Showing 93001 words to 96000 words out of 207756 words
ga wanda ma suka haifi ubanninsu a wajen ba'a su ba. Wannan zaɓin speakers yasa a ranar sau kusan uku jam'iyyar da shugaban ƙasa ya fito suna zaman meeting wanda ko guda a ciki ba'a gayyaci wani na jikin shugaban ƙasar ba kuma.
Raudha kanta da basanin minene siyasa ko mulki tai ba zaɓin ya mata ɗari bisa ɗari. Ta kuma sakasu a cikin addu'ointa sosai akan ALLAH ya cigaba da tallafa musu wajen ɗaura mutanen kirki bisa muƙaman da dole sai dasu ne mulkinsa zai tafi cikin nasara da sauke hakki.
Bayan fidda speakers shugaban ƙasa ya cigaba da wasu naɗe-naɗe da suka shafi office nashi da suka sake bada mamaki, masu bashi shawara akan fanoni da dama na mulkinsa da sauransu akwai manyan dattijai da akasan su akasan jajircewarsu wajen faɗar gaskiya da yin gaskiya akan ayyukansu da ma tsaurinsu. A zaɓin nasa ya kasance akwai matasa masu jini a jika irinsa ya muƙar sake ɗaukar hankalin talakawan ƙasa a kansa, har yanda wasu ke nuna masa ƙauna ma sai ya baka tsoro. Yayinda dattijan ƙasar NAYA musamman waɗanda suka ƙwallafa rai a mulkin suka fara shaƙa daga takun na shugaban ƙasa, dan suna masa wani kallone kamar na TAKUN SAƘAr nuna kishin matasan ƙasar da mayar musu murtanin sun babake komai a baya suma. Hakan yasa ba ƴan jam'iyyarsa kawai ba, har wasu ƴan jam'iyyun da sarakunan gargajiya suna zaman yin meeting da tattauna take-taken Ramadhan ɗin.
Sarai yana jin wasu abubuwan dake faruwa, amm sai yay biris kamar kunnensa a toshe yake, idanunsa kuma a makance. Yay matuƙar maida hankali wajen tsara yanda yake buƙata a tantance masa cabinet nashi da taimakon mayan mutanen dake zagaye da shi na kirki duk da akwai masu fuska biyu kuma a cikinsu dai suma harma a matasan, kafin su amshi muƙaman da ake burin bama kowannensu..
_________★_________
A daren yau manyan dattijan nan, da al'amuransu ke keɓantattu ga al'ummar ƙasa sukai zaman tattaunawa na musamman a tsakaninsu, dan gane da ganin bayan Alhaji Hameed Taura, da zukatansu ke raya musu komai shugaban ƙasa Ramadhan yanayine bisa umarninsa. Wato a zahiri dai Ramadhan shine shugaban ƙasar NAYA, amma a baɗini Alhaji Hameed Taura shike mulki. kamar dai yanda suke ga sauran shuwagabanin baya, wanda shima Ramadhan ɗin haka suka tsara a kansa. Sai dai tun kan aje ko'ina ga komai na shirin sukurkurce musu.
A cikin tattaunawar tasu ne. Oga kwata-kwata ke ambaton “A wannan gaɓar ya kamata matar shugaban ƙasa ta nema office nata”.
Cikin mamaki sauran duk suka dubesa, dan sam basu fahimci muhimmancin yin hakan ba a garesu. Ɗan murmushi ya saki tare da ɗaukar kofin abinda ke gabansa ya zuƙa ya ajiye. Cikin ɗacin rai yace, “Na fahimci a yanzu da kujerar first lady kawai zamu iya fara yaƙar wannan yaron tunkan al'amarin nasa ya ƙara nisan kiwon da bola sai ta fimu daraja”.
“Amma ranka ya daɗe, ko ka manta first lady sweet seventeen ce. Sannan girman ƙawai, iyakar karatunta o level ne. Babu abinda ta taɓa sani a siyasa balle sha'anin mulki, rayuwarma yaushe ta gama fahimtarta?”.
“Duk wannan raunin nata ne ya sani tunanin a bata office”.
