Showing 141001 words to 144000 words out of 207756 words

Chapter 48 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1257

ko tv babu, wama yake da lokacin zaman kallo, yo fitinar Abbansu ma tasa idan rashin kuɗi ya ciyosa ya kwashe ya siyar kona wacece a gidan babu ubanda ya isa yace wani abu kuma. Bata da tarkacen ƙawaye, idan ma kika kasance mai rawar kai a aji bata shiga harkarki, sannan bata zaman fira in group daga boko har islamiyya, hasalima faɗa takema su Safara'u idan taga sunayi. Tasan dole ne ta shiga ruɗani da sabon yanayin da Ramadhan ke son jefasu a tsakanin nan. A wani bangaren kuma tanada gaskiyarta akan shiga ruɗani. Tun farko ta sakama ranta Ramadhan yafi ƙarfinta. Shima kansa ya tabbatar mata yafi ƙarfin nata. Mahaifiyarsa da danginsa harma da mutanen duniya sun tabbatar. A baya babu abinda take gani a cikin idanunsa sai saɓanin abinda take gani a yanzun, duk da dai harga ALLAH tasan bai taɓa muzantata da baki ba, bai taɓa hantararta ko wulaƙantata ba, kawai dai baya shiga sabgarta. Dolene canjawarsa a ƙanƙanin lokaci ta zama abu mai rikitarwa a gareta. Amma tayi alƙawarin hakan bazaisa ta taɓa saɓama umarni ko hani daga garesaba, zatai masa biyayya matsayinsa na miji inhar bai hau turbar sabama ALLAH ba. Zata yi biyayya ga umarnin UBANGIJI akan binyayya ga miji da dokokin aure kodan tabbatar da martabar tarbiyyarta data gidansu a idanunsa saɓanin wadda aka sanar masa da wadda duniya take kallon ahalinta dana iyayenta da shi......
      Ƙarar landline ɗin ɗakin ta katse mata tunaninta, gabanta ya faɗi. Sai dai tunanin ko Mama Ladi ne ya sata buɗe kanta a bargon ta ɗaga.
       “Ustazah! Haka aka koya muki kula da mijinne wai a islamiyyar?”.
       Batama san bakinta ya suɓuceba wajen faɗin, “Wlhy Yaya Ramadhan zaka kasheni da raina!”.
        Murmushi yay daga can, “Idan na kasheki Ustazah dawa zanyi angwancin?”.
       “Na shiga uku”.
Dariyar da batasan ya iyaba ya ƙyalƙyale da ita daga can. Tasa hannu ta rufe fuska tamkar tana gabansa. A zuciyarta ɗunbin mamaki da al'ajab ne danƙare. (Dama haka yake kokuwa yanzune ya canja.....?)
     “Ina jiranki kizo ki bani abinci kar yunwa ta hallakani ga ciwo”. Ya faɗa cikin katse mata tunani yana yanke wayar.
       
