Showing 63001 words to 66000 words out of 127542 words
kawayena hhhhh aka kwashe da dariya duk inda Na'im ya kai da son danne dariyarsa ina abin ya gagareshi, Zainura ta takura musu a motar da abin dariya iri iri har sunyi Nisa basu sani ba Sabo da iya shegen Zainura,Yanzu tace zata gwada Maganar Na'im yanda yayi a biki.
AsmaBaffa
[1/14, 5:14 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉
111-115 116-120
Official
By
AsmaBaffa
ZULY BEAUTY,ADABIYA ISAH,MRS MUKHTAR,BIBA,RAMCY MAKEUP
Wannan page naku ne.
AUTA ina godiya Allah ya bar kauna.
Mummy tana nan yanzu ba laifi ta rage damuwa sai dai duk hirarta in dai ba zancen Na'im zakayi ba to baza ta wani saurareka ba,amma idan Na'im ne to fa ko kwana zakuyi bata gajiya,duk an ganota ma ko magana za kayi in dai kana so Mummy ta nutsu to ka fara kawo zancen Na'im kana karfafa mata gwiwa cewar za a ga Na'im zai fito yana nan a raye.
Yau ma Aisha tazo tana so Mummy ta bata kudi zata canja mota ta samu Mummy a daki ta zauna gefenta tare da cewa Mummy naji a jikina Na'im ya kusa bayyana kwana nan,Mummy ta washe baki tace ai insha'allah,Aisha tace Allah yasa yana hannun na gari,kinga dakinsa Mummy shi yasa kullum sai na gyarashi gashi kinyi tunani da aka kara canjawa dakin komai kamar Aljannar Duniya ai Bro yana dawowa za a ga Murna,Mummy tace wlh kuwa ai kin sanshi da son harkar wanka,Allah sarki Na'im dina Allah dawo min dakai lfy,Aisha tace Ameen dai Momma zamu shirya shagali ranar ai har anko da party zamuyi,suna ta hirar Na'im Mummy tana Jin dadi sai Aisha tace Mummy yawwa dan Allah tuna miki zanyi kudin motar da za a bani na Canja,kisa ya Irfan Ya min Transfer dan Allah Momma kar Na'im ya dawo ya ganni da tsohuwar mota,Mummy dadi ya kamata fa tace duk motocin gidan nan Aisha gashi duk su Irfan sun canja sababbi har na Na'im ma fa saida su akayi aka kawo sabon yayi ki dauki daya ciki,Aisha tace Mummy wannan ai sai irin su Na'im sun min girma ina mace, waya Mummy ta dauka tare da dannawa Irfan kira lallai yau ya yiwa Aisha transfer na Milyan biyar zata canja mota,Irfan yace to Mummyn Na'im zan bata.
Aisha da murna taci gaba da hirar Na'im a gaban Mummy.
Borno state dangin Salma,Maimuna matar Hashim ta samu ciki wata Uku kenan,kullum bata da lfy laulayi,amma Hashim sabo da rashin godiyar Allah irin na Hashim duk ya manta yanda Maimuna take bashi kulawa a baya,yanzu kullum fada sukeyi,abu kadan tayi masifa,sabo da baya samun yanda yake so lokacin tana Amarya duk ya manta,wulakanci iri iri yake mata,Yana kallo tana Amai amma ko surarta bazaiyi ba,
Yanzu ma yana Palo yana kallon Indian film tana waje jikin pampo tana ta sheka Amai amma ko kallo bata isheshi ba,haka ta gama da kyar jikin ta yana rawa ta wanke wajen tare da gyara jikinta, ta dan matso jikin inuwa ta kwanta a kasan wajen,sanyin kasan take so sai da ta yayyafa ruwa me sanyi a kasan simintin ta jikashi sannan ta kwanta a kai,nan kuma ta jika dankwalin Atamfarta sharaf ta lulluba dashi tana jin dadin sanyin.
Hashim sai da ya gama kallonsa ya fito ko tausayi babu ya kalleta shekeke tare da cewa kar ki bata min Siminti da Amai fa ki kiyaye ki karaci kazantarki,kazamar banza wlh aure zan kara idan na gaji kin isheni,Maimuna ta kalleshi kawai hawaye ya gangaro mata ta dauke kanta tace amma kasan ba dashi nazo ba kai ka haddasa min wlh ban taba ganin marar Imani irinka ba Hashim,ke karki kawo min raini zan tattakaki ba ruwana da wani cikinki aikin banza wata tsiya kike tsinana min,da dare cuta,rana Amai,ko yaushe cuta wanne hakkina kike sauke min,malalaciya da an tabaki kice zazzabi kike tsaki yaja yayi gaba tara da bugo murfin kofar.
