Showing 93001 words to 96000 words out of 127542 words

Chapter 32 - Kamarsu Ce Daya 1 Hausa Novel Complete

17 Nov 2024

412

Sallama ta shiga motar suka tafi Airport.
Yau a kusa da Irfan take,Na'im kusa da Salma,Hunaif yana gaba,Mummy motarsu daban,Malam da Umma har Airport suka rakasu a motar Malam.
Irfan suna hira Da Zainura yace ai gwara ma da za a koma tunda kika zo ko ganinki ba ayi,Zainura tace kai Ya siyi kawuna wlh busy ba time ina ta Zumunci,shi dariya ma take bashi kamar wata Babba idan tana magana.

Na'im ne yace Salma Hijab zata sa sabo da a mota ko jirgi zai dan dinga zura hannunsa yana wasa da dukiyar Fulaninta ba tare da kowa ya gani ba,Suna mota tayi mukus a jikinsa yana ta tabe tabensa a jikinta,Salma in taji dadi sai dai ta kudundune cikin hijab kamar tana Jin sanyi,sai ta dinga fakewa da shigewa jikin Na'im wai sanyi take ji,Irfan har ac yasa aka kashe amma taki daina ji
Zainura ta gane me sukeyi kunya ta kamata harda baccin karya wai Salma tana sata kunya ko uban wa ya San me sukeyi oho amma wai haka kawai dan taga Salma na lumewa cikin jikin Na'im sai taji kunya wai.

Zainura taji itama inama ace da Irfan suke haka suma da taji dadi wlh nan Zainura ta fada tunanin Iskanci itama jikinta ya mutu,firgit ta dawo normal sai ji sukayi tace Bana so ma,me zanci dashi tir Allah kiyaye,sun San Zainura uwar shirme sai suka shareta,taci gaba da tunaninta,Irfan ya leka fuskarta tare da cewa lfy? Zainura ta girgiza kai tare da cewa wani abu na tuna,Wayarta ta dauka tare da turawa Salma text cewar dan Uwarki kina tayar da hankalin marasa aure ni na gane me kike sa mijinki yana miki ,Salma tana gani ta karanta sai ta nutsu ta zame jikinta an ganota,su kuwa su Irfan hankalinsu bai kai nan ba Sam basu San ma me suke ba.
Ta kara turawa Salma text dolene wai sai kin kwanta a jikinsa ki tashi mana mu baza ki dinga samu tunani ba.










AsmaBaffa[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉







171-175 176-180






Official








By
AsmaBaffa






JANNAT wannan page din Naki ne.








Sun Sauka lfy a birnin Tarayya Abuja yayinda drivers da Securities suka zo daukansu har zuwa gida,kowa ya kule bedroom domin hutawa.
Aisha ita kadai a daki kamar mayya taji dadin dawowarsu koda Na'im ya shiga dubata zai mata Allura sai kuka takeyi dan Allah a bude ta haka,Na'im yace Sam sai an gama komai lokaci ya cika,taci kuka har ta gaji,Mummy har tausayin Aisha taji,
Bayan kwana biyu Zainura son Irfan ya shigeta sosai duk da cewa bata San so ba amma tace zata tambayi Salma taji ko cutar so ce ta kamata,kullum tasan lokacin da Irfan zai dawo ko zai fita sai ta san yanda tayi ta buya ta kalleshi a boye ba tare da ya sani ba,
Yauma da yamma ta cakare ansha wanka ta fito kamar kallo take amma Irfan take so ta gani taji sanyi a ranta,bata dade ba sai gashi ya shigo cikin shiga ta Alfarma,yasha light blue jean da farar riga,ba karamin kyau yayi ba dama suna kama da Na'im sosai kamar me,Zainura ta kalleshi a sace ba tare da ta bari ya gane ba ta dauke kai irin ko kallo Bai ishe taba,Ganin kwana biyu tunda suka dawo akan Mummy tace ko yana son Zainura shine ya rage kulata sai gaisuwa take hadasu,itama da taga haka shine take shareshi sai taga dama take gaisheshi ma,

Yanzu ma ko sannu da zuwa bata masa ba ta dauke kai,Irfan yayi mamaki yana jira ta kulashi yaga ko kallo Bai isheta ba to ko baiyi kyau bane yau?bedroom ya shiga ya kalli kansa ya kara fitowa ya wuce ta gaban Zainura sai ma ta kalli TV tana dariya irin bata San an halacci Irfan a wajenba,ya shiga kitchen ya fito dauke da Bowl karami me kyau da fruits ciki yana Sha da fork ya zauna kusa da Zainura.

