Showing 156001 words to 159000 words out of 207756 words

Chapter 53 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

642

ɗin ya sauke kasa. kafin ya koma toilet ya ɗauro alwalar barci sanna ya hawo gadon da danna wani abu net ɗin ta buɗe gaba ɗaya ta lulluɓesu. Sai ɗan hasken fitilar cikin gadon daya kunna ya kashe ta ɗakin gaba ɗaya. Bargon da Raudha take ƙudundune a ciki ya ɗage, sai yaga ashe kai da ƙafa take kwance. Kansa ya ɗan girgiza kawai, yasan tadata yanzu wani aikinne kuma, sai kawai ya kwashi piilos ɗin shima ya maida inda tasa kanta dan bazai iya yarda da kwanciyar kai da ƙafa ba shida matarsa. Gara ace ɗaki suka raba ko gadon. Dan lokaci Amnah ko faɗa sukai da ita bai yarda da raba ɗaki ba. Dole ta kwana tare da shi ko zata kwana masa kukan baƙin cikin daya tusa mata. Inma itace tai masa laifin duk zafin da yakeji a ransa ya gwammaci su kwana waje guda ɗin, shi kuma yasan a inda zai fanshe haushinsa ai (🤣😂mugu ɗan masa🙊).

        Sai da ya janye bargo gaba ɗaya ya karemata kallon yanda kayan barcin sukai mata ƙyau kafin ya saki wani ɗan guntun murmushi da iya laɓɓa ya tsaya masa. jikin nata ya taɓa yaji zazzaɓin ya sauka, sai kaɗan da bai ida hucewa ba dai. Filon da take kai shima ya ɗaura kansa suna fuskantar juna. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta sannan yay musu addu'a yaja bargo tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

