Showing 3001 words to 6000 words out of 127542 words
suka koma gida suka nuna Ahmad Tall Man baban Salma ga kowa dake da alaka dasu a rugar Fulani duk da cewar yan uwan nasu suma kusan duk sun kare sai kadan daga ciki sai makwafta da abokan arziki,
Kamar wasa tsakani da Allah suke rike Salma ko yarsu baza taji dadi haka ba sabo da gatan da suke nuna mata,ubanta Tall Man idan yazo ganin yarsa dadi yake ji ba kadan ba yana shi musu albarka,haka mutanen gari ma,Salma sai abinda take so shi yasa ta taso cikin shagwaba da tabara ta gaske,amma suna bata tarbiya ta gasken gaske, tana da shekara biyar suka sata a schl tana ilmin addini dana zamani,kamar yanda alkawari yace suna kai Salma Hutu cikin danginta tayi Hutu acan,duk Hutu a Borno take yinsa Affa da kansa yake kaita can abin sha'awa.
tana da shekara takwas Ahmad Tall Man mahaifin Salma ya rasu sakamakon ciwon Koda daya kamashi ba tare da doguwar jinya ba,masu rikon Salma sunyi kuka sunyi zaman makoki,Salma tana primary 4 aka fara ganewa kamar tana da tabin kwakwalwa,sai aganta tana ta maganganu ita kadai,ko aga tana dariya ita daya,wani lokacin kuma tayi ta kuka tana shagwaba,sai ta dinga kallon waje daya,watarana kuma tayi ta wasa tana maganganu kamar da wani takeyin maganar,sai aga tana shafa iska ko ta rungumi iska,a schl ma haka takeyi,watarana kuma aji tana ta rawa tana cashewa kamar tana Jin kida har karkata kunne takeyi,bata da kokari a sauran Subject da dama banda English da French,amma fa Idan anzo exam,a class duk tambaya zata amsa amma kuma bata da kokari kan kowanne subject sai dai English kadai sai French idan ana musu,har kure malamai takeyi indai akan yare ne to baka isa ka kureta ba.
Haukar Salma bata kara ta'azzara ba sai da ta shiga js1 nan aka fara kiranta da living things,sabo da bata iya ba,ance what is living things?Salma tayi sauri ta mike cikin iyayinta tace Living things cike da shagwaba,tace living things is a living things that live on earth with a life,akwai aka kwashe da dariya sabo da Salma kowa yasan a exam kadai take kokari ta cinye du ana mamakin hakan,
Gata dakikiya a class amma da anzo sauran Subject sai ta koma jaka sentence daya baza ta iya kawowa ba bare ta bada definition na abu, sai languages, wani lokacin ma gani za ayi ta tsurawa waje daya Ido tana murmushi ko tana Surutu kasa kasa,kayi mata dariya taci ubanka tana da karfi idan tsokanarta kayi amma idan ita ta tsokaneka to sai ka mata duka baza ta iya komai ba,wasu har suna cewa Aljanune da Salma living things, Sunyi wani Sabon Malami komai sai yace collaborate,shine kullum Salma ta rike aikinta tace Collaboration,shike nan wannan sunan ma yabi Salma,Salma Collaborate ko Salma Living things.
Salma tana da hakuri da Hankali,bata Harka da kowa daga iyayenta da suke riketa shike nan kowa nata ne ba ruwanta da duniya da abinda ke cikinta,Salma me tsananin kyau ce na gasken gaske,fara ce ba fara can ba normal farinta yake,hanci me kyau dan dai dai dashi,bakinta dan karami me dauke da kananan hakora masu kyau farare,tana da Dimple,skin dinta luwai luwai,doguwa da ita ba siririya ba ba ramammiya ba,gashinta ya wuce kafada baki me kyau da santsi,ga wani kwantacce yalala a gaban goshinta dankwali baya iya rufewa har wajensa, idan kaga Salma sai kace yar kasar Ethiopia ce skin dinta da ko irin nasu ta hadu karshe a Ethiopia ma sai kyakyawar gaske za a samu irin Salma komai yaji ga uban Hips.
