Showing 1 words to 3000 words out of 92177 words

Chapter 1 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

[11/2, 10:29 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA*




*37*



Ko da Mimi ta shigo ban saurare ta ba, ina tsaye bakin k'ofar dakin Ummanmu muna magana da ita.Simi-simi tazo ta shige dakinmu tana b'oye abu cikin mayafin ta, naji zuciyata bata yi min dad'i ba, futowa tayi ta tsaya kusa dani tare da fad'in "Shine kika tawo kika barni a hanya ko."? Umma tace" nima yanzu nake tambayar ki tace ta barki a hanya, amma kun Dade gaskiya sai da kwalliya ta biya kud'in sabulu tunda gashinan lallai yayi kyau sosai."

Mimi tace"wallahi kuwa Umma mun tadda ita tana yi wa wasu shiyasa." Tace" abuncin Ku na kicin."

Kicin din na wuce ba tare da na tsaya kallon Mimi ba, abuncin na dauko a kula nan rumfar Umma na zauna tare da bude food Fula's din ina k'okarin zubawa. Jiki a sanyaye Mimi ta k'araso inda nake zaune duk ta damu ganin yanda na share ta.Umma ta mike ta futa tsakar gida tana amsa sallamar da ake yi.

Mimi ta kalle ni bakinta na rawa tace"kin San me Asma'u. "? Nace" sai kin fad'a."
"Guy nan fa wayarsa ya bani had'addiya baki ganta ba, wai zai dinga kirana da ita.....gabana ne yayi wata irin fad'uwa!! Tuni naji abunci ya futa kaina na kalleta cikin dauriya tare da fadin" kin dace Mimi Allah ya kara k'auna" Mimi babu kunyar komai tace" ameen Ashe haka yake da saukin kai."? Nace"Hummm"? Hirarsa kawai take min takasa cin abuncin nace "Mimi so ya hanaki ki ci abunci ko? Ki dai yi a hankali." Dariya tasa cike da farin ciki, duk Wanda yasan Mimi a lokacin zai fahimci fara'ar ta da walwalarta ya k'aru.


*******
Kai tsaye Company nasa ya nufa Wanda ake aiki tuk'uru ma'aikata iri-iri sai kai kawo suke, insha Allah yau za'a gama komai sai abunda yayi saura had'a wuta tare da fenti amma komai ya kammala kuma ma'aikata suna tsaye a kai. Yaji dad'i sosai da sosai ganin yanda sabon company shi ya koma tamkar Wanda aka dauko shi daga America aka dasa shi a gurin tsari da k'atuwar company ba'a cewa komai, nan ya zauna da tsofaffin ma'aikatan sa suka yi meeting akan yadda za'a tsaurara matakan tsaro a gurin, kuma dole za'a dibi sababbabin ma'aikata, Amana ya damk'awa Bashir Manager saboda yasan ya wuce chana gobe zuwa jini domin yaga wane irin cigaba a ka samu a can d'in.

Harabar gurin ya futo yana kewaya wa hannunsa goye a baya, tabbas zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzu ana shaho sai yayi

Wani ma'aikacin gidan talavition ne ya k'araso gurinsa a nutse yace." Ranka ya Dade dama tun d'azu muke jiran futowar ka, mun dad'e a waccan rumfar muna zaman jiran ka."
Kallon gurin da yake nuna masa yayi sai ya gansu a zazzaune su kusan hud'u. Cike da mamaki yace." Me zaku yi min kuma."? Ma'aikacin yace." Ranka ya dad'e 'yan tambayoyi zamu yi maka a gurguje." Girgiza kansa yayi ya rasa me yasa suke bibbiyar sa, yace." Muje can d'in" wata k'atuwar rumfa suka nufa wacce take kewaye da wasu had'addan kujeru na silver gurin hutawa ne an kammala tsaf hatta da tayel an saka a gurin fenti ne kawai ya rage, kujera suka gyara masa ya zauna sannan kowa ya sai ta na'urarsa. Cikin nutsuwa d'aya daga cikin 'yan jaridun ya fara kwararo masa tambayoyi kamar haka."

