. Idan ni ba alkairi bane ga ƙasar NAYA ALLAH ya hanani damar samun wannan kujerar, ALLAH ya bamu wanda ya fini alkiri”.
A take wajen ya ɗauki tafi, fuskokin mutane cike da fara'a. Yayinda wasu suka shiga masa kirari da suna *_DOGARO GA ALLAH JARI_*.
Harya ɗaga ƙafa zai wuce wani ɗan jarida yace, “To amma ranka ya daɗe baka ganin mutane zasuga kamar basu da galihu musamman dasu suka kasance a rana tun daga fara campaign amma ko sau ɗaya ba'a taɓa ganin budurwarka ba a wajen, gashi kuma yau ranar zaɓe ma babu alamar zata fito jefa maka ƙuri'a?”.
Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi na sakanni uku, sai kuma ya janye yana sakin murmushi. Shi lauya ne, yanada sauƙin karanta da fassara kalman mutane, dan haka ya ɗan dubi Raudha da kanta ke ƙasa, a ranta tana jera godiy ga ALLAH ga kuma Ramadhan daya bata facemask ɗin nan, dan da batasan yanda zatayiba.
Sarai ya fahimci ɗan jaridan yayi wannan magana ne saboda son tabbatar da Raudha matsayin wadda ake ta raɗe-raɗin zai aura. Sai kuma ya janye ya maida ga ɗan jaridar tare da kai hannu ya ɗora kan kafaɗarsa ya ɗan bubbuga. “Duk da hakan ba huruminka bane zan baka amsa, Ganin wadda zan aura a wajen campaign ba shine ya kamata kai da ire-irenka su maida hankali ba. addu'a da neman zaɓin ALLAH na samun shugaba na gari ya kamata mu maida hankali. Ƙuri'a kuma insha ALLAH zanje na jefa tare da my wife to be insha ALLAHU yanzun”.
Ya ƙare maganar da juyowa ga Raudha yana ɗan ranƙwafawa da maida hanunsa ɗaya baya ɗayan kuma ya nuna mata hanya. Wannan respect daya nuna ga Raudha ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da ƴan jaridar dake a wajen, dan take aka shiga zuba musu ruwan camaras tare da darewa aka basu hanya suka fito daga zoben da akai musu.
Wata irin nannauyan ajiyar zuciya Raudha ta saki lokacin data shiga motar da aka rage domin su, dan sauran kowa ya shiga. Shigowarsa gefenta ya sakata ɗauke numfashi, bata sake ƙwaƙwaran motsi ba har suka iso cikin Taura.
Garin ya matuƙar burgeta, dan an gyarashi titi ta ko ina, ga fitulun solar ma birjik. Cike garin yake ta ko'ina da mutane saboda masu jefa kuri'a. Wani wajen kuma sifiku ne aka warware kiɗa na tashi da waƙokin da aka rerama Ramadhan iri-iri na campaign, wani gefen kuma na abokan hamayya ne. Dan duk da nan ɗin tushensane wasu basa ra'ayinsa magoya bayan Alhaji Audi ƙaura ne da sauran ƴan takara.
A jere motocinsu da tun shigowarsu garin ya ɗauki sabuwar hayaniya suka isa ƙofar ainahin family house ɗinsu dake tamkar masarauta a garin saboda ginine na ƙawa da aka narka kuɗi wajen yinsa. Sai da suka fito Ramadhan ya miƙama Raudha katin zaɓenta da batasan dashi ba. Amsa tayi kawai tare da faɗin “Nagode” a hankali batare da tunanin yajita ba.
Bappi da Anne ne suka fara jefa ƙuri'arsu. Sai Pa da matansa uku, sannan *_Ramadhan B. Hameed Taura_* da *_Raudha Ramadhan B. Taura_*. Har cikin rai taji haushin jin cire mata sunan Abbanta da akai aka ɗora na wanda baima zama mijin nata ba tukunna. Daga haka Yafendo da Inna ma suka jefa, sai sauran al'ummar gidan suka biyo baya.