Still Zainura saima ta koma danna waya tana dariya,kallonta yayi tare da cewa baki ganni bane? Zainura tace na ganka mana mene ne?ta fada tana kallon wayarta,to ki gaisheni,akan me zan gaisheka? Irfan yana kallon gefe can daban yace har tambaya kike,kofa Sannu da zuwa baki min ba,Hunaif ne ya shigo yace wow Zeena yau kinfi kullum kyau nan gaba za a ga zukekiya,rannan da mukaje gidan Dada frnd din nan nawa yace wlh yana Sonki zan hadaku idan ya miki baki gani ba komai da mace take so ya hada,

Zainura ita Irfan take so amma ta danne tace to Sai yazo na ganshi mun saba idan halinsa ya min shike nan, Hunaif ya haura side nasa.
Irfan ya gama kulewa shi taki kulashi tana Kula Hunaif har wani Saurayi zai mata,kallonta ya karayi amma ko ta tasa batayi,yace baza ki min sannu da zuwa ba,kawai
Zainura tasa headphone ma a kunnenta yaji haushi ya Mike tare da fisge Headphone din ya tsinkashi gutsi gutsi ya watsar tsawa ya buga mata ni sa'anki ne? Zainura ta firgita bata taba Jinsa haka ba yafi sauran hakuri ba shiri tace Sannu da zuwa an dawo lfy to Alhmdllh,ya hanya ya aiki tana sunkuyar da kai kamar wacce tayi karya,ba kunya yace lfy yayi gaba abinsa ya barta nan.

Salma ce ta fito ta zauna tare da cewa Zainura Irfan yace kin rainashi yanzu wai kina kallonsa kin daina masa magana gaba kikeyi dashi,Zainura tace gaba kuma?da dan masu gida ni na isa,kawai naga yana wani shareni ne shi yasa nima Naja mutuncina,ni kin San ban son raini zanyi wasa da dariya amma da naga za a rainani zan canja wlh haka nake ni,da ace tun farko ma naga irin masu wulakancin ne harkarsu bazan shiga ba,ni ban masa laifi ba naga yana wani daure fuska ni dama gidan aka zo domin ko wanne part na iya bugawa.

Salma tace to naji ai ba haka ake ba baza ki nuna ba mutunci ba gaba daya ke da mutuminki har sirri kukeyi Ku kashe Ku rufe amma sai kuma ku dinga haka,ki daina dai ko ba komai ya girmeki yayanki ne,Zainura tace uhm naji amma kin San ni bazan zauna yana Sha min kamshi ina kulashi ba,kefa banza ce Zainura anya kina da hankali,Zainura tace ya za ayi kiyi hankali nayi,Salma nafa girmeki ehe,to shine bazan fada miki gaskiya ba da wata nawa kika girmeni gaba daya zaki dameni,Salma wai dan Allah idan kana son ganin mutum kullum,kuma idan ka ganshi kaji dadi yana ratsaka yana birgeka,kana son kasancewa dashi,kana son jin ko muryarsa,idan ka ganshi gabanka na faduwa,baka da burin da ya wuce ka birgeshi mene wannan nakeji? Salma tayi murmushi tace so yayi miki mugun Kamu,kina bukatar serious treatment cikin gaggawa,ya miki babban Kamu ke wane wannan kike sonshi haka? Zainura tace wani dan makarantar mu ne ya shiga raina na rasa me nake ji,tab yaro ne ina zai aureki ki canja sharawa schl mate fa,Zainura tace ae naji ina son abuna ni haka,Salma tace Allah taimaka.

