Showing 138001 words to 141000 words out of 207756 words
ƙasar.
“Maah! Lafiya kuwa naga kamar ranki a ɓace?”.
Duk da tasan halin ɗiyar tata na rashin ɗaukar abu da muhimmanci hakan bai hanata fara zayyane mata cikinta ba rai ɓace.
“Miyema bai faruba Mardiyya. Yanzu a duniyar nan babu abinda ke cimun rai da ƙonan zuciya sama da auren ɗan uwanku. Na tsani yarinyarnan da duk wani mai alaƙa da ita a duniya. Ji nake zan iya kasheta da hannnuna wlhy.....”
“Wa'iyazubillah Maah miya kawo wannan maganar haka?”. Mardiyya tai saurin katseta.
“Humm Mardiyya kenan, yanzu ke tunda kike a duniya kin taɓa jin matar shugaban ƙasa mai shekara sha takwas? Jahila da ko karatun sakandire banajin ta kammala? Daɗin daɗawa ƴar karuwai marasa tarbiyya da kowa yasan aikinsu a bayyane yake.” hawaye suka silalo mata, ta kai hannu ta share da cigaba da faɗin, “Mardiyya na tabbatar a ƙuntace Ramadhan yake, biyayyar da yakema kakanninku ce kawai ta sakashi haƙura ya amshi raunanniyar yarinyar nan, wai dan takaici sai yanzu take shiga jami'a. Matar shugaban ƙasa fa daya kamata ta zama vary educational, wayayya ta nunawa a duniya, wadda duk inda tasa ƙafa zata fiddashi a kunya muma ta fiddamu. ALLAH dai ya tsinema wannan aure na Ramadhan albar.......”
“Haba dan girman ALLAH Maah wane irin furicine haka babu daɗin ji. Idan kin tsinema auren Brother tamkar shi kika tsinemawa dan zata iya yuwuwa yanzu haka an samu rabo tsakaninsu. Maah ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ni wlhy banga wani aibu ga yarinyarnan ba. Inma iyayenta sunada wancan halin ai ba itace kedashi ba. ALLAH kuma yana fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Karatu ko karancin shekarunta normal ne ni a wajena. Miye amfanin ya auri wayayyar mai ilimin tazo ta zame masa damuwa shi da mulkin nasa damu kammu. Yanzu ko shi zai bama matarsa tarbiyyar data dace akan tsarin mulkinsa ta tashi akai kuma yay alfahari anan gaba Maah. Dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan ki musu addu'a sai kiga wataran komai ya zama yanda kike so. Kwana nawane zata kammala karatun ma, ina amfanin ya auri sa'arsa tazo ta rigashi tsufa........”
Hannu Gimbiya Su'adah ta ɗaga mata a fusace. Cikin zafin rai ta nuna mata ƙofar fita. “Tashi ki fitarmin kafin na saɓa miki Mardiyya. Nama manta tare nake da mara kishin kanta balle waninta. Shasha kawai da batasan abinda ke mata ciwo ba”.
Miƙewa Mardiyya tai ta ɗauka bag dinta da faɗin, “ALLAH ya huci zuciyarki Maah, amma nidai gaskiya na gaya miki, ita rayuwa bata da tabbas. Banga kuma aibun yarinyarnan ba, hasalima yanda take da ƙarancin shekaru idan kika jata a jiki zakisha mamakin ribar da zaki samu akan shi kansa Ramadhan ɗin da kike ganin kamar an nisantaki da shi. Ni na wuce dama zuwa nai na dubaku tunda ban samu shigowa gidan ba koda babbar salla”.
Ko kallonta Gimbiya Su'adah bata sakeyi ba. Itama saita fice a ranta tana nemawa mahaifiyar tasu shiriyar ALLAH da fatan ganewa. Dan tuni ta fahimci Adda Asmah na ɗaya daga cikin masu rikita lissafinta akoda yaushe. Su kansu wani lokacin haɗata ake dasu taita zuba musu tujara kamar ba ita ta haifesu ba.