Shiru sukai suna sake ninƙaya a nazari, dan har yanzu basuga wani alfanun hakan ba a garesu sam sai tsagwaron kwamacala da shirmen da ƙasar tasu ke tunkara. To amma sun san halin oga da shegen zakule-zakule. Sai dai duk sanda ya zaƙulo abu zaka samu mai muhimmanci ne a garesu daga baya....
★★★
A lokacin da suke can suna tattauna yanda first lady Raudha Dauda Hutawa data koma *_Raudha Ramadhan Taura_* zata mallaki Office, anan Taura House Ramadhan dake ganawar sirri da kakansa ke zaune a keɓantaccen falon baƙi na Alhaji Hameed ɗin suna tattauna muhimman batutuwa. A cikin tattaunawar tasu ne kuma Alhaji Hameed Taura yay ma Ramadhan batun saka Raudha a makaranta ta cigaba da karatu, dan hakan nada matuƙar muhimmanci a mulkinsa da ita kanta.
Ramadhan dake kai yankan kilishi bakinsa yay wani ɗan guntun murmushi da baida maraba da takaici, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “Bappi wannan shi naso nuna maka akan auren nan. Taya za'ai shugaban ƙasa da mata mai matakin o lavel a ilimi, sannan ƴar shekara sha takwas tayi yarinta da yawa?”.
“Wannan duk ba damuwa bane Ramadhan, sai ma kafi jin daɗin control nata yanda kakeso, zakace nina faɗa maka nan gaba idan idanunta suka buɗe akan abinda kake ganin kai bazata iya ba”.
“To amma Bappi ni a wannan gaɓar ma banga amfanin yin karatun nata ba, dan nidai yanzu bazan bari ta ƙetare ƙasar NAYA ƙaro ilimi ba, sannan bani da sha'awar iyalina shiga harkar siyasar nan”.
“Sosai tunaninka ya sani farin ciki, sai dai kuma baida nasaba da daƙile mata zancen cigaba da neman iliminta. Ba lallai saitaje ƙetaren NAYA ba. A cikin ƙasar nan dama ya kama tayi, kai kanka hakan kimace a gareka, da ƙara bama talakawa hope game da mulkinka. Zata iya shiga duk jami'ar da takeso a ƙasar nan, kokuma tayi online school na ƙasashen ketaren inma suke take so, amma zamanta babu karatu bazai yuwuba. Koda bazata shiga siyasa ba akwai abubuwa da yawa da suke bukatarta a mulkin koda kai da ita baƙwa buƙatar ta kasance a cikinsu”.
Ɗan jimm Ramadhan yayi, sai kuma yaɗan ɗage kafaɗa da cigaba da cin kilishinsa. “ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi”. Kawai ya faɗa ya tsuke bakinsa. Shima Bappi komai bai sake cewa akan hakan ba. Bayan murmushi da yay ma sai ya ɗakko masa wani zancen daya shafesu kuma..........✍
[6/22, 7:58 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62b0ba6cf0deac225fe20185
*_Episode 33_*
..........Yau ta kasance asabar, Ramadhan na gida bai fita ko'ina ba, dan yana buƙatar hutu saboda doctor ɗinsa ya tabbatar masa sugar nashi yayi low, sannan jininsa ya haura sama alamar hayaniya ta fara masa yawa. Shawarar doctor yabi, dan ayanzu yana matukar buƙatar ganin ingancin lafiyarsa fiye da baya, kodan ya samu damar sauke hakkin mutane a kansa. Barcin safe yayi sosai har takai su Raudha basuyi tunanin yana a gidan ba.
Kusan sha biyun rana su Lubnah na baje a bedroom na sama, wanda a tsari shugaban ƙasa da iyalansa ne kawai keda hurumin zaman cikinsu. Zaune suke a baje kowa na sabgar gabansa, ga kayan ciye-ciye da suka saka kuku ya shirya musu, wasuko anyi order nasune a wajaje daban-daban. Su duka ukun babu mai shigar mutunci, daga mai bomshot da best sai mai 3quarter singlet.
A can falon ƙasa, wanda shine na uku a jerin faluka uku da kai tsaye zai kawowa sashen iyalan shugaban kasa Raudha da Basma da Bilkisu ne zaune. Bilkisu na daga gefe tana aikin nata na karatu da bincike-bincike, Basma da Raudha na kallo a lap-top ɗin Basma ɗin cike da shauƙin film ɗin. Sai mama ladi da ke gefensu tana saƙar hannu, wadda alama ya nuna kayan sanyi ne na yara. Sai dai rabin hankalinta nakan television da ake nuna maimaicin labaran daren jiya.
