Showing 114001 words to 117000 words out of 127542 words
das das har toilet din Na'im da dakin ta gama gyarawa gadon da yake kaine kawai bata gyara ba ko ina ya dau kamshi da sheki,room dinta ta koma tare da salla wanka,ta shirya cikin kana nan kaya wando crazy Jean fari Kal pencil sai Riga peach color me dogon hannu sama ta Dame kasa ta dan bude kadan iya mazaunanta ta tsaya,ba karamin kyau Salma tayi ba sabo da kyan diri da surarta,ba wata kwalliya tayi ba powder da red jambaki ta shafa sai kwalli da ta zizara tasha kyau ba a cewa komai sai kamshi ke tashi ta ko wanne lungu na jikinta,da sauri ta koma bedroom din wayam taga ba Na'im saman bed,karar ruwa taji a toilet ta gane ya shiga wanka,kafin ya fito ta gyara bed din tare da kara gyara dakin neat ta zabowa Na'im kayan da zai sa tunda fita zaiyi zai je office yau.
Yana fitowa yana murmushi Salma da wuri ta karasa tare da goge masa jikinsa ta shafa masa mai tana masa hira me dadi cike da kalaman so,fes ta shiryashi cikin kana nan kaya yaci Uban kyau na ban mamaki,tana yi tana duba time ta daukar masa komai da zaije dasu Hospital tare da Jan hannunsa zuwa dining ta bude abinci iri iri sai kamshi suke,Na'im ya kalleta tare da daga mata babban yatsa kin hadu Sweetheart ta ko ina thts y I always love u,kin San me ya kamata,Salma tana murmushin jin dadi ana yabonta ta kara kasa da murya tana zuba masa Abinci tace honey Bana so ka makara fa kalli time kace 10am kake so kaga patients duba 10am ta kusa,Kallonta yake ta faman yi yanda ta birgeshi tayi kyau komai nata me kyau ne,ga iya wanka,ido suka hada da sauri ta dauke nata idon,sabo da wasu taurari da take gani a cikin idonsa suna kashe mata jiki tana susucewa ta kasa control na kanta, yace ko dai kin gaji dani ne Sweetheart? Naga sai sauri kike kina murna na bar gidan,murmushi Salma tayi ta dan kalleshi tace taya zanyi murna Honey ban son kayi wasa da aikinka ne amma ai buri na bai wuce mu kasance tare ba,babu yanda zanyi ne shi yasa,hanyar da kake nemo mana ai dole na goya ma baya amma ni in zakaje dani ma zan bika pls.
Murmushi ya saki na birgewa tare da kashe mata Ido daya yace got u Dear.abincin ta shiga bashi itama tana ci har suka gama sannan ta daukar masa wayoyinsa suka fita har inda motocinsa suke kala kala ya zabi wacce zai hau,Salma tace Honey da kanka zakayi Driving? Driver yana waje nace ya tsaya taya zan barshi kin zo rakani ya kalle min ke shi yasa nace ya jirani a waje sai na fitar da motar da kaina mu wuce,alright cewarta, a jikin motar ya rungumeta ya dinga kissing dinta ba adadi da kyar ta kwace sukayi Salma sosai sannan ta koma ciki shi kuma Ya fitar da motar Driver ya karba suka tafi.
Tun a motar basuyi nisa ba ya kira Salma ya kusa karasawa,da yaje ma ya fada mata ta masa addua,ya fara duba patients wani lokacin sai ya kasa sabo da tunanin Salma sai ya kirata a waya yaji Muryarta sannan yaci gaba,haka Salma ma da taji shuru zata nemeshi taji lfy.
2pm Salma ta kira Hello Honey am just missing u kaki dawowa na gaji da jira ni kadai gidan so bored ba dadi,pls ka dawo zanyi kuka,No..no..karki yi kuka kinji zan dawo aiki ne ya rikeni sai wurin 5pm ba yanda zanyi Operation zanyi kin San aikin Babyna ceton rai kiyi hakuri,ok ba matsala to naje gidan Zainura? a'a ba yau ba sai weekend zamu je tare,kukan shagwaba ta fara masa da kyar ya lallasheta ta hakura,sai jiran Na'im akeyi yazo a shiga Operation yana ta faman lallashin matarsa,har mamaki ya bawa Doctors,Doctor Aliyu kuwa dama ya dauki Hutu bazai je aiki ba sai yayi 3wks.