Salma bata da makusa sai dai akwai babbar matsala Salma bata Sallah ko kadan,duk yanda ka damu da tayi Sallah to baza ta taba yi ba,haka duk wani abu da ya shafi addini bata yi,yin duniya baza tayi ba,ko na ganin Ido sai taga dama,tana da surutun tsiya idan ta samu waje fadi ba a tambayeka bace,komai ta fada idan taga dama bata da sirri,haka ga tambaya har tafi dan jarida amma ba a gane hakan sai Salma ta aminta da mutum sosai zatayi ta zuba har sai ya gaji. Halayen Salma kenan zaku iya tsintar wasu a cikin novel nan gaba.
AsmaBaffa
[1/14, 5:09 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉
6-10 11-15
Official
By
AsmaBaffa
Godiya nake fans Allah ya bar kauna.😍❤.
Salma kamar kullum ta dawo daga Islamiyya wajen magriba ta ajiye Jakarta ta fada kitchen dinsu wanda kamar yanda gaba daya gidan na kara da yayi ne irin bukkar fulani,haka shima kitchen din nasu,
Tuwon da Ummitu ke tukawa shi ta karba tare da cewa Ummitu kawo na tuka miki,a'a jeki ki huta kiyi sallah ga magriba ta gabato,badan taso ba haka ta fito ta dauki buta tayi alwala tana jin bakin ciki a ranta kamar ta kashe kanta Sabo da takaici haka dai taje tayi Sallah tana kunci.
Tuwonta ta karbo taci ta koshi,suna zaune a tsakar gida Affa ya shigo ya dawo daga kiwon shanunsa da baza su wuce guda biyar ba,domin Affa talaka ne sosai a rigar tasu,sannu da zuwa Salma ta masa tana washe baki,sai da ya huta shima yana cin tuwonsa Salma tace Affa ka dinka min Sababbin kayan sawa nawa duk sun mutu gashi muna komawa hutu zamu shiga Ss2 kaga na zama yan mata,kuma aure za ayi min,wai Affa yaushe za ayi min auren ne?nima na huta? Dariya Affa da Ummitu sukayi in da Sabo sun saba da shirmen Salma,Magana Affa yayi yana murmushi yace 'Yata kenan bakya rabo da shiririta ina Saurayin naki?ke da ba kya kula kowa a samari da wa za a daura auren?
Da Sauri Salma tace Affa ai ina dashi kullum wlh yana zuwa zance Sunansa Raheel fa,baka ganshi ba babu me kyansa a duniya,ya hadu,kuma me kudi da ilmi,tun ina primary yake zuwa zance wajena yanzu ma har kasashen waje yace zai kaini harda China,Paris etc ni wlh Bazan taba son wani sama dashi ba shi nake so idan ba shi mutuwa zanyi kawai.
Ummitu ta saki baki tana jin rashin kunyar Salma,Affa kuwa dariya yayi yace To Salma Allah nuna mana,yanzu sabon dinki bani da kudin da zan miki Sabo ki jira Allah ya hore min,kinga shanuna sun kare saura kadan wanda dasu muke samun na abinci da muke ci da makarantarki.
To Affa Allah ya hore maka,ta tashi tare da cewa sai da Safe bacci nake ji,Tare da Ummitu suka shiga dakin tana tursasata dole wai sai tayi Sallar Isha ,gefe guda ta kalla sai suka hango trolley set guda kala Uku masu tsananin kyau,Ummitu da gudu ta bar dakin tana kiran Affa jiki na rawa.
