Showing 135001 words to 138000 words out of 207756 words
sauke damuwar kan ƴar mutane ba, koda yake bawai komaine ke ɓata ran nasa ya aikata ba. Cikin katse tunanunta tace, “Ai mijin nan naki kam sai addu'a Aminatu, wani lokacin idan ya birkice tamkar mai iskoki a ka haka yake. Sai kinta haƙuri kinji. yanzu dai asamu kayan ƙamshi ai masa shayi da su citta ya fito sosai a ciki harda tafarnuwa. A abincin da yace yana so ma asaka yaji ya ɗan fito. Nasan sa da son wanka da ruwan sanyi ki hanashi, hakama ruwa mai sanyi karki bari yasha koda fura ne ko madara. Ruwan shansa ya zama da ɗan ɗumi haka, ƙafarsa ta kasance cikin safa. Yasha magani idan yaci abinci insha ALLAH zai taimaka masa hakan dan haka nake masa idan yana mura. Zuwa anjima zan kira, idan zazzaɓin bai sauka ba sai a turo Dr Shamsu.”
Raudha dake jin lisaafin kamar na ɗan goye ta jinjina kanta kamar tana a gaban Anne. “To Anne insha ALLAH yanzu duk za'ayi. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana.”
“Amin Aminatu ALLAH ya saka miki da alkairi yay miki albarka.”
Cike dajin daɗi Raudha ta amsa mata kafin suyi sallama........
Wayar ta sauke da ga kunnenta tana sauke numfashi. Sai kuma taɗan kallesa ta maida kanta ƙasa da sauri ganin ita tsurama idanunsa kumburarru. “Mizaka ci to sai a girka kafin magrib insha ALLAH an kammala?”.
A hankali ya janye idanunsa a kanta batare da yasan ya shagala a kallonta ba tun tana waya da Anne. Shi kansa zuwa yanzu ya tabbatar yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, sai kuma baijin zai..... Kasa ƙarasa abinda zuciyarsa ke son faɗa yayi badan yasan dalili ba. Cikin dasashshiyar muryarsa ya sake dubanta yana magana a hankali tamkar mai raɗa. “Koma miye ki dafa zanci”.
Kanta ta jinjina masa tana miƙewa. Ya bita da kallo harta nufi stairs. Sai da ta ɓacema idanunsa ya sauke numfashi da ƙyar yana ɗaukar remote ya canja television zuwa inda zaiga labaran shida na yamma.
Sanin maitarsa da nama ya saka Raudha haɗa masa farfesun da taimakon mama ladi. sai kunun gyaɗa, madarar shanu dake gidan ta tafasa itama ta juye masa a flask sai shayi. Aikin bai wani jasu da nisa ba tunda kaɗan iya cikinsa ne. Kuku kuma sukai sauran iya dai su dake sashen.
Da taimakon mama ladi ta hauro da kayan anata kiraye-kirayen sallar magriba. Ya tashi a falon, dan haka Raudha ta amshi sauran kayan hanun mama ladi tana mata godiya. Ɗakinsa ta nufa, tai knocking har uku bataji motsi ba, sai kawai ta tura ƙofar ta shiga da tunanin ko yana alwala. Ɗakin na nan tsaf yanda ta gyarashi da safe, sai dai duk ya watsar da kayan daya dawo office akan gado da ɗan stool ɗin jikin gadon zuwa ƙasan carpet. Kayan hanunta ta ajiye tana kwashe kayan, sai lokacin idonta ya sauka kansa a gado nannaɗe cikin bargo. Tausayi ya sake bata, ta ƙarasa ta gefesa, ɗan ranƙwafowa tai a ɗarare takai hannu taja bargon daya rufa har saman kansa, rawar sanyi ma taga kamar yanayi, yana ƙoƙarin ture hanunta da son hanata janye bargon sai hanun ya shiga cikin nashi, damƙewa yay da iya ɗan ƙarfinsa ya fisgota. Abinka da ba ƙarfi ɗaya ba sai gata gaba ɗayanta a kansa.