Sanye cikin ƙananun kaya nashan iska ya fito, baƙin trouser dogo mai layin fari guda biyu a gefe da gefe, sai baƙar t-shirt. Kayan sun masa matuƙar kyau kasancewar sa mai hasken fata, sai dai fuskar sam babu ɗigon fara'a alamar barcin da yay bai gama sakinsa ba, duk da dai dama bawai ya cika yin fara'ar bane sai ga wanda ya gadama.
Tsaf falon yake a tsaftace, ga wani ƙamshi na musaman na tashi mai saka nutsuwa da kwanciyar hankali. Da ga can gefe cike tebirin dining yake da kayan breakfast kamar yanda kuku bai gajiya da shiryawa a kullum, duk da bai taɓa ganin alamar wanda akeyi da shi yaci ba sai matar gidan kawai.
Duk da yunwar dake cin cikinsa, maimakon ya nufi dining ɗin kai tsaye sai ya samu ɗaya da ga cikin kujerun falon ya zauna. Yana ƙoƙarin kunna television su Lubnah suka fito daga corridor ɗin bedrooms na Raudha suna kwasar dariya.
Turus sukayi a tsaye suna duban wanda basuyi tunanin gani ba zaune hakimce a falon. Yayin da Ramadhan yay tsam shima domin shigar muryoyin dariyar ƙanen nasa cikin kunnensa da shi sam baima san da zamansu a gidan ba ko yace ya manta da batun zuwansu.. Duk da kuwa Maa ta jima da sanar masa zasu dawo nan da zama kafin ta dawo. Amma jin Bappi da Anne babu wanda ya masa maganar ya sashi ɗaukar mahaifiyar tasa ta janye batun duk da a yanzu haka tana ƙasar England ita da Pa.
A hankali ya ɗago idanunsa ya zuba musu, tare da watsa musu wani irin gigitaccen kallo daya gama kiɗima su gaba ɗaya har fitsari na neman kufcema wasun su, dan a rayuwarsa yayi matuƙar tsanar shigar banza. Shi ko akan iyalinsa ne bai cika son ganin matarsa da ƙananun kaya ba anyhow.
Sanin dokarsa ya saka Lubnah da Muneera kwasa a guje suka koma hanyar da suka fito, yayinda Aina ta daburce matuƙa, dan tun randa ya kamata a U.S tana aikata abinda bai dace ba suke wasan ɓuya, ta kuma haramtawa kanta zama duk inda zasu haɗun tunda ya dawo NAYA. Ko maganar haɗata aure da ake da shi, tana matuƙar buƙatar hakan, dan tana mutuwar son Ramadhan tunba yanzu ba, sai dai tana fargaba da sanin mawuyacin haline ya amince da aurenta, shiyyasa tafi yarda da zuga mahaifiyarta (Adda Asmah) akan tarwatsa auren Ramadhan ɗin kawai.
Tun kafin abinda ta hango a cikin idanunsa ya fita a fatar bakinsa ya sake gigitata ta kai durƙushe ƙasa, sai kawai ta tafi da rarrafe dan batasan taya zata miƙe ma tayi gudun ba tsabar rikicewa..
Wani irin numfashi Ramadhan yaja na tsananin ɓacin rai, lip nashi ya tura cikin baki ya cija da ƙarfi, yayinda zuciyarsa ke ambaton sunayen ALLAH domin son yin controling fushinsa. Tsahon mintuna biyu ya buɗe idanunsa, tare da miƙa hannu ya ɗauka telephone ɗin dake bisa copy table na kusa da shi. Sai kuma yay shiru da tunanin wayar ina zai kira?.
Telephone ɗin ɗakin Raudha ya kira. Sai dai harta katse ba'a ɗauka ba. Siririn tsaki yaja, tare da maida akalar kiran zuwa ta falon ƙasa, dan iya nan yasan zata iya zama inhar bata bedroom da nan falon upstairs
Da sauri Mama Ladi data ɗaga kira ta mikoma Raudha da suka maida dukan hankalinsu a kallo ita da Basma kan wayar. Ta ɗago da sauri tana duban mama ladi dake miko mata kan wayar, suma su Bilkisu ita suke kallo. “Ranki ya daɗe inaga daga sama ne kiran nan dan ba'ai magana ba”.
