Showing 126001 words to 127542 words out of 127542 words
yaro ya samu cuta sai dai Salma tayi planning tun daga haihuwa biyu Suleim da Queen bata kara ba yace ba yanzu ba,Idan kaga su Zainura da yaransu ka rantse ba a Nigeria suke Zama ba sabo da yanda suke kyalli da sheki gami da kyau. Yanzu yaran Queen dasu Arif tare da King dukkansu tare driver ke kaisu schl,Queen da King basa shiri Sam sabo King girman kai ne dashi bai son hayaniya,ita kuma Queen akwai Surutu sai suyi ta fada,Arif kuwa gentle ne baya shiga harkar wani bare ayi fada dashi,duk weekend gidan Mummy suke yinsa ko gidan Dada har Suleim da Sauran ana kaisu,Zainura Uwar yara itace ke kaisu wuraren wasannin yara suna zagawa gashi tana biye musu ayi shirme shi yasa kullum suna gidan Irfan idan ba schl,Dan Ma Irfan yace takura masa suke su hanashi love sai dai ya musu wayo ya tattara su ya kaisu gidan Hunaif, shima Hunaif ya dinga masifa ya hada har nasa yace su koma Part din Salma,sun San ma Na'im bazai bari su cika masa kunne da hayaniya ba Bare Salma da bata bari suyi wasa har su Queen duk bata bari suyi wasa wai suna bata mata gida shi yasa yanzu duk sunfi Zama gidan Mummy daga can ake kaisu schl har Suleim,Omar dasu Rayyaan ne kawai suke Zama wajen Iyayensu sabo da sunyi kankanta,Queen tafi sabawa da Umma tare da Malam Magaji ko gidan Mummy suka je tofa tana bangaren haka King din yake fada.
Tunda su Salma suka gama Service Na'im yace to baza tayi aiki ba ko daya,haka ma Zainura dukkansu ba wacce zatayi aiki,Aisha ce kawai Doctor Aliyu yasa Na'im ya bata Company daya take kula dashi sabo da yaga tana son aikin.
Duk kawayen Zainura na kauye Su Zainab wanda duk sunyi aure suna zaune cikin birni suma da yaransu suna zaune lfy da mazajensu sannan suna zumunci dasu Salma,gaba daya ba abinda ya canja suna waya a junansu asha hira ayi dariya suma yanzu duk sun waye sun goge,suna chat a WhatsApp group dinsu guda Salma ta bude musu,idan ta kama suna kawowa Su Zainura Ziyara suma su Zainura Suna ziyartarsu daya bayan daya.
Karfe 8pm Yaune Zainura ta cika 24years yaune Birthday dinta sai murna akeyi,tace Sam sai ta hada shagali karami a iya gidansu,Dada,Ummitu,Umma,Mummy sai Na'im,Salma,Hunaif,Afrah,sai Oga Irfan tare da kaf yaransu duk sunci uban wanka ko wanne da kalar hadewa da yayi kamar za aje Party duk suna palon Zainura wanda yaci Uban Kwalliya iri iri ko ina wuta iri iri da walwali na tashi ga abinci an shirya ba kalar da babu a wajen tare da katon Birthday cake dinta na Alfarma wanda Irfan ya siya mata,Kida a speaker ke tashi me dandano, Na'im ya kashe kida yace a fara da addua,nan Irfan ya Mike a tsakiyarsu suka dinga Kwarara addua wa Family,Zainura tare da Alummar musulmai,bayan an shafa Zainura ta Mike cikin gown yar gaske kamar wata Amarya taci uban kyau tace jama'a yan Uwa maza da mata yarana musamman mijina sai ko aka kwashe da dariya Aisha tace Mummy na wajen fa,Zainura ta rufe ido ta bude tace ammm ina matukar Godiya da halartarku wannan taro nawa na gode sosai Allah yaja kwana na ya bani rai da lfy mai amfani ya samu a aljanna,Irfan ya kwalla da karfi yace yeahhhhh Dear Ameen tare da dage kafa daya sama wai ya daga mata kafa ta shiga Aljanna tunda ance Aljanar mata na kasan kafafun mazajensu,dariya da tafi akayi sosai,Mummy harda dukan Irfan a kafada baka da kunya,Na'im ne ya Mike shima yace ina me farin cikin sanar daku Salmata tana da 2mths pregnant sai murna da addua ake,Salma ta buya a bayan kujera wai kunya,yaran kuwa sai tsalle suke zasu yi kanwa ko Kani,
Hunaif ma ya Mike ba abinda yayi sai yace tunda abin son kaine nima ina mika jinjinata da godiya ga rabin rayuwata,Ruhina,kuma barin jikina Afrah,Ummitu tace Ku tashi mu tafi wannan Harka ba ta manya bace,Umma ma tace ai ba kunya ce dasu ba ta kalli Na'im tare da cewa dama dana na Dade da Sanin baka da kunya,Dariya yayi yace Afwan Umma na manta kina wajen,Umma tace jibeshi da Allah a kauye mene baka yi na fitsara,Dada kuwa Rankwashi ta zubawa Hunaif sannan suka fita tare da shiga Mota Driver ya jasu suka tafi.
