Showing 105001 words to 108000 words out of 207756 words
ne, k wai kuwama kinsan mike miki ciwo? Kina matsayin matar shugaban ƙasa amma ko waya baki da shi?. Ina karatun da su Feena suka koya miki badai a banza ya wuce ba?”
Raudha taja ajiyar zuciya kawai batare da tace komai ba, hakan ya sake tunzura zuciyar aunty Hannah, cikin takaici tace, “To wlhy inma zaki dawo cikin hankalinki kiyi maza ki dawo. Bazai yuwu ki zauna kina mana ƙauyanci ba da shirme, kinsan nawa first lady ta narkar na kuɗi akan a koya miki abubuwan can kuwa? Amma Raudha gaba ɗaya kina nuna ma komai bai shiga kanki ba......”
“Mom nifa bawai bai shiga bane ba. Kawai dai duka yaushe na shigo gidan. Kofa wata biyu ba'a cika ba. Yanzu dan ALLAH idan yaga ina rawar kai da wuri ai saima ya gane komai. Shifa ba irin yanda kuke tunani bane ba, mutum ne mai lura da saurin fahimta. A yanzu haka bawai ya gama yarda banda alaƙa da wanda yaso kashe Bappi a filin idi bane ba......”
“Kusun uban can, kujimin ɗan iskan yaro. Duk yankan da kikasha bai gani ba zaima dinga ɗaukar haka? To aiko zai gane kurensa wlhy. Yanzu abinda zan faɗa miki shine komi zai baki na magani karki sha, ko shi ko danginsa. Dan na kula waccan shegiyar uwar tasa zamu dama da itane, kaɗan daga aikinta tabi duk hanyoyin da zatabi danta daƙileki ga ɗaukar ciki. Ni kuma babban burina yanzu na ganki da ciki, dan koba komai kema ya kasance kinada wani kaso a dukiyar Taura. Sannan shima shugaban ƙasar komansa yazam namu ne. Abu na biyu ki fito ki nuna masa kina son fita fa kema a dama dake a harkar mulki, dan haka a baki office naki. Kuma wlhy ki nema waya bana son wawanci, ko kina nufin duk sanda nake buƙatar magana dake sai na dinga tako ƙafa nazo nan a matsayina na matar vice president?”.
Kai kawai Raudha ta jinjina mata, a takaice tace, “To duk zanyi”.
“Karma kiyi mana”.
Cewar aunty Hannah a ƙufule.
Koda suka fito tsaf aunty Hannah ta canja yanayinta kamar komai bai faru ba. Itama Raudha dai bata bada wata ƙofa na fahimtar komai ba. A zaman nasu ne daga cikin matan ta ke kawo shawarar ya kamata first lady ta buɗe musu office. Ma'ana dai irin ƙorafin aunty Hannah. Atake kuwa duk sukai na'am. Raudha dake ɗan murmushi tace insha ALLAH zatayi shawara. daga haka ta tsuke bakinta. dama can ba komai take saka musu baki ba.
Wasu a cikinsu suna ɗauka dan tana ganin kanta sa'ar ƴaƴansu ne kawai shiyyasa take girmamasu da ƙin cewa komai. sai dai kuma hasashensune wannan, Raudha tana karantar kowa da lafazinsa ne kawai.
Bayan wucewarsu baifi da mintuna goma sha bakwai ba sai ga su Maneerah. Ko kaɗan Raudha batai farin ciki da zuwansu gidan ba. Musamman ganin babu Bilkisu da Basma a wannan karon. Amma sai ta danne ta musu tarba ta mutunci duk da kallon banza da suke mata suna wani dariyar iskanci.
Cikin dauriya ta bama mama tambaya umarnin a gyara musu ɗakin da zasu zauna. Amma sai Aina ta katseta. “Talaka bai iya cin arziƙi ba idan ya samu waje”.
Lubnah ta doka tsaki tana ma Raudha wani shegen kallo. “Shi wanda ya ajiyeki a gidan bai miki bayanin inane masaukinmu ba ne?”. Kafin Raudha tace wani abu Manirah ta ajiye wayar hanunta tsakkiyar centre table. Saukar maganar gimbiya Su'adah kawai taji a cikin kunenta a bazata....
“Bata wayar.”
“A wlhy Maa wannan trash ɗin bazata taɓamin waya ba. Gashi nan nasa hansfree yi mata magana”..
Munirah ta faɗa tana harar Raudha da tura wayar gabanta. Cikin kaushin murya da ga can gimbiya Su'adah ta cigaba da magana a kausashe, dan kuwa warning mai ƙyau taima Raudha cikin kausasa harshenta, ta kuma tabbatar mata a wannan karon idan tai wani abinda Ramadhan harya dawo da su Ainah sashen baƙi wlhy itama sai ta ɗanɗana kuɗarta sannan tabar gidan. Daga karshe ta bita gorin kasancewarta ƴar talaka jinin karuwai kuma mayya.