“Wayyo ALLAH na”. Ta faɗa cikin matse fuska saboda ƙirjinta daya bugi jikinsa, sauƙinma laushin bargon ya bata kariya sosai. Ƙoƙarin tashi take kamar zata fasa kuka, hakan ya bashi damar ɗaga bargon ya turata ciki. Rawa jikinta ya farayi, dan al'amarin yazo mata a bazata, ta shiga son fita da janye jikinta daya tura a nasa ya matse, duk da a halin ciwo da yake ciki hakan bai hanashi sauke ajiyar zuciya ba. Cikin rawar muryar da ke tabbatar da baida lafiya yake magana a kunenta cikin raɗa da sambatu na ciwo (Dan idan yana ciwo tofa akwai sambatu kamar su oh eh😂. bazan faɗi suna ba dai🤭 lol.)
“Anne sanyi nakeji ki ƙara min bargo, Anne kaina ciwo kamar zai fashe, wayyo Anne kaina jikina zafi Anne ko'ina ciwo”.
Dariya, tausayi, tsoro, mamaki, duk suka dira a zuciyar Raudha lokaci guda. Gata matse a jikinsa tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa ga zafin jikinsa na matuƙar ratsa nata jikin. Sosai ƙirjinta ke bada sautin fatt! Fat!! Da ƙarfi, da ace lafiya yake babu abinda zai hanashi da kiranta matsoraciya. Cikin rawar murya tace, “To ka bari na tashi na baka magani gashi magrib ma tayi”.
Jin muryarta saɓanin ta Anne da yake tsammanin ji ya ɗan buɗe ido, ba ganin fuskarta yake ba dan ya rufe musu har kai a bargon, “Kinada tausayi kuwa?”. Ya faɗa yana sake ƙanƙameta har saida tai ƴar ƙara saboda ƙirjinta. gaba ɗaya a birkice yake, “I'm sorry”. Ya sake faɗa a hankali cikin kunenta yana sassauta mata riƙon, sai kuma ya sake faɗin, “Kiyi shiru bana son magana kaina na ciwo”.
To yau dai Raudha taga takanta. Ɗan ƙwalisar nan Ramadhan mai shegen ɗaukar kan nanne haka. Shugaban ƙasar NAYA jinin Taura da ko kallon arziƙi sai ya gadamar wanda zai yimawa. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai jinƙai. Maiyin yanda yaso, ga wanda yaso. Cikin ƙanƙanin lokaci in yaso kamaka da ƙanƙanin abu sai ya firgitaka ka mance kai waye? Miye matsayinka?. Taja numfashi a hankali da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na REED. Zuwa yanzu ta nutsu a jikin nasa badan taso ba, babu abinda ke ratsata sai zafin jikinsa da sautin bugun zuciyarsa. Sai saukar numfashinsa a wahale. Magana yake a hankali bisa laɓɓa da bataji, sai dai tanajin alamar motsin bakinsa. Ta fahimci sambatune na ciwo kawai ke ɗawainiya da shi. Kusan mintuna talatin suka samu a haka, ganin lokacin salla na sake shigewa ta fara magana a hankali cike da lallashi.
“Lokacin salla nata sake nisa, ga abincin na kawo maka kuma da magani kayi haƙuri na tashi na baka kar mu makara salla”.
Sarai ya jita, dan idonsa biyu. Sai dai bai nuna alamar yajin ba har bayan shuɗewar wasu mintuna.
