Showing 45001 words to 48000 words out of 127542 words

Chapter 16 - Kamarsu Ce Daya 1 Hausa Novel Complete

17 Nov 2024

386

gida zaiyi Isha Ashe abinda sukeyi kenan lallai dole a dau mataki,Dan kar su ga Malam suji kunya ba dadi sai Malam ya juya a 80 ya fita daga zauren ya fara tari da gyaran Murya wai dan suji su gudu,ai ko suna ji Salma ta kwace bakinta dake cikin na Na'im cikin Rada tace yazo ka fara magana,Na'im yace tunda baza ayi mana aure ba muyi Iskancinmu,Salma tace abinda kace ko mene zanyi,da badan kar Malam ya ganni ba ai yau gado daya zamu kwana,ni to tsoro nakeyi ance ciki wai akeyi,to mene sai mu haifi danmu me kama da Malam kyakyawa tunda yaki yarda mu ina ruwanmu,Malam ya hangame baki yana Salati dan zina me kama dashi,amma ko kulashi basu yi ba,tunanin Malam basa hayyacinsu basu ma San yazo ba,Salma tace wayyooo mu ba sai anyi mana auren ba ma dinga yin irin wannan kullum,ko muje daji muyi,ko mu buya wani waje ko? Na'im baiyi magana ba Malam yaji ana tsotsar abu ya kara ficewa waje tare da rafka Sallama da uban karfi kamar zai fasa Zauren,Umma ta taho da gudu tana Malam lfy?

Na'im yayi nisa yanzu da gaske yake shi,Salma ta tafi tuni wani garin,bulala Malam ya samo a kofar gida wai tunda sunyi nisa bari ya sambada musu sai su dawo hankalinsu,yar bulala Malam ya tsulawa Na'im a kafafunsa 3qrt ne a jikinsa da kasan ba kaya,ya samu Salma ma ya tsula mata amma kafar kawai suka motsa kowa ya shanye abarsa,Malam yaci gaba da Zane musu kafafu a zahiri sun dawo daga hayyacinsu amma sai dai a ga sun dage kafafu sama sun dawo da abinsu.

Umma tace Maganinka kenan Malam na fada kaki ji,Salma ce taji kunya matuka ta fito wuf daga hijab din tare da janye abinta ta saka da sauri tayi waje da gudu,Na'im daga shi sai 3qtr da singlet ya tsaya idonsa ya koma red harda kwalla ciki,Malam ya haska torchlight,shi kanshi Na'im yanzu yaji kunya da nauyin Abinda sukayi kawai sai ya sunkuyar da kai ya durkusa har kasa gaban Malam yace dan Allah kayi hakuri,Malam yace yanzu idan Allah ya kaddaro ma bakayi aure da wuri ba sai ka butulce masa kana saba masa,nufinka wannan shine zaisa ayi ma Aure ko tunda bakayi aure ba bari ka rage Zafi,abinda nake hangowa gaba shine dalilin da yasa nace bazan ma aure da Salma ba ban sani ba ko tana da auren wani,

Umma ta tabe baki wlh basu da laifi nasihar me zaka musu ai Allah ne yace ayi auren idan kana da Hali shine kariya daga sabon Allah,har kana da wani bakin fada Malam?tashi muje Na'im insha'allah za a muku aurenku,
Malam ma yasan dai bashi da gaskiya,amma Dole haka ya fita ya nemo Salma a kofar gida ya kara musu fada da Nasiha sosai amma kamar Iska haka suka ji zancen Malam,suna fitowa Na'im yace shi bazai hakura ba har yau?Salma tana fushi tace muje wajen Me gari gobe muyi shawarar Umma kawai.