Waɗan nan lafuzza na Gimbiya Su'adah sun yima Raudha zafi da ɗaci mai tsanani, harta kasa iya riƙe hawayen da suka ciko mata idanu sai da suka zubo. Batama jira Munirah da suke dariya ta ɗauka wayarta ba ta bar wajen zuwa upstairs da ɗan gudu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata.. Babu zato taci karo da mutum har goshinta na buƙagar ƙirjinsa. Da sauri taja baya tana ƙoƙarin maida kukan nata ta haɗiye, sai kuma tasa hannu biyu ta goge hawayen da suke rige-rigen sakko mata.
Shugaban ƙasa Ramadhan dake tsaye hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da ido batare da yace komai ba. Cikin muryar wanda ke son yin kuka Raudha ta ce, “Ina yini ya jiki?”.
Bashi da niyyar amsawa, sai cigaba da kallonta da yakeyi kansa tsaye, kusan mintuna biyu Raudha ta fahimci ba amsa mata zai ba, ga shi kukan da taketa dannewa son kwace mata yake, raɓashi tai ta wuce hawayen na ƙwace mata. Komai zata iya ɗauka daga Ramadhan da danginsa. Sai dai kalmar karuwanci da ake jifan iyayenta da shi yana taɓa mata zuciya. Tasan gaskiya suke faɗa, amma kalmar na mata zafi, zafi irin wanda ke ƙona zuciya.
Tsaiwa ya cigaba da yi a wajen kunnuwansa na sauraren darerakun su Aina'u da ke downstairs da maganganun banza da sukeyi akan Raudha ɗin. Iska ya ɗan furzar da tura lip ɗinsa cikin baki kaɗan yana ciccizawa. Sai da wayar jikinsa da ke ring na gab da tsinkewa sannan ya cirota a ljihu, ya haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa kafin yay dialing no ɗin dan kiran ya riga ya katse.
“Barka da yamma”.
Ya faɗa a tausashe dan son danne ɓacin ransa. Da ga can gimbiya Su'adah ta amsa masa a gadarence cikin kaushin murya da ragowar fushin Raudha dake a muryarta. Shima dai ɗin gargaɗin tai masa akan su Lubnah. Ta kuma jaddada masa idan taji wani abu yaje kunnen su Anne ransa sai ya ɓaci matuƙa. Da ga haka ta yanke wayar batare da jiran cewarsa ba.
Karon farko ya saki guntun murmushi yana kai hannu bisa sumarsa ya shafota da tura wayar a aljihu tare da hanunsa duka. Kamar yanda bai furta mata komai ba, a yanzun ma data yanke komai bai ceba duk da akwai abin cewar a bakinsa. Tsaiwar wasu ƴan mintuna ya karayi a wajen tamkar mai nazari, kafin ya nufi hanyar ɗakin Raudha cikin tafiyarsa da babu garaje, wadda da yawan mutane ke kallon girman kai ne ke sashi salon takun kawai da nuna shiɗin wani ne. Sai dai sam ba haka baneba, halitarsace hakan kawai...
Koda ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga tsaye yay kawai yana kallonta batare da ya shigo gaba ɗaya ba. Tana kwance a saman gado rubda ciki tana kuka, ya shaida hakane saboda yanda shashshekar kukanta ke tashi a ɗakin. Sam bai cika son ganin mutum a damuwaba a tayuwarsa, saboda ya ɗanɗani ɗacin damuwa baiji da daɗi ba, kai zai iya cewa har yanzu tana ƙunshe da ciwon damuwa, baya tunanin kuma zai samu waraka har sai randa ya koma ga ALLAH.
Ƙarasa shigowa yay ɗakin yana ɗan bin ko'ina da kallo. A ɓangaren tsafta ya jima da bama Raudha lambar yabo, ba komai yasa haka ba sai kasancewarsa mutum mai tsananin son tsafta da ƙamshi. Zamansa a bakin gadon ya fargar da Raudha shigowarsa, tai saurin share hawayenta da miƙewa zaune har kafarta na ɗan shurin jikinsa. Bai juyo ya kalleta ba, bai kuma ce mata komai ba duk da yana kallonta ta wutsiyar ido.
Hawayen da ke cigaba da sakko mata take sharewa da ƙoƙarin ganin ta tsayar da kukan. Tsahon wasu sakanni kafin ta samu nasarar danne hawayen da ƙyar.
“Kana buƙatar wani abu ne?”.
Ta faɗa cikin girmamawa da tausasa harshe a garesa tamkar yanda ta saba. Sai lokacin ya ɗan juyo yana dubanta, ya kafeta da shanyayun idanunsa da ke nuna alamar bai jima da tashi a barci ba, ko kuma dai akwai abinda yake saɓanin barcin a cikinsu.
