Showing 147001 words to 150000 words out of 207756 words

Chapter 50 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

657

kanta ƙofar ɗakin nasa. Ji take kamar bazata iyaba amma ta daure matuƙa. knocking tayi kamar bataso. Tana shirin sake na biyu aka buɗe ƙofar. Bata yarda ta kallesa ba, dan tasan dai shine ɗin. Shiko idonsa a kanta ƙyam yana ƙaremata kallo yanda abayar tai matuƙar mata ƙyau. Matsawa yay ya bata hanya ta shige batare da yace komaiba. Sai da ta gittashi ta shiga ya maida ƙofar ya rufe. Saman kujerar daya tashi ya koma ya zauna tare da ɗaukar Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincin”.
     “Zuba”
Ya faɗa a taƙaice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taƙi amsar lallashin sam. Bai kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa ƙamshi, yaji haɗi na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake ƙaunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawai”.
    Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.
      “Na sallameki ne?”.
Jitai kamar ta fashe masa da kuka kawai, amma ta daure dan kar yaga kamar ta cika rashin wayo. Hankalinsa ya maida ga abincin zuciyarsa na tunanin ta yanda zai ɓullo mata ta saki jikinta. Sai dai ya kai laumar nama baki yake faɗin, “Uhhmm Bestie kinji wani gashi na musamman kamar a birnin sin. K karfa ki zata santi nake naji abunne har cikin kai”.
       Murmushi ne ya suɓucema Raudha. A hankali tace. “Uhhmm!”.
           “Ai bakiji Humm bama sai kinci”. Ya ɗago gareta da tsoka daya ciro jikin dogon tsinken da Bilkisu ta tsiro guda uku. “Buɗe bakin kiji kar ayi babu ke”.
      A kunyace tace, “ALLAH ni na ƙoshi”.
     Fuska ya ɓata yana ɗan hararta. “Keni bansan gulma buɗe baki. Ni nasan tun kan ki kawo namannan kike addu'ar ALLAH yasa na sammiki”.
          “Ya ALLAHU”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta dariya na suɓuce mata.  Shima murmushin yake tare da sake kai mata naman bakinta. Dole ta buɗe saboda cewarsa. “ALLAH sai na miki ɗura. Kuma saina tauna yayi laushi na juye miki a baki dole ki haɗiye”.
     Fuska ta yamutse alamar ƙyankyami. Ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyarnanfa ƴar wulaƙancice wani lokacin. Wai ƙyanƙyaminama kikeji? Koda yake hakafa kikaimin kwanaki ina mura. Har shaƙa miki murar nai amma kikaƙi ɗauka saboda ɗan banzan ƙarfin jininki”.
     Yanzu kam kasa daurewa tai ta sanya dariya. “Kai Ya Ramadhan ko tausayi babu?”.
      “K nifa kibar wani cemin Yaya niba Yayanki bane bamsan kalar dangi. Nasan dai akwai abota tsakaninmu sai kumaaaaa......”
       Ya ɗanja ƙarshe yana kashe mata ido batare daya ƙarasa ba. Ba shiri ta miƙe zaram amma yay saurin riƙeta ya maida. “Ustaza bansan fassara irin taku ta Ustazai fa. Kijira na karasa mana kafin ki kaini inda banje ba”.
    Dole ta dawo ta zauna kamar ta ɓuya a kujerar dan kunya. Ya dungure mata kai yana kai nama bakinsa da taɓe baki. “Gulmammiyar yarinya nafasan kema kin kamu. A yanzu nan duniya bayan Mommy da Abba babu wanda kike so Kamar Ramadhan...”
     “Ni yaushe nace!”.
Ta faɗa cikin suɓutar baki tana taɓe fuska.
              “Yo sai kin faɗa? Yanda kika kadandaneni ram ɗazu ke daɗi mijima ai ya isa shaida.”
     “Innalillahi....”
Ta faɗa kamar zata fasa kuka dan kunya. Dariya ke cinsa yanda tai wuri-wuri da idanu na kunya. Ya danne da ƙyar. “Oh kice baki son nawa mana kiga in gobe banje an ɗauramin aure da ƴammata uku ba galla-galla”.
         Ji Raudha tai kamar ya kwaɗa mata guduma a tsakkiyar zuciya. A take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Tai ƙasa da kai zuciyarta na mata zafi da kalamansa.....
     Wani daɗi ya baibaye Ramadhan kamar ya tashi ta taka rawa. Cikin shafa sumar dake zagaye da kumatunsa yace, “Oh su Ustazah ba kunya anga sumulmulin yaro ɗan jikan Anne an maƙale. Irin wannan kishi haka Ƙawata? To indai baki so nayo kishiyoyi yau kam dole naje farautar triple koda yake kefa huɗu ma naji kina faɗa saboda tsabar haɗama keda ma ko ɗan kiss ɗin nan na zamani sau ɗaya aka taɓa mik.......”
        Ai bata bari ya ƙarasa ba ta daka tsalle ta guntse masa baki da hannayenta. Wayyo dariya kamar ta kashe Ramadhan. Yasan ya riga ya gama da ƴar darunsa yau. Sai dai wani farin ciki ke dawainiya da shi ganin kishinsa ƙuru-ƙuru tattare da ita. Koba komai yaji daɗi bashi kaɗai ke wahalar banzaba akanta ashe. Jikinsa ya jawota ya rungume. Cikin raɗa yace, “Na nayi shiru tashi kici abinci”.
        “Kaci kayanka, ko kaje kuci da ƴammatan naka”.
     “Wayyo Ramadhana anyi kasuwa. Uhm-uhm fa Bestie ALLAH karki tsaya kallon ruwa ƙwaɗo ya miki ƙafa. BABU SO MIYA KAWO KISHI?”.
     Turesa ta shigayi da faɗin, “Wama zaice yana sonka ɗin. Abotarma an fasa”.
            Nanma dariya kawai yakeyi yana sake riƙota dan ya fahimci so take tai amfani da damar ta tsere. Ya jima da gane tanada wayo duk da ƙarancin shekarunta. Matseta yay da ƙyau duk yanda taso ya hanata damar dole ta nutsu saboda abinda ya raɗa mata a kunne kamar ta nutse. tanaji tana gani ya tilasta mata cin nama da kunun wanda yay mata matuƙar daɗi. Dama da ƴar sauran yunwarta ta rana. Bayan sun kammala ta tattara kwanika zata fita da su ya hanata. Acewarsa ta tayashi salla ya bata labarin faransa tunda ita bata tambaya ba. Ganin ya zama serious doleta haƙura. Sai dai ta masa complain na rashin hijjab yace abu mai sauƙi yana da shi ai....