Zainura tace tofa so ya kamani kai wannan tafi so sai Kauna,ya Zama chronic disease,Bedroom ta koma bata yarda ba wai chemist ko asibiti a dubata,zata je amma me yasa ma zata tambayi Salma ga Na'im babban Doctor, taje ta Samu Salma har Bedroom muje ki rakani wajen mijinki likita tambayoyi zanyi masa ke ba Doctor ba me kika sani,Salma tayi dariya muje to amma kin San ba likitan Soyayya bane ko? Wai Salma me yasa kike min haka kamar ba kawarki ba,suka tafi har palon Na'im Zainura taga haduwa iya haduwa a part din Na'im,Na'im ta gaisar da fara'a ya amsa Zainura tace Salma fada masa ni dai ya min Kwarjini yau,Salma ta korawa Na'im bayani shi dariya abin ya bashi,amma sai yace to Zainura babbar cutace ta kamaki sai kin Sha Allurai da Karin Ruwa,Zainura taji Allura tace yanzu soyayya za ayiwa Allura?Ya akayi kika sani ke ba Doctor ba ai har operation sai anyi miki,gobe za a tafi dake asibiti a fede miki ciki sai a cire cutar,Zainura taga basa wasa da Na'im ta san ma da gaske yake fede ta za ayi,sai ta fara hawaye Kuka,Na'im yace Salma rakata wajen Mummy ki sanar mata ayi hadin kwanciya a Hospital zuciyar Zainura ta Kamu da cuta sai anyi aiki,Zainura taji da gaske ne fa ta kara fashewa da Kuka ita baza a fede ta ba,Salma sai dariyar haukar Zainura take,tun daga Ranar Zainura ta shiga damuwa za ayi mata aiki a fede ta,Mummy tace Zainura lfy kuwa kwana biyu kin hana kanki sakewa sai tunani kike,Zainura tace Ciwon Zuciya ne ya kamani wai Sai an Fede ni inji Na'im,Mummy jin ance Na'im ya fada itama sai ta yarda ta fara jimami,ganin haka ya karyawa Zainura zuciya ta dinga Kuka kamar me,Mummy ba hakurin da bata bawa Zainura ba amma taki yin shuru,daga karshe ma daki ta koma take ta Kuka,
Hunaif ya dawo Mummy ta sanar masa ga abinda Na'im yace sun dauka wani gwaje gwaje akayiwa Zainura shima ya firgita ya jajanta harda zuwa ya mata Nasiha,Zainura tace Ashe ni mutuwa Zanyi,Irfan bai San me ake ba Mummy harda cewa kar a fada masa zai fi kowa damuwa.

Zainura tasa abin a ranta tana kwanciya sai tayi Mafarki ance mata wani satin zaki mutu,shike nan tana farkawa ta kasa cin komai bata fadawa kowa ba,carbi ta dauka da Qur'ani ta kulle kanta take ta yi tana Istigifari, kwana daya shuru,biyu,shuru,ukushuru har sati ya cika ranar da taji ance zata mutu sai ta hau Saman gado ta kwanta tana ta salati tana jira taga Mala'iku daukan rai amma shuru,tace to ko sai wani satin ake nufi nan ma taci gaba addini ba ji ba gani,sati ya zo na biyu tace to watakil na sati Uku ake nufi ko wata daya,kafin sati Uku Zainura ta rame sosai an rasa gane mata komai kana magana sai Wa'azi zata fara irin ta saduda

Irfan yayi duk yanda zaiyi ta dinga shiga harkarsa amma Bai sani ba Zainura ita ta kanta take zata mutu,Mummy ta gaji da halin da Zainura take ciki ta kira Na'im tace lallai ya kawo takaddun gwajin Zainura,Na'im ya dinga mamaki yace wasa fa nake mata wlh bata da wata cuta kawai shirme tazo min dashi shine na tsokaneta amma ni bata da wani ciwo,Hunaif ya dinga dariya yace to wlh ka dau hakki gata can bata ko cin abinci ta rame sosai ko fitowa bata yi sai addini take ta Saduda da duniya.

