Showing 51001 words to 54000 words out of 127542 words

Chapter 18 - Kamarsu Ce Daya 1 Hausa Novel Complete

17 Nov 2024

394

yau na kare masa kallo,Jamila tace dan Allah? Zainab tace na rantse da Allan daya halicceni ya halicci tsohuwata da tsoho na,ga Zainura tambayeta kiji,dan Allah zainura ya yake tafiyarsa,nan Zainura ta Mike tana gwada tafiyar Na'im yana basarwa a nutse cike da gadara da takama yana Isa da takama kamar dan Sarki,Salma ta dinga dariya ganin exertly Zainura ta gwada yanda yakeyi kuma hakane.
Zainab tace Zainura basu kala ya yake magana fisabilillah? Nan Zainura ta kara mikewa ta shiga tsakiya tare da dan Yafito Salma a hankali tana dauke kai tana wani basarwa,Salma ta sheke da dariya,Zainura ta duba wrist dinta wai yanda yake kallon agogo,ta make murya a hankali tare da lumshe ido ta shanyesu sosai kamar me jin bacci wai irin na Na'im sannan tace sai yayane kana zuwa min yanzu?,muryar ma saida ta lalata hausar yanda Na'im ke yi sabo da har yau yana magana zaka San ba a kasar nan yake ba hausarsa still bata fita duk kuwa da cewa yanzu ya iya sosai sai dai yanda yake karya words kamar zaiyi turanci,
Zainura taci gaba ta dage gira daya tace ya fa?Mena irin wannan abi haka,kasan Salmaaana tana jirani,wai har yanda taji yace Salma ba normal Salma ba Salmaaa ..sannan yasa na karshe.

Dariya suke Sha sosai domin Zainura baiwace da ita ta iya gwada komai da wani yakeyi indai ta gani ko taji to sai ta iya irinsa haka Allah yayita da abirni take da ta Zama wani abu,amma kauye iya Secondary ake barinsu wasu ma jss3 wasu ma basa yi dan ma yanzu kai ya waye kusan ko wanne kauye akwai makaranta kuma ana zuwa ai an rage.
Suna hira sai ga kiran Na'im a wayar Rahina,da wuri ta mikawa Salma ta dauka,suna tare lfy lfy da Salma suna wasa da dariya sai suka ga Salma ta koma kalar Kuka da shagwaba kamar ka tabata ta rushe da kuka, Cike da shagwaba tace Hello,Na'im cikin muryarsa me dadi ya tambaya lfy dai? Salma tace na gaji ni...kiyi hakuri ai an kusa gamawa kinji yana lallabata tace Ni...ni...Allah kazo to,yace ok ai zanzo yanzu karfa kiyi kuka,fada miki zanyi an daura aure lfy,Salma kamar bata sani ba ta nuna farin ciki tace Alhmdllh,sai ta tuno ta taba Raka Umma gidan biki taji irin adduar da tayi,sai ko ta fara shekowa Na'im addua Allah ya Sanya alkhairi,Allah ya bada zaman lfy,ya bada rai da lfy tare da Nisan kwana me amfani,Allah yasa lfy aka yiwa,Allah ya bada ikon sauke hakkokin Allah,Allah ya kawo kazantar daki musha suna hhhh kunji fa readers ita Salma bata San ma me ake nufi ba kawai dan taji Umma tayi itama tayiwa Na'im amma kuma adduarta tayi kyau.

Na'im kuwa Ameen Ameen yake ta amsawa,shima nan ya sheko tasa Allah bada zaman lfy,Allah baki ikon yi min biyayya,ki sauke hakkokin ki kaf tunda ai haka Malam yace ko?tace ae Ameen,Yace Allah yasa yi nayi bari na bari ai dai kinji me gari ya fada tace hakane Ameen,Me gari yace shinfidar miji idan nace kizo ai kizo ko?yes cewar Salma yace to Allah yasa kizo din,Umma tayi nasiha kan saduwar aure duk basu San me take nufi ba,Na'im yace Allah bamu ikon Saduwa tace Ameen Ameen,yace ki shirya gamu nan zamuzo za ayi pics da video sosai, tace ok ya kashe wayar.