         Raudha dai dauriya kawai take amma tabbas a tsorace take. Bayan sun idar da salla ya dafa kanta yay addu'a kamar yanda musulinci ya tanada ya kuma dace ace tun randa aka kawota gidan hakan ta faru. sai dai lokacin gogan nata na bisa gajimaren hayaƙi hakan bata faru ba. Sosai Raudha tai mamakin yanda taji yana kwararo addu'oi. Sam batai zaton yanada ilimin addini kamar haka ba. Sai taji ya sake birgeta zuciyarta ta ƙara nauyi game da shi.
      Bayan sun idar ma ta buƙaci son zillewa ta gudu ya sake hanata. Ƙarshe ma kayan barci da batasan daga ina ya samosu ba ya bata wai ta saka. A matuƙar kunyace ta dubesa cikin marairaicewa amma ya nuna mata babu wani ɗaga ƙafa yau anan zata kwana. Shi ya gaji da raba musu makwanci da takeyi. Daga karshe ya haɗata da kunyar data sakata bin umarninsa dole.
        “Ustazah a haka za'a samo ƴan huɗun kina gabas ina yamma. Gara dai kiba marasa ɗa kunya ki haifama Maah jikan da taketa fatan gani. Gashi ma kin ƙudiri surprising ɗinta har ƴan huɗu kika shirya.”
       “Kai Ya Ramadhan magana wai bata wucewa a gunka”.
    “Oh ikon ALLAH na kulafa kin fara bin hanyar rainani yarinyarnan. Ni miye nawa tunda faɗa kikai naji. Ai har Anne zanma albishir gobe”.
       “Na shiga tara dan ALLAH ka taimakeni”.
      “Hhhh taimako ɗayane zaki samu sai kin saka kayan nan”.
     Wannan kandagarki nasa ya sata shiga toilet ta canja. Sai dai ta jima tana duban kanta a mirror ɗin toilet ɗin ta kasa fitowa. Sai kallon kanta take cike da kunya da ganin ƙyawun da tayi kamar ba itaba. Sai dai gaskiya bazata iya fita da rigarba gabans....
      Maƙalewa tunaninta yay jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Tai mugun diriricewa ta ruɗe. Tama rasa mizata jawo ta rufama jikinta. Ramadhan da kamar suman wucin gadi ya riska a bakin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa ya ƙaraso gareta. Sai dai a zahiri yanda yake a nutse bazaka taɓa fahimtar halin da yake a ciki ba. A bayanta ya tsaya idanunsa kafe akanta ta cikin mirror da suke fuskanta, sai dai ita ta duƙar da kai ta kuma kuɗindine jikinta da towel ɗin data sami nasarar jawowa.
        Ta bayan nata ya zuro hannayensa duka biyu ya zare towel ɗin data rumtse a cikinsu. A wani irin tashin hankali taja numfashi a fisge da rumtse idanunta da ƙarfi tana ayyanawa a ranta. “Shike nan tawa ta ƙare ni Aminatu”.
        Lallausan murmushi ya saki yana yaye towel ɗin a hankali saboda furicin zuci datai ya fito fili. idunsa kuma a kan cute face nata da hawaye ke silalowa a hankali. Tabbas matarsa ƙyaƙyƙyawa ce, mai kuma ƙyawun surar jiki abin buƙatar kowane irin namiji mai lafiya. Ya ja nannauyar ajiyar zuciya da kamo kafaɗunta duka ya juyo da ita tana fuskantarsa. Rawa jikinta ya farayi dan ƙafafunta bazasu iya riƙe nauyin gangar jikintaba a yau.
          Tausayinta ya sake kamashi, sai kawai ya rungumota cikin jikinsa dan shi kansa ji yake jini na haura masa har saman ƙwaƙwalwar kansa. A tare suka saki kakkaurar ajiyar zuciya, sai kawai ya ɗauketa cak suka fice.
        Cikin gadonsa da kullum Raudha ke ƙwaɗayin ganin an saki runmfar net dake jikinta ya nufa da ita. A hankali ya fara kai ƙafarsa ɗaya ya dire gwiwar sa akan lallausan gadon yana rankwafawa ya direta a gadon itama. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da rauni yace, “To sakeni”.
