Showing 48001 words to 51000 words out of 207756 words

Chapter 17 - Bakar Inuwa Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

625

sakashi zuwa wajen taron har sai da ya nuna ɓacin ransa shi da Anne da Pa. Koda ya shigo yaga mutanen dake wajen daga sa'an Pa sai sa'annin Bappi baiji ko ɗar ba, a lokacinne ma yaji kibiyar son yin mulkin ta soki ƙirjinsa. Dan yana ganin yakamata sumafa matasa ace anayi dasu a ƙasar NAYA dan sune ƙasar.
     A yanzu kuma boren nasu ya sake harzuƙa zuciyarsa dajin eh lallai zai amince ya amshi mulkin ƙasar NAYA inhar ALLAH ya saka hakan a cikin ƙaddarar rayuwarsa. Da ƙyar shugaban jam'iyya ya tsawatar akai shiru, kafin ya yanke hukunci akan gobe za'ai primary election duk da a ransa yasan dolene candidate nasu ya tsallake. Duk sun amince da hakan, daga haka kuma taron ya watse wasu ransu ɓace wasu ransu fal murna, sai dai masu murnar zukatansu sun rabu gida biyu akan dalilin murnar.

    Wani meeting ɗin su Alhaji yaro glass suka sake shiga iyakarsu kaɗai akan batun, kafin kuma da yamma shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya su sakeyin wani zaman da wasu jiga-jigan jam'iyyar.


*_JIHAR DILLO. HUTAWA L.G.A_*

         Koya ya shiga matuƙar mamakin yanda M. Dauda ya dawo garin hutawa a jiƙe da kuɗaɗe shi da abokinsa, dan maimakon su rufe sirrinsu sai sukazo sunama jama'a fankama da kuɗi da nuna sumafa sun kai yanzun. bama shi ba abokinsa M. Gambo ma dai ajiƙen ya dawo. Nan take aka fara ƙananun magana da dangantasu da ɓarayi saboda hankalin jama'a ya tashi musamman da suka san dai ba ko sisi su M. Dauda ke magani ba, dan inhar ba sata ba ko wannan kidnapping da akeyi ba babu ta yanda za'ai daga barinsu gari na kwana uku su dawo haka. Aiko nan take manyan anguwa suka haɗa kai suka kai ƙararsu gidan hakimi, hakimi baiyi ƙasa a gwiwa ba ya aika a ka kira masa su M. Dauda daya saka innarsa da iyalansa haɗa ƴan kayansu dan so yake a gobe ya fara gyaran gidansa. A gefe kuma yana tunanin sake sabon aure da lallaso Asabe ta dawo (bayan saki uku ne tsakaninsu🙄).
          Hakimi da ƴan fadarsa babu kalar binciken su M. Dauda da basuyiba amma sun dage akan sufa basu kuɗin nan akayi. Ganin kamar suna son rainama fada hankaline saboda ambatar sunan manyan mutane da sukayi yasa hakimi saka ƴan sanda suje da su. Haka kuwa akayi, a ranar a police station suka kwana, washe gari hakimi kuma ya kai magana fadar mai-martaba sarkin Dillo. Bako a ɓata lokaciba wajen yayubar su M. Dauda sai cikin birnin Dillo fadar sarki.
        Nan ɗin ma dai amsar da suka bama hakimi ita suka bama sarki akan inda suka samo kuɗi, sai dai shima bai gamsu ba saboda sunayen da su M. Dauda ɗin suka ambata na manyan mutane. Sai ma hankalinsane daya sake tashi dan gani yake kamar su M. Dauda nason yin amfani da sunan manyan ne dan ɓata musu suna. Baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen fara neman waɗanda yakeda kusanci da su ciki harda Alhaji Hameed Taura da tarihi ya nuna karatu ya taɓa haɗasu a jami'a.
         Da ƙyar ya samu damar magana da shi a ranar ta hanyar P.A ɗinsa, bayan sun gaisa cikin mutunta juna matsayinsu na manya da ƴar tsokana ta tsoffin abokai mai-martaba yayma Bappi bayani game da su M. Dauda. Da farko sam Alhaji Hameed Taura bai gane ba saboda baiyi tunanin su M. Dauda sun koma ba, kuma shi har yanzu ma bai basu ko sisi ba su shugaban ƙasa ne sukai musu ƙyauta. Sai da aka haɗashi da M. Dauda, yana ko jin muryarsa ya gane, amma duk da haka sai yasa aka tura masa hotunansu ta email.
      Yana gani kuwa ya gane, dan haka yayma mai-martaba bayanin da zai iya fahimta. Jin alaƙar dake shirin faruwa tsakanin su dan babu wanda baisan abinda yaso faruwa da Alhaji Hameed ɗin ba ran salla sai shima mai-martaba ya shiga mamaki, harma yake cema Alhaji Hameed anya kuwa baya ganin tun farko dama akwai dalilin daya saka yarinyar masa garkuwa.
     Alhaji Hameed Harith Taura mutum ne mai sauƙin kai da tsarkake abu koda ace yazo a yanayin daya kamata a zargesa, hakan yasa shekaru aru-aru su Alhaji Yaro glass keta cutarsa yana ƙyautata musu zato dan bai taɓa damuwar zama ya zargesu ba. Cikin nutsuwa ya fahimtar da mai-martaba shi dai zaiyi ne bisa ƙyaƙyƙyawar niyya, kuma baijin yarinyar zata aikata haka dan yarinyace ƙarama kuma nutsatstsiya.
     Cikin ƙanƙanin lokaci mai-martaba ya yarda dan shima mutum ne mai fahimta, harko yay alƙawarin za'a dama dashi a harkar bikin shine ma uba ga Raudha tunda dai a ƙarƙashin mulkin jiharsa take. Alhaji Hameed yayi matuƙar farin ciki yayi kuma godiya.