         Baki buɗe Ramadhan dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya lap-top a cinyarsa alamar aiki yake ya saki yana kallon Raudha data shigo bayan tayi knocking ya bata izinin shigowa. (Lallai yarinyar nan kanta da motsi) ya ambata a ransa yana ɗauke idonsa gareta. Sanye yake cikin kaya masu taushi baƙaƙe. Duk da badan kwalliya ya saka ba sun masa ƙyau da sake fiddo hasken fatarsa. Idanunsa dake cike da abubuwa kashi-kashi ya janye yana maidawa ga aikin gabansa.
        Gabansa Raudha ta ƙaraso bayan ta ɗakko basket abincin data shirya masa tun ɗazun, komai a cooler yake dan haka bata tunanin sun huce. Table ɗin ta kalla inda ƙafarsace fara tas a miƙe, ganinta da abincin kuma baisa ya sauke ba. Kallonsa taɗan sata a ranta tana gulmarsa ganin yanda ya tsuke fuska tamkar bashi ya gama mata abun kunya ɗazun ba (Humm da gaske mutumin nan dai yanada aljanu). A fili kam sai cewa tai “Ga abincin”.
     Banza yay mata kamar baiji ba. Ta sake maimaitawa cikin marairaice fuskarta dake cikin niƙab data sako. Ganin yaƙi nuna yasan da zamanta a wajen sai takai durƙushe a gabansa tana dire basket ɗin a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsoro naji ɗazu ɗin”.
     Nanma banza yay mata yana cigaba da sarrafa keyboard ɗin lap-top ɗinsa hankali kwance. Sai dai ya fahimci maganar tata nada alaƙa da tunanin gudun datai ɗazun ne.
       “Dan ALLAH!”.
Ta sake faɗa a hankali. Idanunsa da har yanzu jan yaƙi kwaranyewa a cikinsu ya ɗan rumtse, ga mura ga fitina da yaketa ƙoƙarin haɗiyewa taƙi hadiyuwa. Iska ya ɗan furzar dakai hanunsa saman goshi ya shafa, tunda tace ALLAH kuma ta gama da shi. Amma hakan bai hanashi yin magana a daƙile ba.
       “Dan kin rainani ni zakizoma da wannan abun a fuska?!”.
   (Oh ALLAH, dama akan niƙaff ne?) ta faɗa a zuciyarta tana lumshe ido. A fili kam hannayenta ta matse waje guda. Cikin sanyin muryarta dake tsumashi batun yau ba tace, “Dan ALLAH kayi haƙuri ALLAH kunyarka nakeji”.
         (Kunya) ya maimaita kalmar a ransa yana ɗan bubbuga yatsansa bisa lips ɗinsa idonsa a kanta. “Okay! Naji ciresa to, inba hakaba kuma ni bashi zan cire ba, wancan zan cire”.
       Kukane kawai ya ragema Raudha ta fashe da shi. Mutumin nan so yake kawai ya zautar da ita a gidan nan, dan sarai ta fahimci abinda yake nufin zai cire. Babu yanda ta iya dole takai hannu tana kwance niƙaff ɗin sai dai ta rumtse idanunta... Hararta yay ya ɗauke idanunsa dan ya tsani ganin hawayen nan.
Jin bai tanka ba yasata satar kallonsa sai taga hankalinsa baya gareta. Saurin saka nikab ɗin tai ta goge hawayen. Kafin ta ɗaura basket ɗin saman table ɗin ganin ya sauke ƙafafun nasa. Abincin ta haɗa masa ranta cike da fatan ALLAH yasa ya barta ta koma ɗakinta. Sai dai addu'ar tata bata amsu ba. Dan bayan ya gama shan ƙamshinsa lap-top ɗin ya ajiye gefe tare da nuna mata gefensa fuska a tsuke.
        (Nidai tawa ta ƙare) ta ambata a ranta tana miƙewa tabi umarninsa dan har tafara jin nutsuwa ganin ɗan sake mata da yakeyi kwana biyun nan, sam bazataso su koma ƴar gidan jiya ba. Duk da 2seater ce sai da taɗan takura sakamakon yanayin nasa zaman. Lap-top ɗinsa ya ɗauka ya maida a cinya yana faɗin “Ohya bani, dan hukun cinki kenan yau a gidan nan ciyar dani abinci daga nan har dare”. Ya matso da fuskarsa gab da tata. Cikin raɗa ya ƙarasa faɗin, “Inba hakaba kuma na rantse ni zan c....”
      A zabure ta ɗaura hanunta saman bakinsa ta toshe, tsabar rikicewa harda tallafo ƙeyarsa da ɗayan hanunta”.
        “Ni dai gaskiya-gaskiya to nama fasa abotar a kwance wlhy”.
     Kaɗan ya rage dariya ta kufce masa. amma yay dauriyar dakewa yana bin fuskarta da idanun ke rumtse da bakinta dake maganar da kallo. Ga jikinta sai tsuma yake. Sosai yake jin nishaɗi idan ya ganta a yanayi na tsorata ko kunyarsa. Hanunsa yasa ya janye nata hanun daga bakinsa harda ɗan bugesa.
        “Ustazah yaushe kika koma hakane wai? To ai mai raba wannan abotar sai mutuwa mun ƙulla kenan”.