“Karfa ki zata lallashinki nazoyi yarinya”.
A yanda yay maganar batasan murmushi ma ya suɓuce mata ba. Ta kauda kai gefe tana sake share hawayen nata. Kishingiɗawa yay yanda zai iya kallon fuskar tata sosai. Shima fuskar tasa da ɗan murmushi dake iya laɓɓa. Cikin kafeta da idanunsa ya ɗan leƙa fuskar tata, “K kuka baya miki wahala ne? Ko dama haka ustazan suke saboda tsabar ƙarfin imaninsu?”.
(Kai jama'a wai miya shiga kan mutumin nan ne kwana biyun nan?) ta ambata a zuciyarta tana kai hannu saman fuskarta ta rufe murmushinta na ƙara faɗaɗa. Hannunsa yasa ya buge hannayen nata data rufe fuska.
“Gulmammiya nasan kinanan kinajin daɗi kamar ki taka rawa shugaban ƙasar NAYA yazo lallashinki kina kuka”.
“Ni Aminatu yaushe nace?”.
Ta faɗa cikin waro masa manyan idanunta gaba ɗaya da ɓata fuska cike da shagwaɓa...........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/24, 7:59 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62b5bb45fa0b02c20d2788dd
*_Episode 36_*
...........“Ki rantse bakiji daɗi kamar zai kasheki ba? Nasan dai ustazai basa ƙarya Ustaza!”.
Dariyar da tazo mata a bazata ta ƙyalƙyale da ita da sake rufe fuska saboda a yanda yay maganar.
“ALLAH nidai ba ruwana”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa. Sosai yaji sanyi a ransa ganin damuwarta ta kwaranye ta sanadinsa. Bazai iya cewa komai a kanta ba, sai dai bazai so a wulaƙantata ba domin ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wannan karatune daya samu daga kakaninsa tun ƙuruciya. Sannan bayaso Raudha tai tunanin akwai wani banbanci a tsakaninsu dan kawai tana ƴar talakawa....
Duk tunanin da yake idannsa na'a kanta ne. Bazai ɓoyeba cute face nata na matuƙar birgesa tare da sumar kanta data kwanta har saman goshinta sosai. Sannan a ɗan zamansu ya fahimci tanada haƙuri da juriya. Shiko yana son mutum mai waɗan nan halayyar musamman mara riƙo. Yanda ta saki jiki da shi lokaci guda duk da tasan ba haka yake mataba a baya ya masa daɗi matuƙa da sashi nutsuwa gareta.
“An taɓa faɗa miki k ƙyaƙyƙyawa ce?”.
Ya faɗa cinkin suɓutar harshe da ƙan-ƙan da murya yna sake shanye idanunsa suka koma ƙanana.
Wani irin dummm taji a kunenta saboda furucin nasa. Bazata iya jurewa ba, dan haka tai azamar maida kanta ƙasa tana wasa da zanen less ɗin jikinta. A ranta mamakin yanda baijin ko kunyar ƙureta da ido a lokuta makamantan haka takeyi, ta matuƙar tsanar kallo a rayuwarta, sai dai ta rasa dalilin da yasa nashi baya mata zafi ko gundurarta sai dai sakata a wani yanayi da yake yi.......
“Uhhmm?!”.
Ya buƙaci jin ta bakita cikin wani yanayi.
Fahimtar amsa yake buƙata daga gareta ya sata saurin jinjina masa kanta tana murmushi.
Basar da zancen yay ya ɗakko wani yana furzar da numfashi.
_“Kuka yana sake raunana raunin mai raunine a duk sanda yake yinsa. A tunaninki kukanne zai iya canja ƙaddararki? Ki zama mai juriya sai ki kasance cikin masu nasara. Ki ɗauki ƙaddara matsayin jarabawa sai zuciyarki ta dawwama a farin ciki. Ki amsa a duk lokacin da aka jehoki da sharri ko alkairi, sai dai zaɓin inda zaki ajiyeshi yana daga karfin imaninki ne. Bana bama mai son ganin kukana dama a duk lokacin da yaso hakan, domin in tabbatar masa da damarsa itace nasarata a yau da gobe na”._
Ya ƙare maganar da miƙewa zaune sosai ya ɗan leƙo fuskarta da hawaye ke sauka saboda nasiharsa ta shigeta. Tissue ɗin daya ɗiba a side drawer nata ya ajiye mata saman cinya yana miƙa mata yatsansa ƙarami.
“Zamu iya zama abokai”.
Yanda yay maganar da abinda ya faɗa ya sata kasa jurewa saida ta ɗago ta kallesa. Idanunsa manya da suka canja launi ya kaɗa mata.