     Wannan shine ya wanke su M. Dauda wajen hakimi da sarki, sai dai ga jama'ar gari sun ƙara gaba wajen ƙananun magana musamman da akaita dawo da zancen abinda Raudha tayi da kuma dalilin rabuwar Asabe da M. Dauda ɗin da ba'a wani jima ba. Kafin kace kwabo zance yaje bakin ƴan jarida da yanar gizo harya fara yawo...........✍


https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09


Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*


*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_



Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k


*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*


*KATIN MTN*👇👇

09166221261
__________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*



Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F


*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77



*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________


*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3


Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*


*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[6/9, 8:02 PM] NANA: *_Typing📲_*







*_Episode 19_*


............. *_BINGO CITY_*

  Ƙananun magana da surutan dake faruwa a gari dama wasu manyan kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo baisa Alhaji Hameed Taura ya damu ba ko janye maganar auren Raudha da Ramadhan. Dan cecekucen jama'a yayi dai-dai ne da cin primary election da Ramadhan yayi zancen tsayawarsa takara ta fito fili. Aifa jama'a da ƴan siyasa ƴan bani na'iya suka samu nayi, yayinda magoya baya keta faman murna. Ƴan jam'iyyun hammaya kuwa tuni suka fara cece kuce akan sam Ramadhan bai cancanci fitowa takarar shugabancin ƙasar NAYA ba. Saboda dalilai masu yawa.