*"Yallab'ai dama muna son Karin haske ne daga gurin a game da labarin da muka samu sati d'aya daya wuce shin da gaske bayan wannan company da ake aikin sa wai akwai wasu guda biyu a k'asashen waje? Yallab'ai muna buk'atar Karin haske akan wannan jita jita da jama'ar gari suke yi mussaman 'yan kasuwa."*


Murmushi yayi kawai yana girgiza kan sa ta tabbata kenan duk abunda yake idanun mutane a kansa yake, shidai a iya sanin sa babu da Wanda sukayi zan can cewa zai bude company a america da Ingila sai Anthony sai granny su kadai ne sukan wannan maganar.


Gyara zaman sa yayi sosai yayi gyaran murya alamun zai fara magana, duk suka matso da lasifik'an su, Yace." *K'warai kuwa ba jita-jita bace gaskiya ne maganar jama'ar gari tabbas ina shirye-shiryen bude company guda biyu d'aya a America daya a Ingila sati mai zuwa za'a gudanar da bukin budewar a can kamar yanda za'a gudanar anan, ina yi wa 'yan kasuwa albishir da cewar duk me sha'awar futa waje yayi odar kaya to ya je company mai suna A'A ABUL ABBAS MAI NASARA, babu shakka zai samu duk wani na'uin kayan idai ya ka sance Wanda d'an adam yake sanyawa a jikinsa ne, kamar kayan mu na hausawa k'ananun kaya suit da sauran su akwai b'angaran kayan mata ko wane iri ne, takalma na maza da na mata duk company zai kawo kan farashi me sauk'i , sannan duk abunda company na kasashen waje zai kawo a kwai shi a wannan company nawa*


D'an jaridar yace." Sai tambaya ta biyu Yallab'ai, ina fatan samun amsa a gurin ka, kamar yanda muka samu wannan amsa ta farko munji kuma mun gamsu."
"Shin Wai kana da aure Ku kuwa? Da yawa mutanan gari suna yi maka kallon Mai lyali Yallab'ai muna son mu samu wannan amsar daga bakin ki." Murmushi ne ya sub'uce masa, ya d'an Sosa kansa kamar yanda ya saba yace." A'a bani da aure a yanzu a sali ma ban shirya yin sa ba, tunda a halin yanzu bani da budurwa da na tsayar a matsayin wacce zan aura, to amma shi aure lokaci ne dashi idan yazo ko da matar a hannu ko babu A lokacin sai Allah ya kawo ta ayi ina fatan daku da jama'ar gari da duk wani me kaunta zaku taya ni da addu'a kan Allah ya zab'a min mace ta gari."

D'an jaridar yace." Insha Allahu Yallab'ai zamu taya ka da addu'ar Neman zab'in Allah ubangiji Allah ya baka mace ta gari tare da 'yaya masu albarka, mungode mutuka da bamu lokacin ka daka yi Allah ya kara maka suttura da daukaka ya kare ka daga sharrin masu sharri."

Hak'ika Amjadu yaji dadin addu'ar da Dan jaridar nan yayi masa, amsa da "Ameen suma ameen nagode K'warai da addu'a."
Nan suka had'a na'urorin su cike da murnar samun nasara yau sun same shi ba tare da sun kai ruwa rana ba."

Sai bayan sallah magariba ya bar company din hankalinsa kwance ganin komai ya kammala, tun a mota kira yake shigowa wayoyin sa, ko d'aya bai d'auka ba, draving din sa kawai yake yi saboda ya san dai bai wuce jama'ar sa ba masu son jin ta bakin sa, tunda ko wace kafar sadarwa ta jahar kano a labaran ta na yamma ta sun sanyo jawabin sa, shine dalili kawai hatta da gidan television na NTA kano suma sun hasko shi cikin labaran su na k'arfe shida, yana ji a jikinsa kamar akwai wani babban al'amari da zai same shi anan gaba.
Kai tsaye gidan granny ya nufa domin yayi mata sallama.