Mintuna kadan sai ga Angwaye sun kai kusan su ashirin duk samari sunyi kyau,Nan aka fara kashe pics da video Camera Man da Anty Rukayya ta kawo yana aikinsa wani kuma ya karbi wayar Na'im yana ta yi musu masu kyau,Salma har Selfie ita da Ango sukayi kala kala,Ango ansha kyau sai kamshi same color da na Salma duk shirin Anty Rukayya ne,Nan Umma ta aiko Rukayya da wasu aka kawo abincin Amare da angwaye Jullof rice tasha nama ko ina nama ne a ciki da vegetables iri iri,sai kuma Alkubus da miya dasu waina,harda zobo da kunun Aya,nan ma ana ci ana pics da video harda video,yan mata da samari sai hira akeyi ana nishadi,Ango da Amarya plate dinsu daya,wani kallon idan Na'im yana yiwa Salma to ba Salma ba har wanda ya gani sai yaji kunya,amma ko a jikinsa shi Bai ma San yanayi ba.

Nan Jamila tace gaskiya wannan rana ya kamata Ango ya bawa Amarya abinci a baki itama ta bashi,Ana ta dariya eh gaskiya hakane cewar sauran,nan Na'im yasa spoon ya ebo ya kai bakin Salma,ta bude bakin zata karba ya janye Spoon din sai dariya Yeee,ya kara kawowa ta gama bayarwa yanzu zai bata ya janye da sauri ta riko hannunsa ta karfi ta cinye,ana ta dariya da tafi raf raf, Salma ta ciko spoon tab da katon Nama Na'im da niyar ya dan ci dai dai bakinsa ya bar mata sauran a spoon ai kuwa ta tura masa du bakinsa ya cika taf,nan ma sai dariya da tafi haka ya cinye da kyar.

Bayan sun gama cin abinci suka ce azo a tafi gaida Umma da dangin Malam,nan Samarin kaf da yan matan suka jero a hanya ana ta rangaji ko wanne da hirar da suke wasu mazan da mata,wasu matan da mata,wasu mazan ma da maza,gwanin sha'awa,ana ta kallonsu a garin ko bako yazo yasan ana biki,Na'im da Amarya Salma ya rike mata hannu ana ta video cov fa ba a gajiya,har Gidan Umma nan mata manya da suka cika gida yan biki suka fara guda ana tsokanar Amarya da Angonta,suka gaishesu Salma taje wajen Umma ta jawota tana dariya tace Umma tun jiya ban ganki ba,Ina Malam fa? Umma tayi dariya tare da cewa ai yanzu kin samu mutumin naki sai da yaje ya taho dake zaki zo,Salma tace Allah a'a Umma,kin dai ci abinci ko?ae naci,Muhd fa? Shima yaci da yawa,aka fara hotuna da dangin Umma dana Malam,Umma Na'im da Salma suna ta daukan pics ,Anty Rukayya ma da kawayenta yan Birni ana ta sambada hotuna,Abubakar ya nemo Malam suka hadu,Malam,Umma,Ango da Amarya sai pics ake musu da video cov abin Shar ko masu iyaye ba kowa zai samu haka ba.

Bayan an gama akace to pics a barshi haka sai kuma 4pm za ayi Dj a sake sabon wanka,Umma tace Salma su koma gidan Rahina zasu fi hutawa,suna komawa Rahina ta bude gidan suka shiga sabo da harda ita da Abubakar suna layin manyan frnds,
Kawayen Amarya sun tafi gida sai yamma zasu dawo,Haka na Ango ma sai Abubakar kawai suna dakinsa na cikin gida tare da Na'im,Abubakar yace ni dai bari naje wajen Matata baccin rana zanyi,tunda yau ba wajen aiki zanje ba,Dama Abubakar har Nce ce dashi teaching yakeyi a secondary schl ta kauyen,Rahina kuma iya Secondary ta gama,shi yasa suke wise dasu.
Na'im yace kace Salma tazo naji muryarta yanzu,Abubakar yace sannu sarkin soyayya nan har kaji muryarta? Na'im dai amsa ba sai da ya dauki lokaci sannan yace ae mana.

