Showing 69001 words to 72000 words out of 207756 words

Chapter 24 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

631

na dogara dan bani da kowa sai kai ɗin tun farkon fari. ALLAH ka ƙyautata ni'imarka garemu a ƙarƙashin wannan BAƘAR INUWA da kowa kema kallon Ni'imtacciyar inuwa a garemu.”_*
    Hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kumatunta har saman facemask ɗin fuskarta da ta gagara cire koda shi ne. A wannan yanayin gidan ya fara ɗaukar hayaniyar mutane alamar an dawo dasu gida suma. Dole ta miƙe ta fara zare sarƙa da tarkacen jikinta gudun kar Anne ta zargi wani abu. Duk da kuwa a ranta yanzu hankalinta yafi karkata da kwanciya akan ta tunkari Anne da batun da taji a bakin su Aunty Hannah. Sai dai kuma bata son tozarta yayar mahaifiyar tata dan koba komai bata da kamarsu a duniya, tunda gashi har ana aibantata da halayensu da suka aikata tunkan haihuwarta.

★★★

     WASHE GARI aka gudanar da rantauwa ga shugaban ƙasa da gwamnoni. Kum harda Raudha shugaban ƙasa Ramadhan yaje wajen. Sai dai tana cikin dogon farin hijjab da facemask yau ma. Abin ya sake burge jama'a musamman talakawa. Da kuwa idan akai dubi da yanda mafi yawan matan gwamnonin suka cakire cikin shiga ta rashin mutunci da kece raini a yau ɗin. Ga gwalagwalai dake ƙyalli da walwali a jikinsu tako ina. Hatta da Hajiya Fanta da aunty Hannah matan vice president shigar tasu ba'a magana. Sai dai a kallo guda zaka gane ran Hajiya Fanta a ɓace yake saboda kasancewar aunty Hannah a wajen bayan mijin nasu yace mata da ita kaɗai zaije banda Hannah. Dan tunda aka maida aurensa da aunty Hannah suke tafka rigima har yanzu kuma babu daɗi a tsakaninsu, tace sai ya saki aunty Hannah ɗin. Shiko ya tabbatar mata hakan bamai yuwuwa bane dan Hannah nada muhimmanci a tafiyarsa ta yanzun.
       Ga ƴan siyasa kuwa sai suka fara takale-takale da zungure-zunguren batun saka facemask da amaryar ta shugaban ƙasa ke yawan yi, dan tunda ya far bayyanata wa duniya ranar zaɓe ba'a taɓa ganin real face nata ba sai da facemask. To yau ma al'amarin yaci uban na da, dan farin siririn gilashi da Raudha ta saka a idonta saboda kumburin da ya ɗanyi na kuka da rashin isashen barci ya ƙara mata wani ƙyau da burge mai kallo. Ga facemask da ya saka ba'a ganin ainahin face nata kuma. Sai haka ya zam ba'a ganin komai nata a waje sai tafukan hanunta kasancewar hijjab ɗin data saka mai hannu ne.
    Uban gayyar shima fararen kayane a jikinsa na wani haɗaɗɗen boyal ɗinkin babbar riga. Ya kawo hularsa tangaran data fita a fice ya murza. Bayan kammala Rantsuwa suka wuce wajen bikin da aka shirya gudun mawa da ga Mai-martaba. Ƙarfe biyu aka tashi aka dawo da Raudha kawai gida, shugaban ƙasa Ramadhan kuwa gidan gwamnati aka tafi masa rakkiya. Bayan idar da sallar la'asar aka gabatar da walima da addu'oi daga manyan malamai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Daga haka taro ya tashi lafiya kuma zuwa anjima za'aima amarya rakkiya gidan gwamnati insha ALLAH tunda angonta ya tsufa acan.