*****

Governor ne da gaggan 'yan kasuwa wad'anda suka ci suka ts dakai marasa tausayin na k'asa dasu Wanda Kansu kawai suka sani. Masu bakin ciki ga duk wani Dan kasuwa da ya sauke farashin kayansa, a cewar su talaka ba abun tausayi bane. Su biyar ne a dakin meeting din gidan gomnati wato government house suna tattaunawa game da yanda zasu b'ulluwa Amjadu domin dukaninsu saurari jawabin sa, na yau, hankalin su yayi masifar tashi sosai jin wai har company biyu ya bude a kasashen waje bayan company shi nan Lallai ya zama dole su San yadda za'ayi su rusa shi.

Alhaji Sunusi mai leshi ne Yace. " Ni ina gani kawai mu hada baki da ma'aikatan sa mu Sakar masu KUDI Sosai mu fada musu bukatar mu. Cewar muna so su sanya algus da mugunta a ko wace irin adduga da zasu sarrafa, a company ta inda duk kayan da za'a futar a company su zama marasa k'wari da karko kunga daga nan Jama'a zasu gane sai su fara guduwa."

Mai citta ya gyara zama hade da sakin murmushin mugunta yace." Wannan shawarar taka tayi kyau kuma itace abar d'auka dole zamu San yadda mukayi mu jone da ma'aikatan nasa idan muka jik'asu da kudi kome ye zasu yi ko ya kuka gani."?
Duk suka yi na'am da haka, nan taro ya watse ko wannen su cike da farin ciki.


*****
Tana zaune a parlor kamar ko da yaushe me aikin ta Iyami na zaune a gefanta tana bata labarin garin su, yayi sallama ya shigo parlor, Iyami dattijiwa mai kirki ta dinga yi masa sannu da zuwa had'e da tsokanar sa, zama yayi cikin kujera yana gaishe ta, ta amsa da fuska a sake, da sauri ta nufi kicin domin ta kawo masa abunci.

Granny ta kalle shi babu yabo babu fallasa tace"K'ato me k'irar damu dawa kana tafiya gotai-gotai da kai babu iyali kai ko kunya baka ji, ka kai munzali amma ka tsaya shirme."

B'ata fuskarsa yayi yace. " zan can kenan daga zuwa sai maganar aure wai a kanki nake ne." Granny tace." Yo ni in a kaina kake ai da tuni ka kashe ni. Dube ka don Allah kamar zaka ji babu jiki a murd'e ai kai kam matarka zata fad'awa 'yan garinsu."
Gyara zaman sa yayi yana dariya kasa-kasa yasan halin kakar tasa da sakin magana ko wace iri ce ita babu ruwan ta, kafin yace wani Abu yaji tace" ka fad'amin in baka da lafiya sai in baza ma nema maka magani ko kauyen su Iyami muka je nasan za'a samo maka maganin k'arfi, ina amfanin girman jiki da k'wanji babu fus!! Uhum? Irin Ku ne matayen Ku suke shan takaici a zahiri dai gaku maza a bad'ini kuwa sai takaici." Ta k'arashe maganar ta tsakanin ta da Allah.
Gyara zamansa yayi da k'awataccan murmushi a fuskar sa yace." E dama na kasa fad'a miki bani da lafiya don Allah ki shiga k'auyika ki nemo min maganin k'arfi kinji."!! Granny ta kalleshi da hankalinta a tashe tace"Yanzu kai k'ato da kana fama da wannan lalurar ka zauna sai dai kaci ka sha ka nemi kudi? Au! Ko da naji shiyasa ko wace mace aka kawo maka sai kace bata yi maka ba, tom yanzu yaya kake ji a jikinka shin kana sha'awar mace sa'i da lokaci ko A'a."!? Granny ta tsarashi da tambaya hankalinta duk ya tashi.
Kamar gaske yace." Kwata-kwata bana jin sha'awar mata, amma ina ganin a haka zanyi auran da kike so nayi." Tace" innalillahi u ni 'yasu! Amma yaron nan kaso kacuci kanta.....Iyami Iyami Iyami.!" Ta dinga kwala wa mai akinta kira.