Minti biyu sai ga Salma ta shigo yanda take tafiyar a matukar sangarce ta saki jiki,tana zuwa ta fada saman katifar kusa da Na'im dake zaune a gefenta,tana wash Bikin nan gajiya ne dashi na gaji,Na'im ya kalleta tare da cewa kefa yanzu kin Zama raguwa yanzu sai ki fara yiwa mutum kuka,Salma tayi shuru,yace taso na cire miki wannan daurin tun safe baya damunki?Salma tace mantawa nayi kanta ta daura a cinyarsa ya cire mata dankwali gashinta sai kamshi da sheki yake,ya dan barbaza gashin tare da cewa saukar musu a katifa yana kwana da matarsa fa kuma Umma tace ba a barin kowa ya shiga dakin miji bare ya hau masa bed,Salma tace su Umma fa tsofaffi ne ka kyalesu komai su ba kyau ni baccina zanyi,Kaima fa nasan dan ka huta Abubakar ya kawoka nan amma zaka ce Umma,yana ta Binta da kallo yanda take kwararo shagwaba shi kuma a duniya abin dadinsa yakeji idan tanayi,sai yaji yafi kowa a duniya.

Tunda kace na saukar musu sai dai na tafi tunda Umma tace na daina Zama a kasa sabo da sanyi zai shigeni,Da sauri Na'im yace kwanta dan Allah yanzu nasan kuka zakiyi next, Salma ta kwanta ta baje abinta tare da cewa baza kayi bacci ba? Kwanciya yayi gefenta yana murmushi,Salma ta kalleshi taga Bai ko rike mata hannu ba,kafin ta gama tunaninta taji ya sa hannunsa cikin nata tare da jawo hannun nata ya rungume shi ,basu San sanda sukayi bacci ba,sai 3:40pm suka farka,basu jira komai suka tafi zasuyi sallah sannan kowa ya shirya a fito wajen chashewa.

Tuni Dj ya saki kida a filing kofar gidan Malam,mutane kamar me,maza da mata yara da manya,kawayen Amarya dana Ango duk suna ciki kawai rawa akeyi ana likin Kudi,yan mata sai rashin kunyar akeyi na rawa,Na'im Da Salma tasa shaddarta maroon da dinkin light blue kalar zaran yadin,tayi kyau,Na'im Anty Rukayya tace ya sa Light blue shaddarsa kalar zaran dinkin Salma. haka suka shiga filin rawa suna facing din juna sun r ike hannun juna basa rawa kawai liki ake tayi musu kamar hauka, dangin Umma sun shigo sunyi nasu,Anty Rukayya ta cashe abinta,dangin Malam,makwafta abokan arziki Amarya da Ango ansha ruwan Kudi yan biyar da yan goma anyi dace ne kaga wani ya lika ashirin guda biyar hhh abinka ga masu karamin karfi.