Da ƙyar Raudha ta samu ya rabu da ita ta tashi, toilet ta shiga tana sauke tagwayen ajiyar zuciya da taɓa jikinda da yay zafi kamar itama ta kamu da zazzaɓin. Ruwan ɗumi ta daidaitamsa domin yin alwala. Tayo tata sannan ta fito. Har yanzu yana cikin bargon ƙudundune. Cikin lallashi tace, “Ya Ramadhan ka daure kayi sallan sai kaci abincin da magani”. Kamar bazai motsa ba sai kuma taga ya miƙo mata hanunsa da ga cikin bargon, duk da kunya dake ɗawainiya da ita hakan bai hanata kamawa ba danta fahimci abinda yake buƙat kenan ta taimaka masa ya tashi. Da taimakon nata kuwa ya tashi, ganin kamar yana tangaɗi sai taƙi sakinsa sukaje ƙofar toilet, sai da taga ya shiga sannan ta sauke numfashi. Kasancewar akwai hijjab jikinta tasa abin salla tayi anan, tana raka'ar ƙarshe ya fito da alama ba alwalan kawai ya tsaya ba yayi wani uzirin nasa daban. A ɗayan abin sallar data saka masa ya tada sallar shima yana faman riƙe kai, kafin ya idan da sallar aka shiga kiran isha'i, hakan yasa Raudha komawa ta zauna domin gabatarwa.
Su dukansu sai da sukai salla har isha'i sannan ta haɗa masa abinci. abin mamaki yau yanka uku Ramadhan yaci na nama, sai romon farfesun kawai ya cigaba da sha. Raudha dake gulmarsa a zuciya ta shiga jinjina kai tana mamakin eh lallai magana ta girma kure na gudun nama yau. To ashe akwai ciwon da zai iya hana Ramadhan cin nama a duniyar nan?. Batace komai ba ganin ya ɗan sha ruwan kunun ya kuma sha romon nama. First aid box data gani a ɗakin ta ɗakko ta duba, cikin sa'a ta samu maganin mura data san yanada inganci tunda tasha amfani da shi itama. Da ƙyar ta samu yasha maganin yana yamutse fuska har yaso bata dariya, ta dai daure ta gimtse.
Koda ya koma saman gado da nufin kwanciya a ɗofane taɗan zauna. gadon da nufin gyara masa bargo kawai sai jitai ya ɗaura kansa a cinyarta, tare da riƙo hanunta yay filo da shi a kuncisa. Idanu Raudha ta ƙwalalo sai kuma ta ƙwaɓe fuska. Oho basai tanayi ba dan harya fara lumshe idanu, dole ta hakura da ƙudirin idan yayi barci ta zame jikinta ta gudu...........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62bdf225f0fb62def3170d0f
*_Episode 45_*
............Tun Raudha na irga sakanni harta koma mintuna, kamar wasa suka cinye rabin awa. Data yunƙura zata tashi Ramadhan zai sake ƙanƙame mata hannu, ga kansa bisa cinyarta. Fahimtar kamar barcin nasa baiyi nauyi ba yasata haƙuri ta sake bashi lokaci harda jingina da fuskar gadon, cikin rashin sa'a itama barci yay a won gaba da ita a wajen mai nauyi dan a gajiye take yau ga rashin barcin jiya cike da idonta dama.
A hankali ya fara buɗe idanunsa da sukai masa nauyi irin na mai farkawa a barci da rashin jin daɗin jiki. Alhmdllhi zazzaɓin ya jima da sauka. Hakama ciwon kan kaɗan-kaɗan yake jinsa shima yanada alaƙa da maganin murar da bai gama sakinsa ba dan barcine taf a idanunsa. Sabo da tashi sallar asuba akan lokacinta ya sashi farkawa. Hanunta da ke riƙe a nasa fuskarsa a kai ya ɗan tsurama ido, tun yana kallonsa dishi-dishi cikin ɗan hasken lamp har idonsa ya dai-daita. Zuciyarsa ce ta ɗan motsa na alamar mamaki, yay saurin ɗaga kai ya dubi sama. Itace kuwan da gaske, kuma akan cinyarta kansa yake. Ta ɗan zama kaɗan ta kwanta saɓanin da da take zaune. Sai dai a kallo ɗaya ya fahimci kwanciyar batai mata daɗi dan a matuƙar takure take a wajen.