Shi kanshi Na'im yayi dariyar wannan shirme na Zainura har Bedroom ya sameta yayi mamakin yanda ta Zabge,ya sanar mata baki da wata cuta wlh Kawai dai da alama Son wani ne ya kamaki,nan Na'im ya zauna ya ganar da ita,taji wani Sanyi a ranta amma har yau akwai tunanin mafarkinta na zata mutu fa.
Sai Lokacin Mummy ta fadawa Irfan,Irfan yace kuma Mummy kamar yara ai in da cutar Ku zai fadawa ba yarinyar ba,ita kuma shine take ta damuwa bari naje na fito da ita Allah sarki zai kashe mana ita.

Ya shiga ya hango Zainura Saman Sallaya ana ta Jan carbi,Irfan yace Zeena Har yau baza ki kwantar da hankalinki ba,ance miki mutuwa Sallama take,Haba yan matan mu,Zainura tace to duniyar nawa take ai kowa na can ne mu dai kuyi mana addua,ita duniya ba matabbata bace,Zainura ta fara wa'azin lahira,to naji tashi muje kici abinci,tace ta koshi,yace gobe akwai schl fa,tace bazanje ba me nake nema a duniya,tashi muje Bana son Surutu,a gaba ya sata Har dining ya dinga dura mata abinci sai da cikinta ya cika sannan yace muje kiyi wanka to,tace ai dazu nayi yace wani zaki karayi,Zainura taje ta sake sabon wanka ta shirya,wai amma baza tayi kwalliya ba,ya shigo wajenta yasata dole tayi,tasha kyau,muje to suka fito har wata dalleliyar motarsa ya bude mata ta shiga shima ya shiga ya ja suka bar gidan,suna tafiya bata ce komai ba yace Zeena akwai wani abu bayan cutar da Na'im yace? Zainura ta fara Kuka sosai, Irfan yaji tausayinta ya gangare gefe tare da gyara parking,Hawayen ya kai hannu zai goge mata,ta matsar da fuskarta irin an hakura da duniya kar ta aikata Sabo,Na'im ya sa hannunsa cikin nata Zainura ta fara kokarin fisge hannunta tana Istigifari,fada min me yake damunki? Zainura taga fa bata da kamar Irfan,tace tun rannan nayi Mafarki ance zan mutu wani satin,nayi ta jira shuru gashi har anyi 1mnth shuru.
Irfan ya danne dariyarsa ya shiga kwantarwa Da Zainura hankali har ta yarda ta daina damuwa sai lokacin ta fara dariya,yace wai zaki kashe kanki ki jawo min masifa,Zainura tayi shuru tare da cewa hmm Son Irfan ne yake azalzalarta amma shi bai ma San tanayi ba,

Wuraren shakatawa ya kaita hadaddu sunyi nishadi sosai sunji dadi tasha kallo tayi nishadi kasancewar Irfan yana kusa da ita masoyinta tuni ta daina tunanin wata mutuwa ma,
Mummy sunji dadi ganin Zainura ta dawo Normal kamar da,Doctor Aliyu ya turo Manyansa an kawo kudin auren Aisha tare da sa ranar biki nan da 3mnths,Mummy tacewa Irfan idan yana da wacce yake so ya kawo sai ayi bikinsu tare da Aisha,yace a'a a gaban kowa Mummy ta masa maganar,Zainura bakin ciki kamar ya kasheta wato ma baya sonta,cikin dare harda kuka Irfan baya sonta Ashe,tana tunanin Zai iya Sonta Ashe ba haka bane,abokin Hunaif da ya damu yana ta bugawa Zainura waya akan ta bashi dama ya dinga zuwa Zance kawai Zainura ta bawa Usman dama badan ta so ba, Saturday weekend tace yazo tayi kwalliya normal gaba daya yau Family suna Palo suna ta hira,Zainura ta fito da takalminta coge tana taku daya daya,ta karasa wajen Mummy ta sanar mata Mummy nayi Bako zanje,Mummy tace kice munyi suriki sai ki kaishi palon baki.
Irfan ya Mike da sauri yace Mummy bari na fita wurin frnds yanzu zan dawo yayi waje,yana fita ya bi ta daya hanyar ya riga Zainura zuwa ya kulle palon bakin,y aje ya tare Zainura a hanya,tayi banza dashi ya fisgota da karfi tare da cewa ki sallami wancen dan iskan ba a zance a nan gidan,Zainura tace to,ya zata taji maganar ya kyaleta kawai amma sai ya hangosu hirarsu ma suke yi a jikin motar suna dariya tana ta yiwa Usman Murmushi,Irfan kamar ya haukace ya koma ciki ya koma Bedroom ya kwanta ya dukunkune Zazzabi ya rufeshi.