Cikin ƙanƙanin lokaci hotunan jefa ƙuri'ar ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyya mai mulki da matar da zai aura ya fara yawo a yanar gizo da kafafen yaɗa labarai. Sai dai wasu har sun fara ƙananun magana akan facemask da Raudha ta saka. Har ƴan yarfen siyasa da abokan hammayya na faɗin, _Matan wasu na wahala shi yana ɓoye tasa da bai riga ya mallaka ba ma..
Duk wanda ya jefa tasa ƙuri'ar yana shigewa cikin gida ne, dan haka ita da shi tare suka shiga katafaren gidan na Taura Family da za'a iya kira da masarauta. Kamar yanda tai tunani kuwa akwai mutane sosai a ciki, sai dai ta gagara ɗaga ido ta kalli kowa da komai duk da tarba ta mutuntawa data samu ga mutane. Sai dai cikin nutsuwa take gaida kowa da girmamawa batare data kalleka ba.
Da alama anan zasuyi breakfast ma, dan an haɗa tarin abinci kala-kala a katafaren falon da suke zaune, wanda tunda suka zauna bata sake jin muryar Ramadhan ba. Batasan a yaya ma yake amsa gaisuwar mutane ba dan ita dai a ƙasa ta zauna kamar sauran yaran kuma taƙi kallon kowa. Babu yanda ba'ai ta hau kujera ba amma taƙi, hakan datai sai ya birge Anne da wasu tsoffi na ahalin gidan, dan wannan dai alama ne na tarbiyya.
Bayan shigowar kowa aka ɗunguma dogon dining table ɗin dake can gefe gari guda domin karyawa. Sai dai gaba ɗaya Raudha ta kasa kai ko lauma guda bakinta. Basma sai zungurinta take ita da Rumaisa dan sune suka sakata tsakkiya. Ramadhan kam nacan falo ma bai taso zaman cin abincin ba yana waya ne..........✍
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: - Nawa aka tura?
Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*WANNAN SHINE BAYANAN*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/10, 7:47 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_Episode 22_*
...........Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da wata wulaƙantacciyar harara data saka zuciyarta da hanjin cikinta tsargawa da ga gimbiya Su'adah. Saurin maida kanta tai tana amsawa Anne da rawar murya. Babu wanda ya lura da hararar sai Pa da Hajiya Shuwa. Dan haka Pa shima yay ɗan gyaran murya da sakin murmushi yana faɗin, “Ɗiyata ki saki jiki kici abinci kinji, munan family nakine na biyu insha ALLAH. Dan haka kar kiji komai kici duk abinda kike buƙata, kema mai baiwa wanine”.
Kai Raudha ta jinjina. Muryarta a risine ta ce, “To Abba nagode”.
Kiran da Ramadhan yayma Bilkisu ya hana kowa sake magana, ta miƙe tana amsa masa. Babu jimawa ta dawo ta fara zuba kunun gyaɗa a kofi. Anne ce tace mizatai da shi.
Cikin ɗan tura baki tace, “Yayane yace na haɗa masa nakai masa can”.
“Kunun kawai?”.
“Eh Anne shi kaɗai yace”.
“Bazai yuwu ba haɗa masa abinci, ni bansan mike damunsa ba yanzu bai son cin abinci duk ƙaunar dake tsakaninsu ada, yanzu babu ita.”
Bappi da tun ɗazun baice komaiba ya ɗan kalli can cikin falon inda Ramadhan yake yana faɗin, “Wannan hayaniyarce kawai ba wani abu ba, bara kiga ya samu nutsuwa zai koma cin kayansa.”
“Hakane”
Anne ta faɗa cikin tausayawa.