Idanunsa ya dafe tare da cije haƙoransa ya tura yatsun hanunsa cikin sumar kansa. ‘Ya ALLAH’ ya faɗa a hankali cike da jin haushin kansa. Dan ya gama fahimtar lallai anyi abun kunya a daren jiya. Inhar irin sambatun daya san yanama Anne idan yana zazzaɓi yay mata itama to shikan dai yagama ganin takansa, raini kuma tsakaninsa da yarinyarnan ya samu gurbin zama. ‘Ni Ramadhan miya shiga kaina ne wai?’.
Ya sake faɗa a fili lokacin da yake tashi zaune hanunsa dafe yaɗan karkata yana kallonta. Duk da takaicin kansa da yake ji hakan bai hanashin jin tausayinta ba. Shi kansa ya sani idan shine bazai iya juriyar kwanciya haka ba dan kawai wani yaji daɗi shi. Jin za'a tada salla ya sashi miƙewa ya sakko a gadon da ƙyar, sai da Raudha ta tabbatar ya shiga bayin sannan ta buɗe ido a hankali. Tun motsawarsa itama ta farka, ta ɗaga hanunta da yay matuƙar tsami da ƙyar taɗan yarfar, wani irin azaba ya ratsata. Saurin riƙewa tai da ɗayan tana cije baki. Da ƙyar ta iya tashi dan kafaɗarta zuwa wuya suma duk a riken suke.
Cikin dauriya ta fita a ɗakin zuwa nata dan shima taji motsin ruwa alamar wanka yake. Itama da gasa jikinta ta fara, duk da ba saki hanun da wuyan sukai ba haka ta daure bayan idar da salla ta nufi kitchen. Tunda ta fito ma'aikatan gidan daketa fitowa domin tsaftace sashen ke zubewa suna gaisheta. Babu sa'anta a cikinsu, ta tabbatar kuma ko'a ilimi sun fita, dan haka take matuƙar jin nauyin wannan girmamawa da suke mata. Sai dai tana dauriyar dannewa da amsa musu a dake dan wani girman idan ALLAH ya baka dole kai haƙuri ka riƙe.
A kicin ɗin ma duk zubewa su kuku sukai suna gaisheta, sukam har sun tsaftace ko'ina sunama ƙoƙarin fara ɗora abinci ne. Tambayar mi zasu dafa tayi, suka sanar mata. Babu abinda ya kwanta mata da yanayin mara lafiya, dan haka tace suyi iya wanda za'aci kawai. Ita kuma ta fara ƙoƙarin haɗama Ramadhan da taimakon Agnes da ita kaɗaice kuku mace a cikinsu. Haka kawai nutsuwar Agnes ɗin ke burgeta. Gata dai ba muslma ba amma bata da rawan kai, kuma bazaka taɓa ganinta da shigar banza ba. Haka farce da ƙarin gashi duk bata sakawa.
Komai suke Agnes a girmame take tayata duk da ta girmeta sosai, amma tsabar girmamawa Mommy take kiran Raudha. Tsaf suka kammala komai, Raudha zata ɗauka basket ɗin Agnes ɗin tai saurin ɗauka cike da girmamawa. “No Mummy zan ɗauka”.
Cikin ɗan Murmushi Raudha tai gaba dan bata son gwasale Agnes ɗin. A tare suka haura saman, Agnes zata nufi dining Raudha ta dakatar da ita ta amsa da mata sannu. Kai tsaye ɗakin Ramadhan ta nufa, haka kawai murmushi ya suɓuce mata tunawa da abinda ya faru jiya dama abinda taji yana faɗa ɗazun, ta gama fahimtar baya ƙaunar raini sam. A zuciyarta take faɗin (karka damu, indai Aminatu ce har abada babu raini tsakaninmu).