         ★★★_______★★★

     An yima amrya shiri na musamman domin miƙata gidan gwamnati da zasu zauna insha ALLAH. Ba wasu mutane masu yawa bane zasuyi rakiyar, dan haka da wuri aka kaita ga gimbiya Su'adah da su Adda Asmah da sauran matan Pa su Hajiya Mufida.
       Duk da a lulluɓe fuskar Raudha take da golden color na veil hakan bai hana gimbiya Su'adah jefa mata kallon tsana ba. Da ƙyar ta iya dauriyar cewar “ALLAH ya bada zaman lafiya”. Daga haka ta tsuke bakinta. Sai su Addah Asmah ɗinne keta karaɗin kwarara addu'oi ga amaryar da ango. Abinda gimbiya Su'adah tayi yasa mutane da yawa fara tsarguwa, dan kuwa basuji daɗin yanda ta sallami surukar tata matar ɗanta na farko ba kuma namiji tallin tal.
        Raudha da dai ba sanin mi ake ciki tai ba. Dan kanta a duƙe kuma a lulluɓe. Tunda ba wani farin sani tai musu ba bata iya tantance muryoyin da sukai magana ba. Daga part ɗin Gimbiya Su'adah part ɗin Hajiya Shuwa aka nufa da ita. Itako ta mata ƙyaƙyƙyawar addu'a harda ƙyauta da babu wanda yasan minene a cikin dan an riga anyi packaging nashi da leda mai ƙyalli alamar gift. Hakama Hajiya Mufida tarba ta mutuntawa taima amaryar da doguwar addu'ar zama lafiya harda fatan nan da baɗi a sake taron suna. Itama dai tayima amarya ƙyautar cheque na kuɗi da babu wanda yasan adadi tunda a ninke takardar take. Sai wani ɗan box a cikin ƙaramar bag.
       Bisa jagorancin Hajiya Mufida aka kai Raudha ga Pa. Inda shima yay masu doguwar addu'a da nasiha ga Raudha tare da ƙyautar key na mota galleliya. Sai sashen su Yafendo inda can ɗin ma tasha addu'oi da kyauta ga dangin su Ramadhan ɗin. Daga haka aka sake maidota wajen Bappi da Anne suka sake musu addu'oi, Bappi ma yay mata ƙyauta a dunƙule wadda babu wanda yasan minene. Hakama Anne, koda yake gara na Anne da alama harda kayan turare dan ƙamshinsu tuni ya addabi hancin kowa. _Sisters turarurrukan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* daban suke dana saura. Zaka tabbatar da haka ne kawai yayinda ka mallaki naka. Ba turare kawai take saidawa ba. Harda kayan gyara amarya galla-galla na musamman da sai an gwada akan san na ƙwarai. Sirrinsu daban ne, idan nace na daban, ina nufin na daban dana saura😉😘😘🤗_.

       Har cikin mota Anne ta kawota, tare da sake musu addu'a domin tuni ango shi ya shiga fadarsa. Amaryarsa kawai yake jira a kai masa.
          Har suka iso a tafiyar da bata gaza mintuna a shirin ba saboda jiniya da aka sakama motocin yasa akaita basu hanya, wannan yasa suka iso cikin ƙanƙanin lokaci. Amarya dai bata buɗe ido ba yanzu ma. Sai dai kunnuwanta naji mata yanda ƴan rakiyar tata ke ta yaba wannan katafaren gida first class. Tsirarun ƴan uwanta kuwa da akazo dasu rikicewa sukai. Bataga laifinsu ba, dan masu shiga ƙasashen duniyar ma da kuɗin ƙugunsu sun yaba balle su.
       Ita dai babu komai a ranta sai addu'oi, dan zuciyarta sai faman tsinkewa takeyi musam da kalaman su aunty Hannah ke dawowa a cikinta tamkar bitar karatu, sai dai Alhmdllhi mafitar data samu a safiyar yau da matakin data ɗauka tana fatan zuwa yanzu an kauda matsalar farko da takema fargaba kafin masu zuwa. Kamar yanda Anne ta gargaɗeta da yin addu'a haka ta dingayi a duk takun da zatayi har suka iso ainahin cikin babban falon farko na gidan.
      Gaban Raudha yay masifar faɗuwa. Tai azamar rumtse idanunta tana ambaton sunayen ALLAH masu tsarki, daga haka bata sake fahimtar komai ba har suka iso inda aka sanar mata falonta. Kamar yanda Hajiya Zuhrah da suka iske gidan suna jiransu ta ambata, ita da ƙanen Ramadhan biyu dake aure Mardiyya da Safina, sai wata cousin ɗin su Pa itama mace mai kirki hajiya Mariya, tun sanda za'ai rakkiyar shugaban ƙasa suka shigo tawaga akai masa rakkiya tare da su.
          “Inaga mu barta iya nan kawai, shi mijin nata idan ya shigo da kansa sai ya kaita ɗakin da yaga ya dace su zauna ko?”.
    Cewar Hajiya Mariya. A tare su hajiya mama suka nuna gamsuwa. Sai dai aunty Hannah ta taɓe baki dan tasan sun riga da sun zaɓa musu ɗakunan da zasu rayu ta hanyar saka ƙaramin symbol a saman ƙofar bedrooms ɗin ta ciki bisa shirinsu. Dan haka cikin kwantar da murya tai magana tana duban hajiya Mariya da murmushi. “Amma auntyna ayi amarya a falo? Kodai muyi haƙuri a kaita nata bedroom ɗin yazo ya sameta kamar kowacce amarya shima, koba komai zai tabbatar shima a yau ba shugaban ƙasar NAYA kawai yake ba, ango mai amarya fil a ledarta ne”.
     Yanda ta ƙare maganr da ɗan shakiyanci ya sakasu sakin dariyar manya. Hajiya Mariya mace mai sauƙin kai da fahimta. tace, “Kumafa kin fini gskiya ƴar uwa, dan gara ya tabbatar da gaske muke yau muke son jika da izinin ALLAH”.
     Nan ma dariyar suka sanya, tare da kama Raudha da kanta ke lulluɓe har yanzu, dan sam bama fahimtar zantukan nasu take ba ita kam. Har bedroom ɗin da suka zaɓa mata aka kaita, sai dai kuma an samu akasi ba wanda su aunty Hannah suka tanada dominta bane. Amma batace komaiba, ta barwa ranta zata dawo da kanta tasa Raudha komawa can ɗin cikin sauƙi.
      Anan ma dai su Hajiya Mariya Nasiha suka sake mata mai ratsa jiki, kafin su tattara su fito suna mata sai da safe.
      Sai a yanzu Raudha ta samu damar rushewa da kuka. Ta zame ta kwanta kan katafaren gadon da tasan ko bata kallaba ya haɗu harya gaji. Ji take inama ba'a haifeta tazo duniya ba, inama Abbansu bai saki momynsu ba har sukazo Bingo. Inama ranar batazo idi ba har ƙaddara ta sakata shiga hurumin Alhaji Hameed Harith Taura. Inama... Inama.... Inama. Sai dai bakin alkalami ya bushe, bushewa irin wadda idan akace sai an tausasashi karyewa kawai zaiyi yabar tawada dabin yatsun hannu.

