Showing 54001 words to 57000 words out of 207756 words
abokan hamayya dama abokan tafiyar.
Duk fita sukai suna masa fatan samun lafiya ganin yayi barci. Sai dai ran Pa a ɓace yake sanin Gimbiya Su'adah ce ta sake saka Ramadhan ɗin cikin wannan yanayin, kuma duk abin nan da akeyi babu idonta a wajen.
A ɓangaren gimbiya Su'adah kam duk taji komai, taƙi fitowane danta sake jaddadama Ramadhan fushinta ya tabbatar da zancen bana wasa bane. Dan taji daɗin yanda taga zancen yayi tasiri a ransa. Hakan yasa babu ɓata lokaci ta kira Asma data bata shawarar ta sanar mata. Cikin jin daɗi adda Asmah tace, “Su'adah ai dama na faɗa miki hakanne kawai zaisa Ramadhan yay mana biyayya. Ni yanzu ina ganin mu haɗa wani shiri da zai sake sakashi tsanarta. Suma kakannin nasa susan mike faruwa idan ma basu sani ba”.
“Okay ina saurarenki wace idea ce”.
Idanu sosai Gimbiya Su'adah ta zaro bayan ta gama jin yayar tata adda Asma. Cikin rawar harshe tace, “Anya Adda Asmah wannan shawaran yayi kuwa? Karki mantafa mulki Ramadhan ke nema. Koyaya abu yake yanzu zai ita taɓa kujerar da yake neman. Abokan hamayya na masa yarfe da ƙazafi inaga wannan ta fito......”
“Su'adah ki kwantar da hankalinki, babu ta inda wannan zai shafi Ramadhan. Sai ma ɗaga darajarsa da zai ƙara”.
“Uhm-uhm Adda kedai bari sai mun sanar ma Fulani”.
Wani irin takaici ya baibaye Adda Asmah daga can, ji take kamar ta jawo ƙanwar tata ta hau duka. Amma a fili sai tace “To hakan yayi”.
Koda Gimbiya Su'adah ta kira Fulani ta sanar mata zaginta ta hau yi. Duk da ta yabama ƙoƙarin ta na farko akan sanarma Ramadhan su waye dangin Raudha ɗin. Amma maganar fita da tsiraicin suce Raudha ce da wani wannan gangancine. “Ku miyasa baku da hankali. a tunaninku dan kunyi video na bogi kunce itama yarinyar karuwace zai hana mutuncin Ramadhan taɓuwa ne. To idan baku san siyasa ba ko mulki ku farka. Wannan abun zai iya ruguza duk wata nasarar da muka samu a campaign duk da kuwa bai aureta ba, idan ma baku sani ba zancen auren nan nata shi kansa wani mutunci ya ƙara masa ga al'umma har a wajen campaign. Idan zamu kaudashi kuwa zamuyine a sirrance bawai mu nuna wa duniya ba marasa tunani kawai. Ku fitar da video ɗin abokan adawa sujuyar da shi akan tare take da Ramadhan ɗin a ciki shashashu kawai”.
Shiru gimbiya Su'adah tai da waya a hannu dan Fulani na gama faɗa ta yanke wayarta. Itama irin wannan tunanin tayi tun farko shiyyasa ta bijirema Addar tata. Inko hakane gara ta tattara zancen Raudha gefe tukunna, dan duk abinda zai hana ɗanta hawa mulkin nan zata kwana ta yini yaƙi da shi ne.
______________________________
Badan Ramadhan ya warke ba ya miƙe ya koma filin daga, amma Alhmdllh ɗan ƙarin ruwan da akai masa yasa jikinsa yin daɗi. Ranar wata juma'a bayan sakkowa massallaci yay campaign nasa na ƙarshe a ƙauyensu Taura. Inda ɗunbin jama'a suka taru har abin ya bama mutane tsoro musamman abokan hamayya irinsu Alhaji Andi ƙaura. Su president kam ji suke kamar su goya Ramadhan a baya dan daɗi. Dan kuwa sun san burinsu na dawowar mulki garesu ya gama cika. Sai kuma fatan kauda Ramadhan a shekaru biyun da suka ɗiba masa (wa'iyazubillah. Sun manta ran kowa a hannun ALLAH yake. Sannan shike bada mulki ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso).
Muslata irin farin cikin da Ramadhan ya shiga a yau ɓata lokaci ne. Dan kuwa ya tsorata da yawan mutanen da suka taru dominsa. Har yanaji a ransa kodai akwai aljanu kamar yanda wasu ke faɗa ne. Sai dai farin cikin nasa bai hana jin ɗacin da tsanar Raudha da ahalinta ba. Duk yanda yake turesu a ransa sun kasa gushewa.