Na'im ma ya likawa Salma yan 50 ita kuma yan 20 ta lika sabo da shi ya bata kudin likin ma sababbi,kawayen Amarya sun cashe haka Abokan Ango ma,Anty Rukayya ta kara zuwa tayi liki tace Umma ce tace nazo a madadinta ga nata likin haka tayiwa Ango da Amarya ta fita,tana fita wani tsageran Matashi dan Kanin Malam ne dama wannan kowa yasan fitsararre ne,ya shiga fili yace a sa masa wakar Oloshi Samata kaya,sa mata wando,aiko aka sa ya dinga takawa ana ihu domin rawar Michael Jackson yayi a wajen irin shegen nan,
Saida ya gama yace ta Malam Magaji ce da Bai zo yayi ba shine ya wakilceshi,Zainura ta shiga da wani Saurayinta Ibrahima suka dinga cashewa ana ta dariya.
magriba ta wuce har anyi Isha ana ta abu daya ana ta daukan photo da video kasancewar wajen Haske aka sa kamar rana,har wurin 8:30 Salma da Na'im suna cikin fili, Salma ta fara kyararrabewa zatayi kuka,Na'im yana gani ya kara bakinsa a kunneta tare da cewa mene ne? Tace Umma da Malam nake tunawa irin abinda suke mana basu sanmu ba,amma suke mana abubuwa iri iri,yau kika taba gani?ya kamata ace kin saba tunda kullum aikin Malam da Umma su faranta mana,kedai kawai kice kin gaji yanzu za a tashi ma ki fadawa Rahina ta raba musu take away dinsu kawai,Rahina ta raba take Away Na plastic plate me kyau ko wacce ta samu wasu ma biyu suka samu,An gama lfy,Na'im ya tafi,Sai ga Rukayya tazo tare da Jan Salma gefe yanzu Dj zai tashi gashi har 9 na dare ta kusa kuma kin San baza ki kara kwana ba sai a dakin mijinki dole yau komai dare za a kaiki muje kiyi Sauri kiyi Sallah ki canja kaya,ba sai kin sake wanka ba idan an kaiki kafin ki kwanta dole zakiyi wanka muje,nan sukaje dan danan Salma ta shirya tare da tattara kayanta kaf na gidan Rahina Anty Rukayya ta karba ta kai mata can gida bedroom dinta na Amarci,Angama kida nan aka yo ayari kai Amarya,Salma ta hade cikin Atamfa pupple and Red gyalenta Red da takalminta dinkin riga da skert ya kamata daf,An jero Ana ta guda aka sa Amarya da kawayenta su biyar cikin motar Malam,wani dan Uwan Malam domin Malam ne yace gidan Rahina ba nisa amma a mota za a dauko Amarya dole,
Amarya tuni suna kofar gidan Malam suna jiran sauran na kafa su karaso a shiga,Salma tana rufe ruf kamar yanda Rukayya ta koya mata tayi shuru,Jamila tana cewa wai ko kukan karya ne tayi.

Suna karasowa aka shigar da Amarya har dakin Umma ta kara yi mata Nasiha sannan aka kaita dan part dinta dan kurcici dashi,bayan mutane sun tafi,Zainura,Barira da Jamila sune suka kara gyarawa Salma gidan tas,Anty Rukayya ta fesa Roomfreshner tare da turare gidan yau dau kamshi.

Bayan 30 min kowa ya watse yan biki ba kowa,sai Anty Rukayya,Umma,Malam sai Ango da Amarya,a daren Umma da Rukayya suka gyara gidan tsab kamar ba ayi biki ba sannan suka kwanta baccin gajiya,Malam ma tuni yayi bacci sabo da gajiyar biki.
Bari muji Ango da Amarya.

Salma tana palonta kamar yanda Anty Rukayya tace haka bata cire mayafin ba yana kanta ta rufe,Ango kuwa tare da Abubakar suka shigo part din Amarya da Leda a hannun Ango Na'im an Sha kyau cikin wani yadi sharashara wanda Umma ta siya masa Milk color yayi kyau sosai yana kamshi,
Da Sallama suka shiga fuskar Amarya a lullube luf tana kallonsu ta cikin gyalenta,Abubakar yayi addua sosai tare da yi musu nasiha su dai ba wani ganewa suke ba har ya gama yace to muje ka rakani kasan Matata ta kusa haihuwa cikinta ya girma Bana so ta gaji da jira na.

Na'im ba sai kawai ya makale kafada ba kamar yaro wai bazai rakashi ba,Abubakar yayi dariya tare da cewa kai naga Alama ma a angwaye kafi kowa zumunidi,Na'im yace gata nan idan tace naje sai na rakaka tambayi Salma,Abubakar ya kara dariya wato tun yanzu har ka Zama mijin tace? Muryar Salma suka ji ta cikin mayafi tace ka gaida Rahina idan ka fita ka rufe kofar gidan Malam nasan sunyi bacci.
Abubakar yace wlh nan kuma baku isa ba sai da safe gidanku ya kwana a bude akuyoyine zasu shugo su bata gidan naku,Abubakar ya musu Sallama cike da mamaki ya tafi gidansa wajen Rahina me ciki.

Waya Na'im ya dauko ya dauki Salma pics tana kunshe cikin mayafi,ya koma gefenta ya musu Selfie da yawa,har cikin gidan sai da ya dauki ko ina a video cov hhhh kamar wani gidan Gomna.