Yace." Nifa ba cewa nayi kiyi min taron dangi ba, uhumm ke kad'ai na fad'awa damuwa ta." Hararasa tayi tace"Naji kana maganar zaka yi aure a haka Uwar me zaka tsinanawa matar taka, abunci da madara kawai zaka bata bukatar ta kuma waye zai biya mata."! Cike da tuhuma tayi masa tambayar." Dariya yake sosai yace." Ai Irina zan auro kinga bani da matsala ."
"To baka isa ba ehe! Nima ai ina son 'yan yara, a gaba, ni kawai zaka cuta.'!!! Tsakanin ta da Allah take maganar, Iyami ta shigo parlor da sauri take fadin" Hjy kira kike ko."? Granny tace"Iyami zama bai kama mu ba, k'ato babu lafiya." Iyami ta kalleshi cikin rawar baki tace"Mai gida babu lafiya Ashe? Allah ya kawo sauk'i.'" Yace." Ameen Iyami ai tace"Zata shiga ta futa ta samo min magani." Iyami tace"Hjy meye yake damun Shi ne." Granny tace"Iyami je ki cigaba da aikin ki zamuyi maganar idan anjima." Iyami ta mike da jiki a sanyaye. Kallo ya bita dashi yana kumshe dariya.
Ita kuwa granny surutai kawai take masa tare da yi masa fad'a ya zauna cuta yaci k'arfin sa, saboda yana so ya zama lusarin namiji.
Aikuwa tana tsaka da fad'an ta taga an hasko shi a TV tashar CTV kano mutane kewaye dashi yana jawabi.
Tace." Duba ka gani k'ato dubi yanda Allah yayi maka kwarjini da daukaka ta jama'a kudi duk kana da su. OO ni! 'Yar nan Allah kar ka jarrabe mu da abunda baza mu iya ba." Granny ta fashe da kuka sosai! Cike da mamaki yake kallonta, ganin da gaske kukan take yasa ya rungume ta a jikinsa yana rarrashinta tayi shiru yasan ko ya fad'a mata da wasa yake ba yarda zata yi ba ganin yadda duk ta tada hankalinta yasa yace." Granny kiyi hakuri ki daina kuka don Allah zan yi aure in haihu, ina ganin ma yanda nake jin k'arfi a jikina in dinga bada k'wayayen 'yan biyu ko uku , ki kwantar da hankalin kinji kiyi shiru kiji wani."Shiru granny tayi tana share hawaye tsakanin ta da Allah.
Wayarsa ya ciro daga aljuhu yace." Bari in kira miki ita Ku gaisa." Tace"wacece kuma"?
A hankali yace "My wifi mana."
"Meye wifi."? Ta tambaye shi dariya yasa yace." Matata mana."? Sakin fuska tayi tace" 'yar albarka ta yarda zata aure ka da lalurar ka ko.'? Gyad'a kansa yayi kamar gaske, yana laluban numbar Mimi, sai da ya kira sau uku ba a d'auka ba, shi da in yayi kira sau d'aya baya sake wa, yau gashi yayi uku, yana shirin yin na hud'u.

Mimi na band'aki a lokacin ta kuma b'oye wayar bayan katifar mu, ina shigo wa naji ringing din waya, dube-dube nake sam ban ganta ba, in da nafi jin karar tayi yawa nan na nufa na janye pillow da ta kare wayar dashi, ina dauka kiran yana katsewa, wayar na rik'e a hannuna ina dubawa cike da mamaki! Tabbas wayarsa ce, ga k'amshin sa nan jikin wayar domin hanci na ya Riga ya gama sanin k'amshin sa.
Wani kiran ne ya shigo kamar kar in dauka sai kuma wata zuciyar tace"dauki kije abunda zai je da Mimi, dannawa nayi na bud'e speaker sosai na aje ta kan kati far. Muryar sa naji yo yana fad'in"Ungo wayar gatanan Ku gaisa, kafin in an kara Naji muryar mace, macen ma ba yarinya ba, dattijuwa me kamali. Motsin Mimi naji a tsakar gida, da sauri na k'wala mata kira ina fadin"Mimi kizo an kira wayar ki."!!!!!!! Granny da shi kanshi uban gayyar suka yi sak! Yayi wa muryar ta farin sani saboda tana da saurin baki kuma bata kaurara murya tana da zaki don haka Ku cikin mata dubu ta shiga zai iya gane muryar ta.