“Ustazah bana son gulma fa, da kika samu ma zaki zama ƙawar shugaban ƙasar NAYA?”. Yay maganar da ɗage gira sama yana ɗan ɓata fuska.
Murmushi tayi da miƙa masa nata yatsan suka ƙulla.
“A rage gulma ƙawata Ustazah”. Yay maganar da juyawa zai fita....
_“Nagode, ALLAH ya dawwamar da farin ciki da nasara a rayuwarka data ahalainka baki ɗaya, ya cika maka burinka na alkairi”._
Cak ya tsaya saboda tasirin da addu'arta yay a dukanin zagayen ɓargonsa zuwa jini. Ya saki wani lalataccen murmushi daya kawata ƙyaƙyƙyawar fuskarsa, sai kuma ya juyo a hankali gaba ɗayansa yana fuskantarta tamkar mai tsoron hakan. Har yanzu tana a yanda ya barta, sai dai hawayene sabbi ke faman mata gudu a kumatu. A hankali ya tako ya dawo zuwa gareta. Saukar numfashinsa a kanta ya sata ɗagowa da sauri, ƙoƙarin jan jikinta tai baya saboda kusancin da suka samu yayi yawa. Amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo haɓarta ya sake kai fuskarsa gab da tata. A hankali ya ɗan hura mata iska a saman idanunta data rumtse, sai kuma yay sama kaɗan ya ɗora tausasan laɓɓansa saman goshinta. Harga ALLAH jitai kamar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya, dan kuwa a bazata taji saukar laɓansa saman goshin nata, cikin yanayin kasala ya sake sakar mata kiss a goshi idanusa a lumshe kamar yanda ta ƙara matse nata tanajin kamar ta saki fitsari kawai ta huta.
“I like you my Friend”.
Ya faɗa a kunnenta cikin wata irin muryar raɗa batare da yasan sanda kalmar ta suɓuto daga ƙirjinsa zuwa harshen ba. Kamar yanda kalmar ta suɓuto masa batare da ya shirya ba haka tari ya subucema Raudha har yawu na sarƙe ta. Sosai jikinta ke tsuma yanzu kam har mai kallonta zai iya ganin hakan. Ramadhan da tuni ya kai ga ƙofa batare da ya juyo ba saboda abinda zuciyarsa ke ayyana masa ya furta, “Kisha ruwa”. Cikin tattausar muryarsa sannan ya fice ko waiwayenta baiyi ba.
Raudha da tari ke neman halaka mata numfashi, dan har ya fara fisga kamar Asthma ɗinta zai tashi ta silmiyo a gadon zuwa fridge, bama tasan a yanda ta ɗakko ruwan ba ta ɓalle murfin kawai ta kafa a baki. Yanda take shansa yana wuce mata a maƙoshi da gudun tsiya haka hawaye ke rige-rigen sakkowa da ga idanunta zuwa fuska. Tas ta shanye ruwan, ta zube ƙasa ita da robar tana maida numfashi.
Sai da taja kusan mintuna biyar a wajen tana kokawa da zuciya da tunaninta kafin hankalinta ya ɗan fara dawowa jikinta. “I like you”. Ta maimaita kalmar daya faɗa a saman laɓɓanta batare da zuciyarta ta amince da sakata a irin gurbin da takejin wasu na ambata ba ga abokan rayuwarsu.
“Tabbas ba haka bane, tashi nada banbanci da tasu”.
Ta sake faɗa a zahiri cikin yarda da kai, dan sam bata yarda da abinda ɗayan sashen zuciyarta ke tabbatar mata ba. Saboda son kauda hakan ma sai ta miƙe ta faɗa toilet kawai maybe idan ta sakarma kanta ruwa zatafi dawowa a hayyacinta fiye da haka.
A wani ɓangaren kuwa mamakinsa take matuƙa. Ina ɗaɗɗaure fuskar tashi ta tafi ne da shan ƙamshi?. Kalaman Anne suka shiga dawo mata a safiyar da za'a kawota nan government house. _Ameenatu nasan zaki iya fuskantar ƙalubale kala-kala a cikin auren nan har ga Ramadhan dake amsa sunan miji gareki. Sai dai ina fatan ki zama mai haƙuri da juriya wataran zaki cimma nasarori. Bar ganinsa haka yana wannan ɗaure-ɗauren fuskar da tsumewa yanada sauƙin kai sosai musamman ga abinda yake so. Ɗan karan surutune da shi sannan yana dariya fiye da zatonki. Sai dai bazaki san duk waɗan nan abubuwanba sai kin zama jaruma sannan mace. Kar kiji nace mace ki zurfafa tunani. Mata da yawa sukan koma muna mata a wasu lokutan a gidan aure koma a waje. Amma