______________________________
*_RANA BATA ƘARYA SAI DAI UWAR ƊIY TAJI KUNYA_*
A faɗin ƙasar NAYA da kewaye yau itace daren zaɓen shugaban ƙasa. Dan haka ta kowanne sashe akwai abinda ke gudana ga kowa. Wasu fatan nasara, wasu shirye-shiryen kota kwana, wasu addu'oi. A cikin masu salla da addu'a a wannan dare harda Ramadhan, Anne, Bappi, Pa, Yafendo, Inna da wasu a cikin ƴan uwan ahalin Taura. A masarautar Bino ma dai Mai-martaba ya kwana raya wannan dare. Yayinda irinsu Gimbiya Su'adah sukejin mulki kamar sun samesa ne.
Duk da Raudha bata jin son Ramadhan ta masa fatan alkairi, harta kwanta kuma zuciyarta taita zingurinta akan ta tashi tayi salla ko raka'a biyu ne. Tabi shawarar zuciyarta tayi kuma ta roƙi ALLAH samun shugaba na gari bawai Ramadhan ba.
*_WASHE GARI:_* kusan tara na safe Feena ta shigo ta sakata shiga wanka. Batare da tasan dalili cewa tai wankan ba tace ai yanzu tai wanka ita. Fita Feena tayi, babu jimawa ta dawo da kaya a hannu da makeup kit. Sam Raudha batason wannan ƙaƙale-ƙaƙalen, amma saboda Aunty Hannah ta shigo ta mata magana dole ta amine akai mata light make-up ɗin. Sannan ta saka kayan da aka kawo matan. Tabbas tayi ƙyau, sai dai bazata iya fita da gyalen da aka haɗo kayan da shi ba. Dan haka ta ɗakko gogaggen hijjab ɗinta daya shiga da kayan ta saka. Duk jarabar aunty Hannah dole ta barta dan kuka ta sanya musu.
Tana zaune fuska a kumbure tana shan tea ɗin da aunty Hannah ta tilasta mata sha Yasmin ta iso da saƙon “Mom wai ga baƙon yazo inji mama tambaya”.
Cikin sauri aunty Hannah ta amshe kofin shayin hannun Raudha ɗin. “Sai ki tashi tunda dama haka kike so ki fita bakici komai ba. Sai ki tashi ya iso kuje ku jefa ƙuri'a muma zamuje tare da tawagar shugaban ƙasa”
Sosai gaban Raudha ya faɗi, ta ɗago da sauri ta dubi Aunty Hannah. Sai dai kafin tai magana Feena ma ta shigo.
“Hajiya suna jiranta fa”.
Da sauri Aunty Hannah ta miƙar da Raudha, bag ɗin da zata riƙe mai ƙyau ta saƙala mata a hannu, hakan sai yay matuƙar sake fito da tsarin kwalliyar tata musamman da hijjab ɗin ke iya cinyarta kawai, gashi mai hannu, ya kuma ɗau guga ya kwanta luf da haska ƙyaƙyƙyawar farar fuskarta kasancewar blue color ne, sai hakan ya ƙara bama skirt ɗin nata fitowa sosai ya buɗe. Kamar zata fasa kuka ta zura takalman da aka ajiye mata masu ɗan tudu da suka sake fidda ƙyawun ƙafarta.........✍
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: - Nawa aka tura?
Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/10, 7:45 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_Episode 21_*
...........Cikin girmamawa baba Adamu driver ya buɗema Raudha jibgegiyar motar yana faɗin, “Barka da safiya ranki ya daɗe”.
Sosai kunya ta kama Raudha, dan baba Adamu ba yaro bane ba, cikin ɗan murmushi tace, “Baba ina kwana”.
Amsawa yake cike da girmamawa da jin ƙaunarta, dan duk yanda kake kanaso a girmamaka a mutuntaka. Yaran gidan su Ramadhan kuwa ƴammatan nan yanda suke masa har ƙwalla yakeyi wataran. Sai dai idan Pa ya gani ko Bappi ko Anne su tsawata musu. Dan Ramadhan shima yana bashi girma sosai. Samun kansa yay da taya Ramadhan murnar samun mace tagari, tare da binsu da addu'ar fatan alkairi a zuciya.
Tunda motar ta fita a gidan Raudha na kallon titi ne kawai da shaƙar ƙamshin motar mai neman sakata barci. Ga wani sanyi dake ratsa jiki a hankali. Da farko a tsorace take, amma ganin babu kowa a motar sai zuciyarta ta samu nutsuwa.