Washe gari kuwa da wuri suka shirya kwas dasu Shar Shar suna kamshi,Umma tace Allah bada Sa'a suka ce Ameen suka tafi gidan me Gari,fada ta cika makil,mutane suna sun kawaye me gari ana fadanci,sai ga Turawan Malam Magaji dama duk gari yanzu an Sansu,Har kasa suka gaida me gari yanda Umma ta koya musu,Me gari da Fara'a ya tarbesu tare da cewa meke tafe daku bakin garinmu? Na'im ya shiga tunanin Kalmar da zai tsara me gari ayi musu Aure,ya fara magana da Mu muna son ayi Mana Aure,shi kuma Malam yace bazai mana ba bamu San dalili ba amma ka tambayeshi kaji,Me gari yace to kai kasan baka da wani Hali na banza? Na'im yace gaskiya ni bani da kawai ina son Salma ina son Iskancinta,sai mutanen fada suka bude baki amma sukayi shuru,Megari yasan dama ba bahaushe bane Na'im,Yace ina jinka,Na'im ya rasa me zai ce yace ni ina da Hali me kyau itama haka,kuma ni Abubakar yace muna ana cinye mata amma ni kuma wlh Bana cinyewa Mata,Iskanci kadai ina so kuma iskancin wannan Salma ya nuna Salma,Salma ta rada masa Love zaka ce yafi ma'ana,Na'im ya kara da cewa we love each other,she love me and I too really love her,Me gari am in love with her,she s my heart my everything,My sweet chocolate.Duk wajen babu me jin turanci,Me gari yace yaro karka zagemu a nan fa,Salma tace a'a yana gaya muku irin son da yake min ne,Sannan me gari yace to to Madalla,Na'im yace jiya ma Malam yace Iskanci ba kyau kuma mu muna son shi,ayi mana aure sai mu dinga yin Iskancinmu kullum,sai yanzu kowa ya gane me Na'im yake nufi a zancen,Me gari yace ka kyauta yaro kar kuyi iskanci ba aure ba kyau,kuje zan samu Malam Magaji muyi magana za ayi muku Auren karku damu.

Salma da Na'im suna ta washe baki,suka Mike zasu tafi Na'im ya kara cewa Me gari itama Salma tana Son Iskanci,Me gari duk ya basu dariya yace ba komai za a magance matsalar kuje na gane,fadar me gari ba wanda Bai tafi da dariyar Na'im ba.

Koda suka dawo gida suna shiga daga zaure Salma ta wuce Na'im zata shiga gida,hannu yasa tare da riko nata a hankali ya juyo da ita tare da jawota saman kirjinsa ya rungumeta cikin so me tsanani,Hancinsu ya hade cikin sigar rada rada ya furta I love u My life,Salma da mamaki tace ina ka San wannan? searching nayi kuma na gano da kyar, ke kuma sai kice me too Mine ko
Kai Salma ta jinjina tare da sa yatsanta a saman kirjinsa wajen botin na rigarsa tana masa tafiyar tsutsa,yaushe zamuje karbo dinkin mu? Lips dinsa ya motsa kawai ta gane yace tomorrow yana kallonta tare da kashe mata Ido daya,jikin Salma ya mutu ta shaki kamshinsa tare da lumshe ido ta kwantar da kanta a saman kirjinsa sukayi shuru wurin 20mnt basa son ko motsi suyi,Salma ta juya bayanta a jiiinsa,bayanta saman kirjinsa hannayensa ya sa tare da rungume waist nata tare da dan rankwafowa yana goga fuskarsa a wuyanta,Salma tayi nisa sai mika takeyi tana kara Mannewa jikinsa,lips dinsa saman kunnenta yace muje ciki,goyaki zanyi a baya fa idan mun shiga kice kanki ke dan Sarawa baza ki iya tafiya ba shine na daukoki,Salma ta kara da sai ince suma nayi sai da kyar na farfado ma,
Nan take ya tsuguna Salma ta haye bayansa ta kwanta lama lama kamar me jin jiki na ciwo,sai da suka dade a Zauren haka yana ta zage Zauren da ita kamar yar Baby,sai cukurkuda masa gashi takeyi,tana taba wuyansa yana ta kunshe dariya sabo da Umma,haka dai ya shiga ciki Salma tayi baccin karya a bayansa,

