Showing 27001 words to 30000 words out of 127542 words
sai tunanin Salma,gashi ba waya a hannunta,yanzu ko zaman Palo ya dainayi gaba daya,sai Bedroom,yan matan ma bashi da time nasu sai tunanin Ina Salma take yanzu?
Haka zai fito yayi ta faman kallon inda take Zama yana tuna acting dinta,haka dakinsa ma zai zauna yayi ta kallon inda take Zama,Abincin ma ya rage ci,Mummy tayi fadan har ta gaji,ya daina walwala Sam,kullum cikin kunci,har ya dan rame ya zabge,Dada ma da yaje mata sai data masa fada tace rashin mata ne da yayi aure da ya huta.
Sai dai yaje ya kwanta a room yayi shuru ko gefen Bed yana tagumi da tunanin Salma,ina ta shiga,sai yanzu ma yake ganin yayi gangancin barinta ta tafi tunda yasan da Aljanu tare da ita.
Salma ta cika 2wks Yau da kyar ya dawo daga wajen aiki zazzabi ya rufeshi sabo da rashin Salma,yana kwance yana rawar sanyi yau 2wks da tafiyar Salma amma bata dawo ba,yana hawaye yana rawar sanyi,Mummy ta kawo mishi magani yasha yana dai kwance kudundune cikin Blanket still,Kirrrrrrrrrrrrr wayar Salma ta shigo da bakuwar Number tsaki yaja tare dagawa da kyar tunaninsa ko Embassy ne ko Hospital nasa,muryar Salma yaji me shegen zaki da dandano, tace Hello Raheel,tana cewa Raheel ya tabbatar Salma ce,bai San sanda ya Mike zaune ba,yace Salma kina ina yanzu? Dariya tayi tace inye naji yau kayi hausa me kyau,stop kidding pls just tell me ina kike? Ta daga kai ta kalli wani gefen titi ansa Enugu tace ina Enugu yanzu Raheel ya kaini ya tafi kuma fa bani da kudin Mota ta furta da shagwaba,What? Ya furta da karfi,Nan take yace za Ana zo a daukeki just wait ki tsaya inda kike kin gane?,
Nan ya kashe wayar jiki na rawa ya kira wani manager dinsa na Company dake Enugu Eseme yace yayi sauri ga kanwarsa bata San gari ba yaje ya kaita airport yayi mata booking Flight back to Abuja,ba bata lokaci Eseme ya figo mota tare da kiran Salma tayi masa bayanin inda take abinka ga wayayya,yana zuwa ya hangota hadaddiya ta siyi Exotic da biscuit tana ta ci a gefen hanya gindin wata bishiya,taci ta koshi tasha ruwa, tana zuwa tace bani Dari biyar, ba musu ya mika mata ta biya masu lemo da biscuit tace su rike canji,Igbo da kudi sai mutunci da godiya kamar zasuyi mata sujjada.
Basu tsaya ko ina ba sai Airport yayi mata komai tazo Abuja lfy tana fitowa ta hango driver na Na'im yana jiranta,saida Suka gaisa yayi mata sannu da zuwa ta bishi sai gida,tun a mota driver yace Na'im bashi da lfy yana kwance,Salma a fara kuka tana a kara gudun motar tayi maza ta ganshi, fara bata hakuri yayi tare da cewa zazzabi ne kawai,ko kulashi bata yi ba.
Mota na parking a gidan ta fito da sauri Allah yasa ba kowa a Palo kawai ta wuce Bedroom dinsa da sauri ko knocking babu kawai ta fada ciki an samu dai tayi Sallama,tana shiga ta hangoshi saman Bed yana kwance amma zazzabin ya sauka,da sauri ta karasa tare da daura hannunta saman wuyansa taji ko yaji sauki,taji ba zazzabi ajiyar zuciya ta saki,tace Alhmdllh ta juya tare da niyyar tafiya idonsa a lumshe yake kawai taji an rike hannunta ta juyo da sauri cike da masifa yace ina kinka(kika tafi) tafiya haka har 2wks?kinsa gabana yana ta fadowa(faduwa) ina kika shiga? Kamar zai mareta haka yayi maganar.
