Showing 30001 words to 33000 words out of 127542 words
shike nan na huta bazan baci ba,wa ya fada miki? da wasu zaki tafi a handbag naki ai sai ki dinga shiryawa a gidan da zamuje, ba musu ta shirya ta cakare kamar zata je party suka fita abinsu sun dace da juna sosai.
Dada sai murnar ganinsu takeyi gaskiya gidan Dada ma me kyau ne sosai,Salma tunda suka gaisa tayi shuru abinta ta zauna ta nutsu daga Na'im sai Dada suke hirarsu bata sa musu baki, abinci da lemuka iri iri me aiki ta kawo musu Sai da Salma taci tayi nak dama ita akwai ci,kawai ciye ciyenta takeyi bakinta Bai hutawa da tauna.har dare suna gidan saida yaje masallaci yayi sallar Isha yace tazo su tafi,da sauri ta Mike dama ta gaji Dada ta bata turare da Sabulan wanka masu kyau da kamshi,tayi godiya suka dauko hanyar gida,saida ya tsaya ya siya mata kilishi da yawa yaga tana sonsa,tun a mota kuwa ta fara bude ledar tana dan yagowa tana cinyewa,yana satar kallonta sai ji yayi tace a daina kallo na,murmushi yayi Bai ce mata komai ba Driving dinsa yake ta yi, tambayarta yayi kin kuwa canja pad?sabo naga Alama Raheel din naki Bai koya miki wannan ba,ba tare da ta kalleshi ba tace sabo da shi ba dan iska bane ai,
Maimakon Na'im yaji haushi ta zageshi shine dan iskan kenan sai ma murmushi da yayi na birgewa tare da tsuke lips yaja yaji shshiiiii ni kuwa dan iska ne sabo da ina son iskanci thts y my ina ta kula mata.harara Salma ta zuba masa tace to Allah ya shiryeka,da sauri yace Ameen tare dake,dariya tayi tace ka fara iya hausa da yawa yanzu,kansa ya nuna da yatsa yace akwai ganowa( ganewa) a class 1st nake daukowa ,amma ke da gani dakika ce (,dakikiyace) Salma tace tsabar kokarina ma yaro Living things ake ce min kaje garinmu ka tambaya,ko kace wace Salma Colaboration a kasar nan za a fada ma domin na shahara na fetsara,Dariya ta kwace masa sosai a kasar wa yasanki a kasar nan in ba a kauyenku ba?,
Salma ta rike kugu a zaune tace Doctor Me Imani Na'im Alawwal,the Consilor of UK Embassy,and Also a prince, the most Handsome Arab man,he look alike with my one and Only Raheel my Heart,my soul mate.
Dariya Na'im ya kara yi sannan yace nima tsautsayi ne ya kamani ai,sai kuma wa ya sanki ba ni ba, irin su Governors,Ministers,Business men etc wanda kina fadan su a Nigeria an Sansu?ni ki daina sani ciki wa ya sanni a kasar nan? Masu kudi wanda suka yi fice nake nufi.
Salma ta sosa kai tace idan ba tsoro ba muje fadar shugaban kasa ka gani idan bamu gaisa dashi ba,Muje gidan minister of petrol a gani,karewarta wife din dan Gote kawata ce kamar yanda nake a gidanku haka nakeyi,ka tambayi Adam a zango karewar ta yan film ma sun sanni,Idan kana ji karyane aje gidan Ali Nuhu a gani mana,kai ka daina kallo na wata shuru shuru ba karamar shegiya ce ni a kasar nan ba,Salman Khan nan in kaga yanda muke wasa da dariya dashi sai kanka ya kulle,Amita batchan,su jitandara,kai kasan Sharukhan?to saida yace yana so na kar kaso kaga wulakancin dana masa, an fada ma ni ta wasa ce,bari ma na kaika wajen turawa kasan dai dan Wrestling undertaker ko? to mun dade tare tight frnd nane,Nancy ta Larabawa har yau har gobe kawata ce,Ronaldo da Messi sanda Ina Spain tare muke cin abinci,Governor na jigawa,kano,Taraba duk sun sanni.
