Showing 15001 words to 18000 words out of 127542 words

Chapter 6 - Kamarsu Ce Daya 1 Hausa Novel Complete

17 Nov 2024

381

ya kalla yaganshi ma kamar ya warke shuru yayi mata baice komai ba,kunya da dariya ta kamata ta dinga kunshe dariya tayi kasa da kanta tana duba yatsunta masu kyau,ya rasa me takewa farin ciki,tana ta faman murmushi da jin kunya yau wannan salon tazo dashi kuma.
Kallonta yayi cikin kasa da murya kamar me rada tare da cewa ya akayi? sai ko ta rufe fuska da tafukan hannu,tana ta murmushi sai da tayi ta koshi sannan ta bude idonta tare da cukulewa kuma irin ba wasa, kin iya hada Coffee? Yeah ta fada da karfi,yace good kinga machine can da komai ciki jeki hado mu gani,
Sai da ta dafa kafadarsa ta sauka kasa coz wajen yayi mata tsayi,tana zuwa sharp sharp ta hada masa a glass cup na tea,ta kawo masa ya karba tare da kurba yaji wani shegen dadi,muryarta yaji tace da dadi? Sosai ma cewarsa,hmm kawai tace,ya tambayeta a ina kika koya?kuma a kauye kike fa? Raheel ne ya koya min komai du na iya,baki ya tabe ke komai Raheel baki komai sai da Raheel,everything Raheel,kamar gidanku daya i can't understand am so confused, Salma tayi warr da Ido ni kuwa ina ganewa ai,must ai dama cewar Na'im.
Zauna na tambayeki amsa kuma nake so me ma'ana,zama tayi a kujerar dake facing nasa,yace bani labarinki,tun mutuwar iyayenta da masu riketa,da Raheel,danginta duk ta iya bashi labari,yace kina kauye ya kika iya turanci haka?kika iya kwalliya da shiga,kin iya komai why?haka ta faru?tace ni Raheel ne ke koya min fa,cikin dake jikinki wa ya miki?Raheel ne ya saka min ba yimini yayi ba,Countries da kike zuwa kin San duk kasashe ba adadi wa ya kaiki?da wanne kudin? Nan ma Raheel,komai Raheel,tun kina 3yrs Raheel,everything Raheel ta tabbata Raheel ba mutum bane kenan ko?,

Kuka Salma ta fashe dashi ita dole fa Raheel mutum ne,zaka ce ba mutum bane kaine Aljani ba shi ba,ta dinga masifa ba ji ba gani wai yana zagin Raheel,tsaki yaja tare da cewa bani Address din gidanku Driver na ya kaiki gida wajen iyayenki ni bazan iya ba kin fiye shagwaba da yawa ,Raheel ne yake shagwabani fa kuma ai Mummy tace ka bari ta dawo,baki da matsala baza tace komai ba gobe za a kaiki gidanku, baki ta cuno wlh bazan tafi ba Raheel ina tare da kai.
ko an kaini sai na dawo wajenka.

Numfashi yaja kene Mayya?ya tambayeta,ni ba mayya bace,to kene Mannira?dariya tayi tace sunana Salma,yace no...no yana dacewa ace iyaye naka Mannira suka sa miki ko mayya,kaine Dan Fulani masu shaniya da noanoa?,yes muna da shanu da Nono kana Sha?baki ya tabe Kazami.. kazami kune Bana so na Shaniya sai na kwali Holandia understand?ni sai na dura ma na Saniyata ka shanye,hannu ya fara karkadawa wai no...no bazan Sha bama na kulle bakina harda tsuke dan bakinsa,Dariya tayi sosai,ya tsaya yana kallonta, Raheel me yake damunka ne? Kana ce mini Raheel ba shine ba,Na'im ne ni,aiki..aikina inayi kazo kana damuna pls back to ur Room banma san Why na kiraka nan ba kana damuna cewar Na'im.
Kida ya kunna na turanci a wayarsa nan take Salma ta fara bin wakar kamar ita ta rera har kada kai takeyi.