      “To an taɓa dole ne?”.
Ta faɗa cikin waro idanu tana sake ƙwaɓe fuska. Hancinta ya lakata kaɗan da ɗage gira sama ya kashe mata ido ɗaya. “Abota dani dolene yarinya. Dama kika samu na zaɓeki zakimin iyayi”. Yaƙare maganar da wani salon taɓe baki kamar wani mace. Hakan sai yay bala'in saka Raudha dariyar da batai niyya ba. Sosai murmushin fuskarsa ya ƙara faɗi shima. Sai dai tana gama dariyar ta ɗago da faɗin, “ALLAH yanda kayi sai kace mace. Baba Laran gidanmu haka take idan tana faɗa”.
      Fuska ya tsuke da kwaɓeta yana hararta. “Waye macen?”.
           Dariyar dake yalwace da fuskarta ta sake ƙyalƙyalewa da ita tana kai hannu ta danne bakin. Yayinda shi kuma ya kai hannu ya mangare mata kai ransa cikeda nishaɗi. Ganin taƙi daina dariyar ya sake bata ranƙwashi....
       “Wayyo Mommyna zai ɓararmin da karatu na”.
    (Kan uban nan) ya faɗa a ransa dariya na kufce masa shima. cak ta tsaya da tata dariyar ta zuba masa ido batare data sani ba. Dan wani irin ƙyau dariyar tai masa. haƙoransa duka sun bayyana ba kuma yana yinta a haukace bane...
      “Sharri kika koma kuma Ustazah?”. Ya faɗa da sake kai mata ranƙwashi yana dariyar har sannan sai ta duƙe kan nata ya sauka bisa cinyarsa hularta na zamewa ta faɗi ƙasa. Ƙoƙarin ɗagota ya shigayi amma taƙi yarda. cakulkulo ya fara mata a wuya, cusa kanta take sakeyi tana dariya da ƙoƙarin ture hanunsa.
      Jinsa yake a wani irin nishaɗi daya jima baiyiba a rayuwarsa. Zai iya rantsuwa tun bayan rasuwar Haseenahr sa da Amnah bai sake farin ciki makamancin hakan ba da yake a kwanakin nan musamman yanzu. Yanda gashinta data ɗaure ke reto ya sashi kama ribbon ɗin ya zare gashin ya tarwatse. Da sauri Raudha ta ɗago dan batama san hulan ya zame kansa ba. Sai kuma kunya ta kamata jin ya tura yatsunsa a ciki. Tai ƙoƙarin matsawa ya riƙeta. Shiru tai tsigar jikinta na tashi, kamar yanda shima yakejin jininsa na haurawa da gudu a kowanne jijiyar jikinsa....
       “Ina son gashin nan sosai”.
Yay maganar yana matso da kansa a kafaɗarta da kamo gashin ya kai hancinsa yana shaƙar ƙamshin haɗaɗɗen turaren *YERWA INCENSE AND MORE...* da yakeyi. Sai kuma ya saka maida yatsun nasa cikin gashin ya tallafo kanta ya ɗaura goshinsa akan nata suna musayar shaƙa da fesawa juna numfashi... Murya a matuƙar shaƙe duk da akwai mura dama tattare da shi ya ce, “Ƙawata!”.
       A yanda ya ambaci kalmar ba ƙaramin tada tsigar jikin Raudha yay ba. Da ƙyar ta iya faɗin. “Uhhyim”.
      “ALLAH yay miki albarka”.
Sosai taji daɗin wannan addu'a tashi da batasan dalilin yinta ba. Muryarta a raunane tace “Amin nagode”.
      Kansa ya ɗan jinjina mata da cigaba da motsa yatsun hanunsa cikin gashin nata. “Ni kuma fa?”.
       _“Kaima ALLAH yay maka rahama da rahamarsa. Ya kareka da kariyarsa. Ya baka ikon sauke hakkin ƴan ƙasa dake bisa wuyanka, ya baka nutsuwar ayyuka da har abada da baza'a manta da kai ba. Ya hanaka cin hakkin kowa koda bai kai girman ƙwayar gero ba”._
        (Ya ALLAH yarinyar nan zata hakalani) ya faɗa a ransa yana mai rungumeta tsam a jikinsa. Wannan shine karo na uku da hakan ta faru tsakaninsu. Amma yau an samu cigaba dan itama tayi luf duk da jikin nata naɗan tsuma kaɗan-kaɗan.
      “Insha ALLAH ke ƴar aljanna ce *_AMEENATU!_*”.
     Murmushi mai sanyi da yalwa ta saki domin jin furicin nasa. Itama cikin rawar murya tace, “Tare da kai da iyayenmu baki ɗaya”.
     Ɗagota yay daga jikin nasa yana ɗan murmushi. “Uhhm an samu jiki mai daɗi an lafe. Ƙawa kemafa naga kina buƙatar ɗumin mijinki gsky”.
       Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi.
    “Gulmammiya ni bani abincina. Kinzo kinatamin kwarkwasa yana hucewa”.
       “Kai Yaya Ramadhan dan ALLAH”.
“Kam kujimin yarinya da kalan dangi, yaushe na zama Yayanki nikan daga ƙawance kuma? Koda yake kije na yafe miki dai bani abinci cikina ya fara kiran Taura”............✍