Waɗan nan maganganu na Mardiyya sun sake harzuƙa gimbiya su'adah. Rai ɓace ta shirya bayan sallar zuhur ta nufi sashen Anne. Abinda takan haɗa kwanaki huɗu batai ba. Dan gaida surukai kullum baya cikin tsarinta duk da gida ɗaya suke rayuwa. Anne tayi mamakin zuwan nata amma sai ta danne ta tarbeta kamar yanda suka saba. Babu wani ɓoye-ɓoye gimbiya Su'adah ta sanarma Anne abinda ke a ranta.
Murmushi kawai Anne keyi jin bayanin surukar tata. Ita bazata hanata zartar da hukuncin aurawa Ramadhan wata matarba, sai dai bazata amince a cutar mata da jika ba dan ita kanta ta jima da fahimtar wacece Adda Asmah.
“Shike nan kije zan samu Dattijo da batun, zai kuma nema Ramadhan ɗin yaji tabakinsa. Idan ya amince da auren mu masu murna da farin cikine akan hakan. Fatanmu ALLAH ya basu zaman lafiya kawai.”
Duk da ranta ya ƙara ɓaci sai ta amsa da amin. Ta fice zuciyarta na ayyana mata maganin Ramadhan da zatayi. Dan bazata taɓa yarda ya nunama kakaninsa baya son auren ba. Tasan yana bijirewa shikenan bazasu bata goyon baya ba.
*__,,,,___________,,,,__*
Barci ya sake sha sosai har wajen sha ɗaya. Ring ɗin wayarsace ma ta tilasta masa buɗe idanu da ƙyar. Ido a rufe ya kai hannu a side drawer da nufin kashe wayar sautin ring ɗin ya hanashi hakan dan yasan Maah ce. Komai bai kawo ransa ba sai tunanin taji baida lafiya maybe. Ya buɗe ido da ƙyar yay picking yana kaiwa kunnensa.
“Barka da asiba Maah!”.
Gaban Gimbiya Su'adah ne ya faɗi, tai saurin cire wayar a kunenta tana kallo.....
“Maahhh!”.
Daya sake faɗa cike da kasala da barci ya sakata gaskata zarginta. Da sauri ta latse wayar ta kasheta gaba ɗaya kanta na juya mata. (Har ita Ramadhan zai amsawa waya yana tare da mace. Innalillahi..... Shikenan yaronta ya gama watsewa hanun jikar karuwai).....
A ɓangaren Ramadhan kuwa tunanin network ne ya sashi sake dialing number ɗin tata da ƙyar yana kaiwa kunne da lumshe idanu. Sai dai switch up ma ake sanar masa. Yanayin rashin ƙarfin jikin har yanzu ya sashi ajiye wayar kawai da tunanin zuwa anjima zai nemeta. Sai dai ya sake jan ƴan mintunan a kwance kafin ya tashi zuwa bayi, sosai yunwa yakeji na ci masa hanji, badan haka ba baya tunanin zai iya tashi yanzun.
Shigarsa wankan baifi da mintuna biyu ba Raudha ta shigo hanunta ɗauke littafin data rubuta lecture ɗin jiya tana ɗan bitar abubuwan da bata fahimta ba, dama tun ɗazun take zaryar dubashi da ga falo zuwa bedroom ɗin. Jin motsin ruwa a bayi ya sata yanke shawarar gyara ɗakin a gaggauce ta fice kafin ya fito. Littafin ta ajiye a stool ɗin mirror batare data rufe ba. Cikin rashin sa'a tana tsaka da gyara kayan saman mirror ɗinsa dake a wargaje ya fito. Sosai ta diririce, tai azamar juya masa baya zuciyarta na luguden daka....