Affa da Ummitu suna can takaicin rashin ganin Salma ya ishesu ga talauci,can Affa ya kokawa yan uwansa matsalar da suke ciki tare da abinda Salma takeyi,nan take yan uwansa suka hadu suka zugashi, shi yasa watarana ma shawara da wasu matsala ce, cewar Salma idan ta dawo ya koreta kawai yayi mata korar kare Domin zata kasheshi tun kwanan sa Bai kare ba,ya dawo ya Sanarwa Ummitu,itama ta gano zancensu gaskiya ne tace Malam wannan gaskiya ne ka duba farar kafa irin ta yarinyar nan tunda aka bamu ita kullum talaucewa mukeyi bamu taba ci gaba ba,munfi kowa talauci a garin nan namu,yanzu akan nema mata magani duk abinda muka mallaka ya kare,saniya ko daya babu,kayan dakina,gonakinmu duk sun kare tas,a abinci har makwafta taimakon mu sukeyi kullum talauci yaki ci yaki cinyewa sai yawan Shan garin kwaki,duk ya tsotse mana jini da ruwa,Uban Salma mahaifi ya zalunce mu dama yasan yarsa haka take Ashe ya lika mana ya mutu ya barmu da wahala..shi yasa yan uwansa suka ki riketa.
Affa ya nunfasa yace yanzu na tsani yarinyar nan wlh Bana kauna na bude Ido na ganta a gidana,dama kaddara ce tasa na dauki jaraba,tunanina munyi yar kirki Ashe jaraba muka Raina da hannunmu,
Bamu karu da ita ko tsinke ba sai raguwa,Allah ya gani munyi iya yinmu munyi na Allah munyi na Annabi munyi na Binta dan haka taje can tayi yawon duniyarta,wannan rainin hankali ne yarinya gantalalliya cewar Ummitu.

Affa yace ko ta dawo idan kika barta ta shigo min gida to Allah ya isa ban yafe miki ba,na gaji da talauci,Ummitu tace oh Ashe gaskiyar bahaushe da yace tsintacciyar mage bata mage mun karbi Bala'i da hannunmu,Affa ya kara da ni dama Bana kaunar rike dan wani,dan wani ko jaraba Allah bai bamu ba mu hakura,dama dan kar nace ban so ne kice wani abu shi yasa nayi miki kara naga kina sonta.

Ummitu ta tafa hannu tare da cewa yo aini ta Dade da sire min dama kwadayin yara yasa na karba jaraba ai zamu yarda kwallon mangwaro mu huta da kuda,nan take shedan ya kara dasawa Affa da Ummitu kiyayyar Salma a zukatansu suka ji ba wacce suka tsana a duniya sama da Salma,suna ganin cutarsu ma takeyi tun farko.

Dan Adam kenan bashi da tabbas,yanzu da Salma bata samu matsala ba ko Allah yasa suna daukota kudi suka samu ta hanyarta ko wani abu da yanzu basu da sama Salma, baza suce komai ba, amma an musu kyautar ya guda tsakani da Allah sabo da kaddara ta sameta ta shafesu suna furta kalamai munana,dan Adam me manta alkhairi,inama Tall Man Baban Salma Bai rasu ba yaga cin Amana,butulci da manta alkhairi wajen Affa da Ummitu,farko sunyi bajinta amma at the end sun kasa jure kaddara wanda ita kanta ba ita ta dorawa kanta ba,
Yanzu da yarsu ce ta cikinsu baza suce komai ba ta Zama dolensu,dole su hakura su karbi komai,kuma baza su taba tsanarta ba,amma wannan sabo da basu San ciwonta ba basu San zafinta ba sun zobe ladansu wajen Allah,dama haka dan Adam yake bashi da tabbas kuma ba a iya masa musamman zamanin da muke ciki,daga naka sai naka,naka iya naka,kowa kansa ya sani baza ayiwa wani Uzuri ba.