      *_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

--------

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.


*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.

_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*

Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:

Amount Paid: - Nawa aka tura?

Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa

Transferred time: - lokacin da aka turo

Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi

Deposit date: - ranar da aka turo

Sai ayi SUBMIT.

*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:

MTN,
9Mobile
Glo
Airtel

Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*


https://arewabooks.com/chapter?id=62be031cf0fb62def317f52f

*_Episode 47_*


.........Duk yanda taso zamewa basa abincin fir yaƙi. Dolenta ta bashi kamar yanda ya buƙata, kunya kamar ta tsaga ƙasa ta nutse a ciki. Shiko ko'a kwalar rigarsa. Sai ma idan tayo ƙatuwar lauma ya harareta wai tafi ƙarfin bakinsa. Amma in namane dataso ragewa zai riƙe hanun da faɗin ‘Ban san mugunta Ustazah’.
       A haka dai yaci ya ƙoshi itama ya tsareta sai taci. Fuska ta marairaice tamkar zatai kuka amma yace saifa taci babu ɗaga ƙafa. Dole ta ɗan tsakura dan a takure take sosai. Bayan ta kammala ta tattare kwanikan ta fita da su. Numfashi ya sauke a hankali da barin aikin da yake a lap-top ya kwantar da kansa jikin kukerar yana lumshe ido da furzar da numfashi. Sai kuma ya kai hannu a wuyansa dan har yanzu akwai zazzaɓi jikinsa dauriyace kawai. ‘Oh Ramadhan Taura ka zama ɗan cali-cali kuma?’. Sai kuma ya sake sakin murmushi da girgiza kansa kaɗan. Shi kansa baya sanin sanda yake biyema Raudha. Abinda ya sani kawai bai son ganinta cikin damuwa kamar baya. Sannan addu'arta a koda yaushe na bashi nutsuwa. Yayinda idan tana a yanayin tsoro da kunya take hana fitinarsa zama lafiya ya dingajin kamar kawai ya...... “Ya ALLAH” ya ambata da kai hannu cikin sumar kansa. Sai kuma ya tashi zaune sosai ya cigaba da sarrafa system ɗin cike da ƙoƙarin son ture abubuwan dake neman fin ƙarfin jarumtarsa......

