Showing 186001 words to 189000 words out of 207756 words

Chapter 63 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

652

bincikensa na jiya ya nuna masa zasuyi taurin kai akan yarda da buƙatar mu, amma idan muka jajirce za'a iya samun nasa ƙila. Sai dai Ramadhan ɗin shine babbar matsala yanzu, saboda akwai yarinyar dake tsaye a kansa game da addu'a hatta azkar baya wasa yanzu safe da yamma, yace inhar tana tare da shi mawuyacine duk wani aiki namu yanzu yay tasiri a kansa dan tanada jajircewa. Hasashena ya bani tabbas shegiyar yarinyarnan ce ƴar karuwai. Maganarsa ta ƙarshe data firgitani itace zaɓin daya bamu akan Ramadhan ɗin, kodai akawar da shi kowa ya rasa shi da yarinyar, kokuma mu haƙur......”
       “Ina bazai yuwuba Mom, wlhy bazan iya haƙura da Ramadhan ba. Idan nai haka ko to tabbaci ban cika mace ba. Har yaushe zuciyarki ta fara tausayine Mom?.”
      “Nima ba tausayi nake jiba Aynah, domin zan iya komai a kanki, ciki kuwa harda kauda duk wanda ya tare min gaba. Tunda muka taso a gidanmu kowa yafi son Su'adah duk da kasantuwarta yarinya mai girman kai da ɗaukar kowa ba komai ba. Ba ƙyau tafini ba, amma ko kaya mukasa kafin a yabamin an yaba nata saboda ta iya tsara ado. Kullum a makaranta takan ɗauki maki na jarabawa fiye da nawa. A gida mahaifinmu yafi sonta fiye da kowane ɗa, dan hatta da shawararsa mai muhimmanci yakanyi da Su'adah baiyi da su Ammy ba. Mu duka ƴaƴan sarki ne amma ita kaɗai ake kira da gimbiya duk da nice babba. A koda yaushe wannan abu nacimun rai, taya zan fita komai amma yazam kullum itace da nasara sama da tawa? Hatta a shekarufa na fita. Abinda ya ƙara baƙanta raina da rayuwa lokacin da muke UK a school, tunda na fara ganin Basheer Hameed Taura na kamu da sonsa. Amma abin mamaki saina tsincesa tare da ƴar uwata Su'adah har sun fara soyayya ni ina nan ina ƙulla yanda zan tunkaresa da tawa soyayyar. Na shiga tashin hankali mara misali Aynah, har takai naji bazan iya jurewaba na tunkaresa da batun. Hummm karkiga irin korar kare da Basheer yamin tare da dogon gargaɗi, tun daga nan karatuna ya shiga hanyar taɓarɓarewa har muka dawo gida babu komai a result ɗina. Itako ta dawo da sakamako mai ƙyau cike da nasarori. Muna dawowa babu ɓata lokaci aka fara shirin aurar damu, ita aka aura mata wanda take so ni aka auramin mahaifinki batare da ina sonsa ba, dan iyayenmu ne suka ƙulla hakan. Watan Su'adah goma cif a Taura House ta haife ɗanta namiji santalele. Niko a lokacin ko ɓatan wata. Naji zafin hakan matuƙa amma naita ƙoƙarin dannewa. Bayan shekara biyu da yayensa ta sake Mardiyya, har lokacin ni babu labari. Nadai taƙaice miki sai a harhuwar Lubnah muka haihu tare, lokacin tanada yara har uku kenan niko 1 kuma mace ke. Na ƙara na biyu ma mace. Wannan ya ƙaramin tsanarta dan koba komai ta ɗarani da namiji kuma ƴaƴanta sunfi nawa. Daɗin daɗawa ɗanta shine ɗa tilo namiji agaba ɗaya Taura family. Nasha auna cutar da Ramadhan amma bai yuwuba saboda kakankinsa kullum nane suke da shi kamar sun san burina. Iyayi nayi Su'adah ta amshi Ramadhan a hanunsu amma sun hanata. Dan haka nasa akai aiki akansa aka tura masa wasu hatsabiban ajanu dakan maidashi tamkar wani mahaukaci. Sai dai mahaukacin ma naso ya koma baki ɗaya hakan bai kasance ba. Tun lokacin aurensa na farko naso ki auresa amma ya nuna baya ra'ayi, dan a yanzu babban burina shine ki auri Ramadhan ki ƙwato mana duk wani abinda Su'adah kejin tanada shi a hannu daya fini, amma kuma sai komai ya lalace bayan mun ɗakko hanyar nasara......”
       “To amma Mom duk da waɗan nan abubuwan shine kike tunanin bazamuyi abinda malam yace ba. Ramadhan nada taurin kai, na tabbatar da wahala ya yarda da aurena, sai dai in uwarsa ce tace zata tsine masa. Idan ma tace hakan shi wannan jakin da aka auramin zai sakeni ne ta cikin sauƙi.....”
        “Inko har duk abinda kika lissafo haka al'amarin zai zama to tabbas dolene Ramadhan ya mutu. Dan kawar da shine kawai zai sakama zuciyata salama akan Su'adah. Tunda bazamu samesaba to kowa ya rasa shikenan ƙurun-ƙus!!....…”
     Wani irin banko ƙofar da akai ne ya dakatar da Aynah data fara dariya, atake sukai diri-diri, gimbiya Su'adah da kanta ke wani irin juyawa tanajin hajijiya ta shiga nuna adda Asmah da hannu sai dai abinda take son faɗa ya gagara fita. Safina datai wani tsalle ta shaƙo wuyan Adda Asmah ta buga da bango, hakanne yasa itama Ayna yin kukan kura a kanta ta shaƙeta. Ƴan biki ne suka fara shigowa a guje saboda ihun da Addah Asmah ta buga na azaba, har goshinta ya fashe jini na zuba......

