Showing 165001 words to 168000 words out of 207756 words

Chapter 56 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

645

sai ta ɓata fuska da ture hanunsa.
       “Ni ba wani kishi”.
Karamar dariya da rabonta da gani a garesa tun jiya yayi har haƙoransa na bayyana sosai. Ya shafa fuskarta da faɗin, “To shikenan naji ba'a son Ramadhan balle ai kishinsa. Sai dai ina bada shawara a gyara kafin naki ɗage kafar tafiya aljannar”.
     Murmushi tayi cike da kunya ta sake sinne kanta a jikinsa. Daga haka suka shirya. Sai dai koda suka nufi ɗakinsa yayin kwanciya babu abinda yay mata sukai barcinsu lafiya.

       ★_______★______★

     Dauriya iya dauriya Ramadhan yayi akan kin sake kusantar Raudha, sai dai salon yanda yake mata abubuwa ya ƙara shaƙuwa a tsakaninsu. Ga Bilkisu na sake ɗaurata a layi sosai ita da mama ladi. Gefe kullum Asabe cikin yima yarta nasiha take akan abubuwa da yawa da abaya tasan ita ta tafka kuskure a kansu a rayuwar nata auren.
    Karatunta na tafiya lafiya cikin aminci, randa Ramadhan bai gajiba idan ya dawo sukanyi karatu ya kara faɗaɗa mata bayani akan abinda bata ganeba. Hakama Bilkisu na iya bakin koƙarinta.  Acan school kuwa sun ɗinke da Queen Billy da batasan wacece Raudha ba. Har yanzu ma bata yarda ta nuna mata fuskarta ba. Duk da tasan kota nuna ɗin da wahala ta ganeta tunda dai babu wanda zaice ga ainahin fuskarta a duk hotuna dake yawo a media ita da shugaban kasa saboda facemask da take sakawa a koda yaushe idan suna tare. Su Basma ma sun karɓi Queen Billy, dan tanada shiga rai saboda barkwancinta da yawan fara'a. Ranar juma'a da take cika kwana biyar ciff batare da Ramadhan ya sake neman komai daga garetaba ta dawo school a gajiye da yamma lis. A falo ta iske Bilkisu da Ramadhan daya dawo gida da wuri yau. Dan shima Alhmdllhi komai yana tafiya masa dai-dai babu abinda gwamnatinsa keyi yanzu sai shimfiɗa manyan ayyuka da yan ƙasa keta sambarka. Irinsu Alhaji Haladu Gwandu da su forma president da God Fathers nasu kuwa na gefe sun shaka sunyi fam da takaici. balle kuma vice president da kamar ya zama hoto ga wasu al'amuran na gwamnati. Dan shegen mugun halinsa da Ramadhan ya fara fahimta ya sashi ɗan janye jikinsa da shi abubuwa da yawa sai dai ya gani a takarda. Ga kuma binciken da suke kanyi akan abinda suka fahimta game da alakar matarsa da Raudha.
      Bilkisu ce kawai ta mata sannu, gogan ko ido kawai ya tsura mata yana kallonta ƙasa-ƙasa duk da fuskarta sakaye take da niƙab. Baki taɗan tura da kauda kanta daga garesa tace, “Ina yini”.
     Shiru yay bai amsa ba, sai ma sake karkatar da kai yayi. Bilkisu dake musu dariya ƙasa-ƙasa ta miƙe cikin sanɗa tabar wajen. Ganin haka Raudha data yaye niƙab ɗinta tana kumbura fuska itama tabar wajen ta nufi ɗakinta. Idanu yaɗan lumshe da saki tattausan murmushi yana shafar kwantaccen gashin fuskarsa da yayma gyara ɗazun da safe san dan samun yin sallar juma'a cikin annuri da haiba.
        Yana nan zaune a wajen har Raudha ta sake fitowa bayan kusan mintuna talatin. Sanye take da skirt da riga na atamfa, sun mata ƙyau sosai sun kuma kama mata jiki ɗam saboda ƙibar data ƙara. Dan sosai Raudha ke buɗewa ta ko'ina tana ƙara girma. Ga wani haske da tayi fatanta ya ƙara kwanciya luff da ɗan duhun da bazaka kirata fara ƙal ba.
       Tsabar jan magana ta gaban Ramadhan tazo zata wuce kanta ko ɗankwali babu. Sai gashinta dake tsefe data ɗaure da ribbon yanata reto. Yi yai kamar bai ganta ba. Sai dai ta kusan gama giftashi ya taɗota da ƙafa sai gata a jikinsa. Ƴar ƙara ta saki mai cike da zallar shagwaɓa. yay saurin buge bakin da yatsunsa biyu.
       “Wayyo Anne zai fasamin baki”.
Ta faɗa hawaye na ciko mata. Zata tashi ya maidata, kamar gaske ya wani tsuke fuska. Cikin ɗage gira da hararta ya sake kaima bakin nata ɗalli ta kare. “Na kula kin fara rainani a gidan nan. Harni zakima ƙwalele da halalina”.
