Showing 69001 words to 72000 words out of 127542 words

Chapter 24 - Kamarsu Ce Daya 1 Hausa Novel Complete

17 Nov 2024

402

da muka kai dare a gidansu mutumin nan kiri kiri ya dinga hararar mu mun rike masa Salma,da ya gaji ba zuwa yayi ya sureta kamar ya dauki buhun Omo wani cilll ya cillata sama yayi ciki da ita.

Zainura tace to anan sai wani munafunci take ta sabawa bawan Allah da soyayya amma zata fake da Memory ya goge,shi ya akayi yake so gashi nan gwara tsohon gwauro dashi wai ba memory tana ta gudunsa sai kiga tayi mukus a gefe kamar yar Iska yanzu haka ta koma.
Zainab ta saki Salati tare da cewa ke ki Bari dan Manzo kuji yar bantan uba tace ga Barira a kusa hadasu da Salma ta ladaftar da ita da kalamai.
Nan aka bawa Salma waya Zainab ma ta bawa Barira,Barira tace Salma? Salma tana murmushi da kyar tace Na'am bata iya sanin su waye wasu Barira ba,Barira tace ke dan Ubanki mu ba ruwanmu da Memory ya goge gwara ki saki jiki,aure ba wayar Salula bane zaki ce baya daukan wakoki ba memory, me yasa kike haka? Har zuwa muke kallon soyayyarku wlh wata zata kwace miki mijinki kina biyewa Memory ya goge,ai ance tun farko kuna son juna kuma kun tuna baya me yasa baza ki dawo da son baya ba da kika tuna Ku ci gaba kina ji kina gani wlh zai nemo wata dama ga kudi ga kyau yan matan birni ne zasuyi rubibinsa ya dauko daya ciki ko biyu ma kina haukar banza,wannan mijin naki to mu dai mun San son Iskanci ne dashi wlh idan baki nutsu ba wata zata janye shi,haka Barira ta dinga masifa kamar Salma yarta ce hhh wai akan ta girmesu da 4mnths shine komai su Zainura sai suce itace Babba ita zatayi fadan manya.

Salma dai ta gama ji tace to na gode zan gyara sukayi Sallama sai Salma ta fara Hawaye wai ta tuno Na'im da yana kula mata da yawa suna Romancing yanzu ma Barira ta tuna mata lallai zai kawo su kuwa,ta shiga uku ita,Zainura ta kyalkyale da dariya tace Me kyau ni zan dinga rakaka zance,Salma ta tunzura ta harari Zainura,Zainura tace dauko Album da wayar da CD a sa kowa ya gani wlh , Na'im yace sai jibi bashi da time.

Zainura ta koma kusa da Irfan tace Wai kai ina budurwarka nuna min ita na kure karyar gayu,Irfan ya nuna mata pics din wata me dan kyau a wayarsa yar gayu da ita,Zainura tace tab yasin baka iya Zabe ba tana haihuwa zata tsufa,kuma da gani yanga zata ma kana Shan wahala da ita,kalleta fa a haka ko shinkafa baza ta iya dafawa ba tun kafin tafiya tayi nisa ka canja wata,haba ai kafi karfin wannan,kalli Na'im yanda ya zabo yar gaske amma kai ka dauko gwalagwaje,Irfan sai lokacin ya hango munin budurwarsa da ta nace masa har yace yana sonta,yace dama ita take so na ni,Zainura tace amma kai kwai dolo wlh me zaka ci da wacce zata dinga sonka bata da aji ita ta damu da kai to taya zaka yi soyayya irin ta Na'im da Salma me dadi?

