Showing 9001 words to 12000 words out of 127542 words

Chapter 4 - Kamarsu Ce Daya 1 Hausa Novel Complete

17 Nov 2024

377

akan me Maimuna? Kullum kullum Malam wlh sai ya sadu dani ba ji ba gani dare rana safe magriba ko yaushe kasheni zaiyi,
Malam yayi salati ransa ya baci yace ayi sauri a kira masa Hashim,Hashim yana zuwa Malam ya lullubeshi da fada dan Ubanka Hashimu ance maka tuwo ne?ko tuwo ne ai sai an wanke hannu ake tsomawa,a wanke goma a tsoma biyar,shashan banza kar na kara ji,abu ka maidashi tuwonka,saida Maimuna taji kunya amma ta maze haka Malam yayi wa Hashim tatas Sannan yace suje kar ya kara ji, ayi saisa Saisa kuma banda Afkawa domin ko tuwo ne sai an wanke hannu ba kawai a tsoma haka ba.

Salma tana ji ta dinga yiwa Hashim dariya,ya kalleta yace banza me cikin shege ai gwara mu da aurenmu.
Watan cikin Salma bakwai yayi uban girma,ta kwanta bacci tana tashi da safe aka ga wayam ba ciki ba alamarsa ma'ana Raheel ya dauke dansa daya sa mata a cikinta,murna wajen Salma ba a magana,haka mutan gidan ma sun tabbatar Aljanune da Salma mutan gari kowa ya shaida Salma Aljani ya aureta har haifar masa yara takeyi labarin da ya karade kasar nan da yawa,abin al'ajabi abin tausayi ga Salma,kowa yaji dole ya tausayawa Salma musamman rashin addini da takeyi,
Ciki na tafiya da Kwana Uku Salma ta shirya tsaf ta koma can kauyensu wajen Su Affa tayi missing nasu,Ummitu tana tsakar gida tayi tagumi tana tunanin yarta Salma ko wanne Hali take oho,Affa yana ta lallashinta katsam sai ga Salma ta shugo da Sallama tana uban gudu ta fada jikinsu tare da hawayen murna.
Kaf ta basu labarin wahalar da tasha da kuma bacewar cikinta sunyi murna da godiya ga Allah.
Ranar kusan kwana sukayi suna hira.

Bayan kwana Uku tsakani Sai ga Raheel ya bayyana cikin dalleliyar motarsa ta Alfarma kamar gaske,cikin wata shadda ta Alfarma milk color, Ummitu sai ganin Salma tayi tayi jifa da tabaryar dake hannunta ta fasa wawan ihu ta rungumi iska,bata San a zahiri Raheel ta daka tsalle ta rungume,kamshin juna suke shaka,nan suka koma yaren turanci Salma harda kukan dadi,Raheel kuwa sai da ya daga Salma ya shillata sama ya cafe ta,Ummitu kuwa gani sukayi Salma ta tashi sama kamar iska,
Gashinta Raheel ya shiga shafawa missed u Dear,me too my love ka tafi ka barni nasha wahala,murmushi ya saki me shegen kyau da birgewa yace na sani my
Heart,yau unguwa zamuje fa shirya Korea zamu je,sadaf Salma tace Ummitu bari naje Makwafta mu gaisa yau ta fice,tana fita Raheel yayi gaba da ita sai Korea, waje waje na bil adama ya kaita suka wuce Dubai tasha tsarabar kaya taci dadi ta more,daga Karshe ya kaita har Saudiyya amma ya hanata tayi ibada,sababbin kaya kamar lefe ya sake mata abin sha'awa.can gidansa na Paris ya kaita sai da sukayi sati biyu tana hutawa tana cin me kyau,abin mamaki kome zata dauka sai taga ya taso yazo wajenta da kansa,za ta dauki cokali ma sai gashi suuuuu yazo mata da kansa.
Sai da Salma ta murje ta murmure tayi kyau sosai tayi kiba kamar wata yar sarki,Su Ummitu sun nemeta sun rasa,ranar da cika sati 2 sai ga Salma bugul a cikin gidan akwatuna reras sababbi a dakinta na kayanta sababbi