Tafiyar da bata gaza mintuna sha biyu ba suka iso, abinka da lafiyayyar mota akan nagartaccen titi. Wani irin tsargawa cikin Raudha yayi ganinsu a *airport*, inda bata taɓa zuwa ba sai dai ta gani a tv. Zuciyarta ta shiga tsinkewa lokacin da take fitowa idanunta sukai arba da gayyar jama'ar Taura Family ƙwansu da kwarkwatarsu. Jitai ƙafafunta na hahharɗewa. Cikin sauri ta shiga ambaton addu'ar da duk tazo bakinta a zuciya. Anne da fuskarta ke faɗaɗe da murmushi ta riƙo hannunta tana faɗin, “Masha ALLAH wannan amarya kam da gaske zata iya ture gwamnatina”.
Raudha dake jin kamar zata nutse ta rissina tana gaida Anne. Sake riƙota Anne tayi ranta fal da jin ƙaunar yarinyar, harga ALLAH shigar mutunci da Raudha tayi na hijjab ya matuƙar burgeta. Bappi ne na biyu data gaida kasancewar shine kusa da Anne, shima kuma yanata zuba mata murmushi tare da sake tambayarta ƙarfin jiki tace Alhmdllhi.
Sauran ƙannen Ramadhan duk sun sake yarda Raudha ƙyaƙyƙyawa ce ƙwarai da gaske, wasun su ta shiga ransu, wasu ko sunajin ƙinta a rai badan ta musu komai ba. Bayan ta gaida Pa ta gaida su Gimbiya Su'adah badan tasan matsayin kowanne ga Ramadhan ɗin ba. Kawai dai yanda ta gansu manya matsayin iyaye yasa ta risina kamar yanda ta gaida Pa suma ta gaishesu. Su Hajiya Mufida sun amsa mata da fara'a musamman ma hajiya Shuwa da dama haka take da sakewa. Gimbiya Su'adah kam bana tunanin tama amsa mata. Sai wani kallon ciki da bai take mata fuska a yamutse.
Oho Raudha bama tasan tanai ba dan taƙi yarda ta kalli kowa. Sai ma juyawa datai ta gaida su Zainab ƙannen Ramadhan ɗin. A take Rumaisa da Fadila da Basma suka riƙota sun murmushi, zasu iya zama sa'anninta a shekaru, sai dai jin daɗi da hutu yasa sun fita girman jiki.
Sai yabata suke da faɗin yayansu yayi sa'ar ƙyaƙyƙyawar mace, ita dai ta kasa cewa komai sai ɗan murmushi, dan duk a takure take. Bata sake tsurewa ba sai da zasu shiga jirgi da batai tunanin nan ɗin zasu shiga ba, dan sanda suka fara taka steps ɗin sai da Bilkisu ta riƙota saboda tuntuɓe da taci zata faɗi. Tambayar zuciyarta ta dingayi ina zasuje ne haka? A ɗayan gefen kuma tsoro ne fal da fargaba.
Can aka kaita sashen vip ba inda sauran suka zauna ba. Duk da kuwa duk cikin jirgin Taura family's ɗinne da ma'aikatan gidansu. A taƙaice ma jirgin nasune. Duk da ba gama tantance ƙamshin turarensa tai ba lokacin da suka iso hanunta cikin na Basma sai da gabanta ya faɗi saboda wani shegen ƙamshin turaren daya daki ƙofofin hancinta. Ta sake waresu da ƙyau tana zuƙa da yin tazbihi ga UBANGIJIN daya azurta ƙwaƙwalwa da gangar jiki akan son ƙamshi da banbance wari.
Sallamar da Basma tayi ne ya sakashi ɗago idanunsa da kallo guda zakaima cikinsu kasan yana matuƙar buƙatar son hutu, yay mata duba ɗaya ya janye ya maida ga magazine ɗin da yake karantawa.
“Yayanmu dama Anne ce ta ce na kawo aunty Raudha ta zauna anan acan zata takura”.
Cak ya tsaya da karatun, sai dai bai janye magazine ɗin daga fuskarsa ba. Tsahon mintuna biyu kafin yayma Basma nuni da kujerar dake kallon wadda yake kai batare da yace komai ba. Bai kuma kallesun ba har yanzu. Duk wannan abu Raudha na laɓe a bayan Basma ne. Sai da Basma ta juyo ta kamo hanunta tana murmushi.
“Bismillah auntynmu ki zauna anan, dan ALLAH ki saka yaya yay surutu, dan tunda aka fara hargitsin campaign ɗin nan ya sake zama shiru-shiru”.
