Showing 63001 words to 66000 words out of 207756 words
da ita”.
Cikin zafin rai Mr MM yace, “Idan ma mun sanar matan tace zata tona mana asiri halakata zamuyi itama a banza....”
“Ai ko yanzu ɗin ba tsira zatai ba. Kana tunanin zata dinga shaƙar gubar nan ta cikin ac ta tsallake itama. Yanda zata dinga masa illa a hankali itama hakanne zata kasance. Sai dai akwai wata allura da za'ai mata wadda gubar bazata yi tasiri a jikinta da wuri ba kamar shi”.
A tare duk suka kalli Aunty Hannah bayan sun ɗauke idonsu ga Dr Bonba daya gama bayanin.
Kanta ta kaɗa musu tana watsa hannaye baya. “Miye na kallon nawa?, kun san dai Raudha ɗiyar ƙanwata ce. Duk da kuwa ina son zama first lady bashike nuna bana son abata ba. Nasan bai wuce kuce ya shawarar ta canja ba game da allurar riga kafin guba. Ku zauna kuyi tunani da hankalinku, babu ta yadda za'ai mu bari gubar tai tasiri a jikinsu lokaci guda, dan komai zai fito ne. Amma idan bayan ya shi ya mutu ne itama ta mutu za'a iya cewa zuciyartace ta buga saboda rashinsa itama tabisa”.
“Woow!”.
Suka faɗa a tare suna tafawa. Shugaban ƙasa mai sauka yace, “Hannah kinada basira, anya kuwa idan mutumina ya zama shugaban ƙasa bake bazaki koma juya ƙasar ba kuwa?”.
Wata shegiyar dariya tayi tana juya idanu, Alhaji Yaro glass ya sake rungumota jikinsa da manna mata kiss a kumatu. “Inaga shugaban ƙasa biyu kam zakuyi”. Ya faɗa cikin raha. A can ƙasan ransa kuwa yana ayyana ashe kuwa itama zata mutu nan kusa, dan Hannah bata isa shiga masa hanci bai fyatota ba duk da take matarsa.........
Zuwa yanzu sosai hajijiya ke neman yadda Raudha a ƙasa. Tai azamar dafe bango jin zata zube a ƙasa. Laɓɓanta sai faman rawa sukeyi amma sun gagara furta komai, dan ko tace zata furta ɗin batasan mi zata furta ba. Da ƙyar ta cigaba da laluben bango ta koma ɗakinta, batasan a yaya ta zube saman gadon ba harda jan bargo ta lulluɓe, jikinta ya shiga wani irin karkarwa na rawar sanyi
Yanzu ta fahimci ba ahalin Ramadhan bane zasu zama BAƘAR INUWAR ta ba, ba Ramadhan bane BAƘAR INUWAR ta ba, aunty Hannah itace BAƘAR INUWAR ta. Shi kansa Ramadhan sun tittiɗashi ya hau kujerar mulki ne badan ya ni'imtu ba, badan ta zame masa INUWA da irinsu talakawa suke hangen masu mulki na ciki ba. bai san sun kaisa BAƘAR INUWA bane, gara ace a rana yake da shiga cikinta. ta sake fashewa da kuka.
ALLAH sarki talaka. A kullum gani yakeyi shi a RANA YAKE, mai mulki shike cikin Ni'imtacciyar inuwa, ashe baisan da wata BAƘAR INUWAR MUKIN gara ranar da shi yake a ciki ba. Yau gashi saboda mulki yayar mahaifiyarta ta ɗauketa da hannunta ta kaita BAƘAR INUWA. Shiyyasa suka dage ashe, shiyyasa suka hana mahaifiyarta nuna ƙin auren, shiyyasa suka babbake ko ina da ina. Miye mafita? Zata bijirema auren ne ta hanyar guduwa ko zata haƙura ta zauna ta ceci rayuwar wanda a yanzu take kallo da fatan ya zama adalin shugaba madubin al'umma kamar yanda talakawa suka ɗora yaƙininsu a kansa da ƙwarin gwiwarsu?.
A take kanta ya fara sarawa, dan tama rasa kalar tunanin da zatayi saboda ƙarancin shekarunta. Ga wani irin tausayin Ramadhan ɗin da ahalinsa na dirar mata a zuciyarta, dan ta taɓajin cewar kakansa Baba alhaji aka bama takarar shi kuma ya bashi saboda yace bai ra'ayin mulki a shekarunsa. Ashe baisan ya kai jikansa BAƘAR INUWA bane. Tabbas bazata iya fahimtar komaiba a yanzu dole saita san komai, sanin komai kuma bazai yuwu a gareta ba sai ta yarda da auren Ramadhan. Sai dai kuma tana buƙatar shawara wajen na sama da ita, wazata tunkara? Hajiyar birini! (Kai a'a gwaggo sai a hankali ce) Hajiya mama (kai itama a'a duk tafiyar ɗaya ce) Mommynsu! (Ina bazai yuwu ba zata sake tada mata hankali) Su Fatisa! (Ina basu da hankalin da zasu iya fahimtarta ta wani fanin ma gara ita). Take wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufeta, sarawar da kanta keyi ya ƙara ƙarfi..