Duk abinda tai akan idonsa ne, har yayi kamar zai basar yanda ya saba sai kuma ya canja shawara. Inda take ya cigaba da takawa yana goge sumarsa da ruwa yaɗan taɓa kaɗan zuwa gefen wuyansa da kunne. Cak ya tsaya sakamakon idanunsa da suka sauka akan littafin nata, ya ƙurama hand writing ɗin ido zuciyarsa na wani irin zillo, hatta da numfashinsa sizing yake wajen fita daga ƙirjinsa.....
Jin kamar tsayuwar mutum a kanta ya sata saurin juyowa saboda tsorata, dan bataji motsin ƙarasowarsa inda take ba. Yunƙurin barin ɗakin tai gaba ɗaya taji ya cafko hanunta tare da fisgota ta dawo baya, gaba ɗayanta ta faɗa masa har ɗayan hannunta na ƙoƙarin sauka akan ƙirjinsa dake nason ruwa. Ido ta rumtse da ƙarfi da son ɗage hannunta ta tokare tsakkiyarsu, sai hakan ya taimaka mata bata faɗa masa jiki gaba ɗaya ba. Sai dai kuma a bazata da tai niyyar jan jikinta baya cikin in..ina tana faɗin, “I'm sorry”.
Har yanzu idanunsa akan littafin suke, sorry data ambata ne ya dawo da zuciyarsa gareta, dan ya lula duniyar wani tunani daban, kamar yanda ya taɓa mata lokacin da ƴan gidansu sukazo dubasa ya ƙara matso da ita jikinsa dan bai saki hanunba dama. Mannata yay da jikin nasa duk da taƙi janye hanun nata. Kamar zata fasa kuka ta sake buɗe baki zatai magana dan ita hankalinta bai kai akan abinda yakema kallon ƙurulla ba saboda a rikice take...
‘Shiyyy!!’ Ya faɗa yana maido idanunsa kanta da manna bayanta da jikin mirror. Kumburarrun idanunsa dake baibaye da mura ya sauke akan face ɗinta, ganin lips nata na rawa alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. Sake rintse idanu tai da ƙarfi. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa idanunsa na cigaba da bin fuskarta da kallo, haka kawai yake shiga nishaɗi idan ya ganta a yanayin tsoron nan.
“Hy! Buɗe idonki”.
Yay maganar a dake kamar ba shi ya gama murmushi ba.
“Dan ALLAH kayi haƙuri..” Raudha ta faɗa cikin tsananin taraddadi kamar zatai kuka.
Sake matsar da fuskarsa yay gab da tata yana busa mata numfashinsa. Cikin wata iriyar muryar da badan a gabanta yake ba zata rantse bashi bane ya cigaba da magana.
“Kinsan ALLAH idan baki buɗe kin kalleni ba zan baki mamaki yau, ba ruwana da Ustazancin ki kaca-kaca zan miki”...........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[7/1, 8:00 PM] NANA: *_Typing📲_*
*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62be031cf0fb62def317f52f
*_Episode 46_*
............So take tabi umarninsa ta buɗe amma ta tabbatar bazata iya kallonsa ba riga ba. Sai tayi kamar zata buɗe sai ta maida ta rumtse da ƙarfin tsiya. Tayi haka kusan 3times amma ta kasa. Cike da mugunta ya saki murmushi yana saka hanunsa guda ya janye nata data tokaresa da shi.
Wani irin ƙuuuu! Cikin Raudha ya bada sautin da har Ramadhan sai da yaji lokacin da taji saukar lips nashi akan nata daketa ƙyallin lipsgloss mai ƙamshin strowbarry. Shi kam da yayi da niyyar tsokana duk yanda yaso janye nasa lips ɗin sai yaji bazai iya ba, cikin rashin ƙarfin jikin da ke tare da shi ya sake manneta da mirror ɗin tare da rumtse ɗayan hanunta dake cikin nasa ya manne jikinsu waje guda yanda har numfashinsu ke fita da ƙyar....