Affa ya kara dagewa da Addua amma ina saima kara talaucewa da yakeyi,
Salma yanzu tunda Raheel ya dawo ya hanata Zama kullum suna yawo a duniya ba addini,kuma yanzu ya daina dawo da ita gida yawanci idan ya kaita waje sai ya jefar da ita a cikin Bola sai dai a tsintota a kan bola ta fadi gidansu a dawo da ita,ko ta dawo da kanta gida,kasar wajene kawai idan ya kaita yake dawo da ita.

Yau Raheel da kansa ya kai Salma cikin garin Abuja ya jefata cikin Dust bin dake gefen gidan su Na'im,Abin haushin kuma ya kara sa mata wani cikin a jikinta ya tafi ya barta,tana zaune shuru cikin Dustbin kato,sai tofar da yawu takeyi,Na'im ne ya fito cikin shirgegiyar motarsa Driver na janshi zaije Embassy,
Lemon gwangwani ya gama shanyewa ya sauke glass ya jefi shi cikin Dustbin din sai kwas a kan Salma,zumbur ta Mike ta kalli motar,Ido hudu sukayi da Na'im da sauri ta bangale masa da dariya ta kwalla ihun murna tare da daka tsalle ta fito daga cikin shara,taje har gaban window nasa Tana washe baki cikin harshen turanci tace Raheel dan Allah ka cire min cikin nan wahala yake bani pls my love,tsoro ne ya kama Na'im nan take yayiwa driver Umarni yaja su tafi mahaukaciya ce.

Driver ya figi mota,Salma tabi motar da gudu tana kuka tana kiran Raheel haka ta fadi tim saman titi ta Mike taje jikin gate din gidan tace Allah sai na jirashi Ashe nan ne gidansu na gaskiya ai kuwa dole ya cire min cikin nan.

Na'im 5pm ya dawo dai dai gate yaga Salma zaune gefe tana sheka Amai tana tofar da yawu,a wahalce ta Mike ta tafi wajen motar da gudu,Na'im ya fasa ihu yace driver ya maza ya shige gida dasu,suna shiga itama ta shiga gidan da gudun tsiya,securities sukayo kanta ganin ko dankwali babu a kanta daga ita Sai ready made na doguwar Riga fitted rubber Fari da baki ta dameta,surarta gwanin sha'awa kamar wata india.
Kowa yaga Salma yasan ta hadu ga shiga me kyau,
Na'im yaki fitowa har tsawon 15mnt securities sai tsere suke a tsakar gida da Salma sun kasa kamata,Na'im ya gaji da hayaniya ya fito a fusace Salma na ganinsa ta tafi da gudu ta makalkaleshi ta daneshi tana ta tura kanta cikin rigarsa tana Raheel wai mene haka kana wahalar dani,kamshinka yau yafi na kullum dadi,dan Allah ka dinga zuwa ina Shaka,jiba har na daina Jin Amai da tashin zuciya,
Ina Sonka Raheel me yasa kake min haka idan ka sa min ciki sai ka gujeni? Talk to me mana,ta koma yaren Spanish taji duf,ta koma faransanci nan ma shuru tayi turanci duf,abinda bata sani ba tuni Na'im ya Sume sabo da tsoro gashi ta tozartashi gaban yaransa zasu ce da gaske ne wlh,karya ya mata kawai yaje wajenta yace sunansa Raheel.