Irfan ma yau 6days da aurensu da Zeena,Zainura dama ita ba Ganda ga saurin aiki,nan taje ta shiryashi tayi komai ya fita Office,abin haushin Irfan baya hasala komai sai chat da Zainuransa yana ta dariya shi kadai,daya gaji ma fitowa yayi tare da barin building din ya shiga mota ya koma gida,1:30pm ya tsaya a masallaci tare da Gabatar da Sallah ya shiga gida,tana jin karar danna password dama tasan da zuwansa cikin wata gown take iya rabin cinya tayi mugun kyau kamar a saceta,da murna ta rungume abinta lips dinsa ta kalla wanda suke zautar da ita ta shagala tana kallonsu,a hankali ya matso da fuskarsa hancinsu na Gogan na juna sabo da Zainura ma akwai hanci me tsini da kyau,kamar zai cinye mata lips haka ya shiga tsotsarsu,Zeena yanzu expert ce a nan bangaren hannayenta biyu tasa tare da sakalo wuyansa tana nutsa yatsunta cikin sumarsa,sun dauki lokaci me tsawo a haka sannan ya zare bakinsa a nata suna maida numfashi kamar wanda sukayi dambe,Zainura bata koshi ba tasa hannu wai dan Iskancin Zainura ma kunnensa biyu ta ruko tana da matso da fuskarsa saitin tasa yana dariya wannan wani new style kika samo ban san dashi ba?Itama dariya tayi sannan tace kunnenka nake tsoro kar ya tsinke sabo da dadi shi yasa na rikesu sai lokacin ta saki kunnuwan ta tallafi kumatunsa da hannun biyu ta kara hade bakinsu wannan lokacin ita take masa salonta iri iri,a hankali tayi masa magana a kunne tare da zura harshenta ciki nan take Irfan ya zauce ya dauketa sai bedroom tun kafin su karasa bedroom din sukayi watsi da kayan jikinsu,da Zafi zafi cikin Zumudin juna suka fara kashe Kansu da kauna tare da shauki.
Hunaif kuwa suna shopping tare da Afrah dinsa,Afrah bata saba da wahala ba komai sai dai ayi mata,girkin ma kadan takeyi sai taga dama,sam Hunaif kuma shi ba haka yake so ba yafi so ace matarsa bata da kyuya,ta dinga dafa masa Abinci,Afrah bata da wata matsala in banda ta kyuya komai sai dai dan aiki yayi sabo da haka ta taso,Hunaif kam yace dole ta Mike shi bai son haka,har fada sukeyi watarana kan hakan,tunani yake wa zai iya gyara masa Afrah,Salma bata cika shiga sabgar wani ba,Zainura itace zata iya,nan Hunaif yace dole zai sa Zainura kullum ta dinga zuwa gidansa idan Irfan baya nan ta gyarawa Afrah Zama,yasan ba sai ya fadawa Zainura matsalar ba tana gani Afrah ta shiga uku da ita.
Aisha ta Kamu Da son Doctor Aliyu gaba daya,dama Na'im ya fada masa kar ya sake ya bar Afrah da frnds,kar ya bari suzo masa gida kuma kar ya barta taje,Aliyu haka ya saka mata mugun tsaro,sai yanzu take ganin Ashe da hauka takeyi tana Kula mata suna lez Ashe duk bata lokacine da dabbanci takeyi,yanzu Istigifari take sosai tana farantawa mijinta bata fita ko ina,ko gidan su Zainura da wajen Mummy da tace zata je,Aliyu ya Sanarwa Na'im,Na'im yace kar ya barta ta fita ko ina yanzu sai nan da watanni shidda,shi dai Aliyu bai San me Aisha ta aikata ba,yasan dai tana kule kulen kawaye da yawo amma su Na'im sun rufawa yar uwarsu asiri basu bari kowa yaji sirrinsu ba balle ace watarana miji a samu matsala ya mata gori ko wani abu,shi dai Aliyu tunaninsa duk sabo da Aisha macece shi yasa suke bata kulawa,yanda Aliyu yake kaunar Aisha ko a gidan karuwai ya ganta ya rantse shi sai ya aureta ba ruwansa da wani Aisha sai ta Zama Virgin ko tayi kaza haka Allah yasa masa Sonta badan wani abu ba.