Ya riga ya mata matsewar da rawar jikin nata ma baya tasiri, sai zuciyarta dake mugun gudu a ƙirjinta har yana iya jiyowa. Randa su Anne sukazo yayi kissing nata sai dai ba irin na yau ba. Na yau babu sassauci, kai tsayene, cike da salon daya sata shagala tuni tsoronta ya gudu saƙonsa ya fara shigarta ɓargo da jini. Itama tanada lafiya, duk da abinda takeji sabo ne gangar jikinta bataƙi amsaba, dan ta kai shekarun da zata iya buƙatarsa. Sai dai rashin sabo ya sake tabbatar da ruɗaninta, dan lokacin daya janye bakinsa kasa tsaiwa tai a kan ƙafafunta. Babu shiri ta sake ƙanƙamesa. Bazata iya ɗagowa ta kallesa ba, sannan ƙafafunta ma bazasu iya tsayawa akaran kansu ba, dan jikinta babu abinda yakeyi sai mazari.
Duka hannayensa biyu ya dafe kan mirror ɗin da suke jingine, kansa na bisa kafaɗarta, idanunsa duka a rufe suke saboda abinda ke faruwa a cikin nasa jikin. Lallai yasan ya takaloma kansa, ya kira ruwa yau. Yana zaman-zamansa da lallaɓa yanayinsa gashi nan ya takaloma kansa ruwa wajen neman tsokanarta ya tsokanoma kansa abinda ke kwance shekara da shekaru.
Sunayen ALLAH ya shiga ambata a zuciyarsa da son janye jikinsa da sauri, sai dai Raudha data dabaibayesa sam ta hana yuwuwar hakan garesa. Sai ma ƙara ƙanƙamesa tai dan bata fatan ya ganta a yanayin da take. Sake gwada janyewa yay itama ta sake ƙanƙamesa. Dole ta sashi buɗe ido yana kallon kansa da bayanta ta cikin mirror. Murmushi ne ya suɓuce masa, sake duban idanunsa da suka kaɗa sukai jajur yayi alamar fitinace kwance a cikinsu. Hannunsa ɗaya ya ɗaga da jikin miron ya kaisa kanta ya ture hular data saka, a take gashinta dake ɗaure ya bayyana. Yatsunsa ya tura ciki baki ɗaya ribbon ɗin ta fice duka.
Babu abinda ke fita a bakin Raudha sai kalmar innalillahi.... Har ƙarshe, ga hawayenta na zarya a kan ƙirjinsa. Murmushi ya saki da sake yamutsa gashin nata da yakeji kamar su yini yana wasa da shi. Cikin wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa cin karon ji da ga garesa ba ya fara magana...
“Ustaza wannan ba mafita bace, idan kika bari naje matakin ƙarshe sam bazan saurarekiba sai na tabbatar da sadakina bisa kanki yanzun nan harda ribar baby insha ALLAH..”
Baima kai ƙarshe ba tai saurin sakinsa da son tureshi, sai dai hakan bamai yuwuwa ba, dan duk da halin da yake ciki ai goma tafi biyar albarka. Yanda tai ɗin ya bashi dariya, sai dai halin da yake ciki bana dariyar bane, yayi imani kuma da inhar aka cigaba da kasancewa a haka babu makawa a yanzun nan bazai iya ƙyale yarinyarnan ba, duk da ƙoƙarinsa na son yin hakan. Kaɗan ya matsa ta samu hanya, ai da gudunta ta fita har tana bigewa da ƙofa.... Shima zaune ya kai jagwab saman stool ɗin mirror bayan ya ɗauke book ɗinta dake a wajen. Ya dafe kansa zuciyarsa na matuƙar gudu kamar zata fito... (Mike damunka Ramadhan? Mikaje ka takaloma kanka wajen shegen tsokale-tsokalen neman ayi?) a zuciyarsa yake maganar, sai dai sam babu nadamar abinda yay tattare da shi. Sai ma a fili daya furta ‘Oh Ramadhan ka lalace, da sa'ar autarku kake wannan abun ko kunya babu.’