*_TAURA HOUSE_*

        Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, mai-martaba da ransa ya gama ɓaci yana ƙoƙarin cewa a kirasu sai ga kiran daddyn Aynah ya shigo masa. Cikin tashin hankali ya shiga ambaton kalmar innalillahi.... Har ƙarshe, kafin ya ajiye wayar ya sanarma ƴan falon da duk hankalinsu ke kansa iya abinda Daddyn Aynah ya sanar masa. Zaram Ramadhan ya miƙe amma sai Bappi ya dakatar da shi.
      “Ina zaka kuma?”.
  “Bappi can gidan mana, kanajifa faɗa mizai haɗa Maah da Mom faɗa a duniyar nan?”.
      “Koma miye ai zamu sani yanzu, ko kana mantawa da matsayinka a yanzune wai. Koma ka zauna Basheer yaje ya taho da su”.
    Babu yanda ya iya ya koma ya zauna kamar zaiyi kuka. Zuciyarsa sai kaikawo take da tunanin mike faruwa? Miya faruwa? Mi akayi?. Hakama sauran kowa tunaninsa kenan sai dai babu mai bada gamsashiyyar amsa akai zaman jiran isowarsu.

          ★Kusan awa guda suna zaman jira dan sai da Pa yay jan ido suka yadda suka taho dalilin ita gimbiya Su'adah na tsoron nata mijin, itako Adda Asmah ta raina nata. Wujiga-wijiga suka shigo musamman gimbiya Su'adah da sai da Safina ta bata taimakon gaggawa acan amma da yanzu labarin ba wannan ake ba kuma. Kowa hankalinsa ya tashi da yanayin nasu, musamman ma Ramadhan da cikin rawar jiki yaje ya taya Safina riƙo Maah dake tafiya kamar zata zube ƙasa sai hakki take sama-sama. Shidai Bappi uffan baiceba, binsu kawai yake da kallo hakama mai-martaba. Pa kuwa yanayinsa na nuna ko'a jikinsa dan dama irin wannan ranar yake addu'ar tazo duk da bai san mike faruwa ba shima har yanzun.
      “Inaga muyi abinda ya taramu kamar zaifi”.
   Cewar Pa da alamun ɗaci a muryarsa. Bappi zaiyi magana Mai-martaba ya katsesa.
      “Gaskiya Basheer ya faɗa dan nima sonake na wuce akan lokaci”.
     Bappi ya haɗiye abinda yay niyyar faɗa kawai yana girgiza kansa. Daga haka aka buɗe taro da addu'a sannan aka fara abinda ya tara ɗin game da sauya maganar auren Ramadhan da Aynah.
       Bayan dawowar Ramadhan hayyacinsa, adare ranar Bappi ya sanar masa duk abinda ake ciki, amma sai ya dage akan shi bai taɓa jin son wata Ayna'u ba. Bakuma zai fara a yanzu ba bayan so na ƴan uwantaka dake tsakaninsu. Ya kuma tabbatar masa komi za'ai shi bazai aureta ba matarsa ta ishesa. Babu irin lallashin da Bappi bai masaba a wannan dare amma yace shifa yana akan bakansa.
    Washe gari ma daya dawo gidan kafin yaje ga Raudha maganar da suka fara tattaunawa da Pa da Bappi da Anne harma da su Yafendo da Mai-martaba a waya kenan amma Ramadhan yace yana kan bakansa. Baice zai auri Ayna'u ba kuma ayanzu bazai amsa ba. Dagiyarsa ya sake tabbatar musu akwai sihiri tattare da shi sanda ya dinga musu hauka akan auren Ayna'u garda ɓatawa da su Anne. Wannan dalilin ya sakasu sallamarsa suka tattauna abinda ya dace a tsakaninsu. Mahaifin Aynah shine ya kawo shawarar a rufe komai iya su ranar ɗaurin aure yanada wanda zai aurama Aynah dan a raba gardama komai ya zama ƙarshe basai anta jan zancen ba. Wannan shawara tama kowa, dan haka suka rufe komai hatta Ramadhan baisan da haka ba sai da aka ɗaura aure da wani daban ba shi ɗin ba.
        “ALLAH na gode maka da hakanma ta kasance, Ramadhan ka yafemin, duk halin daka shiga akan Ayna'u hardani a ciki, daban basu goyon bayaba da ba'a nema sabautamin rayuwarka har gashi yau ana iƙirarin kashemin kai ba...”
     Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin kuka hanunta riƙe dana Ramadhan. Tsitt falon yay cikin rashin fahimtar kalaman nata..........✍
     