Irfan girman turai ba wayo sai ya dauki maganar Zainura tana ta Zugashi tana kushe masa Budurwa har yaji dama Ashe ba sonta yake ba wayo tayi masa,yace zanje dake zance ki ganta kuma wlh tayi ta yanga da kyar take magana baki gani ba wahala take bani,Zainura tace ka dauko caka Allah sarki za a cinyeka a caca a banza,Irfan yace naji dadi da kika ganar dani gaskiya,Zainura tace af ka kiyayi mata marasa aji masu Mannewa maza ba don Allah suke son mutum ba,kyanka da kudinka suka gani ni yanzu kaga yar kauye ce ni ko?yace eh tace to bazan aureka ba gwara na auri Ashiru na ko Audu me kifi sabo da dan Allah nake sonsu,Irfan yace gaskiya ke na garine Zainura mijinki ya huta,Zainura tace Allah ne yasa iyayenmu sun mana tarbiya mu bama son mutum dan abinsa,kuma mu idan muka rangada girki to mutum fa sai ya manta agogonsa,Hunaif ya kyalkyale da dariya dan yana jin yanda Zainura take ta yiwa Irfan wayo baya ganewa shi sai yaji Zainura da iyayenta sun birgeshi ma wlh.

Zainura tace kuma cewa kuma tana da Addini?Irfan Ya tabe baki cikin hausarsa da shima dai ba fita take can ba yace ni nan dai Bana taba Jin tana kiran ko name of Allah sau daya ba,Zainura ta tabe baki tace to anya kuwa tana Sallah? Kaga ko ta nan baka yi dace ba domin baza tayi addua ba,yaranka ba tarbiya,Irfan yaja tsaki tare da cewa kinga tana kirana,Zainura tace daga muji,ya daga hello sai ga muryarta tace Babyna ina ta sauraronka shuru anjima zan shigo wajenka gidanku,kuma kace zaka sake min mota har yau ban jika ba,Irfan yace sai kinzo ya datse wayar.
Zainura ta jinjina kai tace abin ya wuce tunani na harda roko? Wai kuma zata biyoka har gida? Irfan yace hmmm haka take min wlh ni shi yasa ma Bana ta sonta, Zainura tace to kayi karatun ta nutsu ka rabu da ita ba tare da wulakantata ba kuyi rabuwar mutunci yanda baza taji haushi ba na San Mummy bata son Wannan Rayhanat din taka,Irfan yace kamar kin sani wlh tace bata sonta bata da tarbiya.
Zan tsara ma yanda zaku rabu da ita ba tare da kun samu matsala tsakaninku ba.Irfan ya mikawa Zainura hannu yace nice to meet u,ta kalli hannun kawai tare da cewa Bana harkar yahudu da Nasara ni,Nan Irfan Ya tuno Rayhanat dinsa da gudu take cafe masa hannu tana rungumeshi tana damunsa da Romancing a ransa yace gaskiya Zainura ta fada Rayhanat bata da tarbiya wata zan canja,hhhhh shegiya Zainura.

Malam da Umma har mamaki suke Na'im da Salma ko Saurararsu basa yi lallai Memory baiyi abin kirki ba ya raba su,su kuwa sun shaku dasu zaman da suke a birni ba Na'im da Salma kusa ba dadi gaba daya ma ya ishesu,suna cika kwana Uku suka fito cikin shirin tafiya kauyensu,Mummy bata so tafiyarsu ba sun saba haka Dada ma da take zuwa kullum wajensu, Mummy ta hada musu Sha tara ta kirki tare da Kudi masu yawa Malam yaki karba ko kwandalarsu,babu yanda basuyi ba yaki karba,sai kaya kawai na sutura da Mummy ta siya musu shaddoji da atamfofi masu tsada da sauran abubuwa shima dan kar Suga Malam ya musu wulakanci ne shi yasa ya karba,Salma da Na'im suka musu godiya tare da cewa suyi hakuri suna tuna memory dinsu zasu zo,Zainura harda kuka za a tafi a barta a birni ita wajen Baffanta take so da kyar Mummy ta shawo kanta tace Irfan zai dinga kaita yawo kuma za a sata a makaranta.