     Ɗan jarida dake hira da wani riƙaƙƙen ɗan siyasa a jam'iyyar hamayya ya gyara zama da faɗin, “Ranka ya daɗe miyasa kuke ganin bai cancanta ba bayan shiɗin matashine mai jini a jika da ba'a taɓa ko kwatanta shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsaba a ƙasar NAYA? Sai nakega kamar wannan wani al'amarine daya kamata kowa yay murna da shi tare da yabama jam'iyya mai mulki data kawosa dan sunyi abinda ba'a taɓa yiba suma. Sannan Ramadhan B. Taura kowa yasan gidansu akwai kuɗi, a cikinsu ya tashi babu yanda za'ai ya handame kuɗin Al'umma tunda ba baƙonsa bane kuɗin”.
     Wata ƙasaitacciyar dariya Alhaji Andi ƙaura ya sake. Kafin ya haɗe fuska da faɗin, “To ai kuɗin daya tashi a ciki suna ɗaya daga cikin abinda yasa bazai iya ba. Banda matsala da ƙarancin shekarunsa dan koba komai muma muna buƙatar matasan ayi dasu. Sai dai kuma Ramadhan B. Taura bai cancantaba saboda baisan komai ga wahalar talaka ba. Idan baka saniba bara na faɗa maka. Shekaru biyar da suka wuce an kashe matar Ramadhan B. Taura da ƴarsa ta hanyar kai musu guba har gida cikin fridge sukasha suka mutu. Idan har wanda bazai iya bama iyalansa tsato da za'a halakasu har gidaba, tayaya zai bama ƴan ƙasa? Maimakon fa a tsaurara binciken gano wanda ya aikata sai ma yabar ƙasar gaba ɗaya ya koma America da zama. shine bai tashi dawowa ba sai yanzu wai shi yazo yay mulkin ƙasa. Inama laifin ya fito kansila ɗin anguwarsu ko ƙauyen Taura, amma ba NAYA ba dan babu abinda zai iya. Kai kana gani ko primary election ɗin nan ba kuɗi daliget sukaci ba da sauran ƴan takarar da suka janye masa tunkan fara jefa kuri'a?. Hutu da jin daɗi ya iya, yaje yayi kayarsa yabar wanda suka san wahalar talaka suyi mulkin ƙasar NAYA”.
        “To amma ranka ya daɗe sai nake ganin kamar jama'a zasuce kana faɗar duk wannan ne saboda kaima ana zargin takarar zaka fito a jam'iyyar hamayya?”.
      (Dariya).
“Dan kawai zan fito takara sai a danganta zancena da ita. To nabama duk mai saurarenmu damar zuwa ya binciki, shin a zancena akwai ƙarya kuwa?”.
         “To amma ranka ya daɗe idan za'a duba a yanzu haka Ramadhan B. Taura yana shirin angwancewa ne da ɗiyar talakawa, wadda kowa ke ganin halaccine garesa bisa itama nata hallaccin data nuna akan kakansa wanda taima garkuwa aranar salla a filin idi. Shin wannan bai kai a yaba masa ba kuma a ƙara tabbatar da yasan kishin talaka da darajarsa ba?”.
        “To ai wannan maganar auren nasa ga kowa ma abayyane take. Dama sunyine domin duniya tai irin tunaninka, inba hakaba taya kake tunanin yaro kamar Ramadhan B. Taura young millioner da tun yana ciki ake tara masa kuɗi a accaunt zai auri ɗiyar talaka mai wahalar neman na masara a kullum. Kai ita kanta yarinyar ma a majiya mai ƙarfi tayi abinda tayine dama saboda an biyata. Sune suka sakata tayi hakan domin ayi irin tunanin da kayi. ka auna mana, dayin abun da fitar sunansa matsayin ɗan takara gaba ɗaya sati biyu kenan”.
        Ɗan jarida ya jinjina kansa yana kallon fuskar camara man. “To jama'a kuna dai jin tattaunawarmu da Alhaji Andi ƙaura acikin shirin SIYASA RIGAR ƳANCI dake zuwa muku anan gidan tv na G tv. Gashi mun kwararo bayani kuma lokaci ya ɗaga mana hannu, amma ku mana afuwa sati mai zuwa zakuji ƙarashen wannan fira insha ALLAH, zakuma kuji amsoshin zantukan Alhaji Andi ƙaura daga bakin makusancin ko nace jam'iyya mai mulki shima insha ALLAH”.
  