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*_________________


*_Typing📲_*







*_Episode 71_*


.........“K Su'adah wace maganar banza ce wannan kike haka?”.
     Fulani ta katseta a harzuƙe.
“Ammy karki wani rufe gaskiya da son zuciya. Dole ne sirrin ɓoye ya fito fili, ban taɓa zaton Asmah zata zamemin BAƘAR INUWA ba sai yau. Ashe gara ranar da nake gudu da ita. Asmah bazan taɓa yafe miki ba, kuma insha ALLAH haka zaki ƙare rayuwarki a rashin nasarar da kike gani kina ciki......”
     A harzuƙe Adda Asmah ta yunƙuro zatai magana Fulani ta ƙatseta, hakan yasa mai-martaba bama gimbiya Su'adah damar faɗar duk abinda ke faruwa. Bako ta ɓoye ba, dan tun daga lokacin da riƙon Ramadhan ya koma hanun su Anne hanyoyin da Adda Asmah ta dinga sakata ita da Fulani har zuwa aurensa na farko, da kuma aurensa da Raudha zuwa son haɗasa da Aynah a yanzu da abinda suka jiyo ita da Safina yanzun. Bugu da ƙari dan ma kar Addah Asmah ta musa haka Safina ta ajiye wayarta da tayo recording duk maganganinsu kowa yaji.
      Sallallami kowa ya shigayi a falon, yayinda Adda Asmah ta haukace musu akan ita ƙarya ake mata. Saharri ne kawai saboda gimbiya Su'adah na borin kunya ta hana ɗanta auren ƴarta. Idanma kuwa tayi wani abun ai tare sukayisa. Wannan magana ta Adda Asmah ta sake tada ƙura, dan ko ba kunya gimbiya Su'adah ta daddage ta yarfama Adda Asmah mari,
       “Su'adah ni kika mara?!”.
“An mareki Asmah, kaɗanma kika gani wlhy, na tsaneki, na tsani ganinki, nayi dana sanin saninki matsayin ƴar uwata ciki guda. Kuma insha ALLAH Ramadhan yafi ƙarfinki har abada yafi kuma ƙarfin ƴarki, sai dai ki mutu da baƙin cikina dana zuri'ata. Munafuka kita zugani akan su Anne da suka riƙemin yaro tsakani da ALLAH kina cemin macutane ashe kece azzaluma mai cin amanar zuminci. Da iznin ALLAH ƙarshenki bazai ƙyauba.....”
      “K ce ƙarshenki baizai ƙyauba su'adah”. Adda Asmah ta faɗa tana kaiwa Gimbiya Su'adah mari, amma saita riƙe hanun ta murɗesa dan ko dai gimbiya Su'ada tafita ƙiba dama zuciya.
      Idanu Ramadhan ya sake rumtsewa kansa na juya masa. Yayinda su Bappi keta faman musu magana amma sunƙi sauraren kowa. Dan wata irin hankaɗawa ma Gimbiya Su'adah taima Adda Asmah tai taga-taga zata daɗi Aynah dake kuka ta riƙota.
       Nuna gimbiya Su'adah tai a kausashe. “Su'adah bakici bulus ba wlhy, ina matsayin yayarki kikaimin wannan abubuwan saboda kina auren mai kuɗi. Ni Asma'u nayi alƙawarin saina sabautar da rayuwarki data ahalinki baki ɗaya, dan wlhy sai kinyi dana sanin sanina. Sai kinsan na haifu cikin uwata da ubana, sai kin gwammaci daban kasance jininki ba!!”.