        Da asuba ya rigata farkawa, sai dai yana motsawa itama ta farka. Gaba ɗayanta a jikinsa take lafe da alama hakan ya mata matuƙar daɗi, sai dai suna haɗa ido tai saurin ƙoƙarin janye jikin nata kunya kamar zata nutse. Riƙota yay ya hanata damar juyawar. Cikin ɗan daburcewa take ƙoƙarin faɗin, “Kayi haƙuri ni ALLAH ban san ma....”
      Ruf ya rufe mata baki da nashi batare daya bari ta ƙarasa faɗa ba (😜ƙazanta ko brush babu🤕🙄). Duk yanda taso kwatar kanta bata samu damar hakanba. Dole ta nutsu ta barshi ya gama yamutsata san ransa tsoro kamar ya kasheta. Dan a tunaninta za'a tafi next level ne😖. Da ƙyar ya iya yakar ƙansa ya barta jin an sake kiran salla na biyu, ya sauka a gadon da ɗan zafin nama ya faɗa toilet. Ruwa mai ɗumi ya sakarma kansa yana mai sauke nannauyan numfashi da rumtse idanu. Sunan ALLAH ya dinga ambata dan yasan lallai akwai matsalolima ba matsalaba. Gashi da alama Raudha tamkar Amnah take itama zatai shegen raki duk da ita daba sickler ɗin ba. Dole ya haɗa harda wankan lada. Koda ya fito yay mata maganar ta tashi bata motsaba dan kunya harya zura jallabiya yasa turare ya fice. Sai dai ya gargaɗeta karya dawo ya sameta a kwance bata tashi tayi salla ba, ta kuma sake shiga ruwan zafi inba hakaba ya dawo da kansa zai sake gasata.
          Raudha da gaba ɗaya a firgice take da Ramadhan ta miƙe da sauri bayan ta leƙo ta bargo ta tabbatar ya fita. Toilet ɗin ta afka itama. Ta watsama jikinta ruwa da ƙara gasa ko'ina duk da dai Alhmdllhi garas ta tashi yau sai dai rashin jin karfi na sabo.
            Koda ya dawo a saman sallaya ya sameta tana karatun alkur'ani. Hakan ya masa daɗi sosai, sai shima kawai ya zauna suka cigaba dayi tare. Duk da mamaki ya matuƙar ɗaure kan Raudha jin yanda yake karatu a nutse cikin daddaɗar muryarsa mai faɗi da amo da gaba ɗaya ta danne ƙarfin tata siririya mai zaƙi. Sunyi karatun da yawa sannan sukai addu'a. Kanta a ƙasa tace, “Ina kwana”.
    Bai amsaba, sai dai ya kafeta da idanu, ɗan dagowa tai kaɗan sai suka haɗa ido, zata maida ya riƙo habarta da hanun damarsa. “Karki kuskura ki rufe idanun nan”. Ya faɗa da sauri ganin tana niyyar lumshesu kuwa. Yanda taji babu wasa a furucinsa ya sata dakatawa. Sai dai taƙi yarda su haɗa ido....
      “Ni bana son irin wannan gaisuwar ga matata shiyyasa ban taɓa amsa miki ba”.
     Duk yanda taso jurewa kasawa tai, sai da ta ɗago ido ta kallesa sai karaf a cikin nashi da launinsu ya canja. Ƙwayoyin cikinsu bakaƙe masu ƙyalli ya juya mata cike da tabbatarwa. Ta risinar da nata tsigar jikinta na tashi dan ta rasa abin cewa kuma. Zuciyarta na tunanin (Banda gulma irin tashi wace gaisuwace kuma bayan wannan da aka banbanta tsakanin mata da miji da sauran mutane? Ita dai tunda ta taso a gidansu irin wannan taga anama Abbansu).
      A bazata kawai taji saukar lips ɗinsa saman goshinta. Kafin ta dire numfashi ya saukesu kan lips nata ya bata light k.. Harya janye kuma ya sake maidawa ya cafkesu da ƙyau yana matse hanunta dake cikin nashi tsam.
       A gwame ta dinga fidda numfashi kamar yanda nashi ke fita a harɗe, har saida yayi yanda yake so sannan ya barta dan kansa. Cikin rufewar idanu ya lalubi kunenta.
     “Wannan itace nake buƙata a kowacce safiya idan mun tashi, da kuma idan na dawo aiki shine sannu da zuwana”.
      (Tabb ashe kuwa akwai tsallen baɗake) cewar Raudha a zuciya. A fili kam yanda yay maganar babu wasa a ciki ya sakata jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Mikewa yay shima ya mikar da ita batare da ya sake cewa komaiba. Dolenta tabi yanda yakeso suka koma gado bayan ya cire mata hijjab ɗin ya barta da abayarta dan shima yana son kauda kansa ga abinda zuciyarsa ke bijiro masa.
      Fargaba ta hanata barci har sai da taji yana sauke numfashi a hankali alamar shi ya fara sannan tai nata itama tunda taga ba abinda take tsoron bane zai faru..........✍


*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*



*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/5, 8:17 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_Episode 53_*