Tun daga wannan rana Affa da Ummitu suka shiga bata Salma a cikin wannan kauyen,duk inda suka shiga sai sun zagi Salma cewar ko Sallah bata yi ga bin maza,bayan sun tabbatar aljanu gareta amma saboda kar aga laifinsu kar a zagesu idan sun kori Salma sai suka fadawa duniya cewar cikin shegenta yafi uku ma,sune suke rufa mata asiri suna kaita can Borno wajen danginta tana haihuwa sai ta dawo wasu kuma aka zubar.
Mutane Fulani na daji da jahilci sun yarda sabo da duk wasu shedu sun samu sabo da Salma duk wani sign na cikakkiyar yar bariki Aljani Raheel yasa ya fito fili an gani wanda a zahiri ba haka abin yake ba,kuma su Affa sun San gaskiyar magana.

Nan garin ya dauka duk majalisa zagin Salma akeyi haka mata ma ana tsine mata,mutanenmu hausawa basa yiwa mutum addua ko aji lafazi da kyakyawan zato idan ya aikata mugun abu kawai sai dai a fara tsinewa mutane ana aibatasu ana zaginsu,ba Uzuri kuma mutum baya hango nasa laifin sai na wani,abin haushi ma yawanci zargine kawai ba tabbas a kan abun.

Affa da Ummitu Rashin Imaninsu bai tsaya iya nan ba,Tall Man ya rasu hankali kwance tunaninsa ya tserar da yarsa daga wahalar duniya zata samu rayuwa me kyau ashe an bar baya da Kura ba a sani ba,shi yasa mutum bashi da wani Plan sai abinda Allah yayi.
Afda suka ce ta inda aka hau ta nan ake sauka muje Borno kawai mu wanke kanmu idan ta dawo idan zasu iya su rike yarsu can,haka sukaje Har Borno suka shiryawa dangin Salma karya da gaskiya su Malam Shehu da Malam Musa Baban Hashim harda Kuka ta bata musu suna da zuriya,suma dama kadan suke jira,zamanin haka yazo idan ka rasa iyaye to kafin a samu me rikeka tsakani da Allah ya tsaya maka sai an tona haka zakayi ta garari ana zaluntarka.
Malam Musa ya kalli Affa yace Allah ya saka muku da alkhairi,Allah ya biyaku da Aljanna,ko a gun Allah kun fita tas,Mu mun San rufawa wannan yarinya asiri kukayi amma ba komai zata zo ta samemu ace Zuriyarmu da cikin shege har yafi uku,nan muka tashi da safe sabo da ta Kware da bariki tace ya bace cikin daga jikinta makaryaciya,Ummitu tace ai zuwa tayi aka Markade jaririn yanzu ciki ko wata tara ne ana iya markadeshi a cire ai anci gaba,makaryaciya ce kar Ku yarda da zancenta,Shehu kanin Baban Salma yace to ai tayi kai,zata zo ne dama ubanta shine ya hada tunda kuwa haka take ai zumunci ba dole ba dole bane sai ka ajiye shi ina zaka iya rike irin wannan.
Ku duba tunda ta tafi ko leko mu batayi ba, nan Kuwa Shehu Murna yakeyi sabo da ya cinyewa Salma Gadonta kaf gonaki,fili, da wasu kadarori da Babanta Yayansa ya mutu ya bari.

haka bangaren mahaifiyar Salma su indai ba wani abu zaka basu ba to baka da mutunci a idonsu,komai a basu,idan kaga ana washe maka baki to sun San zaka basu wani abu,ita kanta Khairat Babar Salma ta bar sarkar Gold da rakuma biyar,tare da gona amma tuni suka je Nijar suka siyar dasu da komai suka handame kudin kaf tunaninsu sunci banza Salma ai yarinyace,duniya kenan Dangi a gyara Hali dan uwanka na jini ya mutu ya bar yara amma a rasa me rikesu,a cinye musu gado kuma still ana zaluntarsu.

Affa harda Hawayen karya,haka kowa ya tashi da tsanar Salma me tsanani dangi da kuma marikanta su Ummitu haka suka dawo Rigarsu Ransu fari Kal sun gama fita daga zagin dangin Salma dana mutanen gari.