Umma da gudu ta taresu tana lfy yace uhm kanta wai ke Sarawa har da suma tayi shine me gari yace na goyata ko bafadansa ya dauketa ni kuma nace ai gwara ni na dauketa akan wani katon banza ko?
Umma tace kayi dai dai Muhammad duk maganar nan da sukeyi Bai sauke Salma ba tana bayansa tana kunshe dariya,Umma tace saukota to ta kwanta a saman gadon dakinta,Nan Salma tayi magana cikin maye irin na me jin jiki niiiii......kar.....a sakko....dani....a sama Bana Jin ciwon sai na kwanta a kasa yake tashi,wayyooo....kaina.....a bani....ruwa....ruwa....Umma ta tafi kawo Ruwa Salma tayi dariya a hankali ita da Na'im a hankali yanda Umma baza ta ji ba tace karka sakkoni wlh dadina nake Sha,Na'im ma yace hauka nake nima dadi nakeji muyi shurushshiiii.

Salma an bata ruwa wani ya shiga wani ta saki baki ya fito,Suna haka saiga Malam Magaji yace lfy me nake gani haka?Umma tace bata da lfy tayi masa bayani,ya balbaleta da masifa kuma sai ki barsu a haka ba muharramarsa ba,sauketa saman tabarma a bata magani Muhammad,Badan sun so ba ya shinfide Salma a kasa,Malam Magaji ya kalli farar T-shirt din Na'im gaba daya red jambakin Salma ne da powder a jiki,ya kalli kansa gaba daya tilin gashinsa a cukurkude wuyansa har ta bayan kunne da keya gaba daya Red jambakin Salma ne,Lips din Na'im ya kalla again yaga ya koma irin na Salma me jambaki red kuma duk ya bata masa gefen lips kamar yara dai sunyi kwalliya,Nan Malam ya gano gaskiya ne zarginsa.ya dan matsa jikin bishiyar dake tsakar gidan tare da ballo bulala siririya doguwa ya fige gayyen,Salma tana kallonsa da Ido daya kadan taga ya nufota zai Zane ta da Alama,Malam ya daga tare da niyyar tsulawa Salma a kafa saiko ta Mike zumbur ta fada bedroom dinta ta kulle ta ciki,kafin Malam ya juyo kan Na'im Shima ya gudu dakinsa ya kulle,Malam ya kalli Umma yace dake ake hada baki ana sabon Allah? Umma tace yo ka musu aure idan ka gaji, ai dama nasan ke kika turasu su fadawa Me Gari,shine ya kirani yace lallai daurin aure Ranar asabar sati me zuwa,to zan daura amma zan rubuta a takarda da shedu ko bayan Kwakwalwarsu ta dawo dai dai suka ce basa son juna,ko Salma tana da aure ko wata matsala ba ruwana su suka ce ayi musu a rubuce za ayi komai.

Umma ta rangada guda tare da cewa da haka kayi ai da mun huta,Malam ya rike baki yana mamakin yanda Umma ke son Salma da Muhammad kamar yaranta da ta haifa,yace to hankalinki ya kwanta a sakar min mara nayi fitsari ya fice waje fiya fiya.

Salma najin Malam ya fita ta dauko radio da suke ji kullum ta kai cool FM music kawai suke sawa nan Salma ta kure Vol ta dinga chashewa tare da kallon Umma tace Bismillah Umma ga rawa fa,Umma dakuwa ta aika mata tare da shigewa dakinta ta bar Salma ko kunya babu,Haka wasu yara maza su uku yan 11years sun shigo an aikosu wajen Umma Salma tace sai sunyi rawa,Yaran yanzu ba kunya garesu ba ga son rawar tsiya suka fara kadan kadan,Na'im yana jikin Window dinsa yana kallon Salma abinda takeyi sai dariya yake domin rawar yau ko wacce ma yi take ta hauka,Umma ta fito ta kashe radio ta sallami yara tare da Jan Salma dakinta,ta fara koya mata dabarun rike me gida,tare da karanta mata mene ne auren ma wai,haka ta dinga koya mata abubuwa,tsafta,kwalliya,iya magana,tarairaya,gyaran jiki etc,Salma taji sosai tace Umma zanyi amma kema haka kikewa Malam? Umma bata Ji kunya ba don Salma ta gane tace eh ko wacce ma haka.