Umma kuka sosai tayi na rabuwa da yaranta da basa tunata Salma da Na'im Malam ma yaji ba dadi sabo da sun shaku matuka,haka suka tafi daga Umma sai Malam sunyi exchange na waya za a dinga gaisawa.
Lfy Malam suka sauka a kauye sannan Mummy ta kira taji sun sauka lfy suka yiwa Allah godiya,Malam yayiwa maigari bayani da kuma Baban Zainura,Baban Zainura yace wlh in suna so ma zan iya bar musu ita ni da gyatimarta zamu dinga zuwa muna ganinta itama tazo Hutu,indai zatayi karatun dama surutun kauye yasa zan aurar da ita amma karatun ai yafi,kuma idan gidan mutunci da tarbiya ne ai da na kowa ne,mene a auren ma na kauye kaga yarinya na wahala,Allah sa mu dace ya Zaba mafi alkhairi,Malam yaji dadi shima.

Salma yanzu Zainura ta tsoratata ta daina nesa da Na'im kullum tana manne a wajensa,wajen aiki ma sai ta fara kuka sai ya tafi da ita,kuma da yace zai tabata ta fara shagwabar Kuka,haka yake kyaleta bai San wannan halin nata ba.
Yanzu ma yayi shirin fita Hospital ya fito da saurin gaske tare da Shan gabansa taci wankan sugar shagwaba ta fara tana doka kafafu Allah..sai ka je dani,ba inda zanje dake bakya bari nayi aiki kuma wahala kike jefani kullum,sai kin jawo ina feeling sai kice ke waye waye,matsa min na wuce ki daina zuwa kusa dani tunda ke baki da Imani naga Alama.
Salma ta cuno baki tana Hawaye bata yarda ba,Zai wuce ta rike rigarshi kam tana binsa kamar jela,Mummy ta fito tare da Zainura,Zainura tace Mummy kalla kiga abinda sukeyi a can kice lallai ya tafi da ita wlh a kauye komai tare sukeyi baki gani ba,Mummy tace Salma lfy?naga kina kuka, Tace shine fa Mummy yake sawa ana kira masa Budurwa yana zance da ita,Na'im yayi dariya jin sharrin Salma,Na'im yace kin San dai Mummy ko mene a gida nakeyi Bana Jin kunyar kowa,nace bani zuwa da ita Office wai sai taje,Mummy tace to ka tafi da ita mana,Na'im yace na rantse ai ni bazanje da ita ba,tana sa mutum yana son Iskanci tana tafiyarta,Zainura ta rufe baki jin Na'im ya tafka abin kunya gaban Mummy,Mummy tace naga ranar da zaka girma Na'im har yau kana nan a haka Allah ya shiryeka,Salma sakeshi ya tafi idan ya dawo kema ki murza kambunki,Salma ta kara fashewa da kuka wai ita an tauye mata hakki,wanne kambu zan Murda masa bayan ya daina sona kuma wata zai kula,Mummy tace maganinka ke nan baka San inda rana zata fadi ba ka dinga shigo da mata gidan nan gabanta gashi nan tana zarginka bata yarda da kai ba,yanzu dadi kaji haka? Zainura tace ke Salma laifinki ne fa ya za ayi sabo da baki da Number 7 a kwakwalwarki ta kwance zakice sai kinbi miji unguwa haka kikaga matan aure sunayi,ke baza ki Kula da gidan miji ba sai kin bishi unguwa,a kauye baya kula kowa sai ke mata ma basu isheshi kallo ba,Na'im yace a nan ma fa ita take korar min yan mata Bana yin komai dasu zata koresu,sai kuma ki dinga zarginsa aurenki ya mutu a haka baki sani ba,wa yace miki ana zargi a aure,Mummy tace yawwa Zainura halina dake kwai wayo da hankali,Salma tayi shuru dai tace ita dan kawai Mummy ta hakura amma wlh da sai anje da ita dole,Mummy tace Zainura je ki taso min Hunaif da Irfan su fito sauri.