Wani kiran na kara kwala wa Mimi tare da fad'in"Mimi wai ki ba kya ji ne, Habibin ki ne fa kiyi sauri kar ta katse........ Muryar matar Naji tana fad'in" D'iyar arziki sanun ki kinji Ubangiji Allah yayi miki albarka nagode mutuka zaki auri jikana duk da lalurar da take damun sa....ko da yake naji yace." Kema baki da lafiya, kuyi hakurin insha Allahu zamu shiga mu futa Dom......Kafin ta karasa naji yo muryar sa Yana fad'in"Nifa ba cewa nayi ki wani jawabi ba, cewa nayi Ku gaisa da My wife dina kin tsaya wani zance."!! Ji nayi tace" Matsa ka bani guri don Allah , ai wannan yarinyar ta isa a jinin na mata saboda tayi jahadi.... Dariyar shi na jiyo Yana fadin"Sai kiyi ai."" Ta cigaba da cewa"Allah yayi miki albarka kinji ko." A hankali nace" Ameeen amma bani bace budurwar tashi tana band'aki ni Sunana Asma'u ita kuma Mimi in ta futo za'a..ban k'arasa ba Mimi ta shigo dakin. Nace." Yawwa ga Mimi nan. wayar na mik'a mata na futa daga d'akin.
Kwata_kwata ban fuskanci komai ba Dan gane da maganganun da matar take,cikin zuciyata dai nake cewa"K'ila sunyi wata hira ne shi da Mimi tace mishi bata da lafiya, tom ni dai a iya sanina Mimi bata da wata cuta wacce bamu San da ita ba, asalima Mimi bata fiye yin ciwo ba, sai shekara-shekara take zazzab'in nan Wanda ake fama dashi.
Cikin zuciyata Naji tausayin ta, kuma nayi alk'awarin sai na tambaye wane ciwo ne yake damunta Wanda har ta kasa fad'ar shi a gida ta tafi waje tana yad'awa... Tsintsaya na dauka na hau share-share dama Umma bata nan taje suna sai mu kadai a gidan. Ta futo daga d'akin sai kace wata Mara gaskiya, kallonta nayi, ni yanzu tausayi take bani ganin yanda ta hada kanta da babban aiki. Sam yanzu na daina jin haushin ta, nace" Kun gama ne " zama tayi kusa dani tare da fadin "Eh, Ashe kakarsa ce wai take so mu gaisa shine ya kira ni." Cike da nazari nake kallonta nace"Mimi wane irin lalura ce dake da har kika kasa fad'ar ta a gida, kika fad'awa saurayi Wanda baki da tabbacin zai aure ki."? Yanda na tsare ta da ido ina tuhumar ta sai ka rantse da Allah uwarta ce ni ko yayarta.
Cike da mamaki take kallona tace." Ban gane abunda kike nufi ba."? K'wafa nayi cike da takaici nace"dama baza ki gane ba, naji wannan matar tana fad'in"Zata je ta nemo miki magani dake dashi kuma kinyi jahadi tunda zaki aure shi."
Ranta a d'an b'ace ta kalle ni tace"Kinga Asma'u ya zaki tasa ni a gaba kina min wata tambaya kamar wata uwata, ni babu wata magana da mukayi dashi. " Nace" Ok k'arya nayi kenan."!? Tab'e baki tayi tace"ke kika sani kuma" a hasale nace"To ki kiyaye wallahi duk inda kike tunanin wannan guy ya wuce gurin, naga soyayya ta rufe miki ido kina nema ki futa waje ki tona mana asirin gida, duk lalurar da ke damun ki nasan kika fad'awa Umma zata yi miki magani iya iyawar ta, ke da kanki Kin san kafin tayi min Abu tayi miki sau dubu me zai sa ki watsa mata k'asa a ido kije ki zauna kiyi tunani da kyau kafin kowa yasan abunda yake damun ki ita yafi kamata ta sani, amma..........Kinga Asma'u.!'" Mimi ta fada tare da D'aga min hannu a fusace ! Ta mik'e tsaye.
"Gwara ki nuna min cewar a gidanku nake zaune,Asma'u gwara kiyi min gori saboda ina zaune a karkashin inuwar Ku, amma ina so ki San wani Abu kin San dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login