Showing 96001 words to 99000 words out of 207756 words

Chapter 33 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

643

wajen da yake, amma bazata iya jure kallon da birkitattun idanunsa suke mata ba. Saboda sunada wani irin kaifi da kwarjini a gareta na musamman.
         Kallonta yake sosai kuma kai tsaye wanda ta rasa mi yake kallone a jikin nata. Dan ta kasa dubansa ita. Tsabar kunya ji take kamar ta nutse a wajen ta huta. Sai da yay mai isarsa ya janye idonsa ya maida ga agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Batare da amsa ban haƙurinta ba ya ce, “Ina bukatar abinci”. Daga haka ya sake ɗauke kansa ya maida ga television ɗin dake ɓaɓatu a katafaren falon da yafi kowanne falo haɗuwa da tsaruwa a gidan.
           Numfashin daya toshe mata maƙoshi taja da karfi ya wuce cikin ciki ta fesosa a hankali tan mikewa. Sai kuma wani irin fargaba ya ɗarsu mata a zuciya dan tasan dai akwai breakfast ɗinsa a dining, tana shakkar nuna cewar zata haɗo wani bata san amsa mizai biyo baya ba. Rashin mafita ya sakata nufar dining ɗin ta shiga buɗe abincin wajen kusan kala uku. Sam hankalinta bai kwanta da su ba, dan haka ta sake dawowa inda yake zaunen tana kai durƙushe gabansa yay mata nuni da kujera.
     Babu fuskar yin musu, sai kawai takai zaune a ɗofane kamar ɗazun. “Dama zance ko a duba lunch dan wancan sun huce”.
      Shiru bai amsa ba, hakan ya sata ɗan ɗago ido ta saci kallonsa, sai taga ita yake kallo, sai dai tana ɗago ido ya janye nasa cike da basarwa.
      “Duk yanda kikai yayi”.
Ya bata amsa tunkan tace wani abu. Tsam ta miƙe a wajen ta nufi downstairs. Shi kuma ya cigaba da kallonsa zuciyarsa na kissima masa wani abu daban akan Raudhan. Baya buƙatar ɓuɗewar idanunta da yawa, sai dai a matsayinsa na shugaban ƙasa yana bukatar matarsa ta zama mai buɗaɗɗen brain kodan mu'amula da mutanen dake a cikin gidan dama masu shigowa. Bai cika son macen aurensa mai ƙarancin shekaru ba, amma shawarar Bappi tasa hakan baya damunsa yanzu kuma.

      Cikin sa'a Raudha ta iske kukus ɗin gidan na shirin tsara abincin lunch ogansu tsaye akan mai shirya abincinsu duk da dama wannan kitchen ne da iyakar su da wanda ya shafi sashen kawai akema girki, dan haka ta dakatar da shi akan a tattaro breakfast dake sama, zataima shugaban ƙasa lunch da kanta. Kuku yaso yin magana sai dai babu fuskar hakan, sai ya miƙa mata book ɗin dake ɗauke da tsare-tsaren abincin da Ramadhan ke ci saboda yanayin lafiyarsa.
        Tana tsaka da dubawa Bilkisu data wuto a falo ta shigo, dan iya su Lubnah kawai aka maida sashen baƙi da ke a falo na biyu. Cikin ƴar tsokana Bilyn dake hawa saman cabinet na kitchen ke faɗin, “Uhm yau da alama amaryarmu da kanta zataima babban yaya ango girki kenan?”.
       Murmushi da kunya ne suka lulluɓe Raudha lokaci guda. Tasa book ɗin ta ɗan kare fuskarta. Littafin Bilkisu ta amsa tana dariya itama da sake faɗin, “That's good my sweet aunty. Dama naso na baki shawarar nan tun randa mukai na dare ɗin nan. Inaga yana da ƙyau ragamar girkin mijinki ya dawo hanunki bawai ki barma kuku ba tunda ke special first lady ce data banbanta dana baya, tunda naga Yaya yafi bukatar ganinki a gida kawai ko muryanki baison fita.”
         Murmushi nan ma Raudha tayi kawai. Bilkisu taci gaba da faɗin, “Yaya mutum ne mai tsantsami, shiyyasa baya cin abincin kowa sai na Anne. Dan na sashenmu ma yasan ƴan aiki keyi.”
       Cikin jin daɗin shawarar Bilkisu da ganin mafitace ma ga fargabar shirin su aunty Hannah data rasa yanda zata ɓullo masa yasa Raudha faɗin, “Insha ALLAHU zanyi ƙoƙarin hakan Aunty Bily. Nagode sosai”.
        “A'a mune ai da godiya tunda za'a kula mana da yayanmu”.
     Nanma Murmushin kawai Raudha tayi. Daga ƙarshe Bilkisun ce ta taimaka mata sukai komai yanda ya kamata. Sai kuku ya zama ɗan kallo, dan bilkisu gwanace wajen sarrafa girki. sai kuma tambayoyi da sukan masa akan na'urar da basu gane ba ko idan suna buƙatar wani abu da basu san inda yake ba.
       Basu wani ɓata dogon lokaci ba komai ya kammala. Suka bama kukus daketa aikin haɗa sauran abincin waje....