Ummitu ana karbar wahala sai abinda yaci gaba,A wannan lokaci Affa idan ka ganshi baza ka ganeshi ba,ya fita daga hayyacinsa,wannan ciwon har karamar hauka ya sashi,domin surutai yake barkatai marasa kan gado,Masa'udu dan Uwansa yace ya gaji su tafi gidansu su zauna zasu dinga aiko musu da abinci,Ummitu tasan korarsu kawai yayi amma ba yanda suka iya haka suka tattara suka koma gidansu,Ummitu ita ke zuwa gona ta samo itacen da zasu danyi girki,yanzu sana'ar sirfe da daka takeyi a kauyen suna samun na Koko da kosai,Affa ana daki ba fita ba shiga komai sai dai ayi masa,Ummitu tana cin bakar wahala tayi kuka har ta gode Allah,kullum idonta jangame da hawaye basa tsayawa,sai suyi sati basu daura tukunya ba,sai dai gidan me gari ko yayarta su aiko musu da abinci sabo da tausayi,Masa'udu kuwa yana fadawa Harira ta kai musu abinci amma sai tace ta kai kuma karya take,Ummitu da Affa suna ganin rayuwa sai yanzu suka San cewar Lokacin da Salma take gidan suna ganin suna talauci basa godewa Allah Ashe cikin wadata suke basu sani ba,sai yanzu suka San Talauci,da ace ma Affa da lfy da sauki,ina ma Affa zai samu Lfy ko da talaucin su Zauna sun godewa Allah.
Affa yana daga daki haukar tasa ta motsa magana yakewa Ummitu Yaushe Alhaji Zakari ya mutu? Ummitu tace tun yaushe Zakari ya rasu ai yafi shekara ashirin da mutuwa,da kai fa akayi komai na zaman makoki amma yanzu ka tambaya?Affa yace yanzu Zakari ya mutu ba a gaya min ba sai ya fara kuka sosai,wata tazo ta kawo dakan gero ta tafi,Affa yace wacce doguwar matace ta wuce min daki? Ummitu da mamaki ta kalleshi tace Hajiyayye ce fa makwaftanmu,kuma ba daki ta shiga ba fita waje tayi gidansu, wace Hajiyayye ban Santa ba? Affa ya tambaya.
Yace Ummitu ta fito dashi waje zai sha Iska ta fito dashi kuwa yana kwance,yake nuna ledoji yace sai an dauko masa suna bin iska,idan ta dakko yace a wankesu a ajiye idan na mutu sai ku zuba Wainar Sadaka a ciki,Ummitu ya bata tausayi ta fara kuka,ya dawo yace sai ta nemo masa me daukan photo dake kauyen,takanas taje har shagon Buba me hoto ta kirashi da camera,Affa yace ya daukeshi masu kyau sai da aka dauki kala biyu Buba ya tafi,Affa ya kalli Ummitu da kyar ciwo yana cinsa yace wannan Hoton ke na daukarwa shi idan na mutu sai ki kalla,wannan gidan nawa tunda Allah bai bamu haihuwa ba na bar miki shi halak malak,ragowar gonata guda daya duk nakine Ummitu na gode Allah ya miki Albarka kinyi kokari kina ta dawainiya dani,Ummitu kuka take kamar ranta zai fita gani take da gaske ne Affa rasuwa zaiyi sabo da ciwon an kwashi wurin 6mnths har yau yaki warkewa,ba kudin asibiti,shi kanshi Affa wannan lokacin sai da yayi kuka sosai na tausayin Kansu.