Komai Raudha batace ba ta kai wayar kunnenta da tunanin kosu Lubnah ne.
“Ameenatu! Ki sameni yanzun nan”.
Duk da ba kowa ke kiranta da wannan sunan ba hakan bai hana gabanta faɗuwa ba tai saurin duban Upstairs ɗin a ɗan firgice. Jin ƙarar ajiye wayar da yay ya saka Raudha mikewa har tana cin tuntuɓe da ƙafar Basma ALLAH dai ya hanata kifawa Bilkisu ta tareta.
“Yi a hankali aunty Raudha karki ji ciwo”.
Kai kawai ta iya jinjinama Bilkisun tai ƙoƙarin fara haura steps ɗin da ɗan gudu-gudu, duk da hakan bai hana bayyana nutsuwarta a tafiya ba, wadda ta zame mata halitta tun bayan da sayyadi Abubakar ya saita mata rayuwa.
Ramadhan dake zaton ganin bullowarta dama daga downstairs ɗin ya shiga watsa mata kallon da tunkan ta karaso hanjin cikinta suka fara barin jikin sauran kayan ciki suna kaɗawa. Tana masa kallon mutum mai ƙarancin kirki amma kallon da yake jifanta da shi a yau yayi tsanani da yawa, gashi batasan akan mi yake yi ɗinba kuma. Dan koda wasa bata taɓa kawoma ranta tunanin zaman su Lubnah a saman zai iya fusatashi ba tunda taga dai ƴan uwansa ne ai.
Bilkisu ta ture books ɗin gabanta ta miƙe da sauri tana gyara gyalen jallabiyar jikinta. Dan bata raba ɗayan biyu su Aina'u ne. Upstairs ɗin ta fara haurawa da sauri-sauri itama. Dan haka Basma ta miƙe tabi bayanta.
Hawowar su Bilkisu saman yayi dai-dai da ƙarasawar Raudha daketa ambaton sunan ALLAH gabansa, dan bata taɓa cin karo da irin kallon muzanci da yake mata ba a wajen wani mahaluki......
Turus Basma da Bilkisu sukai ganin wanda basuyi zaton gani ba suma. Dan duk zatonsu su Aina ne ai sukai kiran Raudhan ta landline. Ganin fuskar yayan nasu ya tada hankalin su Bilkisu dan kowa yasan idan yay fushi fita hayyacinsa yakeyi. Duk da dai basu san dalilin kiran Raudhan ba, amma tsoron da suka gani akan fuskarta ya sakasu shan jinin jikinsu suma. Cikin ƙarfin hali Bilkisu ta ambaci sunansa cike da ladabi da shakka.
“Yaya!”.
Wani shegen kallo ya watsamata itama, sai dai kafin yace komai wayar jikinsa ta hau ring. Yasan Maa ce, dan haka ya ɗaga yana jan numfashi da ƙyar tsabar ɓacin rai, baya raba dayan biyu su Muneera ne sukai kiranta. Ba wata magana ta bari sukai mai tsayi ba, dan bata bashi damar cewa komai ba ta yanke wayar.
Ransa ne ya ƙara ɓaci, Yana ajiye wayar Bilkisu data fahimci wadda ta kirasa saboda sunanta daya ambata a farkon wayar takai zaune gabansa a ƙasa. Cikin tausasa harshe ta ce, “Am so sorry Yayanmu. Wlhy ba laifin Aunty Raudha bane ba.....” tsaf ta zayyane masa komai a randa sukazo. Komai baice ba, sai dai ya tura hanunsa cikin gashinsa, tare da jingina bayansa da kujerar ya wani lumshe ido. Tsahon minti ɗaya kafin ya buɗesu a hankali suka sauka akan Raudha da Basma ta riƙema hannu gam-gam saboda lura da yanda jikinta ke rawa ɗazun. Tasan dolene taji tsoron yayansu a irin yanayin nan tunda ba taɓa gani taiba maybe, kosu da suka saba gani a duk sanda ya birkice irin haka tsananin tsoronsa suke.
Janyewa yay ya maida ga Basma. “Kiramin su”.