Dariya Na'im yashata kamar cikinsa zaiyi ciwo matar da take wannan kurgumin dajin badan ma Aljaninta ba ai da baza tasan ma me akeyi a duniya ba,Na'im yace karya naki ya isheni haka pls, tace yo dama kana dan kauye me ka sani kai,kaifa dan kauye ne ni ban taba ganin kauyis irinka ba wai kamata ace na fika wayewa Allah kiyaye wlh anyi asarar kaika Uk,Salma yanda ta dage tana caccake Na'im kamar gaske,yace na dai fiki kyau ai,tace Allah sittiri bukwi inji kishiyar me doro,farinka ne kawai ya ceceka,hancinka yayi tsayi da yawa ya bataka,lips naka karami da yawa ba kyau yayi red ba wacce zata so ka,gashinka santsi zaisa a tsaneshi ma,Na'im yayi dariya ke fa na fiki manyan Ido wooo,idon naka kamar na mage abin tsoro da dare miyau miyau harda gwada kukan magen, hmm gashinki kamar dutse ba laushi,Salma ta taba na gaban goshinta tayi fari da Ido tace uhmmm laushin Bala'i wlh,kai nifa am sweet komai nawa sweet muahhh tayiwa kanta kiss,Na'im ya tintsire da dariya yace to kawo na taba da kaina naji,da sauri tace ai kana tabawa za aga bingir ka Sume sabo da laushin gashin ina bazai yuwu na karasa gawar da ba tawa ba.haka sukai tayi har suka je gida cike da nishadi.
Yau gidan Malam musa me kawo musu maganin mata tazo da kwandonta guda,nan fa a kira matan gida ko wacce ta fito harda Maimuna ta ebo dan kudinta ta fito, Hafsatu me magani tace yau fa akwai sabon Harka ta dakko wani me karfe a jiki ta daga musu sama tace kun San wannan?sukace a'a tace to me mukulli kenan,idan kina so ki kulle mijinki ko kishiya yayi miki bakya so ya sadu da ita sai ki dauko shi kice Bissmillahi na kulle mijina wane sai ki saki karfen zaice das shike nan kin kulle mijinki bazai taba Jin sha'awar kishiyarki ko wata mace ba sai ranar da zai shigo dakinki ki kara dakkowa kice bismillahi na bude wane mijina to da yazo dakinki sha'awarki kadai zai ji,amma ko neman mata yake dan Ubansa kina sa masa mukulli kin gama da shege,mata sukace heeeeeee suka saya zasu gwada,can ta dakko wani tace wannan ki karanta Fatiha kafa bakwai ki jefa a tsohuwar Rijiya ba ke ba kishiya ke dai zai makalewa sai kin dinga korarsa,ga me kunama na matsi ne shima Oga ko kurnu ne dole yaji a jikinsa,ga dan kumasa a daga a hada da zuma ayi matsi ahaf ai sai ke ko kishiya ce kece a gaba,ga Sokoto timjim, daga jin sunan ma malama Basai kin mana bayani ba ai zamu Zama timjim cewar Maimuna,nan Malama ta miko hannu suka kashe ana shewa,ta kawo turaren kwanciya a shafa a cibi,kirji,da hips da ya shaki kamshin zai rude miki nan tayi ta karanta musu wasu maganin mata ne normal wasu kuma an hada da shirka a ciki,mata a kula yanzu garin neman maganin mata har abin ya koma shirka da bin malamai,ana rubutu jikin kwai,kaza,da sauran Abubuwa da gani kasan an koma bin malamai,ko ace kar ayi amfani dashi sai za a sadu za ayi tsarki da ruwan rubutu ko alwala gasu nan iri iri ana kaucewa a fada fushin Allah,har kullum a dinga tunawa da mutuwa,baka San ranar tafiya lahira ba,ko yaushe zata iya zuwa,me zakace da Allah,haka kishiya mene abin kulla mata sharri ko wacce idan ta biya allonta ta wanke ke dai ki zage kiga ya zaki kiyi zarra wajen mijinku ba ta hanyar bokaye ba ta abinda Allah yace,duniyar nawa take har za a dinga cutar da juna ana jifan juna,wannan ya jefi wannan wannan ya jefi wancan,waccen ma haka kowa wajen