A fili kam sai tai knocking ƙofar kaɗan dayin sallama. Bataji an amsaba sai kawai ta tura ƙofar tana ƙarayi. Duk abinda take yana kwance yana jinta, sai dai yay luf fuska a tamke dan kawai yasan tunda har jiya yay abun kunya ta gama samun hanyar rainasa. Raudha har zuciya bata kawo lanbo yay mata ba. Ta ajiye basket ɗin ta fita.
Da kallo ya bita harta fice.
★★Sai da ta kammala shirinta na fita tsaf cikin kayan mutunci sannan ta fito tare da kulle ɗakinta dan tasan a koda yaushe su Lubnah zasu iya dawowa gidan. Koda ta koma ɗakinsa ta iskesa still kwance sai jikinta yay sanyi, duk zumuɗinta na son tafiya makarantar kuma sai ya fita mata a kai. Ajiye bag ɗinta da hijjab tai ta nufi toilet, tsaftacesa tai ta fito ɗakin shima ta gyara iya inda bazata takura masa ba. Daga haka ta ɗauka bag ɗinta ta koma ɗakinta dan ta haƙura da makarantar kawai tunda shima bazai fita ba.
Acan waje tuni securitys ɗinta da jiya ta gudumawa suna falon ƙasa suna jiran fitowarta. Hakama driver ya shirya tun da wuri dan gani suke jiya sakacinsu ne ya sata fita a gidan badasu ba. Basma ta kira ta sanarwa yau bazata shigo school ba. Daga baya sa nuna mata abinda aka kawai. Bata bama Basma damar yin ƙorafi ba ta kashe wayar gaba ɗaya itama ta kwanta, dama barcine taf a idonta ga ciwon da jikinta ke mata akan kwanciyar jiya.
Tunda cos ya ga takwas ta wuce shugaban ƙasa bai fitoba yasan murar jiya ta kwantar da shi kenan. Saƙo ya tura masa kawai ya cigaba da abinda ya dace dan Alhmdllhi ma yau abubuwan da Ramadhan ɗin zaiyi duk ba masu tsawwalawa bane. Zaman meeting ne sau kusan huɗu duka kuma an riga an tsara wanda zasuyi zaman. Abinda yake tilas saka hannu ne akan wasu takardu.
_______________________________
Tunda su Basma ke bada labarin Raudha ta fara karatu a school ɗinsu zuciyarta ke a ƙuntace. Lallai ta sake tabbatarwa ɗanta baya tare da ita. Komai daya shafesa sai dai taji a shanun ƴan talla. Tana cikin wannan yanayi Mardiyya tazo gidan, ɗiyarta ta biyu dake bin Ramadhan. Daga office take taga ya dace ta biyo ta gaishesu dan rabonta da gidan tun bikin Ramadhan ɗin. Haka take ita bata da kwaramniya, ga haƙuri. Lokuta da dama mutanen gidan kan ɗauketa wadda bata ɗaukar abu serious, sai dai kuma ba haka bane. Ita irin mutanen nan ne da babu ruwansu da shiga sabgar daba tasu ba, muguwar ƴar I don't care ce ta bugawa a jarida. Halayyarta ya saka bata wani shiri na'azo a gani da Gimbiya Su'adah. Yaranta huɗu, tare da mijinta suke aiki a companyn su na kansu da sukai haɗin gwiwar ginawa ita da shi. Ba ƙaramin bala'i a lokacin taci ga Gimbiya Su'adah ba. Amma tai fumfurus ta shareta. Da farko robobi companyn ke fitarwa, a hankali abubuwa suka kara bunƙasa takai har designes na wasu abubuwan daya shafi kayan kitchen suna sarrafawa. Kamar wasa sai gasu sun bunƙasa suma ana kwatantasu a jerin manyan kamfanoni dake sarrafa abubuwa masu muhimmanci a