............Kasancewar an kwashe abincin breakfast dake a dining ɗin ɗazu ya bama Raudha damar shirya wanda suka shigo da shi ita da Bilkisu da Basma. Har yanzu yana a inda suka barsa. Sai dai saɓanin ɗazun da yake kallo yanzu yan aiki a system ne. Har sukai suka gama bai ɗago ya kallesu ba. Sai da su Basma suka sauka Raudha ta ƙaraso inda yake.
     Bata mance abinda yay mata ɗazun ba, dan haka takai zaune akan kukerar dake facing nashi a ɗofane. “Ga abincin an shirya”. Ta faɗa cikin sanyin muryarta dake da matuƙar tasiri ga Ramadhan batare da ita ta san hakan ba.
     Kansa kawai ya ɗan jinjina mata batare da ya ɗago ba. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya miƙe ya nufi dining ɗin. Itama Raudha baya ta dafa masa tana mai satar kallon yanda yake taku cike da ƙuruciya da mazantaka irin ta masu shekarun da basu gaza nashi ba, alamar akwai lafiya da ƙarfin jini a tattare da su.
         Duk yanda Bilkisu ta bata shawara haka tayi, duk da ya ɗanyi mamakin yanda tayi komai kai tsaye bakamar waccan ranar ba da dare sai ya danne, cikin nutsuwarsa ya fara cin abincin bayan ya kalli agogon dake ɗaure a hanunsa. Raudha tai ƙoƙarin barin wajen dan a matuƙar takure take dama.
       “Ji mana”.
  Wani irin tsargawa cikin Raudha yayi, dan a tunaninta ko abincin ne bai masa ba. Ta dawo da baya tana ƙoƙarin haɗiye fargabarta. Abincinsa ya cigaba da ci tamkar bashine yay kiranta ba. Sai da yaja kusan mintuna biyu a hakan.
       “Ba'a ajiyemin abinci a wuce a barni a wajen sai kace mara gata har sai na kammala”.
       Idan ta fahimci zancensa yana nufin dai dole ta zauna a wajen har sai ya kammala. Kai mutumin nan zai illatata, shi bai san a takure take da hakan ba? Nasihar Bilkisu data Anne ta sata komawa ta zauna, a ƙasan ranta tana ƙara ganin laifin su hajiyar birni da ko nasihar yanda zata rayu da miji basu mata ba. Sudai kawai farin cikinsu zata auri shugaban ƙasa ɗan babban gida.
         Ita dai tunda ta koma ta zauna kanta a ƙasa, shiko laokaci-lokaci yakan ɗago ya kalleta, sai dai komai baice mata ba harya kammala. Shiru wajen ya sake ɗauka, shi bai tashi ba shi bai mata magana ba har kusan mintuna uku da wasu sakanni. Sai dai kaifin idanunsa dake kanta ba karamin kassara duk wani ƙwarin gwiwa na Raudha yake ba. Ji take tamkar ta fasa ihu ta huta.
        “Na fahimci komai sai na koya miki shi a gidan nan?”. Ya faɗa a hankali tamkar bada ita yake ba.
Da sauri ta ɗago ta kallesa dan furicinsa yazo mata a bazata. Ya kaɗa bata ƙwayoyin idanunsa masu rikita mata lissafi. “Miye burinki a rayuwa?”.
Babu shiri ta maida kanta ƙasa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ganin baida alamar sake maimaita tambayar balle ta tabbatar da abinda tajin a farko ya sata ƙarfin halin faɗin,
       “Karatu. Na addini dana boko”.
Karan farko a duk yinin yau ya saki murmushi, sai kuma ya ɗan kauda kansa a kanta ya maida ga ƙaton hotonsa dake manne a falon, irin wanda a duk wani office dake ƙasar NAYA shi zaka gani manne.
        “Wane mataki gareki duka a yanzun?”. Ya faɗa batare daya ɗauke idonsa ga hoton ba.
     Sai da ta juya maganarsa sau uku kafin ta fahimci inda ta dosa. “Nayi saukar Al-qur'ani watanni bakwai da suka wuce. na haddace littafin arba'una hadith tun shekaru uku da suka wuce, a yanzu haka akwai hadithai sama da talatin da bakwai a kaina bayan arba'una hadith, sai sauran littatafai suma wani na ƙarisa wasu ina gab. A fanin boko secondary na kammala, sai dai ko result ban amsa ba”.
        A hankali ya janye idanunsa daga kan bakinta dake motsin masa lissafin cike da nutsuwa. Ya ɗan haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi tare da kai hannunsa ya shafi gashin dake kwance a fuskarsa. Jin baice komai ba itama sai bata sake cewa komai ba.
Miƙewa yay kamar zaibar wajen sai kuma ya ranƙwafo kanta. A ɗan rikice taja kanta baya jin saukar numfashinsa kusa da ita.
Cikin magana irin ta masu raɗa yake magana saitin kunenta. “Shiyyasa kike zubamin ustazanci a gida ashe”. Yana gama faɗa ya janye jikinsa baya yabar wajen, dariyar yanda ta diririce na cinsa.
Da ƙyar Raudha ta iya sauke numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya da kai hannu ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta ta dafe.
      Shin mike damunsa ne wai? Mike son faruwa da ita ne? Ta taɓa so a baya akan ya sayyadi, sai dai akwai banbanci da abinda takeji a yanzun game da Ramadhan. Mike nan hakan?. (Yana miki kwarjini ne kawai, da abunda bakiyi tunani daga garesa ba) wani sashe na zuciyarta ya faɗa cike da tabbatar wa.
     