..........*_JIHAR ƊILLO (HUTAWA)_*

           A Hutawa kam kowa yaga M. Ɗan-azumi yanzu sai yay matuƙar mamaki. Dan kamar yanda ya ƙudiri ƙara sabon aure ya auro dalleliyar budurwa sabuwa dal a kwali. Kai daka ganta kasan ƴan kuɗin ta biyo. Baƙaramin tashin hankali Larai ta shiga ba, dan saika ɗauka ma wani sabon haukane ya hau kanta. Data nema birkice masa sai ya aikata gida taje ta huta. Roƙo iya roƙo ita da danginta amma ya birkice musu ƙememe dama fitinarta ta isheshi, ga baƙin cikin rabasa da masoyiyarsa Asabe da har yanzu ko ɗigon sonta baibar zuciyarsa ba. Ganin haka Baba Nafi ta ƙara kama kanta da mutuncinta a gidan, dan tun dawowar Inna da ƙaninsa da matarsa dama gidan ya sake zama sai a hankali. Gadai jin daɗi yanzu a cikinsa amma kowa zaman haƙuri yake da ɗan uwansa saboda fitinar sirikarsu dabance a rayuwa, shi kuma M. Dauda na biye mata dan duk haukarsa yana ƙaunar Innarsa.
          Tun auren Raudha alaƙar zuminci mai ƙarfi ke tsakaninsa da hakimi, hakama jama'ar gari sosai suke respecting nashi kowa burinsa ya zama abokin mu'amularsa (kaiko sirikin shugaban ƙasa fa ba wasa ba😝). Da wannan damar M. Dauda kan samu na hura hanci sai ya zaɓi wanda yaso ayi zumincin, shi da M. Gambo ne dai ana nan tif da taya, sai dai baisan M. Gambo nata masa zagon ƙasan ƙoƙarin kiran Asabe a wayaba kullum, wani lokacin harda mata ɗan text na soyayya dan ƴar sakandire ɗin nan dai shi da M. Dauda sunyita. Ita Asabe har zuwa yanzu batasan wanene ba. Dan tun tana sharesa da masa masifa idan ya kirata harta ɗan fara kulashi.
       Hakimi daya fahimci rawar kan M. Dauda bata risinaba saima giyar kuɗi dake neman ɗorasa a wani layin bayan wanda yake kai yasa shi ƙara jansa a jiki yana masa nasiha, ya kuma bashi sarautar data tilastashi kullum zuwa gidan Hakimi ayi fadanci dashi. Koda yake mugun ɗagawa da faɗi yake da sarautar, inma ka kira sunansa baka haɗa da sauratarba to kuwa kaji barbaɗin jaraba daga sama har ƙar zai zugeka yana hura hanci da kiran shi ya wuce raini ai. Surikin shugaban mai ƙasar yake baki ɗaya, Baba sama baba ƙasa yake kiransa kuma saiya risina yake gaisheshi koda a wayane balle wani ƙaton ƙawai da talauci yayma katutu. (😂🤣ALLAH ya bar mana Man Dauda).
      Ya sayi ƴar kwariɓar motarsa ana yanga da ita kwana biyu ta birkice, cike da masifa ya maidawa bakaniken daya saida masa yace wlhy koya dire masa kuɗinsa kokuma yasa azo daga Bingo a cukuykuyesa yasan dai uban matar shugaban ƙasa yake. Da farko makanike ya ɗau abin wasa, dan mahaukacima suka maida M. Dauda shi da yaransa. Saiko gashi ko mintuna ashirin baiyi da barin wajenba motar ƴan sanda har uku sunzo sun yayesu gaba ɗaya har yaran nashi. Dan kuwa M. Dauda yana zuwa police station d.p.o da ayanzu ya gama haddacesa shi da yaransa koda ɗunbin alkairin da suka samu a ranar auren ƴarsa da shugaban ƙasa sukai masa tarbar mutunci. Harda matsar kwallan munahinci wajen faɗa musu abinda akai masa a gareji. Rai ɓace d.p.o ya bama yaransa umarnin zuwa a kwasosu yana bama M. Dauda haƙuri.
       “Baba ai kun wuce ko kallon banza yanzu a ƙasarnan, kunefa iyayen masu ƙasar. Gamu nan tunda ɗanku ya hau mulki albashinmu ma ninkashi akai tsabar adalci na wannan shugaba. Ai mu babu abinda muke sai fatan alkairi a garesa, mun kuma tabbatar lallai matasa masu jini a farce ƙasar NAYA ke buƙata irinsa.. ALLAH ya ƙara masa zaman lafiya da matarsa nan da watanni asake zuwa taron suna NAYA muci musha muyi warkan. Dan muna alfahari first lady tamuce wlhy”.
     Daɗi kamar zai kar m. Dauda, ya dinga washe haƙwara yana sake baje babbar rigarsa dan ɗinkunan alfarma da Alhaji Hameed Taura yay masa na biki har kala goma sune suka zama na faɗi yanzu a gari. Lokacin da aka shigo dasu Gali a ɗage M. Dauda yake kallonsu da watsa hannaye gaba. “A rufeminsu har sai na manta da wanzuwarsu sannan a tunamin”.
     Cikin roƙo da magiya kanikawan nan ke roƙon Alhaji Dauda (dan tunifa dama gargaɗi yake abar kiransa M. Dauda😂😜). Amma ko kallonsu baiyiba. Cikin takun ƙasaita ya buga babbar rigarsa aka fice dan d.p.o ya bada motarsa a maidashi gida.