Baki ta turo tare da kwace hannunta tace gida naje mana ka sani,karya ne kakeyi,if gidane kinka je baza su yarda dake ba har ki zauna 2wks,just tell me,Raheel nefa tace,sai lokacin ya tuna da shi ma,tafiya Bedroom nata tayi tare da yin wanka ta shirya cikin English wear riga da skert tayi kyau matuka marasa nauyi,kitchen taje da kanta tana tambayar masu abincin me suka dafa suka fada mata duk bata son su,Indomie da dankalin turawa ta dafa ta koma saman Dining ta zauna tana cin abarta dama Salma akwai cin abinci tana cikin ci sai ga Mummy da Irfan sun fito,me tafiya ta dawo ko nemanmu ba a ayi?cewar Mummy, Da murmushi ta juyo da cewa laaaa ai na zata bacci kikeyi,uhm rufe min baki amma nasan dole kin nemo Na'im ko cewar Mummy,Irfan yace wlh tana shigowa bedroom dinsa ta wuce da gudu ina kallonta,Salma tace ai dan bashi da lfy ne zaka sa min Ido,sanmin indomie din taki naga zatayi dadi,Fork ta mika masa ya zauna tace sai dai muci tare bazan iya barma ka cinye du ba,Mummy ta wuce kitchen abinta,Irfan dai ya zauna ya fara sharbar indomie Salma ma tana ci,Na'im ne ya sakko daga side nasa cikin shirin fita yasha kyau,hango Salma da Irfan suna cin abinci shi ya bata masa rai gaba daya yaji haushin abin ai gwara taci tare da shi Na'im dan me sai Irfan,sabo da takaici ko sauraronsu baiyi ba ya fita abinsa, har yaje zai shiga motarsa yana tunanin yanda ya bar Salma da Irfan,fuuuu sai gashi ya dawo tare da banko kofar kamar zai tashi sama,dakinta ya wuce kamar nasa ya dakko mata mayafi kalar kayanta yana zuwa ya yafa mata a kanta da ba dankwali ya ja hannunta tana fisgewa amma ya figeta tare da jefata a mota ya shiga ya figi motar da gudun tsiya suka bar gidan.
Irfan shi abin ma dariya ya bashi amma fa yana son Salma ya fara sonta,Mummy tana kallonsu tace kwaji dashi dai taja bakinta ta tsuke, Aisha ce ta dawo gidan a chake tasha tayi tatil tana layi da tangadi ta shigo tare da jefar da handbag dinta sannan ta fada saman Sofa bacci ya kwashe,lips dinta ya kumbura sumtum kamar anyi mata duka a wajen,ga kuraje kanana sun feso a kansa,Mummy da mamaki tare da tsoro taje ta shinshina bakinta taji kamar warin giya ta tabbata tasha wani abu amma bari Na'im yazo ya duba mata yau ita kadai tasan me zata yiwa Aisha a gidan.
Na'im bai tsaya ko ina ba sai wani hadadden garden na hutawa,Salma ba tsoro take ji ba domin ta saba da zuwa waje waje,fitowa tayi tare da shakar Fresh air dake kadawa a wajen,wow wajen yayi kyau,sai yanzu ta kula da shigar Na'im 3qrt da T-shirt yayi kyau,jikin wata gada suka karasa kasa titin mota ne sama garden,Daukan Salma yayi cak tare da zaunar da ita saman ginin gadar iska na kadasu me dadi yana kasa a tsaye hannunsa ya daura saman kusa da wajen da take zaune tare da tallafe kumatunsa yana kare mata kallo,cike da nishadi,sai shilla kafafunta takeyi tana murmushi tare da dauke kanta gefe kunyarsa takeji.