★Tun daga wannan ranar Raudha bata sake jin ɗuriyar Ramadhan ba tsahon kwana biyu, kota shirya abincin safe da Bilkisu ke tsaye kanta kullum yanda suka aje haka kuku ke kwashewa. Dama dai basa shirya lunch tunda sun san yana office. Na dare ma ba'a taɓawa haka ake kwashesa. Raudha bata sanin sanda yake fita balle shigowa.
     Yana ɗan bata tausayi, dan ta fahimci sam bashi da lokacin kansa. Gaskiya mulki ba wani daɗi bane ba. Da wahalhalun cikinsa yafi daɗin yawa. Musamman ma irin na Ramadhan dake zagaye da maƙiyansa batare da ya sani ba.
      Addu'a ta cigaba da masa, tare da maida hankalinta ga abubuwan da Bilkisu ta duƙufa koyar da ita, wanda take matuƙar jin daɗinsu har tanajin canji a al'amuranta. Duk da ba baƙinta bane, saboda kusan duk irinsu ne su aunty Hannah suka koyar da ita a wancan lokacin. Banbancin kawai tana maida hankali a waɗan nan saboda fahimtar lallai zaman gidan bazai yuwu mata ba sai ta zama mai buɗaɗɗen brain irin na manyan mata. Ba komai ya sata irin tunanin nan ba sai ziyarce-ziyarce da matan manyan mutane irin ƴan majalisu da gwamnoni ke kawo mata cikin gidan. Kallonsu kawai wajen iya tsara ado firgitata suke. Balle a magana da sauransu.
          Bata taka kowanne irin mataki da yay kamanceceniya da nasu ba, sai suttura kawai a yanzu da zata iya fin wasu saka masu tsada ma saboda Anne tsayin daka ta tsaya ita da Hajiya Mariya wajen haɗa lefen Raudha da kayayyaki na alfarma saboda hangen irin hakan.
       