Koda suka wayi gari da safe Raudha babu lafiya aunty Hannah bata kawo komai a ranta ba sai tunanin fargabar aure da akasan kowacce amarya da shi. Tunda sassafe suka nufi can gidan dan yau zasu wuce Hutawa su duka har Hajiyar birni. Su Fatisa kam tun jiya suka wuce harda su Yasmin.
Asabe ce kawai ta damu da ganin halin da ɗiyar tata take ciki. Suko hankalinau nakan kuɗaɗen da aka aiko daga gidan su Ramadhan injisa aba amarya na hidimar biki, sai tarin kayan rabo. Ko irin ɗan faɗa da nasihar da akema amarya babu wanda yay mata a dangin mahaifiyar tata. Sai ita Asaben ce ta jata gefe taita lallashinta da mata nasiha. Tare da ƙarfafa mata gwiwar ta ɗauka Ramadhan shine zaɓin ALLAH a gareta. Maybe shine kuma mafi alkairi. Dan ita kanta tayi addu'a tayi sadaka akan rushewar wannan aure amma babu alamar zai rushe ɗin.
Raudha ta yarda da maganar Mommy takuma ɗauki aniyar haƙuri, dan ita kanta tayi addu'ar sosai akan zaɓin ALLAH game da auren komai kuma bai canja ba, tunda gashi har gobe idan ALLAH ya kaimu ɗaurin aure.
Ƙarfe kusan sha biyu suka bar Bingo zuwa jihar Dillo a ƙaramar jukumar hutawa. Kasancewar lafiyayyar motace kuma drivern yasan aikinsa zuwa huɗu na yamma sun iso. Asabe tayi mamakin yanda aka tarbesu, ga gidan nasu data sani duk ya cinye a baya ya zama wani haɗaɗɗe yanzun. Dan harda su gate aka saka.
Kowa burinsa yaga Raudha matar shugaban ƙasa. Dan haka maƙwafta da ƴan anguwa sukaita tururuwar shigowa ganin amarya. Sai dai kuma ita amarya Raudha ta ɓoyewa ganinsu saboda zazzaɓi dake damunta har yanzu. Abu biyu ke tayar mata hankali. Zancen su Aunty Hannah da tsarin auren nasu daya sha banban dana saura. Babu wani jituwa tsakaninka da ango balle wani maganar biki ma ya shiga. To gaba daya ma sau biyu ta taɓa ganinsa a zahiri, babu kuma wanda wata maganar kirki ta shiga tsakaninsu a ciki.
Duk yanda taso cigaba da zurfafa tunanin nata dole ta haƙura saboda hayaniya da gidan ya ɗauka. Kai kace yau ne ɗaurin aure. Ga dj ya warware kiɗa tun da safe dan su Fatisa suka ɗakkosa tun daga Bingo. Tun kuma a daren jiya aka fara raƙwashewa duk da amarya bata iso ba. Shiko Mal. Dauda dama babu ruwansa, dan shi kansa yana gefe da abokansa yana ɗan rausaya ƙafa saboda yanda kiɗan ke shigarsa tsumin baya na neman motsawa.
Kowa ka gani a cikin farin ciki yake a gidan, ƴan uwa da wandama kalan dangine duk bakuna a washe. Musamman Inna dake nuna cewar yanzu tafi son su Raudha fiye da kowa a duniya. Larai ce kawai take cikin tashin hankali, dan ta koma gidan malaminta yafi sau shurun masaƙi yana cemata ta dai jira ai ba'a ɗaura auren ba ko. Kowace daƙiƙa ta agogo dake matso da lokcin ɗaurin auren na bugawane da bugun zuciyar larai. Duk ta fita hayyacinta tsabar rashin nutsuwar zuciya. A daren jiya har faɗa sukai da Mal. Dauda ya shashaheƙa mata mari da tabbatar mata idan ta ɓata masa farin ciki a taron bikin nan zai yanka mata jan ticket ɗin komawa gidansu dan bazai zauna da mai masa baƙin ciki ba.
Wannan shine dalilin daya sakata kama kanta sai idan ta shiga ɗaki taita haɗiyar zuciya. Baba nafi kam babu ruwanta. ta shige cikin dangin Asabe dana mijinta anata harkokin arziƙi da ita. Hakama ƴaƴanta na ma'auri da wanda basuyi auren ba. Yanda take ɗin yasa Mal. Dauda mata ƙyautar kuɗi masu tsoka wai itama ta tarbi baƙinta.