Salma tunda Na'im ya fita ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta koma waje da hijab dinta ta zauna a garden tana ta jiransa abu kadan ta kalli agogo,Waya ta dauka da ya siya mata ta danna masa kira ya dauka,ko magana baiyi ba tace lokaci ai dai yayi haka ko,Na'im yana dariyar Jin dadi Salma na sonsa yace sai fa 6pm yanzu 1pm fa gaba daya,Salma tayi rau rau da ido,idan na dawo me zaki bani? Salma tace sai zan baka abu zaka dawo gida wajen matarka? Yace to sai 6pm wlh am serious ki daina ma tambayata yaushe zan dawo ina da aiki da yawa,nan taji muryar wata Nurse tace Sir a kawo tea? Salma tace dan Allah nazo?na San Office din fa,Yace Embassy zan tafi yanzu kiyi zamanki na fada miki Bana son Nacin magana zamu bata dake.
Salma ta kashe wayarta ta Mike ta tafi neman Shawarar Zainura.

Zainura kuwa dakin Hunaif ta kwankwasa yace ke gani nan karki balla min kofa Mummy ce ke nema na,Zainura ta jikin kofar tace na shigo muga dakin naka? Shigo mana,ta shigo taga Room hadadde yasha gyara tace gayu an sanka ba asan makwancinka ba yanzu haka dama kake Kazami ciki kake kwana,Hunaif yayi dariya tare da cewa wlh karya kike yarinya an fada miki saurayinki ne Audu me Kifi? Kayi sauri ka fito to bari na taso uban masu motsa jiki,tana shiga Dakin Irfan taga ma kamar yafi na Hunaif haduwa tafi raina Irfan knocking kawai tayi da Sallama ta shiga,Yana fesa turare ta kalleshi taga bai ma ko kalleta ba,tace Yasin da irin su Audu me kifi ne ko ubale Alquran da tuni yana kallona yana zare Ido anga mace,Irfan ya dinga dariya yace to ni ba su bane kuma kullum sai naga mata hadaddu,haka a UK wacce macece ban gani ba,idan tsirara zakiyi wlh sai naga dama zan kalleki,Zainura tace ja jiki malam shaddar kasuwa ka gani,muna matane dama can jikinsu kowa ganinsa yake,kai yanzu kaga jikina ba sai kwakwawarka ta juye ba,na kananan kwari kake gani jakan mata amma mu irinmu mun fi karfin a kallemu a wuce.

Yan matan naka duk jagwal dasu ina mata anan,fuska kamar Aljanu sura kamar an daurawa Sanda zani,Irfan yana kallon yanda Zainura take zaro zance yana mamaki ba a kureta a magana,yace naji jeki,har zata fita, girman turai ba kunya yace ke Virgin ce? Zainura tana ji ashe tasan Kalmar ta zaro Ido waje tare da cewa kaifa? Yace ni ba shi bane tace shi yasa Ashe ranar lahira akwai tsomen lipton a wuta,hhh wlh sai an maka tsomen lipton kaga dai yanda ake sa lipton a cikin ruwan Zafi a cire ko?tace to ko zaka shiga Aljanna sai an ma haka an wanke ma najasa tas hhhhhh Irfan yace ke wlh fitar min a daki kina mun mugun fata,Zainura tace za a gani ai tunda naga Alama gidan nan ba na gari a ciki sai me kyau shima naji tarihinsa ai.

Tana fitowa taga Aisha anci wanka za a fita Zainura tace uhm Aisha ba kudi ba gadara,ke baki da kudin kanki sai gadara,komai sai dai ayi miki amma gani kike kinfi Dan Gote kudi,Aisha ta kalli Zainura tace ki shiga hankalinki tam,Zainura tace da cikin hankalinki nake? Kina fita dai zaki ga wacce tafiki kyau wlh,ni tun a Tafa naga wacce ta fiki tana nan cikin yan tuwo tuwo na tasha farkon layi.
A wai ke fa nan ji kike da kanki ko?matar da ko saurayi baki dashi ban taba ganin anzo wajenki zance ba,wlh idan muka gaji sai na zuga Mummy ta hadaki da Muhammadu me gadi,ko Ilu me goge windows,Mummy tana jinsu a gefe suna ta cacar baki da Aisha da Zainura wannan ta fada wannan ta fada,Zainura tace Insha'allah sai an cire miki tallafi a gidan nan,kuma sai nayiwa Ilu albishir,Aisha tace kanki ake ji dakikiyar banza dadin abin dai kayana na baki kwance,Zainura tace kuma idan nasa nafi wacce ta bani kayan kyau a ciki ba,domin ni fam nake cika su wata kuwa sanda take dawowa a ciki basa mata kyau Shi yasa ta bawa me kyan diri su tace kadan suka yi mata.