Da Sauri Affa ya shigo ya ga akwatina shima ya girgiza,yace kar a taba sai ya fadawa malaminsa,Amma Salma ta kalli jikin Bango gefe daya sai dariya take bangalawa,tana magana cikin yaren Larabci kamar balarabiya ta koma,
Suna tsaye tazo ta bude akwatin tana murmushi,kaya ne na alfarma kamar lefe kayan kalar na yaran shugaban kasa haka suke Sabo da karshe ne wajen tsada da haduwa,shaddoji,atamfofi ,laces,materials,kanan kaya, inner wears,ready made dogayen riguna dasu Pakistan,takalma na gaske da jakankuna,harda cosmetics masu tsadar gaske,sai Uniform sababbi kala biyu da schl bags kala biyu da sandals,harda hijabai na sawa komai wanda mace zata nema akwaisu a wannan kaya,ba abinda babu komai yaji,Ummitu da ta manne jikin Affa Sabo da tsoro tace kaga dariya ma take tana jin dadi.
Salma kuwa tace da wannan hadadden saurayin Aljani Raheel tnx alot ka gama birgeni dan Allah karka juya min baya Bazan iya rayuwa babu kai ba,matsowa yayi cikin takunsa na birgewa tare da rungume Salma tana shakar madarar kamshinsa,
Ki shirya Babyna zan baki ajiyar yarana idan time na haihuwa yayi zan dauke abina,Salma Hawaye ya tsiyayo mata tace ai za ace cikin shege nayi fa ta karasa cike da shagwaba,
Raheel ya saki murmushi yana lashe mata Hawaye da harshensa yace kwantar da hankalinki bafa saduwa zanyi dake ba kawai cikin Matata zan Sa miki months din haihuwa na cika sai na kwashe abina,murmushi Salma tayi tace tunda ina Sonka ai ba komai yanzu yaushe zan fara yin sallah kullum kullum ka hanani yi,
Nan take Raheel ya bata fuska yace ba yanzu ba sai nan gaba kafin mu rabu Sabo da naga Alama sai mun rabu watarana,Shagwaba su Affa suka ga Salma nayi hade da kuka da burbuwa tana Allah mutuwa zanyi idan ka rabu dani,ina zan samu me kyanka a duniya?
Wani kallo me dauko da zallan so Raheel ya cillawa Salma wanda yasa nan take taji kunya tare da wani sabon shaukinsa,yace akwai mai kama dani sak a duniya watarana kuma zaki ganshi,suffar mu iri dayace ba banbanci,share zancen tayi tare da cewa ni tunda kama kuke ba kai bane Bazan taba sonsa ba,kwantar da ita saman cinyarsa yayi yana shafa kanta a hankali tace My love ya kamata ka aureni mun dade tare tun ina yar 3yrs na sanka nake ganinka muke tare muna soyayya gashi har na zama yan mata,
Ina 17yrs fa yanzu,kallonta Raheel yayi cike da shaukin yana wani lumshe mata ido kirjinta ya tsurawa ido sannan yace lallai kin zama yan mata Salma ina matukar son wannan Balls din naki guda buyu,hannu yakai da niyyar shafawa Salma ta rike hannun tace ai kayi alkawari sai munyi aure fa karka taba.
Dariya yayi hakoransa masu matukar kyau suka bayya dimple dinsa ya lotsa yace ashe baki manta ba,yanzu kunyi hutun schl My Heart ya kamata mu koma Paris wajen yan uwana ku gaisa sannan na kaiki yawo ki zaga duniya ki waye ki san me duniya ke ciki,
Murna ta fara yi tana tsalle gaba daya su Affa suna kallon ta ita kadai basa ganin masoyinta,Kallon Raheel tayi tare da shafa gemunsa tace wannan kayan da ka siya min kasan Su Ummitu baza su yarda kuma zasuce magani zasu yi min wai bani da lfy.