A daren ranar duk yanda Raudha taso maƙalewa taƙi fita ƙofar gidan inda su Fatisa suka tara ƙawayensu dama wanda ba'a gayyataba hakan bai yuwu ba. Acewarsu yaune sukai taronsu na ƙawaye. Dole aunty Hannah ta matsa mata shiryawa cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar Material a cikin akwati guda da aka kawo mata na kayan fitar biki. dan ba'a kawo lefe ba Ramadhan ya hana. Yace idan an ɗaura zai bata da hanunsa. Su Bappi sun goya masa baya dan auren Amnah ma haka yayi. Shiyyasa aka kawo mata kayan fitar biki kawai da aka ɗinka akwati guda da duk abinda zata buƙata na ado.
Light makeup Feena da suka taho tare saboda kwalliyar amarya tai mata, aka gyara mata dogon gashinta data gada wajen Asabe tare da naɗa mata ɗauri mai ƙyau. Kanta ke matuƙar ciwo ga zafin zazzaɓi amma haka ta daure ta fitan. Nanfa ƙawaye suka shiga mata hotuna duk da dare ne harma da jama'ar gari. Burin kowa ace ga hoton matar shugaban ƙasa a wayarsa ya samu na fafar faɗama wasu yanada alaƙa da ita koda anan gaba idan ganinta ya musu wahala. Wasu ko a take suka shiga watsashi a media dan hannayensu na ƙaiƙayi.
Wajen ya sake ƙawatuwane lokacin da Hajiyar birni tazo ta farke ƴan ɗari biyar-biyar ta hau yima Raudha liƙi. Sai itama aunty Hannah ta farke ƴan dubu-dubu. Sai ga Mal. Dauda ma da kansa ya farke nasa dubu-dubun. Nanfa yaran dj da mutane suka shiga wawaso. Abu kamar wasa sai ya zama gasa akaita shigowa anama Raudha liƙi. Wasu ma ƴar dubu ɗaya ce suke canzowa goma-goma ko biyar-biyar suyi dan dai ace suma sunyi.
Alhmdllhi dai sai ga taron ya zama wani ƴar ƙwarya-ƙwaryar wasa. Amarya ce kawai zuciyarta ke a ƙuntace da damuwar data dameta. Suna mata kallon wadda zata shiga Ni'imtacciyar INUWA basu san BAƘAR INUWA bace, gara ranar da suke ciki ta fita kwanciyar hankali.
Jirin da tace tanaji yasa Hajiya mama maidata cikin gida, aka bata tea da magani tasha ta kwanta. Kasancewar maganin naɗan saka barci aka dace barcin yay awon gaba da ita dan dama akwai bashinsa a kanta.
*_WASHE GARI_*
Tunda farar safiya motocin jami'an tsaro kala-kala suka fara shigowa garin Hutawa suna masa zobe. Al'amarin tuni ya fara tsorata masu tsoro suka nutsu a gidajensu. Zuwa ƙarfe sha biyu garin ya fara ɗaukar haramar baƙi. Babu abinda ke danno kai cikin garin sai jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi. Kai harda su helicopters. Tuni gidan hakimi daya amshi ɗaurin auren ya cika ya tun batsa da manyan ƙasa dana baƙin ƙetare. Dan babu kalar fatar da bazaka samu ba. Tunkan shugabanci gidansu Ramadhan babban gidane sannne, sai ya zam samun mulkin ya sake haskesu.
Ƙarfe sha biyu da rabi dai-dai tawagar shugabn ƙasa kuma ango *_Ramadhan B. Hameed Taura_* ta dira cikin garin hutawa. Dan tun a daren jiya nasa baƙin ta kowanne ɓangare ke danna kai birnin Bingo, yau kuma suka ɗungumo a motoci zuwa Hutawa, duk da kuwa su Alhaji yaro glass sun so hanashi ya tabbatar musu bazaibi jirgi ba zaizo a mota saboda wani dalilinsa.
Ta ko'ina garin ya sake harmutsewa. yayinda wasu a abokan nasa ke matuƙar mamakin inda Ramadhan ɗin ya ƙwaƙulo matar aure a wannan garin da idan ka ɗauke ɗai-ɗaikun manyan gidaje da lafiyayyen titi babu komai a cikinsa sai hayaniya da tarkacen talakawa (🙄🤗ALLAH mun gode maka daka yimu a talakawa).........✍
*_Sai ku shirya. Dan bai kamata ayi bikin nan babu mu a wajen ba gskiya. Zafafa biyarma duk zasuje. Dan suna nan suna sallar dare shugaban ƙasa Ramadhan ya haɗasu da muƙaman ministoci😹😹👩🏼🦯_*
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: - Nawa aka tura?
Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/13, 8:47 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_Episode 24_*
............Kusan tare tawagar ango da tasu Bappi ta iso tare da forma president. Sai wasu gwamnoni masu sauka dama wanda sukaci zaɓe. Dama wasu tuni sun iso, dan a kaf jihohin ƙasar NAYA arba'in da ɗaya babu gwamnan da baizo ɗaurin auren nan ba da sarakunan gargajiya. Sai waɗanda lalura ta hana kuwa, suma sun bada wakilai. Hakama masu ƙananun muƙamai irin members na majalisa dama na jihohi da cabinets na tsohon shugaban ƙasa dana gwamnoni, attajirai da manyan malamai, kai harma da jama'ar gari da aba'a gayyata ba. Dan a cewarsu dole suzo su kashe kwarkwatar ido, ɗurin auren shugaban ƙasa guda ba wasa ba.
Tsabar cikar da garin yayi sallar juma'a wasu har akan tituna, motoci kam har an rasa wajen fakin. Badan jami'an tsaro dake zagaye da garin ba ma da ba'asan yaya zata kaya ba.
Ango yayi shar cikin wata muguwar ɗanyar shadda da zaman neman addin kuɗin da aka sayeta ma ɓata lokacine. Takalma da agogon hanunsa zuwa hula kuwa dole a kirasu na musamman. Yayi fayau dashi saboda ƴar ramar campaign da har yanzu bai gama cikowa ba.. Ga gyaran fuskar da ya sha da tsagar kan gashin girarsa na tabon ciwo sun sake ƙawata fuskar tashi. Ƙamshi yake na musamman, ga securitys zagaye da shi, kai kace zasu iya karesa daga cika aiken mala'ikan mutuwa ne (😕🤕).
A kusa da kakansa Bappi yay salla a sahun farko, ɗayan gefen haggunsa Mal. Dauda ne hakimi a gefensa. Sai can ɓangaren shugaban ƙasa mai sauka tare da mai-martaba da sarkin Dillo. A yau sarkin musulmi ne ya jagoranci sallar juma'a. Bayan idar da salla aka gudanar da ɗaurin aure kamar yanda shari'a ta yarda. Jikin Mal. Dauda sai rawa yake, dan harga ALLAH a firgice yake ganinsa tsakkiyar manyan mutane da bai taɓa tunani gani ba koda a mafarki. Daya sani ya bari ƙanin nasa ya karɓi auren kamar yanda Inna tace. Amma sai ya bijire dan kar wasu su zata ba shine mahifin Raudha ba. Ko wani yayima Sabilun alkairi saɓanin shi daya cancanta.
A hankali shugaban ƙasa Ramadhan ya lumshe idanunsa lokacin da ake sanar da ƙulluwar auren nasa kamar haka. *_(Alƙawarin ALLAH ya cika. Domin kuwa Aminatu Dauda Haladu ta zama mata ga Ramadhan B. Hameed Taura. akan sadaki mai daraja. ALLAH ya bada zaman lafiya da zuri'a mai albarka)_*.
Annan take waje ya ɗauki gungunin faɗin amin, yayinda irin su Alhaji Yaro glass ke faɗin (Ba amin ba) a zukatansu. Gefe kuma daga can wajen masallaci aka shiga busa algaitu daga sarakuna domin girmamawa ga shugaban ƙasa. Yayinda maroƙa suka shiga kirari da yabo ga ango kuma shugaban ƙasar NAYA.
Wani irin iska ce mai shiga jiki da sanyi tamkar na tsakkiyar hunturu suka shiga ratsa Ramadhan batare da yasan dalili ba. Tabbas bayajin sonta, yayi biyayya ne kawai ga iyayensa. Shiyyasa ya rasa dalilin yanayin daya shiga a yanzun. Dan lokacin aurensa da Amnah tsintar kansa yay kawai da zumuɗin ganinta a lokacin da aka shafa fatihan aurensu. Saɓanin yanzu da yake jin tamkar an sake aza masa wani nauyine bisa kansa bayan wanda yake ɗauke da shi. Ya shiga sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da Bappi ya rungumesa yana musu addu'ar zaman lafiya da fatan alkairi.
★★★
A can gidan su Raudha ma taƙe yake da mutane har wani baya iya jin zancen wani. Amarya na maƙure jikin Asabe dan zazzaɓi ne mai zafi a jikinta har amai tayi ɗazun saboda takura mata taci abinci da Hajiyar birni tayi. Kwalliya kam sai da hajiyar birnin da Aunty Hannun sukai tamkar zasu halakata dan bala'i sannan ta amince akai mata.
Cikin