_______________★★_____________

         Alhmdllhi zamuce abubuwa sun fara daidaito tsakanin Ramadhan da Raudha, ta saki jiki dashi ba laifi suyi ɗan wasa da dariya. Idan kuma taga ya haɗe fuska ta kama kanta ta nutsu. kwana ɗakinsa dai bata sake yarda tayiba tun randa yay zazzaɓi. Amma yanzu tana ƙoƙarin tashi a kowace bayan sallar asuba ta haɗa masa breakfast da kanta. hakama abincin dare kafin ya shigo takai komai bedroom ɗinsa ta ajiye. Wataran ya leƙata da matsa mata tazo ta bashi abinci. wataran ya shareta yaci abinsa sai da safe idan tazo gyaran ɗaki ta tattare.
          A washe gari Ramadhan da Bappi suka gana, ganawar data zama ta farko a zahiri da har ƴan jarida suka fitar. Sai dai babu wanda yasan mi suka tattauna a zaman nasu sai ni (Bilyn Abdull cctv footage ɗin ku😉😂). Sosai kansu ya tushe da mamakin ganin rubutun Raudha dai-dai da takardar da aka turama Bappi ana jibi ɗaurin aurensa da Raudhan. An musu nuni ne da karsu yarda Ramadhan ɗin ya tare a gidan gwamnati har sai an cire ac ɗin dake a bedrooms nashi da falukansa saboda akwai poison a ciki. Ranar sun shiga tashin hankali musamman Anne datace Ramadhan bazai tare government house a kashe mata shi ba. Shi da Bappi sukaita lallashinta da mata nasiha harta nutsu, inda basuyi ƙasa a gwiwa ba randa Ramadhan ya shiga gidan gwamnati kwana biyu da aurensa da Raudha suka canja duk ac ɗin dake sashen harma dana office ɗinsa. Hakama sai da suka bincike lungu da saƙo na ɗakin barci da falukansa na sirri gudun ko an saka camaras a ɓoye. amma Alhmdllhi babu alamar hakan sai iya ta inda ya dace kawai da dole a samu a kowane gidan gwamnati saboda tsaro. Dan wani yaron Aunty Zuhrah ne yay aikin. Sun sake tsintar kansu a tashin hankali lokacin da suka samu poisons a cikin ac's ɗin. Ranar har hawaye Bappi yayi. Daga haka kuma ya ɗarsama kansa zargin akwai boyayyen al'amari. Sai dai kai tsaye bai fito ya ambaci sunan kowa ba. Babban fatansu kawai susan wanene wannan mai turo saƙo. Hakan yasa ganin wannan hand writing da yay dai-dai dana Raudha yay matuƙar ɗaure kansu.
        “Wannan ya sake tabbatar min yarinyar nan Alheri ce kuma akwai dalilin zuwanta garemu”. Bappi ya faɗa lokacin da suke ganawa da Ramadhan a office.
     Cikin sauke numfashi Ramadhan yace, “Tabbas akwai abinda bamu saniba kuma ita take ɓoye mana. Abin ɗaure kan anan kawai shine a gaba ɗaya tarihin yarinyar dana bibiya babu wani alamun alaƙarta da wani sai danginta ko anan cikin Bingo. Sai dai sister ɗin mom nata tanada alaƙa da matar forma president, a yanzu kuma matace ga Alhaji Yaro glass Vice ɗina, dama kuma sun taɓa zaman aure ta fita. Bappi inhar hasashena yana kan dai-dai akwai boyayyar manufa tsakaninka da abokan nan naka gaskiya”.
      Murmushi Bappi yayi yana ɗan jinjina kai. “Komai zai iya faruwa musamman idan akai la'akari da abubuwa masu yawa. Sai dai bana so zargin sunan kowa anan har sai muntabbar. Shawarata gareka anan lkawai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login