Kwana Uku tsakani Haka kullum Umma take sa Salma gaba tayi mata huduba wani ta gane wani kuma ta watsar,haka Na'im ma kullum take masa nasa daban ba kunya sabo da kar ayi kuma azo a samu Matsala tunda yanzu basa cikin hankalinsu.

Malam yace Salma ta kwashe kayanta ta koma dakin Umma da zama,nan aka kawo kayan aiki aka hade Dakin Salma dana Na'im suka koma guda biyu manya ciki da Palo kenan,da ceiling da fanka da komai normal gidane dama me kyau a kauyen, sannan Malam ya musu katanta ya da dan filin tsakar gidansu sai toilet dinsu yar karama me kyau a part din,sai dan kitchen karami an siminte ko ina, wajen nasu Salma harda dan murfin kofarsu idan ka fito tsakar gidan Malam. paint kawai aka sake musu ruwan toka tare da labile masu kyau na cikin birni suma ruwan toka,kanwar Umma ce dake birnin Katsina ta shirya hakan,kujeru na zamani yan Nigeria amma kamar yan Dubai haka suke suma ruwan toka da baki,haka bedroom bed kato da mudubi da sip yan gaske suma dai ruwan toka da baki,carpet shima same color aka malale musu dakunan,abin sha'awa kamar ba a kauye ba, Na'im ya koma dakin Umma da kwana,Umma ta koma turakar Malam, har kayan cin abinci komai an siyawa Salma na me gida,harda dan karamin reshow na girki wai ko zasuyi sha'awar dafa wani abu cikin dare,da tukane da sauran kayan kitchen na amfani yan dai dai gwargwado aka sa mata Leda a kitchen din tare da jera kayan kitchen, komai yaji an shirya tsab, Malam iya kayan daki ya kashe yafi Dubu Dari hudu,dama filinsa da gona ya siyar musamman sabo da auren turawansa,cikin birnin Katsina suka je da Malam da Umma sai Na'im a motarsa gwanin sha'awa suka shiryowa Salma lefe akwati biyu Babba da karama,Na'im yace bikin yayi kusa ba a gama shiryawa ba a kara sati daya sabo da ba a kai dinkin kayan da zasu angwance ba, ai kuwa shadda masu kyau dai dai kudi na rufin asiri Malam yace Na'im ya zabi kala Uku,ya dauki fara,light blue sai arsh,ya dauki lace dan Dubu biyar kala biyu,Atamfa biyu,shadda biyu da material daya suka koma inda suka kai dinki da Salma ya kai musu wani ya karbo wancen da aka dinka musu,yace wannan ma ayi size daya dana farko,Malam ya biya kudi,suka taho gida sabo da Malam yasan su Salma dai ba yan kauye bane ko kallonsu kayi shi yasa ya dage kuma a hannunsa suke hakkinsa ne shi yasa yayi bajinta.

Lefen Salma karamar akwati kayan kwalliyane wannan iri iri komai an sa na dai rufin asirin talaka,babbar kuma atamfa yar dubu 4 zuwa yan Dubu Uku masu kyau guda kala biyar,Laces dan Dubu biyar guda biyu ruwan toka,da light blue kalar Shaddojin Na'im ne,sai Materials kala biyu,fari da baki,da kuma dark brown,sai shadda kala daya yar dubu takwas Maroon me kyau da ita,kala tara kenan,sai ready made doguwar riga guda biyu,sai gyale kalar kayan Na'im ya Zaba kala 5,sai panties da bra du kala shida ko wanne, tight na ciki kala biyu,da skert na ciki shima biyu,sai vest guda uku,Takalma kalar mayafai guda uku masu kyau,sai na tsakar gida daya,dana wanka daya,jaka kuwa pose daya da kuma me hannu daya itama shike nan kaya suka hadu ras, ciki Na'im ya Zaba ya bada dinkin,Sarka da yan kunne da bangles dasu ribbom kala shida shida,kayan bacci Na'im da ya Zaba saida Malam da Umma suka ji kunya sabo da wasu shegu kamar tsirara ya zabo kala Uku.