Irfan Da Mummy duk sun fito sun gani a idonsu harda Dada yau tana gida,ga Aisha da Hunaif ma sunzo Hutu daga turai duk suna wajen,
Irfan ne yaje yace to dan sakeshi Madam kinga ya suma bari ya farfado sai ku daidaita, dariya Salma ta kyalkyale da ita tace na gode amma kai kaninsa ne ko kuna kama,ni na San Raheel mutum ne amma ake ce masa Aljani ko dan yana da kyau,

Ruwa Irfan Ya fesawa Na'im yaja ajiyar zuciya ya farfado nan kwance a kasa,Salma ta masa murmushin da ya jawo hankalin kowa kanta sabo da tsananin kyawu irin na Salma,
Irfan kasa motsi yayi,Na'im kuwa fuska ya tamke tare da cewa ke ina dankwalinki?ni fa ba Raheel bane,Salma ta cukule itama tace kaine mana Raheel dina ne kaine Allah kuma anan gidan zan zauna wajenka,ka sa min ciki kace ba kaine ba,ka manta soyayyar mu,Na'im mamakinsa da mace ta taba shi za ayi jifa da ita amma banda wannan yarinyar,ita lafiya lau ,Mummy ce tace a ina kika sanshi?Salma tace tun ina yar 3yrs yake zuwa zance kauyenmu,kuma yana kaini kasashe da dama shi ya koya min komai har gidansa yana kaini mu dade,ya kaini Paris ai acan yan uwansa suke,harsu Dubai,makkah,Usa,China etc tun daga bayanin Salma kowa dake wajen ya gane ba Na'im bane.

Irfan yace ba shi bane Kamarsu ce daya da Na'im kinga wannan sunansa Na'im,
Salma cike da masifa tace Malam kayi min shuru karan kada miya ina ruwanka dani ai dai ba kai bane Raheel wannan ne kuma Wlh ko sama da kasa zata hade shine,dan kawai Ku raba mu zaku ce ba shi bane ta fashe da kuka,ta tafi da gudu ta fada Jikin Na'im dake tsaye ta rungumeshi tsam dan Allah karka bari a raba mu kaji pls my Love ka tuna soyayyarmu,
Sai sheshekar kuka takeyi,Na'im a ransa yace ko bata da hankali ne?

Dada ce tayi magana tace to muje ciki maybe zuwa anjima ta gane ba Masoyin nata bane,da Sauri Salma tace shine ma iya wlh shine.

Hunaif da Aisha dariya sukeyi kawai yanda Na'im yake zare Ido gashi Salma kamar jela ta cukwikwiyeshi,
Palo suka shiga gaba dayansu Family din,Na'im cike da izza ya zube saman kujera Salma ma batayi kasa a gwiwa ba ta fada kansa tayi Flat tace My Love muje dakinka zanyi bacci,Salma ta saba da Raheel bata tsoron hada jiki dashi dama sun saba ba kunya, Mamaki ya kashe Na'im ba shiri ya hankadota kasa ta fado ta fasa goshinta sai jini,amma Salma ko a jikinta saima cewa tayi yau mugunta kake ji My Heart.a fusace Na'im ya kwasheta da Mari har sau biyu fuskarta take ta kumbura sumtum,
Mummy ce ta masa fada sannan ya Mike a fusace yayi sama part dinsa,Salma zumbur ta Mike tana kuka da shagwaba ta rufa masa baya,yaje zai shiga Dakinsa yaganta a bayansa yace ke wacece jakara ce (ke wacce Jaka ce),Shuru ta masa tana tsoronsa jikinta na Rawa tace Wai me nayi maka? Ur Father stupid cewar Na'im, kuka ta saka masa tana shagwaba da burburwa,ya salam cewar Na'im, ba imani ya sa kafarsa ya harbota Saura kadan ta gangaro daga steps Allah yasa ta bige da karfen benen nan take Hannunta ya karye Baras,Kuka ta kwalla tana wayyo hannuna wayyo Raheel dina, wayyo Affa wayyo Ummitu ,a fusace Na'im yayi shigewarsa bedroom ya barta nan tana ta kuka,abinka ga sun Saba Rayuwar turai ba wanda ya kulata sai Dada da Mummy ne suka je kanta.