      Idanu ta waro sosai sai kuma ta rufe fuska. “ALLAH dai yana gani ni babu ruwana. Kawai fa wucewa zanyi ni koma ganinka banyiba”.
     “Oh really?”.
Ya faɗa yana mikewa dauke da ita. Roƙonshi ta farayi tana wantsala kafafu akan itafa badashi takeba ALLAH yunwa takeji. Dan ALLAH yayi haƙuri bazata sakeba. Ko kulata baiyiba ya maida ƙofar ɗakinsa ya datse da key duk da yasan babu mai zuwa sashen. Cakulkulo ya fara mata daga kuka ta koma dariya da bashi haƙuri, bai ƙyaleta ba sai da suka dire cikin gadonsa. Salon daya fara bi da itane ya sata shagala da farko, sai da labari yay nisa a nanfa ido ya raina fata. Ta shiga magiya da roƙo akan abinda shi kuma anzo gaɓar da bazai iya ɗaga kafarba. Aiko taji ajikinta, dan har dana sanin shiga huruminsa tayi. Kuka kam ba'a magana.
           Sun fito wanka yake dubanta da murmushi yanda ta lafke a gado tana sakin numfashi da ƙyar kamar wadda ke a cikin ciwo. “K kuwa yarinyanan an miki wankan jego kina jinjira? Shikenan da'an ɗan taɓaki sai ki sharɓema mutane a haka za'a haifa ƴan huɗun?”.
       Shiru tai masa kamar tai kuka. Haka kawai yaji dariya ta taho masa. Bai iya dannetaba ya ƙyalƙyale kuwa. Haushine ya kama Raudha, a ganinta tsantsar muguntace ya gama wajiga rayuwarta ya dawo mata dariya. Sai kawai ta sakar masa kukan karya.
     “Okay kukama kike? To bari kawai na sakaki mai dalili mana da kiyi na banza gara kiyi na lada.....”
     Kafin ya rufe baki har takai ƙofa. Baki ya buɗe zaiyi magana gabansa yay wata irin masifaffiyar faɗuwa tare da kansa daya sara masa. Da sauri ya dafe kan yana ambaton sunan ALLAH. Raudha data zata wayau yake son mata tai tsaye kawai tana kallonsa da murmushi. “Ya Ramadhan na riga nasan wayonka ai. Shine harda pretending?”.
      Jin shiru bai amsa mataba ga kujera ya dafe har lokacin hanunsa dafe a kansa kamar maijin hajijiya yasata daina dariyar ta tsura masa idanu. Da sauri ta ƙarasa garesa ganin ya tafi kamar zai faɗi. Tarosa tai, sai dai yanayin jiki ba ɗayaba yafi karfinta musamman da jikin nasa ya saki sai suka zube ƙasa ya faɗa kanta. Ƴar ƙara ta saki da ambaton sunan ALLAH saboda wani raɗaɗi daya ratsa mata hanunta da suka faɗi a kansa. Tai ƙoƙarin dannewa amma ta kasa dan azaba. Kuka ta saki tana son turesa sai dai ina. A take jikinta ya fara rawa, ta turashi iya karfinta yay ƙasa da ƙyar, sai dai kafin ya dire a bazata taji ya ɗauke fuskarta da mari.
      “K! Baki da hankaline ni zaki ture?”.
    Ya faɗa a matuƙar kausashe da muryar da ko sanda basa shiri bata taɓa ji daga garesa ba. Lallai ta maru, dan yay bala'in shigarta, zata iya rantsewa kuma shine na farko a duniya daya taɓa marinta, tsabar azaba har kifewa tai akan table sai ga goshinta ya fashe. Idanu ya waro a ɗan tsorace yay kanta yana ambaton “Ya salam Ameenat....”
       Sai dai yana kai hannunsa jikinta ya sake tureta da ƙarfi ya sake dafe kansa dake juya masa. Duk yanda yaso yin addu'a bakinsa yay masa nauyi ya kasa furtawa. Duk da azabar dake ratsa Raudha a goshi da hannu haka ta sake nufarsa tana kiran sunansa a tsorace. Sai dai tana matsawa garesa ya sake hankaɗeta a matuƙar tsawace yace, “Fitarmin anan!!”.
       “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Ya Ramadh.....”
      “Nace ki fitar min anan!!”.
Ya faɗa a wani irin yanayi na fita hayyaci da tsananin ɓacin rai. Sosai jikin Raudha ke rawa kuwa yanzu. Ta fita a ɗakin da sauri kuka na kufce mata. Ga jini harya wanke mata fuska duk da taresa da tai da hanunta mai lafiya. Hanunta daya bugu kuwa wata azaba yake mata harya fara yawa da kumburi. Bata samu kowa a falon ba, sai dai karar buɗe ɗakinta da bugo ƙofar ta rufe ya fargar da Bilkisu dake gaban mirror tana kallon film a lap-top. Da sauri ta fito sai idonta yaci karo da ɗigon jini, a razane tabi jinin da kallo har ƙofar ɗakin Raudha, ai bama tasan kalar tsallen datai kawai ta ganta jikin ƙofar ba.............✍