Cike da shagwabar da ta saba tace sai kallona kakeyi lfy?bai kulata ba sai dan gyalenta daya gyara mata sabo da iska ta kusa cireshi,suna haka sai ga wata hadaddiyar budurwa tasha kyau da wanka tana zuwa tace Oh Na'im kaine a nan yau,juyowa yayi sukayiwa juna murmushi Ajja ya kake(Hajiya ya kike) yace,tace missed u Badly ina so nazo ma ziyara na kasa samun time amma zan daure,
Kafin yayi Magana Salma tace sakkoni na gaji,Daukota yayi tare da direta a kasa,harara ta gallawa wannan wacce ya kira Hajiya,Hajiya tace kaji min yarinya dan ubanki ni kike harara haka?kin San koni wace?wannan Kanwar taka bata da kunya,Salma ta murguda mata baki tare da yin fari da Ido shi ko Na'im ya shagala da kallon murguda bakin da Salma takeyi Bai ma san me Hajiyan ke yi ba,Salma ta kara rike kugu tare da murgudashi tana yi mata kallon up and down,Hajiya tace sai na mari wannan yarinya fitsararriya,sai lokacin Na'im yaji maganar Hajiya,hannu ta miko masa tana zan wuce ni sai munyi waya ko shima ya miko mata hannu zasu gaisa ta wuce Salma ta rigata gaisawar da Na'im ta rike hannun tana jinjinawa yanda maza sukeyi kuma tana kallonsa tana murmushi tace muje kawai,kamar wani rakumi haka ya bi Salma sukayi tafiyarsu aka bar Hajiya da miko hannu,hannunta ta janye tare da cewa kan uban can kai,yarinyar nan batasan wace ni ba amma zanyi maganinta,shi kuma wai ya bita ya wulakantani to wai ma wace wannan?zan bincika.
Abun zaman da aka tanada a wajen suka zauna cikin daya aka kawo musu lemuka da chicken's shawarma Masoya mata da miji sai love suke Sha a wajen ana soyewa,Salma taga wasu Arna mace da namiji sun rungume juna tace Yeee ai Allah Raheel yana yi min irin wannan,can wani ya zauna ta kwanta saman cinyarsa,aaaaaa....wannan ma indai yazo sai na kwanta a cinyarsa cewar Salma,kai kaga wancan ma tab ai duk muna yin irinsu,ta nuna wani yana hurawa wata chika Ido tace an wuce wajen tun ina 5yrs yake min wancan,lemonta ta zuka tare da kallon Na'im tace kai a duniya ana dadewa fa mantawa akeyi,ai ko ni naga yau naga jiya na gobe nake jira kawai,Na'im yace kin San sunanki?tace sai ka fada yace dan Iska indai ko kana da gaskiya duk wannan kina yi tare da Raheel to Ku duka dan iska ne( sunan Salma yar iska itama wai indai duk wannan da ta fada sunayi ita da Raheel to su yan iska ne)
Dariya Salma ta dingayi tace to ai Bana Jin komai ni.tabe baki yayi gaba daya yaji kishin Raheel dole ma yayiwa Salma maganin Raheel,Raheel ne ya fito ya zauna gefen Salma itace kadai take ganinsa komai har kayan iri daya dana Na'im sai taga Raheel guda biyu gefenta Na'im dayan Raheel,Na'im yace gobe zaki fara sallah kullum tare zamuyi,kafin ya gama magana Raheel yace karki yi karyane,Kawai sai ta kalli gefen Na'im ta kalli na Raheel ma kowanne da abinda yake fada mata,Na'im yana zancen Sallah da maganin da zai fara mata yaje wajen wani me maganin Aljanu,Raheel yana hanata karta yarda indai ta yarda sai ya bata wahala zai kasheta ne gaba daya ko ta haukace kuma sai ya dauketa daga gidan su Na'im ya batar da ita,yana gama fada ya bace bata. Na'im dagashi Sai Salma yake gani a zaune,Salma ta fara kuka tana yankani zasuyi,zan haukace.
Na'im yace wlh kome za ayi sai dai ayi amma magani ba fashi nama fasa sai gobe a yau za a fara da dare dole ta rama sallolin yau.