Yau asabar yaune sati hudu da kai su Salma Amare sabon gidansu wanda suke kwasar love,yaune kuma dangin Salma na Maiduguri sukayi waya tare da sanarwa Mummy gasu nan a hanya anjima zasu karaso Abuja,Sabo da dama Salma ta basu address da komai na su Mummy,Mummy tayi murna tare da duk Masoyin Salma,Salma tunda taji labarin tafi kowa murna ta gigice sabo da dadi,ga Na'im yau weekend yana gida amma taki saurararsa sabo da murnar da take ciki itama yanzu tana da yan Uwanta,sai shige da fice take ta rasa ma me zata shirya musu,Na'im ba abinda zaiyi sai na ya taya Sahibarsa murna,da yamma suka sauka gidan Mummy sun samu tarba ya gaske,su Kansu basu taba ganin gida irin na Mummy ba yanda ya hadu,mamaki suke wai Allah ne ya daukaka Salma take wannan daula ,ni kuwa nace ai gidan Mummy ba komai bane kallon duniya na gidan Amare,Malam da Umma sune gaba wurin saukar su Malam Musa dasu Shehu,sunci sun Sha sun nutsu sannan Malam,Umma,da Mummy suka kara basu labarin komai na Rayuwar Salma da tayi,duk da cewar suma sun sani amma sai yanzu suka kara fahimtar abin,sosai suka dinga yiwa Malam da Umma godiyar rike Salma tare da Mummy itama,anyi addua sannan Salma da Na'im suka karaso gidan Mummy cikin shiga ta alfarma,sun gaisa da juna sannan su Shehu suka dinga bawa Salma hakuri suka bawa Na'im ma kan abinda suka masa da yaje neman Salma wajensu sanda ta bace,Salma cike da murna tace ya wuce ita dama bata rike kowa ba,kuma komai ta yafe koma mene har Gadonta duk ta yafe,da Murna ta nemo su Zainura a waya suka zo dukkansu har Afrah suka ga yan Uwanta suka gaisa sosai har su Irfan,sannan driver ya kaisu gidan su Amare Salma,sunsha kallo sun gigice sabo da haduwa gidan, kwanan su Uku a Abuja Maimuna da Iklima sun samu kaya sosai wajen su Salma da Zainura har Afrah,kudi da abin arziki suka tafi dashi gida lfy,sai watarana kuma Salma zata je musu suma,Salma an shirya da family itama yanzu tana waya sosai da yan Uwanta musamman Shehu kanin Babanta yana yawan kiranta,Sai Hashim,Na'im kuma Bai son Hashim ya dinga kira masa mata tunda yaji Dan uwan Salma ne kuma ba muharrami ba akwai aure tsakaninsu shike nan ba dama suyi waya dashi sai yayi ta faman kishi yana fushi ana ji masa muryar mata.
Salma ta sani kawai sai ta shareshi har ya gaji da fushinsa ya hakura,yau ma Hashim ya kirata suna gaisawa yana hadata da dangi suna gaisawa,yace mata kuma Na'im yaje shekaran jiya,ya bada kwangila za a canja musu gidansu na Zamani ya bawa ko wanne namiji jari me karfi both dangin uwar Salma da na ubanta,Salma tayi mamaki yaje har can bata sani ba dama ranar yace mata zaije meeting Maiduguri dama ba meeting bane abinda yaje yi kenan,dadi da farin ciki ya kamata,son Na'im ya kara mamayeta ta ma rasa me zatace,suna waya da Hashim ya fito yana latsa waya duk ya bata rai,Sallama tayiwa Hashim tace sai watarana kuma in sunyi waya.