Cake Zainura ta yanka tare da bawa Irfan shima ya bata Palo ya dau tafi ana Happy Birthday,Na'im ne me sa wakar Happy Birthday ta turawa,bayan an gama Hunaif yace me yasa aka kawo yaran nan yanzu bazan iya rawa a gabansu ba wlh an cuceni da aka zo dasu,Nan Irfan yace a sa Driver ya kaisu gidan Mummy ai gobe ba schl,kida aka sawa yaran suka dinga rawa sannan aka zuba su a mota driver ya kaiwa Mummy su.
Hunaif Yaja hannun Afrah sai da suka cashe Irfan da Na'im dama basa rawa su dariya kawai sukeyi yanda Hunaif ke cashewa,Zainura tace sai tayi,Irfan yace kadan zata yi ta shiga ta dan taka ta zauna ana dariya,Aisha ma ta cashe ta zauna,Salma ta Mike Na'im ya rike ta tare da jawota jikinta yace a'a kannen mijine fa ba muharramanki bane,kwanciya tayi a jikinsa tana masa magana a kunne yana dariya,Doctor Aliyu yazo daukan Aisha yayi mamakin ganin yanda aka ci aka Sha ake ta faman shagali abu karami sun mai dashi Babba Ashe da gaske suke abin shima sai da ya zauna akayi dashi sannan yace bacci yake ji Aisha ta tashi su tafi,
Hunaif ya dauke Afrah daga cewa zata gyara fuskarta suka shiga bedroom na kasa dake palon basu fito ba suna can sun sa key ma suna making love.
Irfan yace Zainura tazo ta canja masa kaya shima tunda suka shiga ko labarinsu ba a kara ji ba,Na'im yace Salma ta tashi su tafi gidansu suka tafi tare da ajiyewa Zainura gift dinta,Suna zuwa suka fada shagalinsu suma.
Hunaif dai a gidan Irfan Suka kwana sai washe gari suka tafi part dinsu.
Da safe da wuri Mummy tasa aka dawo musu da yaransu sun dameta da surutun tsiya sai ga Doctor Aliyu mijin Aisha yazo daukansu zasu yi Hutu a gidansa da tsalle da ihu suka bishi zasu je wajen twins.
Salma tana kallon Yanda King Yake uban iyayi kamar Babba sai kace King din gaske,Queen kuma kamar wata Budurwarsa sai wani basarwa take irin Bai dameta ba abin dariya yake bawa Na'im da Salma har so suke King yazo gidansu su kwashi kallon Yanda yake nuna Sarauta da gadara ga iyayin tsiya.
Salma tana saman bedroom jikin Window ta dage labile tana leken yaran har suka bar gidan,ta baya taji Na'im ya rungumo hips dinta zuwa jikinsa yana rada mata maganganu cikin kunne wani lafewa tayi a jikinsa tare da juyowa ta kara kankameshi kana ta dago tare da hade bakinsu wuri daya tana tsotsa dan danan ta rikita Na'im.
Bayan wata 8 Allah yasa Salma ta haifo danta Namiji sak Na'im kato lafiyayye,yaci sunan Baban Salma wanda ya rasu,Salma tace shi Prince za a dinga ce masa idan an haifi wata mace ko Zainura ko Afrah sai a sa mata Princess.
Wannan Family ba karamar rayuwa me dadi suke ba,sai dai abinda ba a rasa ba na rayuwa,amma Alhmdllh suna zaune lfy gwanin sha'awa.
Salma tayi arba'in Na'im yau Ango yake sai zumudi da murna ya rasa inda zai sa kansa,Salma tasha gyara da kyau wata arniyar rigar bacci tasa Da ita gwara babu fara Kal,gashinta yasha gyara,Na'im yana zuwa sunkutarta yayi sai bisa Bed blanket ya rufa musu baka iya jin komai sai nishinsu da Gurnani tare da kukan dadi,Baka ganin komai sai blanket dake motsi kawai alamar ana ehhhhhhh.
ALHAMDULILLAH
Anan na kawo karshen wannan Novel KAMARSU CE DAYA..da fatan an amfana anyi nishadi a ciki,ayi min Afwa idan an samu Kuskure ko wani abu da baiyi ba,dole dama sai da kuskure Dan Adam ajizine ne.
Ina matukar Godiya gareku fans readers na kowanne group,ina gaisheku da jinjina,Musamman masu Sharhi kune a gaba kune nawa kuma naji dadi na gode.
Ayi min Afwa fans na rashin page na yan kwanaki ban baku ba na shiga Busy ne ayi hakuri kunji hakan baza ta kara faruwa ba insha'allah.
Masu kirana ta waya da masu turo text na gode da kulawarku Allah ya bar kauna,wanda ban samu na daga ba ko kun kira kuyi hakuri Bana kusa ne na gode.
DIYAR KATIBI ina gaisheki,ban miki page ba sai Next novel Insha'allah.
Sai mun hadu a sabon Novel dina ba da dadewa ba,bazan fada muku sunansa ba sai na fara zaku gani, yanzu duk me Sharhi tayi ina Online ayi Sharhi mu kwashi nishadi Fans.
AsmaBaffa loves u all.
Zanyi missing dinku masu Sharhi,musamman AsmaBaffa fans club,Hause of Hausa novel,taskar fiddausi sodangi etc .😭😭😭😭😍😍😍😘😘😘😀🤣🤣😍😘.
AsmaBaffa
COPY BY ZAINAB BUTALAWA