     Kuka taci sosai a wajen har kusan rabawar dare, Ba kuma tako ɗaga mayafin nata ba balle ta kalli wani abu daya shafi ɗakin kamar yanda bata kalli falon da gidan ba sanda zasu shigo, wani wahallen barci da zazzaɓi suka fara fisgarta, duk da kuwa kafin yau tasan tana da burin ganin fadar shugaban ƙasa tamkar kowane ɗan ƙasa. Har lokacin babu angon nata babu alamarsa, ta riga da ta fidda rai da shigowarsa, duk da dama bata sanya ran hakan ba tun farko. Tasan bata kai kodarajar ma'aikatan gidansu ba. Ya amshi aurentane kawai saboda halacci ga kakansa. Bazai sota ba, kamar yanda itama batajin son sa ko kaɗan a ranta. Sai dai tana tausayinsa matsayin shugaban ƙasarta dake cikin wani tarko mai wahalar sha'ani da nazari ga wanda baida yawan maida hankali akan abu. Harga ALLAH tana cikin razanin zantukan su Aunty Hannah har yanzu. Dan ko maganar aunty Hannah taji a kwanaki ukun nan ji take kamar ta saki gudawa a wando saboda razana da mamaki. Yanzu miya kamata tayi a wannan ranar da tasan shugaban ƙasa zai fara kwana a ɗakin da take da tabbacin an haɗa Poison da suka ambata cikin ac ɗin tunda bata da tabbacin saƙonta ya kai ga Bappi zuwa yanzun? Zata fito ta sanar masa ko zata jira taga idan saƙon nata yay nasarar kaiwa, ko yaya zatayi?. Wa zata tunkara da sauran batun ya bata shawara ne? Idan ta samu nasarar daƙile wannan ta poison ɗin ac?. Wane damar yunƙurine da ita a wannan dare na farko a gareta na shiga BAƘAR INUWA tare da shugaban ƙasarta?, idan tayi yinƙurin faɗa masa ya tuhumeta da a ina ta sani wace amsa zata bashi?, idan ta iya faɗa masa komai tanada tabbacin zai yarda ba turotan sukai ba kamar yanda su can yake a garesu zasuyi amfani da ita ne wajen cutar da shi. (“Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke *_BAƘAR INUWA ce_*. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki *_BAƘAR INUWAr_* da sai kin gwammaci *_GARA RANA DA NI!_*) furucinsa a randa ta fara ganinsa a TK special hospital tare da kakansa, cikin halin ciwo take amma ya rumtse ido ya faɗa mata waɗan nan kalaman da tasan sune gaskiyar abinda ke a ransa. Inaga yanzu kuma da take cikin mugun ƙullin da bashi kaɗai ba, mutane da yawa ma idan suka ji bazasu fahimceta ba. Dan kuwa ba kowa ya gama yarda domin ALLAH ta bama dattijo Alhaji Hameed Taura garkuwa ba ranar idi, ciki kuwa harda mijinta, shugaban ƙasarta kuma a yanzun..
     Da wannan tunanin barcin yay galaba a kanta.........✍


*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/15, 1:23 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_Episode 26_*


............A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yana cikin gidan lokacin da aka kawo Raudha, sai dai yana tare da wasu manyan mutanen ƙasar NAYA da sukazo masa gaisuwar barka da shigowa gidan gwamnati. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa da suka shafi ƙasar tare da shi. Zaman saurarensu kawai yayi da tankaɗa da rai-rayar dukan kalamansu. Alhmdllhi zaman kuwa ya masa daɗi duk da yana buƙatar son kwanciya ya huta, dan ya fahimci abubuwa da dama wanda ada bai kawosu cikin ransa ba.
      Bai samu shigowa ba sai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a galabaice yake da son kwanciya da kuma jin yunwa, dan haka ido rufe yashigo ciki batare da tunawa da wanzuwar Raudha matsayin mata kuma amarya a gidan ba.