Aisha taji haushi tace Mummy wlh kiyi mana tsakani da ita bani ba ita ta daina min magana wlh zan zaneta fuuu tayi waje,Mummy tace Zainura kyale masifaffiya,Zainura kuwa an Kware da kisisina tace Mummy ita wai bata San wasa ba daga wasa sai ta maidashi fada ina so mu dinga zumunci amma ita sai fada,Mummy tace ai ita haka take daban take cikin yarana sun fita wayewa ai yanzu ne ma Allah ya shirya min Aisha amma da Ai abin ba kyau.

Zainura tace ai ko ni bazan daina kulata ba ana zaman tare zaman mutunci dole na dinga kulata ina mata wasa har ta hakura mu shirya,Mummy harda jin son Zainura a ranta ita kuwa Zainura so take ta dinga cusawa Aisha takaici shi yasa tace sai sunyi zumunci dole hhh

6:30pm Na'im ya shigo a gajiye Salma tana part dinsa tana jiransa taci uban wanka tana ta kumbura kamar zata fashe,Da Sallama ya shigo ta Mike tsaye ya nuna shi Sam bai San tana fushi ba,ya rungumeta tare da dagata sama ya direta saman Sofa yana dariya tare da cewa kinyi kyau Wifey,wa ya taba min ke naga kamar fushi kike,fada min shi nayi maganinsa,Salma tace kaine,ya zaro Ido yace da me?kaki tafiya dani,idan naje dake wa zai gyara min part dina? Wa zai min abinci ko yan aiki kike so suyi min? Salma tace to ai ni nayi ma yau Zainura ce tace haka nake ma a kauye wai naci gaba,Yau dai sai mun kalli CD da wayarmu da album na kauye muga me akayi ciki.

Da kanta ta shirya Na'im yau da kyar tana kunya ta sa masa kaya yaci abinci ya dauko wayar Kauye Cd plate da Album,ya kira kowa na gidan suka taru a Palo ya kuna Cd yasa plate kowa ya nutsu za a fara kallon shagalin biki.

Salma da Na'im aka fara nuna hotonsu tare da adduar aure wani take na Larabawa yana tashi,Zainura tana kusa da Irfan,Mummy da Hunaif ga Aisha a gefe.
Kauyen su Zainura ya bayyana,sai aka nuno wajen Daurin aure,motoci guda 8,ga Malam,su Me gari,Zainura tana laaaaaaaa wlh ga Babana,Baffa gashi ya wuce yeeee Irfan yace yana ina ta nuna musu shi kamar an shigarta Aljanna,daya bayan daya take ga Baban Zainab,yayan Jamila,mijin wance haka take ta yi kowa sai da ta fadi,aka dawo sai ga Ango Na'im cikin shadda Ruwan toka yasha kyau,da frnds nasa duk inda yayi tare da Abubakar,zainura tana musu fashin baki,nan har aka gama daurin aure ana ta hada hada,sai ga cikin gidan Malam an nuno Mata ana saukewa ana dorawa,Umma da Anty Rukayya na hada hada cikin Murna,Na'im da abokai na shige da fice, Anty Rukayya sai kula take da Ango haka Umma da Malam,Na'im yaga yanda suke masa tuni ya fara Hawaye a zaune,Aka tafi gidan yan Matan Amarya Salma,Salma ansha kyau irin color na Na'im,ana ta hira ana cin abinci,sai ga Ango yanda yake manne da Amarya,Haka Amarya tana ta zuba shagwaba yana bata abinci a baki tana bashi,Zainura tana kara karanta abin da wanda ma ba a nuna ba,Har aka zo aka gaisar da su Umma ana ta pics,anzo wajen kida yanda aka rakashe,ana zuwa wajen me rawar Michael Jackson Na'im da Salma suna hawaye suna dariya,yan dakin ma sai dariya suke,ana ganin irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login