Washe gari suna tashi da Safe Affa ya daga kasan pillow nasa yaga kudi sababbi yan Dubu Dubu har Naira Milliyan daya,daga sama yaji murya na masa magana cikin nutsuwa ance kudin shanunka ka siyo shanu Kaci gaba da kiwo,haka ma kuma arzikinka zai bunkasa tunda ka rabu da me kashin tsiya.
Affa ya rasa inda yaji maganar ji yayi kamar a kunne aka rada masa,amma yace yanda yaji haka zaiyi,nan ya tafi kasuwa sai ga Affa da shanu har bakwai maza da mata,ya siya musu kayan abinci da yawa,yayi musu dinkuna sababbi ya samu ya siyi gona har biyu na noma,daga nan yaci gaba da kiwonsa cikin nishadi da jin dadi arziki ya Karu,tun daga wannan rana Affa hanyoyin samu suke bude masa,mutane sai murna ake tayashi cewar gwara da ya rabu da Salma tsiya.
Readers tunaninku Affa da Ummitu Aljanu suka sasu aikata hakan rabuwa da Salma da zaginta?ba ruwan Aljanu a nan da gaske sukayi wannan abun,hali ne na Dan Adam dama yana faruwa.
Dama Raheel kuma yace bazai barsu suyi arzikin da zasu nemowa Salma magani ba,gashi sun ce baza su bar ma Salma ta shigo musu gida ba shi yasa ya basu kudin da ya lashe musu ya biya su arzikinsu ya dawo,sai suke ganin dama Salma ce me kashin talauci ita ta jawo musu.

Allah sarki Salma tana Hospital na Na'im hankalinta yanzu kuma yayi gida babu wanda take tunani sama da Ummitun ta da Affa tare da yan Uwanta na borno,yanzu kam tace ta gaji da ganin Raheel dole yasa a kaita kauyensu ta gano lafiyar su Ummitu domin bata da Kamarsu a duniya, su Mummy sun dawo daga ziyarar yan Uwa a Kebbi kullum sai sunzo duba Salma da kayan dubiya iri iri.
Irfan yana yawan zuwa susha Hira da Salma yana jin shirmenta.

10am Na'im ya shigo room din Salma cikin Hospital sanye yake cikin light blue shadda yasha kyau kayan hausawa suna masa kyau,sai kamshi ke tashi,mutane ana ta faman kallon bature da kayan hausawa,Salma sai da ta kalleshi ta kara kallonsa kamar ta cinyeshi haka take ji,harara ya watsa mata yau yan wulakancin da rashin mutunci ne a kansa fuskarsa ba rahma yace tashi mu tafi,zumbur ta dawo daga tunanin da ta Lula bata dauki ko tsinke a kayan da ya siya mata ba iya pant da bra ne kadai nasa a jikinta amma rigarta daya ganta da ita farko ita wata nurse ta wanke mata ta gogo mata ta bata tasa abarta sai bakin dankwali data dauka cikin kayansa ta yafa a kanta,duk da bata yi kwalliya ba amma tayi kyau ta kara fresh, dauko kayanki ne fa,ni Bana so ina dasu a gida wanda suka fi wannan kyau ma Raheel ya siya min,
Raheel din daya barki a wahala ga cikin ki ya fara girma kalli ana ganinsa a rigarki kadan amma ko zuwa bayayi yana dubaki,ai gwara ni Na'im da Raheel,Kwalla ta cika mata Ido tace wlh gwara Raheel dina ya fika,ok kin gane kenan yanzu ba Raheel bane ni? Raheel ne mana kai amma mugu ne wancan me kirki me sona sai ka dinga zuwa min a fuska biyu,awai wa zaka yiwa wayo yaro,Bai San sanda murmushi ya kwace masa ba,nine yaron?ae yaro mana danye ma da nawa ka girmeni?ta wani cuno baki tayi gaba yana Binta a baya,sai kallon hips nata yake suna ta rawa abin sha'awa.

Mota security nasa ya bude masa ya zauna a baya ta zauna gefensa Driver yaja,securities sukace Oga wannan kauyen ya kamata ace ayi escorting naka haka Mummy tace,no Need Ku je da sauran cars din gida I wl talk to her never mind,ok sir suka tafi,suma driver yajasu sai hanyar Abuja can rigar su Salma,sai murna takeyi zata ga Ummitu da Affanta har wakoki take rerawa.