Kasancewar a cikin kunne tai mata maganar yasa Raudha saurin duban gabansu, sai dai kafin ta iya furta wani abu Basma ta kamata ta zaunar a kujerar har gwiwarta na ɗan gogar ƙafarsa daya harɗe ɗaya saman ɗaya. Kamar walƙiya kuma Basma ta ɓace a wajen.
Zan iya ce muku a wannan lokacin zuciyar Raudah ce kawai zata iya sanar muku halin da take ciki, dan faɗa da bakima ɓata lokaci ne. Ta kasa dubansa balle ƙwaƙwaran motsi, abinda ta iya ƙarfin halin yi kawai shine faɗin, “Ina kwana”.
Bata damu da amsawarsa ko akasin haka ba, dan koya amsa bata tunanin ƙwaƙwalwar kanta zata iya banbance da wane yare ya amsa ɗin. Magana da na'ura ta farayi na a ɗaura belt ya sashi janye magazine ɗin daga fuskarsa a hankali. Akan Raudha idanunsa suka sauka. Harya janye idanunsa daga kallo guda dayay mata yana ƙoƙarin ɗaura belt ɗin sai kuma ya sake dubanta. Harga ALLAH yana matuƙar son blue color, shiyyasa duk inda yaga kalar da wahala bai nutsu a duba ba. Balle wannan daya haɗu da farar fata da cute face ɗin Raudhan. Motsin da zuciyarsa tayi a cikin ƙirji ya sashi janye idanun nasa gaba ɗaya daga gareta, harya sake ɗukar magazine ɗin zai buɗe sai kuma ya fasa ganin bata motsaba balle tai yunƙurin saka belt ɗin, ga jirgi ya fara ƙugi alamar zai tashi.
Cikin yatsine fuska da sake ɗaureta ya matso da jikinsa. ganin ya matso da hanunsa da gargasa suka ɗan bayyana a white skin nashi yasata saurin dubansa, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska ya sata saurin rumtse idanun ta matse jikinta.
Lip ɗinsa ya taune na ƙasa da balla mata harara yana girgiza kai, sai kuma ya taɓe baki lokacin daya zugo belt ɗin yabi ta cinyoyinta da shi batare daya taɓata ba ya sakashi a ɗayan gefen. Wani shegen numfashi dake fita da sassarfa ta saki ganin ya koma ya gyara zamansa kamar yanda yake a da. Sai taji kamar ta saki kuka kawai ta huta ita kam.
Bai sake bi takanta ba har jirgin ya ɗaga duk da yaga yanda ta dafe kai lokacin da jirgin ke shillawa cikin gajimare. Karatunsa ya cigaba dayi duk da ƙamshin khumra ɗinta ta mugun addabar hancinsa, amm ya fuske kasancewar sa gwanin jin kai.
Gaba ɗaya Raudha a birkice take bata samu nutsuwa ba har sai da jirgin ya sauka, dan kwata-kwata tafiyar mintuna ashin da uku ce ta kawosu jihar Bino. Ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya lokacin daya miƙe yana ajiye magazine ɗin, komi baice mataba ya kwashi phones nasa guda uku da wani ɗan leda. Sai da ya ɗaga labulen wajen zai fita sannan ta tsinkayi tattausar muryarsa mai faɗi da ɗan buɗewa cikin kunnenta.
“Zaki cigaba da zama ne anan?”.
Da farko bata fahimci da ita yake ba, sai da ta waiga taga dai ita kaɗaice a wajen sai ta miƙe tan ɗaukar bag ɗinta ta sakala a kafaɗa a sanyaye. Sai a yanzu ta samu damar iya kallonsa. Sanye yake cikin wani skay blue yadi mai shegen taushi, dan yanda ya ɗauka guga da ɗaukar idon mai kallo kawai ya isa kasan an sayesa da kuɗaɗe masu nauyi. Ga telan daya ɗinkasa ya fidda komai yanda ya kamta dai-dai da jikinsa kuma. Rigar iyakarta cinyarsa, hakama hanunta gajere ne iya gwiwar hannu, sai hula daya murza black da takalmansa suma black half covers. Sai agogonsa omega, fuskrsa tayi fayau saboda ɗan ramar da yayi da kuma gyaran fuska da Bappi ya takura masa yay jiya da yamma.
Da sauri taja da baya ganin ya juyo a bazata lokacin da suke gab da fitowa, ledar hanunsa na facemask guda biyu ya ɓare ɗaya ya miƙa mata. Ɗan ɗagowa tai, sai dai tai azamar janyewa kasancewar idanunta da suka faɗa cikin nasa a bazata. Karon farko da taji wani abu ya tsarga mata daga ƙwaƙwalwa zuwa yatsan ƙafa mai kama da tainkewar jini, taji tamkar ta saki