★★

       Hasken ranar daya leƙo ta cikin labulen window ya haske fuskar Raudha ya sata fara motsa idanun da gyar, dan kanta har yanzu ciwo yake mata har a cikin barci. Idanun ta buɗe da ƙyar kuma a hankali, sai dai hasken ya sakata sake maidasu ta rufe sannan ta kare fuskar da hanunta. Sake buɗewar tai duk da nauyin da yay mata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi, tare da bin jikinta da kalllo zuwa ɗakin, ganin time ya sata tashi a zabure ta diro ƙafafunta bisa tattausan lafiyayyen carpet dake gaban gadon. Bata da nutsuwar cigaba da kallo da mamakin ɗakin, ta nufi ƙofar da zuciyarta ke tabbatar mata toilet ne. Ilai kuwa tayi sa'a dan ta dace da hasashenta. Nan ma bata damu da zaman yima komai kallon ƙurilla ba, duk da akwai abubuwan kallon kuwa bila adadin, tai alwala ta fito.

       Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin data idar da salla. Tsami da ciwon zazzaɓi dake cin ƙashinta ya sata yanke shawarar sake komawa cikin toilet ɗin tayo wanka da ruwa mai ɗumi. Sosai taji daɗin jikinta, sai da ta fito kuma idonta ya raina fata, dan babu kaya ko ɗaya a ɗakin sai na jikinta. Jiri da takeji da rashin mafitar inda zata nema kayan sakawa ya sata faɗawa gadon ta sake kwanciya tare da jan bargo ta ƙudundune. Rawar sanyi ta fara a hankali kafin wani zazzafan zazzaɓi da yafi na daren jiya yay mata rijib.

★★

         Tun kammala tsaftar lungu da saƙo na gidan da farar safiya da ma'aikatan gidan sukai shugaban ma'aikata ya tattaro kowa sukai zaman dakon fitowar first lady dinsu domin gabatar mata da kawunansu. Sai dai kuma har kusan goma na safe babu ita babu alamarta. Shugaban ƙasa ko tun bakwai na safe yabi ta sirintacciyar ƙofar da bai zama lallai kowa na gidan ya gansa ba inba wanda suke a harabar gidan ko aiki ta sashen ba ya fita zuwa office.
    Basu gaji ba suka cigaba da zama har kusan sha ɗaya, wasu a cikinsu dai sai ƙunkuni suke a zuciya da sukar wulaƙancin first lady, waɗan da suke a gidan tun zamanin tsohon shugaban ƙasa na ayyana (ita kuma da salon wulaƙancin da tazo kenan). Wasu ko masu ɗan hankalin ciki na ayyana maybe ango ya angwance ne har first lady ɗin kuma amarya ta gagara fitowa. Haka dai sukaita tunani barkatai kowa da irin nasa hasashen har su aunty Mariya da sukazo kawo akwatinan lefen Raudha suka iso gidan.

         Kusan a tare suka iso da su aunty Hannah da sukazo domin amsa. Sai dai halin da suka iske Raudha a ciki ya sakasu mantawa da wani karɓar lefe ko badawa. Aunty Mariya da tunaninta ya tsaya akan shugaban ƙasa Ramadhan yayi angwancine amma ya tsallake Raudha ya fita sai faɗa takeyi. Dan duk wanda ya dubi yanyin Raudha ɗin, da idanunta da suka koɗe saboda kuka dole kai tsaye ransa ya basa abinda aunty Mariyan ke zargi.
         Duk falo suka koma bayan sun mata sannu, aka bar aunty Hannah kawai tare da ita, acewarta zata taimakawa Raudhan ta gyara jikinta. Dan tasan yaran yanzu da son jiki yanzu haka bata shiga ruwan zafi ba.
      Kalaman aunty Hannah ba ƙaramin ƙona ran Safina ƙanwar shugaban ƙasa dake bi masa a haihuwa da Aina'u da tazo kallon ƙwaf suke ba. Dan koda akace bara a kimtsa Raudhan Safina ta dubata tunda likita ce, ca tai bata iya duba patient na gida.
        Tsaf aunty Mariya ta fahimceta, dan kaf ƴaƴan gimbiy Su'adah idan ka cire Bilkisu da Basma babu mai ƙaunar auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login