Ta kalleshi ya daure fuska kamar bai taba dariya ba,Hannunsa Salma ta rike tare da hade yatsunsu waje daya,Honey lfy naga ranka ya baci? Me ya faru dan Allah ka fada min,Na'im cike da shagwaba kamar yaro yace ni...Bana son kuna waya da wannan Hashim din,bana Zarginki don't misunderstand me kawai kishi nake ji tunda dan uwanki ne ba muharaminki bane,sanda naje nemanki ma duk ya damu da bacewar ki lokacin,komai naki baya ganin laifinki,da anje da zancenki shi zai tsaya ya wuce gaba ya saurari lamarinki haka kawai ni tsoro nake ji yaje ko Sonki yake ji a ransa yazo ya dinga ji min muryarki a banza,komai yace Salma aikin banza yaje yace wasu matan mana ko su Iklima ai suma yan uwansa ne matan yan Uwa kuma amma ni sai Salmata,gashi kuna kama dashi wlh kyakyawa dashi dan ma baiyi wani boko ba iyakarsa secondary Ashe amma yanzu na nemo masa admission a University na Maiduguri naga yana da brain,dariya Salma tayi tare da cewa kaima kana ganin kamarmu da Hashim Ashe?Wlh kowa haka yake cewa,ai cousin dina ne ,Da farko fa bama shiri dashi fada muke sosai amma yana da hankali ai,matsalarsa kawai yana dan yiwa matarsa ba dai dai ba amma Malam ya masa nasiha yanzu lfy suke zaune ya daina shirme.
Ni ki daina yabonsa wlh ba ruwana da hankalinsa ni dai ki rage waya dashi ki daina dadewa kuna gaisawa ki kashe ko kice aiki kike,Salma kawai tace to na daina ba matsala in dai akan Hashim ne ka shafawa kanka ruwa pls,naji Ashe gidanmu kaje ban sani ba,duk ya gaya min abin arzikin da kayi musu Na gode Allah ya kara arziki da Budi,Allah yasa kafi haka,Na'im ya Mike yana cewa ki daina min godiya na fada miki shi yasa Bana son na fada miki abinda zanyi zaki fara godiya,to addua fa nayi Honey,Ameen yace ya haura sama yana jin dadin adduar da Salma ke masa.
Zainura ma ba Irfan ne yaje ya gyarawa iyayenta gida ba Na'im ne bai yi shawara da kowa ba yaje ya aikata komai tare da kara musu jarin noma,sai labari Zainura taji,ta sanarwa Irfan yace ai mu haka muke family dinmu idan naga dama zanwa dangin Salma abu ba sai na fadawa kowa ba,Zainura har Na'im tayiwa godiya yace ai ta Zama family nasu duk Wanda ka aura to kun Zama daya shima ya Zama danginka,Irfan kuma ya biya musu aikin Hajji gaba dayansu Har Hunaif da matarsa,Salma da Na'im Saura 4mnths su tafi kasa me tsarki daga nan zasu je Lebanon wajen dangi da kuma Uk sai su dawo Nigeria
Hunaif takanas yaje wajen Zainura yace dan Allah idan Irfan baya nan ta dinga zuwa wajen Afrah duk abinda taga Afrah tayi ba dai dai ba ta tabbatar ta gyara mata Zama,Zainura ta dinga dariya bata kawo komai ba ta dauka wasa yake tace to insha'allah,yau kuwa ta sanarwa Irfan yana fita Office ta gama komai nata ta shirya ras ta dauki wani hadadden keken Irfan da yake fita exercise dashi kullum,irin kamar na yan tseren keke,dama ta iya kekenta tun a kauye ta fito dashi sanye take cikin doguwar riga baka hadaddiya me adon Golden da wando tight a jikinta golden,kamar Balarabiya haka ta fito ta hau keken Irfan fiiiiii ta kai kanta part din Hunaif,Afrah tana sama ta hango Zainura a Keke ta window ita kanta abin ya bata dariya da sha'awa Zainura kamar wacce take turai,tukin keken ma iri iri takeyi har tukin carrier takeyi har tazo gidan ta danna bell,tuni Afrah har ta bude mata kofa,ta shiga suna ta hira cikin harshen turanci, taga Afrah komai sai dai yan aiki suyi mata,girkin ma ba sosai takeyi ba sai taga dama,idan taga daman ma sai tayi wanda baza ka iya ci ba irin na Larabawa ko tace Wai tuwon Dabino da miyar Kubewa danya zatayi,kubewar ko yankawa baza ayi ba haka suke tsumbulasu guda guda wai anyi miya,ga kuma tuwon dabino hhhh,ko ta kawo ganye kawai da gurasa ana karyar wani green pepper,Zainura tace a bata abinci ai kuwa da murna tace yau tuwon Dabino miyar Kubewa za su ci yana cikin