Raudha kam duk abinda ake tanaji kamar kowa, sai dai tana tsakurar abincinne da satar kallon yanda aka loda masa uwar madara a cikin kunun da bai gaza rabin kofi ba. A ranta take gulmar kunu zai sha ko madara?. Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye gulmarta a ciki.
Koda Bilkisu takai masa kunun kawai ya ɗauka da farfesun kan rago, sauran kuwa ta dawo dasu. Adalilin dawo da kayanne take jin Yafendo na faɗin, “Ai kunga dai bazai cin ba, amma ya ɗauka masoyinsa Nama da madara, dan wancan kunu dai madarace kawai ba kunu ba”.
Dariya suka sanya, yaran nayi ƙasa-ƙasa. Anne tace, “Ai Ramadhan da nama sai kace wani kure, shi dai yaci nama. Bansan irin wannan ƙauna ba. Ko rai aka ɓata masa baya ƙin cin nama saboda son shi da yakeyi”.
Nan ma dariyar suka ɗanyi, ita dai Raudha nata murmushi ne kawai.
★★★
Da zasu koma batare da shi da Pa da Bappi ba, su sun wuce cikin masarauta ne, su kuma direct airport. Hakan ya saka Raudha jin daɗin komawar, dan sai ita kaɗai a vip ɗin. Sai dai tanata kallon tarkacensa daya bari a wajen da shaƙar ƙamshinsa tamkar yana nan, ta sake rimtse agogonsa dake cikin hannunta wanda da zasu fito daga falo a Taura Anne ta lura da shi ya manta a inda ya zauna, shine ta sata ta dakkosa. Koda ta ɗakko ta bama Anne cewa tai ta ajiye a wajenta ta bashi da kanta. Wannan shine dalilin tahowa da agogon har cikin jirgi tunda bata gansaba har suka baro Taura, yanzu kuma sai take ganin kamar bai dace ta ajiye anan ba gara ta bari ta bashi hannu da hannu. Sai dai kuma a ina? Yaushe kuma?. shine ke mata kaikawo a zuciya har jirginsu ya iso Bingo city batare da ta yanke kwakwarar shawara ba. Daga ƙarshe ma sai ta turashi cikin bag ɗinta batare da tasan dalilin yin hakan ba..
Koda suka sauka Anne sawa tai a maidata gida direct. Tai godiya batare data iya kallon kowa ba. har mota su Fadila suka mata rakkiya da nacin ta basu number ɗinta. Fuskarta ɗauke da murmushi tace musu itafa bata da waya.
A tare suka waro idanu waje. Rumaisa tace, “Kamarki matar Yaya guda baki da waya? To miyasa? Dami kuke gaisawa da Yaya kuma?”.
Cikin son kauda musu zargi tace, “Dokar Abbanmu ne sai kayi aure zaka riƙe waya”.
“Woow imagine! Dama akwai masu biyayya irinku har yanzu game da waya?”.
Basma ta faɗa da mamaki, dan su tun suna jss 1 ma sunada wayoyi, koda Ramadhan ya ƙwace a wancan lokacin basu ƙulla wata gudaba iyayensu mata suka saya musu wasu sukace su dinga ɓoyewa kar Ramadhan ɗin ya gani. Kuma haka akai har suka shiga ss 1 bai san sunada waya ba. Sai da ya saya da kansa ya basu.
Murmushi kawai Raudha tayi, yayinda Rufaidah ke faɗin, “Ai yanzu an saka miki ranar aure ya kamata Abba ya barki ki riƙe, zan faɗama Yaya kuwa”.
Kafin Raudha tayi magana har sun ɗaga mata hannu sun bar wajen saboda kiran da Sumayya ta ƙwala musu.