malamai ana shirka a juna,tsakanin musulmi da musulmi maza mata Malamai ana kashe juna,ana kullawa juna Bala'i ya kamata wlh a kiyaye a gyara halaye, malaman nan masu bada maganin kusan yanzu duk bokayene suke fakewa suna shiga rigar malamai,ya shirya karya kamar gaske yana aji tsoron Allah idan magani yaci karki cutar dashi idan kika mallakeshi etc sai ki dauka na gaske ne baki San mashirki bane yana ta tsafi yana yiwa Allah shirka,ayi addua da kanmu mana ki tashi kiyi Zikhri wanda Allah yace,time din da ake amsa adduar bayi,Karatun Qur'an,Nafeela etc kiyi sujjada kuwa Allah kirari ki zubda hawaye kikai kukanki wajen Allah wanda kullum baya Hutu baya bacci,kullum Office din Allah a bude yake kiyi kullum ki gani idan Allah Bai saurareki ba ya amsa miki,ya baki ma abinda baki zata ba a duniya kuma nasa me dorewane,amma tsafi fa karyewa yake baya tasiri,ga fushin Allah.Allah bamu ikon gyarawa,amma da ki ba malam kudi ya miki aiki gwara kici kaza gashashiya ko ki gyara kanki da kudin gyaran jiki.
Kwana biyu Salma ta canja salon Aljanunta yawo take fita kullum ba tare da an sani ba sai dai aga bata nan,da yamma lis ta dawo ko dare,kuma idan ta fita sai ta koma mahaukaciya sosai tuburan take hauka a titi da bola,amma idan ta dawo gidan su Na'im sai a ganta fes,Na'im abin ya damesu gaba daya bashi da sukuni,tana fita yake fitowa da mota amma baya ganin inda ta shiga,Abuja kuma ba a barin mahaukata a titi,Na'im baya ganinta bare yace sai tayi Sallah ko ya mata maganin da Malam ya bashi,haka yauma ta fita ba dankwali a kanta tana ta tsince tsince a titi tana dariya ko ta bata rai,motar dake tsinto mahaukata tazo wucewa ta ganta a hanya aiko suka tsaya caraf suka kamata nan take suka buga mata Allura bacci ya tafi da ita suka jefa ta a mota sai asibitin Mahaukata na Abuja aka kai Salma suka sa mata Sarka kafafu da hannaye dasu take yawo,da ta tayar da Aljanu a maka mata Allurai,yanzu tana can cikin Uniform na mahaukata tana Shan Allurai,Na'im sati guda yaga bata dawo ba,har kauye yaje wajen su Affa ya tambaya saida Suka zageshi tas sannan suka ce bata nan,haka ma Borno yasha cin mutunci iri iri shi dai yace Jahilci ke damun su ko a jikinsa.
Cikin Abuja kullum a yawon nemanta yake lungu da sako,haka Irfan ma sai yanzu yasan ma Ashe son Salma ya kamashi da yawa Bai sani ba,
Mummy da Dada sai jimamin bacewar Salma suke sun damu kwarai,Aisha da Hunaif ma takanas suke daukan mota suyi ta zagayen nemanta layi layi amma ba alamar ta.
Yau Salma da Raheel suna tare a asibitin Mahaukata suna ta hirarsu amma Sam yanzu bata son Raheel tafi son tayi hira da Na'im,sai taji Raheel baya birgeta Sam,Raheel yace na fada miki dama indai kika yarda sukayi miki magani saina haukataki,kuma na daukeki daga gidan,yanzu nan ne gidan zamanki tunda ban gama cika burina a kanki ba sai kin kara ajiye min yara biyu sannan kika gama min aikina,Salma dai tayi banza dashi Na'im kadai take so ta gani a duniya.
Likitoci sunga Salma na magana ita kadai tana Hawaye ta fara shagwaba tana shure shure kawai suka ebo Allurai zasu danna mata Raheel yasa ta shaki daya da karfin Aljanu tayiwa likitoci dukan gaske,amma duk da haka saida securities suka riketa suka tsira mata Allurai har kala Uku ta zube a wajen sharaf sukayi ciki da ita aka kaita can wani daki tare da shinfidar da ita.