😥🙏🏻aimun afuwa. Jin daɗi baya dorewa sai da ƙaddara. A lokuta da dama jarabawa itace ke ƙara. kai mutum ga ajin nasara. Ba'a samun wannan nasarar kuma sai da haƙuri da juriya.🚶🏻   


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*



Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

--------

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.


*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.

_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*

Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:

Amount Paid: - Nawa aka tura?

Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa

Transferred time: - lokacin da aka turo

Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi

Deposit date: - ranar da aka turo

Sai ayi SUBMIT.

*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:

MTN,
9Mobile
Glo
Airtel

Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.

*WANNAN SHINE BAYANAN*



*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/7, 1:31 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_Episode 57_*


..........“Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un aunty Raudha jini kuma?”. Bilkisu data shigo ɗakin a birkice ta faɗa tana ƙarawo gareta. Kamata tai suka nufi toilet, ta haɗa ruwa mai ɗumi ta taimaka mata ta wanke fuskar da hanunta, jinin dai bai tsaya ba. Sai dai sun tare da tissue. A bakin gado ta zaunar da ita, ta ɗakko first aid box ta shiga ƙoƙarin tsaida jinin, da ƙyar aka rufe wajen da audiga da bange. Ita dai Raudha babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya.
      “Aunty Raudha wai garin yaya? Ina Yaya kuma?”.
   Komai Raudha kasa cemata tai, sai hawaye take sharewa kawai. Hankalin bilkisu ya ƙara tashi, sai dai ta barta bata sake maganaba. Tana niyar mikewa ta maida first aid box ɗin ma'ajiyarsa ta lura da kumbirin hanun Raudha kuma. Gaba ɗaya saita sake ruɗewa ta kamo hanun tana kallo. “Ya ALLAHU, nan ma ai ciwon kikaji Aunty! Kinga bara na kira Yaya da mama ladi dan ta iya gyaran ƙashi”.
       Ita dai Raudha komai batace ba, babu jimawa suka dawo da mama ladi, bilkisu ta sake fita. Duk da ta fahimci akwai matsala ƙofar Ramadhan ta dingama knocking a ɗarare. Shiru babu ko motsi, sai ta ɗan tura ƙofar ta leƙa. Gabanta ne yay masifar faɗuwa hango Yayan nasu zaune akan tum-tum ya dafe kansa. Babu shiri ta shigo ɗakin da sassarfa. Muryarta har rawa yake ta durƙusa gabansa “Yayanmu dan ALLAH mike faruwa ne? Aunty Raudha taji ciwo sosai wlhy har a hanunta mi'akai mata”.
        Da ƙyar ya samu damar fisgo kalmar innalillahi... A cikin zuciya. Ya ɗago jajayen idanunsa ya zuba kan Bilkisu datai matuƙar razana. Dan rabon da su gansa a irin wannan yanayin tun rasuwar su Haseenah. Baya taɗan ja jikinta na rawa. Shima sai ya cije lips sinsa da ɗago hanunsa ya kalla. Sai kuma ya dafe kansa dake matuƙar juya masa. Kusan minti ɗaya ya sake ɗagowa ya dubi Bilkisu da gaba ɗaya ta gama tsorata. Cikin yanayin damuwa yace, “Ina Ameenatun?”.
       “Tana ɗakinta Yaya, nabar Mama ladi zatai mata gyara a hanunta dan harya kumbura, ga goshinta ya fashe da ƙyar na iya tsaida jini....”
      Ai bama ta ƙarasa ba ya miƙe hankali tashe. Sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarsa ba. Fita yay Bilkisu tabi bayansa. Kai tsaye ɗakin Raudha ya nufa, sai dai yana ɗaura hanunsa bisa handle ɗin ƙofar ya dafe kansa da yay masifar sara masa. Da sauri ya shiga girgiza kansa yana ja da baya. Barin wajen yay ya sake komawa hanyar ɗakinsa. Bilkisu ta bisa da sauri tana kiransa. Wata razananniyar tsawa data sakata jan birki ya daka mata, yay shigewarsa ya bugo ƙofar da ƙarfi har Bilkisu na zabura.
          Kuka Bilkisu ta fashe da shi. dan kuwa ta fahimci lallai akwai matsala, sai da tayi mai isarta ta koma ɗakin Raudha. Ta jiƙe sharkaf da zufa kamar ba ac a ɗin saboda gyaran da mama ladi tai mata. Mama ladi dake naɗe mata hanun da bandage ta dubi Bilkisu. “Taji ciwo sosai, dan gocewar ƙashi ta samu. Garin yay hakan?”.
        Kafin Bilkisu ta bada amsa cikin share hawaye Raudha tace, “A toilet ne na zame”.
      Sannu Mama ladi ta shiga jera mata. Bilkisu dai wani irin tausayin Raudha ɗinne ya lulluɓeta. Dan ta tabbatar daga yayansu aka samu matsalar musamman da taga shatin yatsu a fuskar Raudha alamar marinta akai. Magani ta sha ta kwanta bayan tayi sallar magrib da isha'i, babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bakajin komai sai ajiyar zuciyarta.
        Tagumi Bilkisu tai zuciyarta nata kaikawo. tama rasa ina zata kama akan wannan al'amari. Kusan tara na dare sai ga kiran Basma ya shigo mata. Da farko kamar bazata ɗaga ba sai kuma ta daure ta ɗaga wayar na gab da tsinkewa. Wani irin dummm kunen Bilkisu yayi jin abinda Basma ta faɗa. Muryarta har rawa take wajen maimaita “Basma shi Yaya Ramadhan ɗin da kansa yace zai auri Aynah?”.
      Daga can Basma tace, “Wlhy kuwa Aunty B. A gabana Maah tai waya da shi yanzun nan sai farin ciki take tana saka masa albarka. Ni nama rasa wanda zan tunkara da wannan abun al'ajab shine fa na kiraki naji ko wani abu ya faru anan”.
     “Nan dai babu abinda ya faru, sai dai yana ɗakinsa. Amma dai wannan lamari da ɗaure kai. Basma anya Adda Asmah bata fara cin galaba akan Maah ba?”.
        “Aunty Kamar ya?”.
Saurin dafe kai Bilkisu tai jin zata saki layi. Ta manta ita kaɗai taji abinda Adda Asmah ta taɓa faɗa akan Mahaifiyarsu kwanakin baya sanda ake tsaka da rikicin auren Yayansu da Raudha. Kuma bata taɓa nuna ta saniba ko taɓa faɗama wani. Sai dai tana kallonta da abun kuma tun daga ranar taji bata sonta duk da yayar Maah ce. Hasalima tafi shiri da ita fiye da kowa a ƴaƴan gidansu, dan ita takan iya zuwa ta kwana gidansu Aynah ɗin ma ba kamar su Basma ba.
          