       Kwanakin kanikawan nan huɗu a ofishin ƴan sanda sannan ya bari aka sakesu da sharaɗin maido masa kuɗaɗensa nanda sati guda. Hakan kuwa akai sai gasu da kuɗaɗensa cif sun kawo, ya dinga antaya musu harara yana sake baje riga da hura hanci. Bayan ya koma gida ne ya nema kuɗin ya rasa da kwana biyu shine ya yanke jiki ya faɗi har saida aka kaisa asibiti. Wannan ne dalilin zuwa su Fatisa dubashi har suka sanarma Raudha, to ayanzu haka dai ya haɗa duk yaran gidan nasa da matan ya tabbatar musu idan kuɗinsa basu dawoba nera dubu ɗari bakwai wlhy suma cell zaisa a zubasu har sai sun magantu.

(🤣😂To bara muga ta inda kuɗin Alhaji Malam Dauda surikin shugaban ƙasar NAYA zasu fito).


*_BINGO CITY (TAURA HOUSE_*

            Barci sukasha sosai kamar yanda Ramadhan yaso. Ga Anne daga falo na musu gadi dan koda su Basma suka taho wai anan zasuyi breakfast korasu tai duk da tasan da wahala hayaniyarsu takai ga sashen Ramadhan ɗin. Dama tunda ya shiga ya gaisheta bayan sallar asuba yace kar ai musu breakfast da wuri. Dan haka ba'a ɗora ɗinba kuwa sai kusan sha ɗaya na safe. Zuwa sha biyu an kammala komai an kawo falon part ɗinsa an shirya bayan an gyarashi yanata ƙamshi duk da bawani datti yayi ba.
         A yanzu ɗinma kusan tare suka farka sai dai motsintane ya tadashi. Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan. Cikin yanayin kasalar barci ya mika hannu ga side drawer ya ɗakko agogonsa yaɗan kalla time cikin lumshe idanu da buɗewa. Har sha biyu ta gota. Agogon ya ajiye da kai lips nashi a goshin Raudha da taƙi buɗe ido ya sumbata. Kafin ya saketa ya sauka baki ɗaya batare da yayi magana ba.
     Bata iya motsawaba sai da taji ya rufo toilet ɗin. Ta miƙe da ƙyar itama dan barcine da bata sabayi ba ace tun sallar asuba har kusan 1. Gadon ta shiga gyarawa a ɗan gurguje, ta maida net ɗin yanda ta gansa, sosai yake birgeta dan ya sake kawata gadon da ɗakinma baki ɗaya. Har falo ta fito neman kayan shara, cikin sa'a ta samu a cikin kitchen bayan ta karema falon da kitchen ɗin kallo. komai akwai na buƙatar ɗiya mace har tana mamakin sai kace mai mata.
     Shara ta gama tana tsaka da mopping ya fito. Bata yarda ta kallesa ba, sai shine dake binta da kallo ya nufi mirror yana faɗin, “Waya saki wannan aikin?”.
      Amsa ta bashi batare data yarda ta kalla inda yakenba dai.
     “Ba kowa”.
  Komai bai sake cewaba harta kammala ta fita da kayan, taɗan jima kafin ta dawo da fatan ALLAH yasa ya saka kaya. Sai dai addu'ar tata bataci ba dan har lokacin ɗaure yake da towel tsaye a gaban Wadrobe da alama kaya yake nema. Kaita kauda cikin sauri ta faɗa toilet.