Kimanin wata daya kenan da bacewar Salma Mummy ta matsa Na'im dole sai yayi aure duk da cewa yanzu baya kawo mace ko daya gidan sabo da shi ta Salma yake,ya zaiyi ya nemo ta,Mummy ta sameshi har bedroom tace Na'im kasan dai ba wasa nake da kai ba ko? Mahaifiyata nima ita ta bani umarni dole kai da Irfan sai kunyi aure a watan nan,duk kun Rame tunda yarinyar nan ta bace baku da sukuni amma idan kunyi auren zaku ji sauki matarku zata ebe muku kewa.
Na'im ya kalleta nan take ya fara hawaye cike da shagwaba yace ina wani ebe kewa ni Bana son kowa me zata min naji dadi,kawai a daura Min da Salma idan a naso a ganni na samu jin dadi,Mummy tace baka da hankali yarinyar da ta bace bat kuma Aljanu gareta tana yawace yawace shine zaka ce wani zaka aureta,ae ni dai ina sonta haka zan mata magani wlh in dai ba ita ba sai dai ko Dada ta tsine mika Momma Danni ba ruwana.
Fuuu Mummy ta bar masa dakin ta koma wajen Irfan yana kwance yayi wanwar Son Salma ya addabeshi Mummy nan ma ta masa bayani budar bakinsa yace ai sai dai a mutu wlh Dadan me itace Mamanki ai ba tamu bace ni wlh in dai ba Salma ba to ba wani aure da zanyi a kan haka ma kuna takura min zan koma neman matana dama ta dalilinta na shiryu.
Mummy tace to kaima Salman ce kenan?yace yeah,to ai baka dace Da ita ba tunda fada kukeyi,Na'im yafi dacewa da ita Irfan to kuwa indai an bawa Na'im Salma nima sai dai na auro Balarabiya tsohuwar budurwata ta UK wacce kika ce bazan auri yar can ba,Kai kafi Na'im ma rashin kirki Irfan ta bashi dukan wasa a baya bakwajin magana Allah dai ya shirya min Ku addua ta kenan,Allah Zaba abinda yafi Alkhairi.
Haka ake son iyaye ba a dauki Zafi akan yaro ba ayi masa dole karshe abin yazo ya kwabe a samu matsala ana dana sani,wasu kuma a dinga zagin yaro ana masa baki akan ya fadi ra'ayinsa a'a dole abinda iyaye sukace ko na sabon Allah ne sai ace sai yayi,idan ba ayi ba su tsine ma ko su fara kuka Allah yayi fushi,yaron ya lalace karshe rayuwarsa taki albarka.iyaye a daina saurin zagi da tsinewa yaro ko zubarwa da yaro hawaye ayi hakuri a dinga dannewa.
AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉
61-65
By
AsmaBaffa
Zainab Atiku Salama Happy Birthday to u,Allah karo shekaru masu amfani,Na'eem ma da Salma sunce HBD.sun bada gift na perfume na saceshi🤣🤣 Sardauna da Ramlat Night wears da kayan daukan wanka kala goma suka kawo a baki gift,Lantan shadda yar gaske,Dafta tare da Hajara sun kawo super Holand kala biyu da readymade ta kasa me tsarki suma du nayi sama da fadi dasu😀
FLOWER,AUTA, ASYCOOL,MARCYCOOL,MAMAN SAMHA,MAMAN MEENAT wannan page naku ne.
Wani Malamin Doctor ne ya gano lallai Salma Aljanu gareta kuma tana da hankalinta,sabo da haka kawai yayi magana da Doctors zai fara gwada mata na Musulunci sabo da asibitin sunayi idan an fuskanci Aljanu gareka.