        Sam bazata iyaba. Dan hanun nata ma rawa yakeyi, ta ƙara ƙanƙame wuyan nasa da hannayenta data tallafo ƙeyarsa hawaye na rige-rige sakkowa.
      “Ameenatu”.
Ya kira sunanta da murya mai tsananin tsada da tsantsane.
           “Uhhmyim!".
Ta faɗa a shaƙe.
    “Kiyi haƙuri na tashi zan canja kaya ne”.
       Da sauri ta girgiza masa kai idanunta rumtse. “Ya Ramadhan tsoro nakeji”.
    Murmushi ya saki mai sanyi, a hankali ya kai bakinsa kan laɓɓanta da goshinta ya sumbata. Cikin sake raunana harshensa yace, “Nima tsoron nakeji shiyyasa na gayyatoki ki tayani kwana kar ojuju ya kamani”.
      Yanda yake mata magana a kunne ya sata sake ƙanƙamesa. Ganinfa ba sakinshi zatai ba sai ya kawai ya kwanto jikinta gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa.
      “Mummy zan mutu”. Ta faɗa da ƙyar jin nauyinsa na fitar hankali. Murmushi kawai yayi ya ɗagata, baice komaiba ya fito a cikin gadon. Ita kuma ta samu damar nannaɗe kanta a bargon zuciyarta na gudu kamar zata faso ƙirjinta ta fito kawai kowa ya huta. Harya koma toilet ya kammala kimtso kansa bata buɗe kanta ba. A haka ya kashe fitilar ɗakin yabar lamps kawai ya shiga net ɗin shima. Bargon data ƙudundune a ciki ya ɗaga shima ya shige..
Murmushi yayi jin yanda ta ƙanƙame waje guda lokacin daya kwanto jikinta. A hankali ya kai lips nashi ya sumbaceta ta gefen kunne, ta ƙara curewa waje guda jikinta na rawa. “Haba Ustazah, tsoro fa na ragwayen mata ne, ko kina so masu zuwa Bingon suzo kuma babu cikin ƴan huɗun uhhm?”.
Kasa cewa komai tai, sai hawayen tsoro dake mata gudu, babu abinda ke cin ran Ramadhan sai dariya. Musamman daya shafa fuskarta yaji hawaye.
“Oh ni Ramadhana, ni kuma haka ALLAH yay dani auren raguwa. Yo raguwa mana, tunkan ace kule ke kin tafi cas...”
Tsabar yanda zuciyarta taje maƙura kuka ta fashe masa da shi mai ƙarfi. Ya danne dariyarsa da ƙyar tare da mirginota ta juyo suna fuskantar juna. Sai kawai ya rungumeta yana shafa kanta murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Sai da ya tabbatar ta nutsu ya dai-daita fuskarsu waje guda, cikin ɗan hasken dake a ɗakin yake kallonta, itako idonta a rumtse gam.
“Kodai mu haƙura da farautar ƴan huɗun kawai Ustazah?”.
Da sauri ta ɗaga mata kanta.
Ya saki murmushi mai faɗi da ɗora goshinsa kan nata ya riƙo hanunta cikin nashi. “Tom naji, amma idan an haƙura minene tukuycina ni?”.
“Wlhy zan maka nama da yawa da safe”.
Raudha ta faɗa da sauri cikin rawar murya. Mi Ramadhan zai inba dariya ba. Wato yarinyar nan ta maidashi mayen nama. A fili kuwa sai ya cewa yay “Okay ALLAH ya kaimu Ƙawata ta amana”.
Daga haka ɗakin yay shiru, jin kamar ya fara barci Raudha hankalinta ya fara kwanciya, itama sai ta lumshe na idanun. Idanu ya buɗe a hankali yana kallonta da murmushi. “Yaro yarone”. Ya faɗa a hankali da jan bargo ya lulluɓesu baki ɗaya.
Can cikin barci ta tsinkayi abinda yafi ƙarfin saninta, sai dai mai girma shugaban kasa da shirinsa yake, dan cikin ƙanƙanin lokaci yay mata dabaibayin daya sakata shagala da miƙa wuya, sai da labari yay nisa ta raina kanta.......