Saida Zainura ta gama hirarta har dare sannan ta shigo gidan Mummy tace je kiwa Irfan Sannu yau bashi da lfy tun yamma yake fama da Zazzabi,Zainura tace to tana zuwa jikin kofar bata shiga ba ta Labe kawai a gefe tayi Jimm ta dawo tare da sanarwa Mummy ta dubashi tayi gaba abinta,kwana biyu Irfan yana fama da Zazzabi amma ko kafar Zainura bai gani tazo duba shi ba,yayi jiran har ya gaji,Mummy ya kira a waya wai tasa Zainura ta hada masa tea,Mummy kuwa ta sanar mata ba yanda ta iya haka ta hada komai ta nufi dakinsa,yana kwance cikin bargo ta shigo da Sallama ya amsa da kyar,

Ya bata tausayi ta zauna gefen Bed din tace Sannu ya jiki? Yace sai yau zakizo?Zainura tayi shuru yace to bani tea din,ta mika masa yace bazan iya rikewa ba sai dai ki bani da kanki,Zainura ta fara bashi tea da kanta yana Sha yana kallonta,ta dauke kai tace kayi sauri ni ina da bako Zaizo kana ta Sha kadan,Irfan nan da nan ya canja fuska tare da kifar da shayin a kasa Cup din ya tarwatse,Irfan yace yaushe zaki waye Zeena? Har sai nace miki ina Sonki baza ki gane ba? Zainura tayi dariya tace ina zan gane Nasan gaibu ne? To koma mene ni ina da wanda nake so,Irfan yace karya kike dole ki rabu dashi,Zainura ta murguda masa baki tare da uwar Harara tace Ai ni ba wanda ya kai min Usman a duniya,ya Mike tsaye da sauri tayi waje da gudu,Ta fada Bedroom dinta ta dinga rawa da juyi ta dinga murna ranar kowa yasan tana cikin farin ciki.

Irfan kuwa tunani yake karfa da gaske Son Usman din take tunda ta daina kulashi ma,Mummy ce ta shigo da niyyar dubashi,ya jawo Mummy ta zauna tana lfy? Yace Mummy Allah Ashe sonta nake,ni ban gane so bane sai yanzu,wlh ina Sonta dan Allah Mummy ki fadawa kanin Abbanmu suzo a kai kudi kinji Mummy,Mummy tace ban gane ba,Zainura Mummy ina sonta kinji,Mummy taji dadi tace to ai kaine da tuni an gama amma yanzu kaga tana da saurayi ka bari sai idan ta amince tana sonka ka nemi soyayyarta sai ayi komai ni bani da matsala.

Irfan ya fara shagwaba Mummy to ki fada mata mana dan Allah,Mummy ta kalleshi kawai tare da cewa sannu Ubana ka zauna wlh kuma ta kawo wani shi zan aura mata.

Irfan yau tunani ya kwana yi,ana tashi daga schl ya tafi dauko Zainura,lokacin Zainura me Rake ya kara kai kararta ta zabi rake saida ta gama jagwalgwala masa taki siya,tana gaban PC tace ba itace bace yar Uwartace Hassana ita Usaina ce,
Pc yace yau a nemo masa wannan Hassana su zo tare,Zainura taje ajin su Salma gama exam dinsu kenan tace tace tazo inji Pc,Salma bata San zance ba suka je gaban pc,Pc yace ke a gidan ubanwa kukayi kama zaki ce itace Hassana?Zainura tace ai ba yan mahaifa daya bane mu,ba kwai daya muke ba kuma kasan ana Samun yan biyu basa kama,
Pc takaici ya kamashi yace a kawo masa bulala,Salma tace Zainura sharrin da zaki min kenan itama Salma dariya take, pc yace zaku ci ubanku yau Zainura tace baza a dakeni ni kadai ba,ana kawo bulala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login