_______________________
Alhmdllhi an kammala zaɓen shugaban ƙasa, duk da dai a wasu sassa an samu ƙananun hatsaniya na matasa da kuma sace akwatin zaɓe. Sai dai Alhmdllh abun bai tsamari ba jami'an tsaro suka tsawatar. Zuwa yanzu babban fatan kowa shine hayewar wanda ya zaɓa. Inda wasu ko barcin kirki basayi musamman ga ƴan takarar idonsu kyam a tv, wasu kuma a redio ana sauraren sakamakon zaɓuƙan jihohi.
Sai dai abin zai baka mamaki idan nace ga Ramadhan ba haka bane, dan shi tamkar ma an basa lokacin samun damar yin barci ne. Ko sau ɗaya bai taɓa zama kallon sakamakon zaɓe ba balle damuwa da yaya komai ke tafiya. Lokaci-lokaci dai yakanji ihun yaran gidansu na faɗin Yayanmu ya haye jihar kaza. Daga haka bazai iya ƙaras da komaiba kuma.
A randa ake tsumayen jin sakamakon zaɓen kuwa ƙasar tayi tsitt kowa ya kasa kunne, inda masu shirin kota kwana ke shirye tsaf na tada tarzoma ta kowanne sashe. Dan dayawan sauran ƴan takarar sunfa fahimci wanda zai iya kai labari kai tsaye. Dan haka suka shirya sai dai kowa ya rasa. A sashen su Alhaji Yaro glass duk da sunga alamun nasararsu hakan bai hanasu shirya nasu ƴan tada zaune tsayen ba suma, dan a cewarsu ko da zata kwaɓe sun shirya.
To suma dai jami'an tsaro sun shirya tsaf dan bada kariya ga al'umma kamar yanda Ramadhan yasa Bappi kiran I.G da General da sauran manyan shugabannin hukumomin tsaron ya nema alfarmar su tsaya da ƙarfinsu wajen ganin wani harmutsu bai tashiba dan ALLAH...
★A ranar talata ƙarfe huɗu da mintuna talatin da bakwai na yamma shugaban zaɓe prof. Rabilu S Barde ya sanar da sakamakon zaɓe ga wanda ya lashe kujerar shugaban ƙasar NAYA.
Sabon shugaban ƙasa da komai nasa yazo da mamaki da sabon sauyi. Matashi na matasa, *Barr Ramadhan B. Hameed Taura*.
A hankali kofin fura dake hanun Ramadhan da fitowarsa kenan daga kitchen ɗin Anne yaje ya ɗebo furan dan yasha saboda barci daya tashi a makare yay sallar la'asar a ɗaki ya sulale ƙasa ya tarwatse saman Mable's ɗin da aka ƙawata falon da shi. Babu zato babu tsammani jikinsa ya kama rawa, dan harga ALLAH sakamakon zaɓen yazo masa a bazata, bai taɓa saka ran zaici ba dan yasan akwai manya a gabansa, duk da shike da ɗaurin gindin masu mulkin ƙasar da manya. Wasu irin hawayene masu ɗumi suka silalo masa a saman kumatu, ƙafafunsa da suka nema gaza ɗaukar gangar jikinsa sukai ƙasa ya durƙushe akan gwiwoyin sa biyu har ɓallin ƙofi na ji masa ciwo. Amma sai bai kulaba duk da zafin daya ratsasa sai ya tafi sujdah.
Anne da Bappi, Yafendo, Inna, Pa Siyama, Bilkisu ma dake falon duk Sujudan suka tafi kamar yanda yayi. Kafin su ɗago su bilkisu su cika falon da ihu saboda shigowar sauran ƴammatan gidan da gudu suna ihun murnar yaya ya haye.
Duk wannan ihu dake faruwa Ramadhan ya kasa ɗagowa daga sujida sai da Pa yazo da kansa ya kamashi ya ɗago da shi. Sai kawai ya fashe da kuka ya rungume Pa ɗin.
Pa dake murmushi shima idonsa cike da ƙwalla ya shiga shafa bayansa a hankali. Tsit falon yayi suna kallon yayan nasu, dan da yawansu zasu