__________★★_★★__________

         A ɓangaren Ramadhan ayyuka ne sukai masa yawa sosai, dan a wannan gaɓar suna tsaka da tantance sunayen mutanen da ya kamata su sami mukamai. Sai dai a zahiri bazaka taɓa jin baki ko cewar shugaban ƙasar ba. Sai dai daga bakin mai magana da yawunsa ko mai magana da yawunsa akan yaɗa labarai.

       A ɓangaren majalisa kuwa bayan zama da kaikawo akan jerin sunayen cabinet na shugaban ƙasa da aka fitar aka sake dawo da sunayen ofishin shugaban ƙasan. Yayinda shi kuma ya sake maida sunayen ga majalisa a rubuce kan a tantance daga dukiyar kowanne na jerin sunayen. Ma'ana duk suzo su bayyana abubuwan da suka mallaka, hukumar bincike da yaƙi dacin hanci da rashawa kuma ta tankaɗe ta rairaye ta ajiye duk wani documents nasu. Wanda ba'a yarda da nashi details ɗin ba a ajiye sunansa gefe guda baya cikin jerin wanda za'a bama muƙamin.

        Tofa wannan magana data fito da ga kakakinsa mai tabbatar da yawun shugaban ƙasa ne ta tada hankalin manyan jam'iyya. Ba komai ya kawo hakan na kuwa sai sanin cewar a cikin waɗan nan mutanen musamman wanda sukai bayar akwai masu kashi a ɗuwawu da yawa. Dan haka Jam'iyya ta bada sanarwar taron gaggawa tare da gayyatar shugaban ƙasa.
       Wannan ne karo na farko da jam'iyya ta gayyaci shugaban ƙasa a bayyane tun bayan hawansa kujerar mulki, dan duk bata kashin da akai akan sunayen cabinet da zaɓin speakers na majalisu a rubuce ne data hanyar zaman sirri. Lokacin da kakakin shugaban ƙasa ya isar da wannan takardar gayyata ga Ramadhan ɗagowa yay yana dubansa. Yay ɗan murmushi yana sake maida dubansa ga takardar batare da yace komai ba.
       Chief of staffs ya sake risinar da kai cike da girmamawa yace, “Ranka ya daɗe, na riga na shirya saƙon maida musu akan bazaka samu damar zuwa ba, nasan zaman bai wuce akan binciken dukiyoyin sunayen cabinet ba. Gashi a ranar ma kanada tafiya zuwa ƙasar China”.
       Ramadhan da har yanzu idanunsa ke kan takardar ya cigaba da nazarinta tamkar mai bita. Sai kuma ya ɗago yana duban cos a nutse, sai dai yanzu babu wannan murmushin na ɗazun. “Tunda zama ne a bayyane zanje, sai dai ka canja musu lokaci”.
       “Amma....”
Hannu Ramadhan ya dagama Cos, dan haka ya haɗiye abinda yake son faɗa. COS baiso hakan ba ya jinjina kai kawai. Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya dace har zuwa iya adadin daƙiƙun da zai iya ganawa da shugaban ƙasar ya cika ya fito.
        Bayan fitar COS. Da wasu sakanni Ramadhan ya ɗauka ɗaya da ga cikin wayoyinsa ya shiga danna-danne. Babu jimawa aka ɗaga kiran da yay. Cikin girmamawa ya fara gaisawa da Bappi, kafin ya zayyano masa batu akan takardar gayyata da jam'iyya tai masa.
    Murmushi Bappi yay da ga can. Kafin yace, “Naji daɗi da kai tunanin zuwa ɗin, domin wannan shine kira na farko da jam'iyya tai maka a bayyane, duk zaman da kukai baya na sirri ne. Amma inaga a wannan gaɓar kar kai jayayya da su, duk umarnin da suka baka koda na janye batun bincike akan cabinet ɗinne kayi hakan”.
         “Amma Bappi hakan ai tauye hakkin talakawa ne? Sannan zamu iya ɗaura ruɓaɓɓu a lulluɓe suzo suna ruguza mana tsari”.
       “Zancenka yana kan hanya, sai dai ka sani Ramadhan bazai yuwu ka samu komai na ra'ayinka hundred percent ba, har sai ka nutsu ka fahimci mutanen man a to z. Dan zuwa yanzu zuciyata ta fara faɗamin akwai manufa a ɗoraka wannan mulkin musamman idan mukai la'akari da saƙon da muka samu daren ɗaurin aurenka da bincike ya kuma tabbatar mana da komai...”
      Wani irin kakkauran numfashi Ramadhan yaja, sai kuma ya jinjina kansa cike da nutsuwarsa yace, “Babu damuwa Bappi duk yanda kace haka za'ayin”.
         “Thanks you my dear, adai sake dagewa da addu'a, kar ai sakaci da ibadar ALLAH. Duk abinda yazo a nema zaɓin ALLAH, a kuma zartar dashi bisa gaskiya da amanar talakawa da tunawa da rantsuwar da akayi.”
       “Insha ALLAH Bappi, ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai mai amfani”.
    “Amin ya rabbi”. Daga haka suka ajiye kan wayoyin kusan lokaci guda. Yayinda kowannensu ya tsunduma a tunani ta ɓangarensa.