         Ɗauke hotunansu ya saka Raudha cusa kanta cikin ƙafafu ta fashe da kuka. Tun farkon fara hirar ta zauna kallo sakamakon cin karo da hotonta da tayi tare da na Ramadhan. Da farko rikicewama tayi dan bata gane shi bane, sai da hajiya mama dake zaune a falon tana kallo ke faɗin, “ALLAH dai ya kaimu randa zanga wannan zuƙeƙen surikin namu ya zama shugaban ƙasar NAYA ɗiyata first lady, ɗiyata da zakimin baƙin cikin zama uwar first lady”.
      Cikin rashin fahimta Raudha ke duban hajiya maman, sai kuma ta maida hankalinta ga tvn dan itako batama san wanda ake kira da mijin nata ba ya fito takarar shugaban ƙasa. Sosai hankalinta ya sake tashi dajin wannan hira musamman abinda Alhaji Andi ƙaura ya faɗa akanta. ALLAH shine shaidarta batayi dan a yaba mataba. Hasalima batasan wanene Alhaji baba ba alokacin. Amma gashi nan ta shiga bakin duniya yau harda masu fassara al'amarin da cewar an biyatane dan tayi, wasu na faɗin neman suna da neman gindin zama ne dama. Wasu na faɗin dan kuɗi tayi.
     Surutu dai iri-iri gasu nan marasa daɗin ji, ita kanta zuwa yanzu harta fara ganin gaskiyar zantukan mutanen, dan tana da tabbacin Ramadhan yafi ƙarfinta. Musamman da zancen fitowarsa takarar shugabancin ƙasar NAYA ya bayyana. Sannan ita tun da ake maganar auran nan batajin ma shi ya sani, tunda tun randa yaje asibitin nan bata ƙara ganinsa ba. Sai ma hannunka mai sanda dayay mata akan zame mata *_BAƘAR INUWA_*  inhar bata faɗi dalilinta na bama kakansa kariya ba. Idan har shi zaiyi irin wannan tunanin dan jama'ar gari sunyi mizaisa ta zargesu.......
      “Raudha!”.
Asabe ta sake kiran sunanta a karo na biyu. Ɗagowa tayi tana dubanta dan bataji na farkon ba. Cikin tausayin ƴar tata tasa hannu ta ɗagota ta rungume. “Haba Raudha kukan nan ya isa mana. Kina sake tayarmin da hankali wlhy. Ni nasan bakison auren nan, bansan miyasa kika amsa musu ba.....”
      “Wlhy ko bataso saita yisa”.
Cewar Hajiyar birni dake fitowa daga ɗaki a fusace. Dan yau da wuri ta baro shago saboda tana shirye-shiryen daina zuwa wai dan zata zama kakar matar shugaban ƙasa (🤔😝😂lol).
       “K dan ubanki saketa kitsaya da ƙafafunki!!”.
     Raudah ta saki Mommynta da sauri saboda gigitacciyar tsawar da Hajiyar birni tai mata. A take hajiyar birni ta haɗasu su duka ita da Asaben ta zage tas Hajiya mama na tayata. Sai da Aunty Hannah ta shigo gidan kusan goma na dare sannan tasa baki dan har lokacin sunata mita.