Salma tace zo muje mu rufe gidan nan Nasan sunyi bacci,ta cire mayafin a fuskarta yana kafada da torchlight suka haska suka rufe kofar gidansu,suka shigo ta wajensu da wata yar lanjarar kofa suka rufe Abarsu sannan suka koma Palo,

Na'im yace to Alhmdllh yanzu kuma ba sai muga me hanamu Iskancinmu ba,Salma tayi dariya tare da cewa hmm bari dai Muyi wanka Muzo yau kwana za muyi muna hirar murna,Na'im yace kamar kin sani labari zan baki na daurin Aure,Salma tace ai mu munyi shagali a wajen Kamu da ina kuka ashe Kamu nishadi yake sawa.

Salma ta Mike tsaye tare da cire gyalenta ta linke,ta shiga Bedroom sai gata ta fito daure da zani tasa hijab,Ruwan Zafi a flask biyu ta juye flask daya ta hada ruwan wankanta tare da mikawa Na'im torchlight muje ka rakani ka tsaya jikin kofa,haka suka je ta dan turo kofar tayi wankanta fes tare da yin Brush da toothpaste da gishiri harda Alum da gawayi,ta fito Sannan ta hadawa Na'im da ruwan zafin daya flask din da Umma ta kawo shima ya shiga wanka ita kuma taje ta gama shafa Cream dinta me kamshi ta dauko rigar Baccin da Rukayya tace ita zata sa,wata yar ficika da ita da kadan ma ta sauko cinya me siririn Hannu silk da ita,Pink me zanen Flower green,zata daura zani a sama ta tuna Rahina tace ba a sa komai a kai haka ake kwanciya timbir tunda ta shiga darikar masu kwana ba wando.

Humra ta shafa me kamshi ta fesa dan body spray dinta irin dan Dari biyu da hamsim sai perfume ta kara fesawa, gashinta ta tajeshi ta gyarashi tas da man gashinta na cikin lefe,Powder ta shafa tare da lipgloss pink tayi kyau sosai ma.
Na'im ya fito shima da Towel a jikinsa dama a kayansa da Raheel ya hado harda Towel ciki,wai dan kar Salma taga jikinsa ya tsaya a Palo ya tsane jikinsa tare da shafa mansa ya taje sumarsa,Riga Armless yasa fara da Short Nicker dinsa ya fesa body spray da perfume nasa ya gama tsaf Salma bata San ma ya shigo ba,ta fito Palo sai ta ganshi yana gyara ledar daya zo da ita daga gidan Abubakar ta kayansa daya ci biki dasu.
Salma tace Ashe ka fito,ya kalli Salma nan danan ya rufe ido ya bude yace kinyi kyau amma kalli wannan rigar taki uhm kamar a film,Salma ta kyalkyale da dariya tare da cewa kai haka Anty Rukayya da Rahina suka ce wai nasa tunda munyi aure haka akeyi,Na'im yace Oh to kinyi kyau sosai haka cinyarki take katotuwa? Amma a haka sai a ganki yar yarinya,Salma tace ai dan baka gani nane,juya mugani cewar Na'im Salma ta juya nan yaga Mazaune da hips kamar zasu fado kasa,yace Uhmmmmm Allah da baiwa yake a nan wajen,ni ya bani da shi to?Salma tace ai kai Namijine shi yasa,yace hakane na gane,Salma irin anyi Aure ta linke kayan da Na'im ya cire ta dauke wanda ya shigo dasu daga gidan Abubakar taje ta adanasu a Sip,ta cire masu Dirty tasa su wani waje daban.

Na'im sai lokacin ya shiga Bedroom din Ya zauna gefen Bed yace ga abinci Fa yana nuna mata bakar Leda dake Hannunsa,Salma ta shimfida Sallaya tace to ai ance ana Nafeela kazo kaja muyi sai muci abincin.
Na'im ba musu yajasu Sallar Nafeela Raka'a biyu sukayi adduar da Malam ya koya musu ta aure,dama sun saba basa Zama ba Alwala,Ledar ya jawo gaban Salma kaza gashashiya guda katuwa da yan shila guda biyar,sai Maltina guda Uku,yogourt Babba guda biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login