Sati daya Raheel ya tabbatar za a rabashi da Salma kawai sai ya juyar mata da memory lfy lau take da hankalinta amma bata iya tuna kowa bata gane kowa gaba daya ta manta abinda ya faru baya,Haka Na'im ya fita Office Embassy kawai Ya fito da niyar tafiya gida,Raheel yazo ba wanda ke iya ganinsa kawai yayi sama da Na'im bat suka bace,bai direshi ko ina ba sai can cikin wani kauye can kusa da Katsina state,Kamar anyi masa duka haka aka tsinceshi a gefen titi duk yaji rauni a jikinsa ko motsi baya yi,shima Raheel sabo da bakin ciki kar Salma ta auri Na'im ya raba musu gari sannan shima Na'im ya goge masa Memory na baya,bazai iya tuna kowa ba sai rayuwarsa ta yanzu.
Kowa yaga Mutum kyakyawan gaske kamar Aljani wasu suce bature gashi kalar kudi komai nasa me tsada ba wanda ya daukeshi haka ya kusa yini yashe a gefen titi,sai da Allah ya kawo wani malami kuma maharbi wato Malam Magaji shine kadai yayi shahada a wannan kauyen ya dauki Na'im ya kaishi gidansa,gidane na na bulon siminti ko ina ba kasa a gidan me kyau,daki Uku ne a gidan sai na Malam dake zaure,Toilet biyu ta wanka ma daban,dayar kuma Masai din irin ta flowshing amma ta siminti,Malam Magaji dama yana da wadatarsa a kauyen yana noma me tarin yawa,ga mutunci da hankali sannan kuma yana zuwa daji farauta.
Har yaran kauyen yana koya musu karatun Allo da safe da yamma,gashi wayayye kamar ba dan kauye ba,haka matarsa Haleematu Dattijuwar kirki ce kwarai gata da bala'in tsafta kamar me komai a wanke a gyare a goge tsaf,gidanta kullum kamshin turaren wuta me dadin gaske,dakunan Bedroom sunsha Red carpet masu kyau da bed kanana dai madaidaita,dakin Malam ma haka,store dinsu da kitchen komai akwai na kauye dai dai me karamin karfi.
Koda ya shigo da Na'im kwance kamar gawa Haka Haleematu ta karbeshi hannu biyu biyu wani magani Malam Magaji ya shafawa Na'im a fuska sai ga Na'im yaja ajiyar zuciya ya Mike zaune yana salatin Annabi,sai kallon Haleematu da Malam Magaji yake faman yi,shi Bai iya tuna komai Bai gano shi waye ma a ina yake Sam ya kasa tuna komai,Malam ya tambayeshi yaro tsintar ka mukayi a titi su waye suka dakeka haka?Kuma daga wanne gari kake? Na'im ya fada tunani yayi yayi amma ya kasa tuna komai,cikin hausarsa da bata da kyau yace wlh bani San kowa ba,bana iya tuna komai,ban san kowa ba,Malam yace subhanallah Wala Allah dukan da mutanen suka yi maka shine yasa sun bugeka a kwakwalwa yasa baka iya tuna komai,yanzu samari Kaci gaba da Zama damu har Allah yasa Kwakwalwarka ta dawo dai dai ka fadi inda kake a maida kai can wajen iyayenka,shi dai Na'im murmushin yake yayi kawai yace to Dad,a'a ka dinga kiranshi Malam ni kuma Umma zakace cewar Haleematu matar Malam,yace to kawai yayi shuru abin duniya ya masa Zafi ya kasa tuna mutane da abinda ya shafeshi sai Hausa da turanci yasan abubuwa bai san ma'anar su ba.
Haka Suka dafawa Na'im ruwan Zafi sukace yaje yayi wanka,ya shiga Bai taba yin wanka da ruwa a bowl ba sai yau haka yayi da kyar,toilet din me kyau ce sosai tasha wanki sai kamshi take,abinda ya daurewa Na'im kai shine kayan sawa akwati guda Malam ya mika masa yace wannan akwati a gefenka muka ganta an ajiyeta kuma kayan sawarka ne a ciki,Na'im mamaki ya kamashi,kuma da gaske Raheel ne ya ajiye akwati guda ta kayan Na'im da ya hado masa a bedroom dinsa,komai na kaya akwai kanana da manya na hausawa,kaya na Alfarma,Na'im yasha mamaki