     Tana gama faɗa ta juya zata fita cike da borin kunya. Ana dakatar da ita bata saurari kowa ba taja hanun Aynah suka bar falon tana mai jaddadama gimbiya Su'adah bazata yarda da ƙazafin da sukai mata ita da Safina ba da mari ta jiraci sakamako.. 
      Wannan Al'amari ya firgita kowa ya kuma bama kowa mamaki. Mai-martaba da tun ƙuruciyar yaran nasa ya fahimci halin kowa ya share ƙwallar da suka cika masa idanu.
            “Ni nasan wannan ranar zatazo. Bammayi tunanin sauƙinta zai kasance hakaba. Tabbas Su'adah nada halayen banza da takejin zata iya taka kowa da komai idan taso. Girman kai, ɗaukar kowa ba kowaba duk halayyartace. Sai dai abinda mutane da yawa basa saurin ganewa daga gareta shine, abin kowa bai dameta ba. Su'adah bazaka taɓa jinta ta zauna surutu akan damuwa da cigaban wani ba, sannan dan taga wani da abu bazakaga ɓacin rai daga gareta ba balle damuwar kishinsa. Itako Asma'u da kuke gani, tanada sauƙin kai da son mutane, sai dai tanada nunkufurci da hassadar bata yarda kowa ya fita ba. Waɗan nan halayen nasu sune suka banbantasu, dan ita Hassada na cinye ayyukan bayi, tana maida mai son yin nasara bayan wanda yake gani bai kai ya fisa ba. Sai kaga mutum da halayen banza. Kai kullum cikin ibada da sauransu amma yanata samun nasariri kai sun gagara zuwa gareka karasa yaya haka? Nafi wane komai a rayuwa mizaisa ya dinga bani tazara? Amsar itace hassada. Hassada na ƙwace nasarori, ga wanda baida ita tana bashi nasarori koda bai kaika ba. Wasu suna tunanin Hassada itace kawai naga wane da abu banji daɗi ba. Hassada na zuwa kashi-kashi a cikin ayyuka.
         _Kaji kai kaɗai kake son kai nasara a rayuwa. Kaji kanajin zafin wanda kafi da komai na rayuwa ya samu wani abu kai baka samu ba. Ka dinga damuwa da yawan maganar cigaban wane. Mutum ya gina ƙyaƙyƙyawan abu ka ruguza masa. Misali mutanen da ke fidda mana littafi ko zuwa su saya dan su yaɗa hassada ce. Shiyyasa zasuga kullum suna wahalar banza da tunanin dakushemu mukuma munata nasara a rayuwarmu domin basu isa hanamu samun abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddararmu ba._
      Hassada na shigowa cikin ayyukan mutane daban-daban ƙarama ko babba, ka sani ko baka sani ba. ALLAH ya rabamu da hassada. Ka tsarkake mana zukatanmu akoda yaushe. Ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABINMU (S.A.W).
     Nasiha sosai mai-martaba yayi a wajen harda Bappi, daga karshe aka sake rufe taron da addu'a kowa ya kama gabansa..
   