Itace ke nuna hanyar kauyen nasu sai gasu a kofar gidan Affa,Na'im yasha kallon rugar fulani kauye daji sosai ana rayuwa a ciki,sai baza ido yake,Salma tace dan kauye kawai ba a saba da ganin hadadden gari ba sai yau ai sai ka tashi anzo,dariya yayi sosai wai nan ne hadadden gari,cike da murna ta bude mota harda wani dirowa kasa kamar Conductor tana mika da hammar gajiya,
Mutane nan take yan fulani suka baibaye motar ana kallo,nan aka gano cewar Salma Living things ce ta dawo daga yawon karuwanci,bariki tayi riba harda Bature tazo yanzu da turawa take harka cewar mutan gari,mata da Maza an cika kofar gidan Affa ba masaka tsinke,tuni Labari ya kai kunnen Affa dake wajen kiwon shanu,Ummitu ma haka nan ta bar girkin da takeyi ba mayafi ta fito,Salma ta kwalla kara tare da fadawa jikin Ummitu,Ummitu babu bata lokaci ta jefar da Salma tare da kwada mata Mari lafiyayye abinda bata taba yi ba,Na'im dake tsaye jikin mota ba shiri ya zaro ido waje,Ummitu tana kumfar baki ta damewa Salma riga tace Jama'a kowa ya matso yasha kallon Katon cikin dake jikin Salma,kowa ya sheda cewar karuwanci takeyi,Karuwace ta kara yin wani cikin bazai wuce wannan baturen ne yayi mata ba,
Na'im ya gane me suke nufi cikin gwarancinsa yace Mummy ina son Iskanci But me am...not....kafin ya karasa Ummitu ta kwalla da karfi tana Salati Kunji ko bayin Allah ko kunya babu wai yana son Iskanci,Sai mutane suka fara tsinewa Salma da Bature Na'im cewar yan iska kwarto da kwartuwa,ana musu ihu sosai an fara watsa musu kasa ana zagi,Na'im me halin turawa so yake lallai sai ya kare kansa kar a zargeshi,ya kara cewa a tsaya pls ni ina son Iskanci sosai da matane Amma....kafin yaci gaba waje ya kara daukan salati ana Allah ya tsine muku etc, da karfi yace ni ina son Mata ina son nayi iskanci,kuma ni ina son Iskanci Amma ni ba.....tas Affa da ya karaso wa wanke Na'im da mari nan take gefen Fuskarsa yayi jajir ya kumbura,(so yake ya fadi gaskiya wai yana son Iskanci da mata Amma shi bai taba Iskanci ba,ba dan iska bane,kuma bai Yiwa Salma ciki ba).

Salma abin yafi karfinta ta kasa gane kan su Affa,tunaninta kawai dan fushi sukayi da ita,taje wajen Affa ta fara bashi hakuri ya samu ya sa Sanda ya maketa ta fadi kasa sai da ta daina gani na wani lokaci,tana tashi Affa yace daga yau babu mu bake,ki kaddara baki taba saninmu ba,wlh na kara ganinki kofar gidana sai na miki gunduwa gunduwa,Ummitu ma ta Dora da yanzu kam bama sanki,jaraba me farar kafa,kin jawo mana talauci,karuwar banza Allah ya taimakemu mun farfado zaki kara dawowa ki jefa mu a Uku,Kije can kici gaba da duniyancinki,fuuuu Ummitu ta shiga gida kaf kayan Salma dama ta hada su har soson wanka duk akwatunanta sun kai goma sha biyu na zamani ta watso mata su waje,tace Maza ku bar mana gida kafin mutan gari da me gari su jefeku daga ke har bakin naki,Affa ya juya ya tafi wajen kiwon shanunsa cike da tausayin Salma Sabo da ba karya a zaman tare dole sai sun shaku da juna,amma yana tuna talauci da Halin da ya taba shiga sanadiyyar Salma kawai sai yaji farin ciki yaji ya tsaneta.
Ummitu kuwa tana shiga gida Salma ta bita a baya tana Kuka wiwi kamar me tana bata hakuri,har durkusawa takeyi kasa tana rike kafafunta tana kururuwar kuka tana gunji ta cika unguwar,ta dinga birgima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login