★★★_____★_____★★★

         Tabbas abubuwa sun kwaɓe a tsakanin Raudha da shugaban ƙasa Ramadhan. Ita gaba ɗaya tsoron haduwarsu ma takeyi, yayinda shi yasha gwada zuwa gareta da zaran ya iso kofar ɗakin sai yaji wani irin mugun tsanarta mai ban mamaki, dole yake juyawa ya fasa. Babu abinda Raudha keyi sai kuka, sai dai duk da haka tana ƙoƙarin zuwa makaranta. Bilkisu tayi-tayi ta faɗa mata ainahin abinda ya haɗasu taki. Takuma roƙota ALLAH akan karta sanarma su Anne. Rasa mi Bilkisu zatai tayi, sai kawai ta zubama sarautar ALLAH ido tana tayasu da addu'a.
       A cikin kwanakin da basu gaza gomaba da faruwar komai Raudha duk ta fige ta rame. Sai uban haske datai ta ƙara tsayi. Kullum babu fashi zataje ta gyara masa ɗakinsa, duk bayan kwana biyu ta wanke masa under wears ɗinsa dan tafi gane wankesu da hannu ba Worthing machine ba. Idan ta gama sai tai drying nasu a machine ɗin. Komai dare kuma sai tayi zaman gogesu bayan ta musu turare na turaren wutarta na kaya mai daɗin ƙamshi sannan ta maida ɗakinsa ta jere masa.
        Sam ya daina shigowa gidan da wuri, weekend kuwa har taci ta ƙare bai yarda sun gamu ba. Bata da aiki sai kuka da gayama UBANGIJI. Dan ta rasa wanema irin tunani zatai akan sauyawar tasa. Koda zuciyarta ta nuna mata dama sabbin halayyar daya fara mata yayine dan ya samu jikinta sai tai saurin ture tunani dayin a'uziyya. A haka suka sake cinye sati uku babu wani canji.

*_RAMADHAN_*

       A sashen Ramadhan shi kaɗai yasan tashin hankalin da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login