Mummy ta sata a mota tare da Raheel suka kaita asibitin Na'im Mummy ta masa waya lallai kazo kasa a duba yarinyar mutane kuma wlh kai zakayi jinyarta harta warke marar Imani kayi gaggawar zuwa kaji na fada maka,Aisha zata baka abinci ka taho dashi da sauran duk abinda patient zai bukata na kwanciya a asibiti.
Na'im kamar yayi kuka haka yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya hadaddun gaske,jean black da Riga dark Green tasha Rubutu da baki,
Yana zuba uban kamshi Dada ta shirya masa komai aka zuba a mota saida yaci abinci ya gama yangarsa sannan ya tafi Hospital cike da Mulki.










AsmaBaffa




A dinga Sharhi Fans
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉 KAMARSU CE DAYA🏉





26-30 31-35






Official






By
AsmaBaffa








AsmaBaffa Fans club Wannan page naku ne sabo da jin dadin sharhinku.







Driver da guards nasa ne suka kwashi komai suka shigar dasu room din da aka kwantar da Salma, Na'im saida ya gama yangarsa sannan ya sallami guards nasa ya shiga hospital din nasa,ma'aikata sai kwasar gaisuwa sukeyi suna masa ya me jiki yau an kawo Kanwar Ogan nasu Hospital sai faman kai kawo likitoci keyi a kan Salma.
Mummy tana gefe da Irfan likitan kashi yazo zaiyi gyara Allurai aka zo za ayiwa Salma,ita a duniya ba a taba mata Allura ba Raheel ke mata magani idan bata da lfy,
Kallon Na'im tayi wanda shigowarsa kenan kamshinsa ya cika wajen,Salma ta zabura tare da cewa zaka ce ba kaine Raheel ba ga kayan jikinka wanda kazo min dasu last wk baki ta cuno tare da aika masa harara tace hummm kuji ni zaka Yiwa zara?

Mummy tace yi hakuri yarinya a doraki tukun idan kin warke ayi maganar,Salma ta fashe da kuka wlh shine za a ce ba shi bane,sai da ta bawa Na'im dariya yanda takeyi kamar yarinyar goye,Salma tace gashi nan ma yana dariya Allah shine ka fada musu gaskiya Raheel kaji pls,

Doctor yace kawo ayi miki Allura zanyi aikina,Salma nan ma tace Ni Raheel ne zai mun magani ai shi yake min ni ba a min Allura idan kun bar hannun ma da kansa zai dorani,so kuke Ku zubar min da ciki na,ina da ciki fa Raheel ya bani ajiyar Babynsa, basu gane ajiyar ba har ga Allah tunaninsu ciki wani yayi mata da gaske amma ko kunya babu take fada musu haka,
Wata uwar Tsawa Na'im ya buga mata ba shiri tayi shuru jikinta ya fara rawa tsoron Wannan Raheel din take ji,wancan kuwa bata tsoransa gaskiya wannan mugu ne ba irin Raheel dina bane.

Kuka ta fara tana ta shagwaba da kyar Na'im ya karbi Allurar da kansa da mugunta ya tsira mata a duwawu tana kuka ya gama mata du yace a fara dori duk su Mummy su fita,suna fita Na'im ya kama Salma ya matseta ya riketa kam ko motsi bata iyawa haka aka gyarata zam zam,ba wani kuka ba komai sabo da dadi take ji tana jikin Raheel dinta sabo da kauna bata San ma an gama gyaran ba,ta lafe a jikinsa tana shakar kamshinsa cike da tsananin so da kauna sai bacci ya kwasheta nan take.

Zameta yayi daga jikinsa ya fita yana niyyar barin hospital din Mummy tace dawo wlh kai zakayi jinyarta kayi wa yarinya mugunta ka barmu da wahala,ga abinci nan in ta tashi ka bata muje Irfan gida,gobe ma ka karawa gwadawa wata mugunta haka indai ba wani abu kazo dauka gida ba karka sake na ganka a gida sai ta warke a nemi gidansu a maidata can,cikin fushi Mummy ta masa magana shi yasa ya kasa musawa har suka bar Hospital din.
Office dinsa yayi tafiyarsa ya dade ciki har 8pm yaje yayi Sallah yaci abinci a wani eatery ya dawo room din Salma.