Umma ta janye Na'im gefe a kasuwa suna shawara ya kamata itama kayan zamani kana na da take gani a birni mata na sawa a siyawa salma,ga kudi suje ya Zaba,Malam yace wannan ai sai shagon kana nan kaya na mata,nan suka nemi katon store na kana nan kaya harda Rukayya kanwar Umma yan Birni suka shiga ita da Na'im, Malam da Umma kin shiga sukayi wai kunya kamar sunga tsaraici ne,haka Na'im ya zabowa Salma yan masifar matsiyata kala biyar ya fito wannan kudin ragunan Umma ne ta bayar gudun muwa,sannan ta kara siyawa Na'im takalma kala Uku masu kyau da hular angwanci kala Uku itama masu kyau wai sai yasa hula dole,Yace a'a Malam yace Bai isa ba,sai yadi kala biyu dai na Umma aka bada dinki na Na'im Shima baya zauna Amarya na saka sabo ba shi yana sa tsoho cewar Umma, suma su Umma sun kai dinkin kala biyu nasu na biki kuma a birni.

An siyo kayan abinci da komai na biki an gama Shar Shar,haka Umma ta kara siyar da gonarta daya ta bawa Na'im wasu kudin tace duk abinda Salma zata nema dasu zai mata karta rainashi,Umma kuma da Kanwarta ta birni sai gyara Salma sukeyi sosai,Rukayya Kanwar Umma tasa Salma gaba suka tafi Katsina kwana Uku ana mata gyaran jiki an dirje mata skin ta kara kyau haske da santsi tare da laushi sai sheki takeyi,kuma ta fadawa Na'im ana gobe daurin aure ya dauko Salma a motar Malam ya kawota Cikin birni da safe ayi mata lalle da Saloon.tunda Salma ta dawo Umma take ta narka mata maganin mata masu inganci,dana Infection,saura kwana biyu biki Umma taje ta karbo dinkin gaba daya,aka kara shirya akwatina,Salma ta zabi wanda za tasa da bikin ta zuba komai a leda Umma tace ta kai gidan Rahina kawarta acan za suyi Kamu da zaman yan matanci,mutan kauye sunsha kallon dakin Salma yanda ya tsaru kaf kauyen ba kamarsa,haka lefe ba a taba yin lefe kamar na Salma ba nan gari ya dauka da labari aka dinga turuwar kallo,
Umma ta bawa Salma chewgum ta kaiwa yan mata da suke mate nata na makwafta tana gayyatarsu biki,Salma bata Kula kowa sai Rahina amma haka ta shiga ta basu gida gida ta gayyaci dai yan mata su sha daya,Na'im kuwa sun saba da wasu sunkai biyar maza sabo da zuwa Masallaci har Abubakar Malam yace ya sanar musu ranar asabar daurin aure a kofar gidan Malam Magaji karfe Goma na safe,haka aka sanar Malam ma ya sanar,Umma ta gayyaci mutane da dama abokan arziki.

Na'im kayansa kaf Umma ta shirya su ta kai bedroom dinsu na Amarci,sababbi da zaisa suna gidan Abubakar dakinsa na kofar gida anan maza zasu Sha angwanci,Abubakar ya dauko musu Dj daga birni zai zo ranar daurin aure da yamma ya kada har dare,Malam ya bawa Na'im wayarsa sabo da daukan pics da video na biki,har Camera Man Rukayya Kanwar Umma ta dauko itama zai dauka pics ranar biki ayi na kati Album guda sabo da tarihi.

Ana gobe daurin aure da safe da wuri Na'im da Salma a Gulf din Malam sun tafi gidan Rukayya ta cikin Kt,Suna hira sama sama hidimar bikin duk ta gajiyar dasu,sunje Lafiya nan fa aka zanawa Salma lalle na gani na fada,haka gashinta me tsayi yasha gyara kamar yar Ethiopian haka ta dawo,Na'im Rukayya ta kaishi barbing saloon akayi masa gyaran gashi na turawa dama gashi bature dan Sajensa da gemu sunsha gyara subhanallah ai ba wanda zai ce Na'im ba yanzu ya sauka daga airport ba yazo Nigeria sai kace daga USA yazo ma,shi kanshi yasan ya hadu karshe.
Rukayya dai ita kanta tana tunanin daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login