Gida suka dawo ya samu Mummy na jiransa ya duba Aisha,Salma ta gudu dakinta ta buya harda sa key,yana duba Aisha yace giya tasha me karfi tayi mata karfi tana da Allergic da ita shi yasa ta kumbura mata lips magunguna ya bata ya wuce ya bar Mummy da bacin rai,
Yana komawa daki yaje ya shirya tare da daura Alwala yaje yasa spear key ya bude dakin Salma tana saman Bed,ta Mike firgit zata gudu ya damkota zata makaleshi ya matsa can zata iya karya masa Alwala,jawota yayi yace a dakinki zakiyi Sallah,har toilet ya kaita tana kuka da komai tayi Alwala dole,ta fito ya shimfida mata sallaya,ta fara Sallah idan tana karatun rai rai sai bakinta ya harde yaki buduwa bare tayi karatun Sallar,yace wlh sai tayi haka ko baza tace komai ba,haka da kyar akayi isha,magrib,da sauran na rana guda,tana gamawa ya dauko ganyen magariya ya zuba a ruwan ya tofa mata ayatul qursiyyu kafa bakwai,Amanar rasulu bakwai,falak,nas,Iklas,fatiha kafa bakwai ya bata tasha taki yayi yin duniya taki Sha,riketa yayi ta karfi tana tsaga ihu kamar ana yankata,Irfan ya shigo ya karbi maganin Hunaif ma yazo suka riketa ta karfi suka dura mata tana burbuwa aka matse mata baki saida ta hadiye tas sannan suka saketa ta dinga tsine musu a gidan ba wanda bata zaga ba.
Ranar kwana tayi tana Aljanu, da safe da wuri Na'im ya kara zuwa ya mata turare da Habbatussauda sai lokacin ta daina,ya lasa mata wata a baki,tayi shuru ta nutsu tana zaune ta rakube a gefe daya,Qur'ani ya mika mata yace ta karanta aiko ta karba da kyar tana karantawa ta danyi da yawa ya karba ya tafi,yinin ranar kaf bata kara lekowa ko main Palo ba,abinci ko an kai mata baza ta karba ba,ta wani manne a jikin bango kamar Almajira kowa ya shigo tsoronsa takeyi kana bude kofar zata firgita jikinta ya kama karkarwa,tun safe Na'im bai dawo dakin ba, ko wanka bata yi ba taki cin abinci kuma tana Jin yunwa amma Mummy ta kawo mata baza ta karba ba,Irfan ya dinga lallabata sai dai ma ta saka kuka haka suka gaji suka kyaleta idan Na'im ya dawo ya gwada nasa basirar ko zata yarda.
5pm ya shigo gidan saida yayi wanka ya shirya yaci abinci sannan Aisha ta fada masa Salma bata ci komai ba,abincin ya Eba ya tafi room nata,tana ganinsa ta kalleshi tayi murmushi yana mika mata ta karba taci ta koshi ya karo mata ta cinye tasha ruwa sannan ya nuna mata toilet taje wanka,kafin ta fito ya zabo mata kayan sawa Riga T-shirt fara me hoton mace da gashi,dogon wando ya Ciro mata pencil me kyau dark blue,pant da bra ma du ya Ciro mata,da gudu ta bude toilet ta fito daga ita Sai towel a guje kamar wani ne ya korota tana fitowa ko wankan ma bata fara ba tacewa Na,'im mutuwa zanyi yau wlh bleeding nakeyi ka gani ina zuwa toilet naganshi zuuu,kafafunta ya kalla jini ke sintiri, period kika fara ba kin taba fada mini ba baki Period shine yanzu ko kina mantuwane? Sai lokacin ta tuna tace to kaje ka siyo pad mana ka tsaya kana kallo na,Ke kinfa rainani ni danki nake ne da zaki bani command haka?to zauna karka siyo wlh ba ruwana haka zan zauna kuma nasa kayana,murmushi yayi wa kika yiwa to? Kanka mana tace, a jikina yake knocking da akayi shi ya katsesu yaji muryar Irfan da sauri ya tura ta toilet ya bude masa kofa,Irfan ya makawa Na'im harara yace wannan jininfa a kasa dis dis? ka takurawa yarinya ka jawo sai tsoronmu takeji.