*_Bily kama bakinki iya nan🤐🚶🏻_*



           ★Kallo guda zakai mata kasan taci uban kuka harta godema ALLAH. Duk da kasancewarta ba fara tas ba yanayin saida ya nuna a fuskarta. Gaba ɗaya ta jangwabe kamar ba Ustazah Raudha ta hutawa ɗiyar baba Dauda da Asabe ba. Lallai ba ƙarya daren jiya anci ƙaniyar sabada. Dan kuwa dai mai girma shugaban ƙasar Naya Ramadhan B Hameed Taura bai nuna yasan wata Raudha ƴar 18years ba balle ya bita a sannu. Babu da kalar yaren da bata roƙesa ba amma ya toshe jinsa da ganinsa ya nuna mata baya fahimtar kowanne yare saina cikar burinsa. Cizo da yakushi kuwa ya samu rabonsa gwargwadon iko har ba'a cewa komai. A ƴan gidansu babu wanda bata lissafo yazo ya taimaketa ba har maƙwafta da su Anne sun sha kira........✍

   _Mace ƴar gatan ALLAH. mace ƴar gatan duniya. Mace sarauniya. Mace farin cikin duniya. Mace duniyar duniya. Mata ina miƙo gaisuwar ban girma amma banda ballagazaye wanda suka gama rabarwa a waje🙄🙄😏👩🏻‍🦯_
      

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/5, 11:13 AM] NANA: *_Typing📲_*







*_Episode 49 & 50_*


..........Da asuba daya tadata suyi salla kuka ta dinga masa sosai. Duk sai tausayinta ya lulluɓesa. Shi kansa yasan ya tsaurara mata da yawa, dan dukan fushinsa na shekarun nan babu ƙwange sai da ya sauke shi tsaf. Bata wani yarda ya taimaka mataba tace zata iya.
   Koda ya haɗa mata ruwa sai ya fita a toilet ɗin ya barta. Zafin ruwan ya sata harar ƙofar tana ƙunkuni ta surkeshi ya koma salaf. A haka ta gyara jikinta ta fito tana faman sinne kai. Ga dariya ga tausayi duk suna cin Ramadhan lokaci ɗaya. Amma sai ya gimtse dan karya sake tunzurata.
      Da ƙyar ta yarda suka sake komawa barci bayan ta idar da sallar. Acewarsa su ɗan ƙara rage barcin idonsu dan anguwa zasuje. Taura house yake son suje hutun nan na kwanaki biyar da akai, amma bai sanar mata ba. Dan kuwa bazai yarda amarcin nan ya wucesa bai ɗana gadonsa na Taura house ba.

(Mutumin nan ko😂😜)

         ★Tun a daren jiya dama ya sanarma ƙanensa yau zasu wuce Taura house hutu gaba ɗayansu. Dan haka da safe ya turama Bilkisu text ta haɗama Raudha abinda duk tasan zatai amfani da shi su wuce su sai zuwa anjima zasu zo. Murmushi kawai Bilyn tayi. Sai dai kafin su fita tai ƙoƙarin haɗa breakfast ta ajiye musu. Mama Ladi kuwa ta zauna gadin abincin nan dan kuwa Anne ta kirata tun sanda suka gane Raudha ce ta aika musu takarda akan saka poison a ac ta ce mata ta dinga saka ido akan kowa na gidan kar'a cutar mata da su Raudha. Duk da tasan bata isa hana zartar da ƙaddarar UBANGIJI akansu ba.

        Yanzu kam Raudha ce ta fara farkawa. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login