Kyalesu maganin su bazai ci mu ba,kuma batun kaya daga yau ko me zan baki baza su iya magana a kai ba shuru zasuyi kisa abinki so nake duk inda kika shiga kifi kowa a wajen,mota ma zan koya miki kwanan nan na siya miki ki dinga hawa,
Murmushi tayi tace to idan su Affa suka ki yarda fa?baza ma su iya magana ba na fada miki,just do as i said,kuma ko kudi kike nema kawai kice Raheel ina son Kaza zaki gani na baki karki ji tsoro kome zaki gani na baki,yanzu zamu fara love ma dama rainonki nayi kuma Babyna ta girma sai na canja miki rayuwa kin koma yar gayu me kudi duk inda me kudi ke jin kansa kema haka.
Salma sabo da murna bata San Sanda ta fada jikinsa ba ta rungumeshi tace ka canja mana katon gida mu bar kauye,Raheel yace a'a ni bazan taimakawa kowa ba sai ke kadai ko zasu mutu da talauci sai dai idan na baki ki taimaka musu amma bata hannu na ba,ni haushinsu ma nake ji suna hanamu sakewa da addua,dan kawai iyayenki ne amma da tuni na batar dasu a duniya,
Salma tace ai kuwa kana musu wani abu wlh na daina kulaka,karya kike yarinya,ko ta dole sai kinyi abinda nake so,Salma tace wlh baka isa ba,cikin hasala yace kin San ko ni waye kuwa kike fada min haka karki sa na gwada miki rashin imani,
Allah indai baka son su Ummi da Affa ni ma Bana Sonka kuma bazan rike ma yaranka ba a cikin cikina ba,nan take idon Raheel ya koma jajir,Guguwa ta tashi tayi jifa da Salma,nan take sai ga Salma ta fara tsiyayo da hawayen jini sharrrrrr,Hannu tasa ta cire dankwalinta ta fara tsigo gashinta tana zubesu a kasa,Affa da Ummitu duk suna kallonta amma basu San me take cewa ba sabo da ta koma yaren Spain Spanish dashi take magana.
Faduwa kasa tayi hannayenta da kafafunta suka shanye tana ta faman kakari da gurnani,
Affa da gudu yayi kanta yana karanta mata ayatul kursiyyu,shima jifa dashi akayi gefe ya Sume,Ummitu ta fice da gudu tana kiran jama'a a taimaka mata,sun taho tare da maza da yawa Affa suka gani har ya farfado ya Dafe kansa yana Nishi,Salma kuwa ba ita ba labarinta,
Tuni Raheel ya Lula da ita kasar Paris,cikin wani katafaren gida ya ajiyeta yana gefenta abin mamaki Salma tana farkawa sai gata garau kamar bata yi komai dazu ba,gashinta Bai ragu ba duk kuwa da yanda ta tsigeshi,Bata san ma tayi komai ba bata iya tunawa,Tana kusa da Raheel cikin hadaddun kujerun wanda babu kamar su a duniyarmu,
Ta saba da gidan yana kaita duk wani abu ta iya amfani dasu sabo da komai na manyan masu kudi Raheel ya gama koya mata ta waye,
Amfani da waya da kuma computer Salma ta gama kwarewa sabo da yanda yake bata nasa yana koya mata,
Cikin yan uwansa duk ya kaita amma a suffer biladama take ganinsu,sunsha yawo kasashe daban daban,ta kara wayewa,kimanin 3wks aka kwashe ba Salma ba labarinta,yau katsam Ummitu da Affa suna tsakar gida sai ga Salma ta fito rike da buta daga cikin bayi,ga jakarta a rataye na kayayyakin da ta siyo a paris.
Ummitu sun rigada sun gano Aljanu ne masu karfi suka kama Salma,basu ce mata komai ba haka suka ci gaba da muamularsu
Cikin kauye kuwa magana ta watsu cewar Salma Karuwanci ta fara yi,ta koma sa kaya na masu kudi ta koma kamar yar shugaban kasa,komai nata me tsada,musamman irin wayar dake hannunta da computer ko a city babu me irinta a tsada da kyau,
Kuma sai aga tana ta fito da kudi sababbi tana kyauta dasu sai abinda take so takeyi,watarana kuma a nemeta a rasa har tsawon kwanaki,basu San Salma har daji Raheel kaita yakeyi waje waje yake kaita,
States na Nigeria kuwa ba inda bata sani ba,karatu ma tunda suka shiga ss2 sai taga dama take zuwa,kullum Raheel na tare da ita ya hanata addini,tana so tayi amma a ranta baza ta iya ba.