Kanta ta jinjina masa, kafin ta zare hanunta da cewa “To”.
Da hannu ya nunama Raudha kujerar gefensa. Zama tai a ɗarare tana cigaba da ambaton sunayen ALLAH.
Babu wani jimawa suka fito su duka kowacce da zabgegen hijjab kamar matan liman. Gabansa duk suka ƙarasa suka zube kowacce kai a ƙasa. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama Raudha ba. Duk da halin da take ciki itama a ranta al'ajabin yanda suke tsoronsa takeyi, gasu dai manya da su suma. Ita dai tana zaune a inda take, yayinda har Basma a yanzu take a gabansa duƙe.
Bai wani tsaya tambayarsu kojin ta bakinsu ba ya fara magana a nutse amma muryansa a kausashe. “Na baku mintuna goma kacal ku tattara komatsanku ku koma sashen baƙi. Idan kuma har na kuma ganin wata da ƴan iskan kaya a jikinta wlhy-wlhy bazata sake taka ƙafarta gidan nan ba harna barsa ƴan iska kawai. Matata kuma karku fasa mata duk abinda kukai niyya tare da kai magana wa Maa ina dai-dai da ku”.
Daga haka yay musu nuni da su miƙe su bar wajen. Sosai Raudha tai mutuwar tsaye akan furucinsa na ƙarshe. *_“Matata kuma karku fasa mata duk abinda kukai niyya da kai magana wa Maa ina dai-dai da ku”_*. (Minene dalilinsa?). Bata da mai bata amsar nan, dan haka taɗan saci kallonsa ta gefen ido. Ta janye a hankali saboda wani shegen nishin takaici da taji an saki a kusa da ita. Muneera ce, ta watsa mata wani irin kallo na zaki san komu su waye tabi bayan su Lubnah da tuni sun nufi ɗakunan nasu tattare kayansu.
Dafata Basma tayi ganin kamar ta tsorata da abinda Muneera tayi, cikin raɗa yanda Yayansu bazai ji ba tace, “Karki wani damu kanki babu abinda suka isa miki, dan wlhy duk tsoron Yaya suke kamar mutuwarsu. Iyakar iskancinsu na bayan idonsa ne. Kuma tunda muma muna gidan ko kallon banza suka miki sai yaji”.
Kanta ta girgizama Basmam a hankali itama tace, “A'a dan ALLAH karku ƙara faɗa masa Basma. Wannan ma da kun bari na masa bayani yanda bazai zargesu ba”.
“Tab wai tsoronsu kike ji? To wlhy kima cire, dan su aunty Lubnah wutar karane sai da izo. karki yarda suga rauninki zakisha wahala. Gara ki fito musu a mara kunya kema dan nan gidankine kowa yazo zai zaunane karƙashin ikonki. Yanzu dai ki samu Yayan ki bashi haƙuri, dan yana son idan yay fushi koda baka da laifi ka bashi haƙuri”.
Duk da maganganun Basma sunyi tasiri a ranta sai bata nuna ba. Harga ALLAH kuma tanajin daɗin zama da Basma da Bilkisu a gidan
Ganin kowa ya fice a falon harsu Aina riki-riki da akwatina yasa Raudha yanke bin shawarar Basma. Sai da ta ɗan ƙara jan sakanni da fitarsu kafin ta dubi inda yake kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki. Duk da yaji alamar idonta a kansa bai motsa ba, Raudha dake a zaune kanta a ƙasa ta ƙara damke bakin ɗankwalin atamfar jikinta data yafo a kanta sannan ta ɗan zamo jikinta a kujerar kaɗa. Zani da rigane sun mata matuƙar ƙyau dan anyi ɗinkin dai-dai jikinta.
“Dan ALLAH kayi haƙuri baza'a sake ba”. Tai maganar a hankali kamar kuma zata fashe da kuka.
Anan ɗin ma baiko motsaba. Sai dai yajita sarai dan shi mutum ne mai ƙarfin ji shiyyasa Anne ko gulmarsa batayi indai yana gidan. Tsawon mintuna biyu, har Raudha ta sake buɗe baki zata sake bashi haƙurin sai tai shiru saboda ɗagowar da yay daga ɗan jingina jikinsa da yayi da kujera yana sauke mayatattun idanunsa a kanta. Zata iya jure zama