Tun daga waje yaji tana ta bige bige tana gurnani,da sauri ya shiga ciki a saman Bed ya hangota tana ta dukan katifar bed din hawaye na shararo mata daga Ido,Dankwalinta ta zame ta fara barbaza gashinta tana tsigoshi,
Na'im yace no wonder nasan yarinyar nan bata da lfy Aljanu gareta,karfin Hali yayi ya shiga tare da rike mata kai ya dinga tofa mata ayatul kursiyyu,Amanarrasul,Falaq,Nas,Iklas etc sai ga Salma ta fadi sharab tana ta baccinta tayi bacci ya kai na One hr lokacin Na'im yana ta danna wayarsa a kujera gefen bed nata ta farka da Kuka tana kiran Raheel,Na'im yace wannan kwai dan iskan Raheel ya cuceni,
Kallonsa Salma tayi ta Mike ta koma kusa dashi tace Dan Allah idan kasan kaine Raheel dina ka fada min,
Zan mareki fa ni sa'anki ne sau nawa kike so na fada miki ba shi bane Na'im thats My Name.

Je kiyi wanka da Brush kizo maza kiyi salloli,Kafada ta make tace Allah ni bazanyi sallah ba,Na'im yace sai kana cewa Period kike yi me wani baja kiyi sallah ba na iskar banja(sai kice period kikeyi mene wani baza kiyi Sallah ba? yar iskar banza)

Hausar tasa tana bawa Salma dariya tace Raheel muyi yaren da muke magana dashi tunda baka iya hausa ba,yanzu zan iya yin sallah kenan ka amince? Zaro Ido Na'im yayi yana mamaki,yace kai dan Uba naki we bakina da hankali? Wlh sai kinayi sallah yau je kayi wanka da Alwala harda Brush ma( ke dan Ubanki baki da hankali wlh yau sai kinyi sallah je kiyi wanka da Alwala da Brush)

Kunkuni Salma ta fara tace ai sai kace nayi Sallah ka yarda ba kawai ka dinga zagina ba Ubana ya mutu amma kana zaginsa,kai idan an zagi naka zaka ji dadi,mikewa Na'im yayi a fusace yayi kanta zai daketa ta fada toilet da gudu tana lallaba hannunta marar lfy, sabo da mugun tsoron Na'im takeji,Murmushi me lafiya ya saki,haka tayi duk abinda yace da hannu daya sai kuma ta kasa daura Towel ta dinga kwala masa kira Raheel.... Raheel, tsaki yaja ya je jikin kofar cikin lion Voice yace what? Cike da shagwaba tace na kasa daura Towel fa Ok na rufe idona just come out ki bani towel naki sai na daura miki,
Abinka da yarda kuma da Sabo Salma ta saba Da Raheel dinta ganin Na'im takeyi kamar shi,haka ta fito zigidir idonsa a rufe ba cin Amana ta Dora masa towel a hannu tare da rike hannunsa ta Dora saman kafadarta nan take ya gane ido rufe ya daura mata sama sama.

Baki ta cuno tana sangarta taje saman Bed ta zauna shi kuma ya bude idonsa,. tace
a bani Body cream dina ya Raheel,idan kinka kanra ce mini Raheel zakina ganin me zana miki,ita hausarsa ce ke bata mamaki Raheel dinta komai ya iya amma wannan turanci kawai ya iya hausar ma sai kadan duk da cewa itama hausar bata isheta ba amma tafi shi iyawa.

Gashinta ta turo masa ko kallonsa ba tayi ba yana gefe yana satar kallonta yanda tayi wani Fresh gashinta me tsayi baki ga santsi,jikinta luwai luwai gwanin sha'awa tana zamanta da Towel ko a jikinta sabo da ta saba da Raheel bata damu ba gani take da gaske Na'im ma shine,vaseline ta murza a hannu da kafarta komai da hannu daya take yinsa,hannu dayan baya komai,Towel din ma nema yake ya zame,Kallon Na'im tayi tace Raheel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login