Sai kuma murmushi ya suɓuce masa, ya kai hannu a wuyansa, “Ni Ramadhana zazzaɓin ma ya dawo” yay maganar a marairaice yana wani langaɓe kai gefe cike da tausayin kansa.... Tuna abinda ya gani ya sashi saurin juyawa ga mirror ɗin, book ɗinta ya ɗauka ya buɗe, sai kuma ya miƙe yana bin rubutun da kallo. “Kai ina..” ya faɗa a fili yana girgiza kansa da miƙewa riƙe da littafin. Bakin gado ya koma, ya ɗauka ɗaya daga cikin wayoyinsa yay snapping rubutun, littafin ya ajiye ya cigaba da danne-dannensa. Tsahon mintuna biyu ya kai wayar kunensa.
Daga can cikin tsokana Bappi yace, “Ɗan gatan ALLAH ka warke kenan?”.
Murmushi yay yana sake ƙoƙarin control ɗin halin da yake ciki. “Oh Bappi nida nake kwance cikin ciwo kake kira ɗan gata?”.
Dariya Bappi ya karayi daga can. “Ɗan gatane mana tunda ciwon naka na ƴan gatane. Bakaji bahaushe yace _mura ciwon ɗan gata ba_”.
Dariya sosai shima Ramadhan ya sanya a wannan gaɓar Bappin na tayasa. Sai da suka nutsu Ramadhan ya fara magana serious. “Bappi wani abune ya ɗan rikitani yanzun nan. Amma na turo maka saƙo ta email ka duba yanzu dan mu tabbatar”.
Bappi ma daya koma serious ɗin yace, “To ALLAH yasa dai lafiya?”.
“Lafiya lau Bappi duba dai”.
Bayan kamar mintuna uku sai ga kiran Bappi ya shigo, lokacin yana ƙoƙarin saka kaya a jikinsa. Dakatawa yay ya ɗaga wayar. “Ramadhan ina ka samu wannan hand writing ɗin?”.
“Iri ɗaya ne ko bappi?”.
Ramadhan ya amsa tambaya da tambaya. Daga can Bappi yace, “Tabbas babu wani babbanci, kenan wanda ya turo takardar nan kamar yanda mukai hasashe yanada kusanci damu?”.
“Bappi kasan rubutun waye kuwa?”.
“Shi na ƙagu naji Ramadhan ”.
“Ameenatu!”.
“Aminatu? Kana nufin Aminatu dai matarka?!”.
“Ita kuwa Bappi. Yanzu naci karo da shi a book ɗinta na makaranta, shiyyasa gaba ɗaya kaina ya kasa ɗauka nima dan na shiga ruɗani”.
“Uhhm to kaga wannan maganar bata nan bace ba, idan ka fita office gobe idan ALLAH ya kaimu zanzo kawai”.
“Bappi na sameka a gida mana anjima”.
“No Ramadhan akwai haɗari. Satar fitarka tayi yawa, ina tsoron magauta su fara fahimta su cutar da kai ta wannan hanyar. Dolene ka canja takunka”.
Fuska ya ɓata, dan gaskiya akace bazai dinga zuwa gidansu akai-akaiba an cutar da shi. Wannan takura har ina dan ALLAH.
★Hajjaju Raudha kam tunda ta fice tana can ɗaki duƙunƙune a bargo. Ji take kamar ta tona tsakkiyar gidan kawai ta shige ta huta. Bawai bata san minene aure ba, domin tanada zurfi a ilimin addininta, shiko musilinci ya fiddo mana komai dangane da aure cikin hikima da rahamar UBANGIJI. Matsalar kawai shine komai yana zuwa mata baƙo ne. Bata saba ba, bata taɓa gani anayi ba. Bata karatun littafi sai ranar da Bilkisu ta bata, ko karatun tanayine cike da kunyar wasu wajajen idan tazo a lokacin. Gidansu na hutawa