   ★★

    Kamar yanda Bappi ya ƙara masa ƙwarin gwiwar amsa kiran jam'iyya a yau koda ya baro office kai tsaye falon da zasuyi zaman anan cikin fadarsa ya nufa. Su huɗu ne kawai. Party Chairman da wasu manyan masu faɗa aji a jam'iyyar su biyu. Cikin mutunta juna suka gaisa, domin dukansu sai dai a kirasu iyaye ga Ramadhan ɗin, ballema ta wani fanin duk suna tare da kakansa ne.
       Kamar yanda Ramadhan yay hasashe akan maganar cabinet ne hakanne kuwa, dan haka bayan ya gama saurarensu bai wani ja maganar tayi tsayi ba ya nuna ya gamsu da abinda suka faɗa ɗin. Duk da acan ƙasan ransa wani irin ƙuna zuciyarsa ke masa da takaicinsu.
      Tabbas sunji daɗin yanda yay musun, dan har fuskokinsu sai da suka nuna hakan, tare da yaba masa na bama jam'iyya girmanta a wannan karon. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa muhimmai bayan an bama ƴan jarida damar sanin wani abun. Basu tashi a zaman ba sai kusan ɗaya da rabi na dare. Dan haka a matuƙar gajiye Ramadhan ya ƙarasa cikin gidansa. Dole kuma ya dakata ya saurari COS na mintuna biyar kafin ya shige. COS kuma shima ya nufi nasa gida.

______________________________

       Kwanaki sun ɗan ƙara shuɗawa da adadinsu ya kai kusan goma sha,  Ramadhan ya ziyarci ƙasar China na tsahon kwana huɗu ya dawo, an kumayi naɗin cabinet da yasaka wasu farin ciki wasu ɓacin rai. Babban farin cikin talakawa a zaɓin matasa da suka shigo tawagar sosai a wannan tsarin ma. Darajar shugaban ƙasa ta sake ɗaukaka a idanun matasa dama ƴan ƙasa, domin abubuwa na zuwa da ba'a taɓa gani ba a ƙasar NAYA. A gefe kuma ana cike da fargabar wasu a cikin cabinet ɗin, domin kuwa ansansu, sun riƙe wasu muƙaman an gani, inda ake yawan zarginsu da handama da baba kere wa dukiyar talaka. Wannan ya kawo ƴan kananun magana ga talakawa ga ma masana akan harkar mulki da siyasa tare da ƴan jam'iyyar hamayya da dama suke jiran ƙiris su hau suka. To komadai miye shi talaka ɗaukarsa a kullum shugaban ƙasa ne keda ikon mulki da zartarwa ga ƙasa, sai dai baisan zagaye yake da masu tilastawa da hanawa ba a zahiri da baɗini, takan kai ma wani lokaci shugaban ƙasa bai isa bayyana ra'ayin kansa ba koda yana buƙatar hakan.

         A washe garin da akai naɗin cabinet bai fita office ba sakamakon hutawa na kwana biyu da likitansa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login