      A ranar aka miƙa amare ɗakunansu zukatan wasu duk babu daɗi. Musamman ma gimbiya Su'adah dake kwance babu lafiya, dan jininta ya hau matuƙa sai dai gyaran ALLAH. Amma Safina da Mardiyya na tsaye a kanta harma da Fulani.

    Raudha dai batasan mike faruwa ba. Dan koda Ramadhan ya dawo sukuku baice mata komai ba ita kuma bata tambayesa ba saboda ba daɗin jikin takejiba sam. Ko lokacin da aka kawo su Bilkisu har falonsa suyi sallama a taƙaice ya musu nasiha ya sallamesu. Bilkisu kuwa ta rungume Raudha suna kuka har abin ya bama wasu mamaki dan da'alama akwai shaƙuwa sosai a tattare da su. Ganin abun nasu bana wasa bane Ramadhan ya rabasu da ƙyar ya rungume matarsa duk da mutane dake wajen bai nuna ya san da su ba. Bayan wucewarsu ya jima yana lallashinta, daga ƙarshe ma yasata sukai kwanciyarsu.

      Dan hatta da Aynah ta tare nata gidan bisa tursasawar mai-martaba. Hasalima shi da kansa yay mata rakkiya har gidan mijin nata ya kuma tabbatar ma mijin ko da wasa yaji a ransa zai iya rabuwa da Aynah duk abinda zatai, to lallai sai ya hukuntashi shima bawai ita kaɗaiba.
    To Alhmdllh, mai-martaba ma dan bai san wanene Aminu ba, idan hatsabibanci Aynah takeji ya taketa ya shanye. Idan iskanci ne gidan ta taras.

*______________________*
 
        Har biki ya tashi lafiya kowa ya kama gabansa babu wanda ya sake tada maganar. Sai dai gimbiya Su'adah da jikinta keta sake tsanani duk da kulawar da take samu. Hakama Raudha ciwo ta kwanta sosai hakan sai ya raba hankalin Ramadhan biyu. Ga kwanakin hutunsu ya ƙare dama sati ɗaya ne kacal. Yanda jikin Maah ɗin keta ƙara tsanani ya saka Pa yanke shawarar tafiya taga likitan ta, dan haka randa su Ramadhan zasu koma government house aranar suma sukai shirin wucewa duk da Anne da taƙi yarda Raudha ta koma can gidan sai da Bappi ya lallaɓata. Aka kuma haɗata da su Basma.
     Tasha kuka duk da ita shaidace a yanzu mijin nata ya dawo dai-dai, sai damuwar da take hange cikin idanunsa da bata san ta micece ba. Ba kuma ta matsa da tambayaba tanata masa addu'ar dacewa dai da warwarewar matsalar tasa...
        
          Abubuwa sun lafa sai dai bazamuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login