*_TAURA HOUSE_*

     A ɓangaren Ramadhan ma da duk ƴan gidansu sunga hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, hakan kuma yasa Gimbiya Su'adah jin wa ɗanta zai aura. Dan tayi-tayi Pa ya sanar mata dama yaƙi. Sai gashi yau taji a shanun ƴan talla.
         Cikin lokaci ƙanƙani ta birkice, su Lubnah na tambayarta amma bata sauraresu ba. Da suka cigaba da damunta ma tsawa ta daka musu tai wurgi da wayar da take neman Fulani taƙi shiga ta fice zuwa sashen Pa duk da yau ba itace da girki ba. Zaune ta iskesa shi da Hajiya Mufida sunata hirarsu. A kallo ɗaya da sukai mata suka fahimci babu lafiya. Dan kowa a gidan yasan shegen girman kai da isar Gimbiya Su'adah. Duk da tanada tsananin kishi kishiya bata isa fahimtar komai daga garetaba. Dan batayin wani abu da za'a samu kafar rainata, ko kallon banza bata amince zamanyi da kishiyaba dan tace zubar da mutunci ne. Hakan kuwa da takeyi yayi tasiri, dan kame kan nata yasa ko shirmensu suke yakan tsayane iya su biyu, ballema suma ɗin kowa ji take da kanta abunka da kowa ubanta ya tara kuma akwai ilimi, dama hayaniyar tasu bata wuce ta harara ko rainin wayo anama juna yatsine-yatsine ko ɗaukar kai.
      Tsam hajiya Mufida ta miƙe tana tattare wayoyinta, cike da kulawa ta dubi Pa. “Bara nayo shirin barci kafin ku kammala”.
    Kansa kawai ya ɗaga mata idonsa akan Gimbiya Su'adah datai zaman ƙasaita a gefensa fuskarta tamkar zatayo aman wuta. Sai da ta tabbatar Hajiya Mufida ta bar sashen saboda akwai cctv da ake ganin shiga da fitar kowa daga nan falon sannan ta dubi Pa.
       Kafinma tai magana yace, “Lafiya?”.
         Idanunta da suka kaɗa zuwa ja ta zuba masa, cikin son nuna isar tata tace, “Abban Ramadhan ban yarda da wannan auren na Ramadhan ba”.
      Kansa ya ɗan girgiza ya ɗauke ya maida ga tv. sai da yaja numfashi ya fesar kafin yace, “Komi yasa?” batare da ya sake kallonta ba.
          Bata damu da yanda yay ɗin ba, cikin kaushi da nuna a wuya take tace, “Saboda bata dace da shi ba. Taya za'ace duk ƴaƴan sarakunan ƙasar nan dana attajirai da masu mulki arasa matar da za'a bashi ya aura sai wannan?! Wad......”
      Cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Su'adah bana son hayaniyar banza. Shin ɗanki aure bautar ALLAH zaiyi? Ko auren kuɗi ko mulki?. Sannan ma ina zuwa, kina nufin Bappi bai isa zartar da hukunci bane a kan ɗayanmu? Ita yarinyar kuma kinsan ƴar waye da kike wannan hanƙoron.”
      Zatai magana ya sake dakatar da ita. “Karma ki ɓata lokacinki a banza. babu abinda zai hana wannan auren sai idan Ramadhan ne ya mutu, ko ita yarinyar insha ALLAH”.
       “To ashe kuwa lallai zata mutun”.
Ta faɗa a harzuƙe tana miƙewa zata fice batare data san katoɓara da suɓutar bakin da tayiba. Wadda ta saka Pa binta da kallo ƙirjinsa na bugawa. (Gimbiya Su'adah ta manta har yanzu akan binciken wanda ya kashe matar Ramadhan da ƴarsa akeyi, tun kuma a wancan lokacin an tabbatar musu wanda ya ajiye gubar suka sha sai dai idan yanada alaƙa dasu ne tunda duk wanda yazo birthday ɗin Haseenah makusancinsu ne. Sannan kafin wancan auren ma ta nuna borenta na ƙin Amnah saboda tanada sikila).
        “Ya ALLAH mi Su'adah keson faɗa ne?”.
    Pa ya faɗa a razane yana miƙewa zaune sosai. Zuciyarsa fal fargaban kar dai Su'adah nada alaƙa da kisan Amnah. Da sauri ya girgiza kansa. Dan a halayenta babu mai kamanceceniya da iya kisan rai. Barta dai da gadara da girman kai wannan kuma ya tabbatar jinin mulki ne ke yawo a jikinta. To amma miye ma'anar furucinta na yanzu? Anya kuwa babu lauje cikin naɗi.
      Hankalinsa ya tashi matuƙa da wannan tunane-tunanen, harta kaisa ga fitowa daga sashen zuwa sashen iyayensa. A falo ya iske su harda ƙannen kakannin nasa su Inna sunata hira hankalinau kwance. Yanayinsa ne ya saka Yafendo tambayarsa ko lafiya?.
      Da ƙyar ya iya haɗiye kaso sittin cikin ɗari na tashin hankalin daya shigo da shi, ya ƙirƙiri murmushin dole ya aza a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login