     Baki yaɗan taɓe dan duk yana kallonta ta gefen ido. Ta jima bata fitoba, har sai da ta leƙo taga baya ɗakin. Da sauri-saurin tai shirinta cikin atanfa datai mata ƙyau matuƙa, ga ɗinkin ya fidda jikinta tsaf kamar ka saceta ka gudu. Ɗauri tai mai sauƙi amma ya mata ƙyar ta saka ƴan kunne kawai harda yafa mayafi sannan ta fito da nufin zuwa gaida mutanen gidan duk da kunya da nauyin ƙin zuwa akan lokaci na cinta. A tunaninta Ramadhan ma nacan, sai dai tana fitowa falo taci karo da gogan nata zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon labarai a television da alama sallar azhar yaje yayo kawai ya dawo.
     Tsamm tayi a ƙofar ɗaki kamar bazata karaso ba. Sai kuma cikin dauriya ta cigaba da takowa har inda yake. Kanta a ƙasa tana wasa da zobon hanunta tace, “Ya Ramadhan zanje naje na gaida su Anne”.
    Maimakon ya amsa mata duk da idonsa ba'a kanta yakeba sai taji ya riƙota ya zaunar saman cinyarsa. Mutsu-mutsu zata fara ya dakatar da ita ta hanyar yaye veil ɗinta gaba ɗaya. “Banda ƙauyanci miye na zuwa gaban miji da veil?”.
        Duk da maganar ta bata haushi sai ta dake. A sanyaye tace, “Wajensu Anne fa zanje”.
      Wasa yake da jelan kitsonta idonsa a tv, “Sunce sun yafe yau ko ƙofar corridor ɗin can bazakije ba nayi gaisuwan da taki ai tun ɗazun”.
      “Kai Ya Ramadhan wlhy bai kamataba ace banje na gaishesu ba. Gashi dama lokaci ya gama shigewa ai da kunya”.
        Maimakon amsa mata maganar ko barinta tafiya sai ya ɗagata daga jikinsa shima ya tashi, dining ya nufa da ita dan shi ta yunwar cikinsa ma yakeyi. Dolo ta haɗiye komai dan yaci serious kamar bashi ba. Tsorone yaɗan fara kamata na gudun karfa mutumin nan ya juya mata baya bayan ya rabata da mutuncinta. Dan taga tun jiya ya koma sha mata ƙamshi irin yanda yakeyi mata a baya. Da wannan tunanin tai saving nashi komai, zata zuba nata ya hanata yay mata nuni data zauna kawai. Dole tabi umarninsa zuciyarta fal tsoron abinda ba haka bane. Shi Ramadhan yana ɗan ɗaurewa ne kawai dan gujema abinda zuciyarsa ke kwaɗaita masa game da ita. Dan tausayinta yakeji matuka. Amnah mai shekaru da suke gab da nashi duk da tanada lalura bata iya jure ɗaukarsa akoda yaushe balle ita. Dan sauda dama idan yaje gareta sai tayi kuka balle Raudha da yakema kallon jaririya. Shi kansa yasan yayi juriyaa shekarun da babu Amnah, amma ya tabbatar ɓacin rai da tashin hankaline suka girmama juriyar tasa, yanzu ko daya ɗan ɗana bayajin zai ɗaga ƙafa duk da ƙoƙarin hakan da yakeyi.
      Tare sukaci abincin Raudha nata sinne-sinne. Shi dai bai kulataba. Daga ƙarshema ya amshe cokalin ya koma bata da kansa. Ina ƙasa ta shige amma babu damar gardama dan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login