Na'im Bai saurareshi ba ya fita me aikinsa wacce ke gyara masa part ya aika ta siyo masa ta dawo,yana shiga ya kwankwasa mata door din toilet yace hannu kawai zaki miko,ta bude ta karba ta kulle ya bar mata room din.
Washe gari har yamma bata leko ba tana Bedroom abinta,Na'im tambayar Mummy yayi Salma bata fito ba?tace ae yanzu ma rufe ido takeyi idan ta ganmu,murmushi yayi ya shiga room din samunta yayi tana kuka ta kalli sama ta daga hannu tana addua tana kuka Allah ka yaye min wannan period,wannan jini ya isheni Allah ka yaye min har Abada,tana jin ya kara zubowa ta kara barkewa da kuka tana Allah ka yaye min na daina yi har abada.
Na'im yana jikin kofa ya harde hannaye a kirji yana ta dariya marar Sauti sai da ya gaji addua taki ci taki cinyewa,Yace a abin arziki bakiyi addua ba sai a wannan,kin San ma ba karba Allah zaiyi ba,ku da akayi muku gata kuna kara lfy,yana cire muku cutuka shine kike Butulu (butulci)
Harararsa tayi sannan taci gaba da adduarta sai dariya yake,saman bed nata ya kwanta yana jin addua Allah yaye mata jinin Haila yana ta dariya duk kalma daya in ta fada sai yayi dariyar wannan shirme.
Da dare ma da ta shiga wanka taga ma karuwa yake kawai ta dinga kuka har ta fito idonta jajir kuma wai kyankyamin kanta takeyi bata iya cin abinci da kanta Sai dai Aisha ko Na'im ko Irfan idan Allah ya kawo wani ya bata taci,Mummy ma tana bata a baki sai taci,yau ma Mummy ke bata saman Dining tace sorry kinji zaki daina ne idan kika saba su Na'im duk suna wajen dama Salma Ido ya kumbura yayi jajir tacewa Mummy ni bazan saba ba Allah,Aisha tace aiki ya samu mata to ya kike so ayi miki in bakyayi ma ai da kyar in zaki haihu,Salma tace ni ina ruwana da yara Bana sonsu indai akan haka ne,Na'im yace kyaleta Aisha taje ta mutu idan tanawa Allah butulci Irfan Ya kara da kuma batayi aure ba ta mutu tab,Salma hawaye ya gangaro mata tace ai yan matan gidan Aljanna zan zama kamar zata narke haka take magana,Mummy tace kyalesu kinji ci abincinki.
Ummitu kuwa tunda ta gama yiwa Salma masifa ta juyo tare da jawo ledar tsire taga wayam ba komai ta fara salati da sallallami Affa yana shigowa tace kagani ko da kudi ne da tuni ma shigowarta Aljanunta sun sace ta talauta mu,gwara da ta tsaya a naman oh kaga jarabar yarinya azzalima,ta zalincemu Affa sabo da bacin ran da Salma ta kunsa masa ko magana kasa yi yayi.
Ummitu tace je ka duba kudin da ka ajiye a kasan gadona,Affa yace af bari na duba me farar kafa yau ta shigo gidan,Shi kuma kudin an samu matsala tun jiya da Affa ya ajiye bera ya dauka namane yaji kamshin nama a jiki kawai ya janye kudin ya kai can dai dai Raminsa na kasan gadon Bai ci komai ba suna nan lfy amma suna bakin ramin bera,Affa da Ummitu neman duniya ba a ga kudi Dubu uku ba nan suka dinga salati Affa yace kin gani ko Allah ya Isar min tsakanina da wannan yarinya ubanta ya jona mana masifa,dan wannan masifa ce, nan suka dinga zage zage.
Yau kwana Uku da fara period din Salma kullum bata da walwala daga kuka sai adduar Allah ya yaye mata,Na'im yace ta shirya suje gidan Dada yawo wai ko zata ji sanyi,tace to ka siyo min Pampers, baki ya bude me zakiyi da Pampers ai sai yara tace uhm to ai pad tayi min kadan sai a gida zan na sa pad tsoro nakeyi kaga kuwa idan Pampers ce