Tun ranar da ta karanta Qurani sau daya sai da tayi sati guda tana kulle a daki Raheel yana gana mata azaba iri iri dole ta daina karantawa da kanta.
Soyayya kuwa Shanta suke basu fasa ba,yanzu anga kawai Salma ta iya tuka mota abinta,kuna tsaye za kaji tace Raheel I need money ko adadi nawa ta fada sai kaga ta zaro daga aljihu ko bag dinta,abin haushi kudin basa mafanar kowa ayi abu me muhimanci sai na shiririta,Affa garin gigin nemowa Salma magani gaba daya ya rasa shanunsa kaf da suke samun na abinci dasu,talauci yayi musu katutu da kyar suke iya daura tukunya watarana,abun yaci tura addua sukewa Salma ba dare ba rana amma kullum abin gaba yakeyi,domin yanzu sai ayi wata guda ba a ga Salma ba,ga gorin mutan kauyen cewar sun kasa bawa yarinya tarbiyya suna fakewa da Aljanu bayan Karuwanci takeyi,me Aljanu za a gani harda mota tana ja ta alfarma,kaya kamar yar Gomna,wa zai ce Salma a kauye suke har ta fi yan Birni komai da komai,kudi wasa takeyi dasu,marikanta suna cikin talauci sai taga dama zata basu yar Dari biyar ko Dubu daya,basu San Aljani Raheel shine Bai son yaga su Affa sunyi kudi ba,sabo da kar su samu kudin yiwa Salma magani,shi yasa ya jefa musu talauci,suna ta cikinsu ina neman wani magani.
Salma yanzu Aljanu take tayarwa sosai watarana sai tayi 3days tana daki tana ta bige bige,addua akeyi amma ba kanta,duk akan tace tana so ta taimakawa Affa da kudi Raheel yake jefa ta cikin wani hali,duk da haka ba karamin so takewa Raheel ba tana Jin idan ba shi mutuwa zatayi, kullum cikin tunani da shaukinsa take ta kasa ganewa ba mutum bane ya hanata ganewa.
Kamar cirar kaya yau wata Uku kenan Salma ta koma normal bata wani Aljanu,kuma bata kara ganin Raheel dinta ba,abinda ke daga mata hankali kenan,kullum a tunaninsa take sai kukan rashinsa,Ummitu tun tana lallashinta har ta gaji,Salma ta rame ta karmashe sabo da son Raheel da takeyi abin ya wuce hankali,da gaske sonsa takeyi tsakaninta da Allah,ko baya jikinta yayi tafiya tofa sonsa yana jininta sun riga da sun shaku da juna,dashi ta saba tun tana karama,baza ta iya auren wani ba sai shi.
Kamar kullum suna zaune Ummitu ta tura mata abinci tace dole sai taci,loma daya takai bakinta ta barke da kukan tuno da Raheel dinta,kullum abincin yan gayu yake bata tana ci na alfarma,
Bata cin garau garau,da karfi tace Raheel sabo da me zaka gujeni dan Allah ka dawo ka taimaka min,
Tausayinta Ummi taji tasan Aljani ya riga da ya auri Salmanta kamar yanda Malam ya gaya musu.
Lallashinta Ummitu ta fara tace kiyi shuru Salma zai dawo ne ai kinji, dan ci abincin kin rame sosai ko so kike idan yazo ya ganki kin lalace ya daina Sonki?cike da farinciki Salma ta karbe abinci taci ta koshi kar Raheel ya ganta ta lalace tun basuyi aure ba.
Ranar kuwa