Masu zaman tsakar gida dai ana ta yi kullum ba fashi ana tona asirin aure,ana siyan magunguna,masu kulle mazajensu da me dan mukulli ma suna ta fama,Ubale ya gano abinda suke masa duk ya koresu gida da saki daya daya tare da rangado sabuwar Amarya Iklima,Iklima akwai hankali da ilmi ga kula da miji bata zuwa wannan hirar ta tsakar gida sai daí idan masu tallan maganin mata sunzo ta siyi me inganci Ta tafi wajenta,
Nan matan suka Sa mata ido wai ita a dole ustaziyya har habaici ake mata,Maimuna kuma bata fita yanzu Sabo da ba lfy,aiki ma Iklima ke zuwa tana gyara mata ko ina na gidan,har girki tana dan yi mata watarana.
Su Shehu ko zancen Salma basa yi ko da wasa ma.
Affa kuwa dabbobinsa sai karewa sukeyi daya bayan daya abin yana damunsa,Ummitu har da kuka cikin shanu 60 saura 45 maimakon su godewa Allah sai su suka kara shiga bokaye cewar Salma ce ta jawo musu ayiwa dukiyarsu katanga da Salma da sauran makiya,Ummitu tace mun riki bala'i da hannunmu har yanzu sharrin yarinyar nan binmu yake yi Allah ya Isa wlh babu wanda zai jawo mana sai Salma ita ce me kashin tsiya,Affa yace bama tare ma Baza ta barmu mu huta ba ko mayyace ne? Wa ya sani ai gwara mayu da wannan yarinyar,haka dai su Affa ko me ya samesu kullum zargin Salma sukeyi su basa ganewa.
Malam yana ta tuki tuni har sunzo Tafa hanyar Abuja,nan suka tsaya za a ci abinci,Na'im yace shi bazai ci ba,Malam yace ka kiyayeni fa na fada ma ka bar ganin ka warke ba ruwana da kudinka ubanka zanci wlh gwara ma kaci,Salma ta sheke da dariya,Zainura tace yo kai me kyau tare da mu ma kaci abinci duk baka sani ba sai yanzu,to har tuwon Dawa ka lashe a cikinka bare nan wajen yan gayu,Na'im ya gallawa Zainura harara harda cewa Salma ki fadawa kawarki ba ruwanta dani, Salma tace Allah yaci abinci da Ku? Ganin basu gane ba Zainura ta dinga raina musu hankali tace to har hannun Barira ya kwace nama ya cinye,Salma ke kuma kinga wannan Ubaliye me makeken baki da zamu taho? Salma tace ae me hakora yellow Zainura tace to kinsha cin tuwo tare dashi kika nace masa sai ya baki sidinsa,Na'im ya dinga dariya yana toshe hanci,Salma harda kwalla,Zainura tace kai me Kyau Allah ne fa ya ceceka Amma ka dade kana son Hadizalo wannan wacce zamu taho tazo tana min rada,Akwo tuni suka tuno suffar Hadizalon da Zainura take Nufi,Na'im yace Oh God have mercy on me.
Malam yace kai kuzo mu tafi mana suka shiga wani dan Restaurant na tashar aka basu Sakwara da miyar Egusi,Zainura ta gyara Zama tare da cewa Malam Allah dai ya dai ya biyaka tana zuba lauma,Haka Salma ma,su Umma,Na'im sai cakala yake cike da kyankyami,haka suka gama ci aka ci gaba da tafiya,Zainura tayi bacci motar shuru kake ji,Salma ma ta kwanta a kafadar Na'im har suka karasa Abuja Lfy Na'im ya karbi tukin motar kawai ya kaisu har bakin gate din gidansu,Nan kowa ya saki baki banda Salma da Na'im duk da cewa an canja komai na gidan new design.
Na'im ne ya fita ya buga gate din tunda ba remote a hannunsa,Securities da gudu suka yanyame gate din tare da dana bindigu,Zainura har yau bacci take abinta Salma ta tasheta,tana mika da Salati tace nan ne gidan ko kuwa wajen shakatawa mukazo,Umma tace ke karfa ki damemu ki nutsu,Zainura tace Umma daga tambaya.
Securities suna ganin Na'im suka gigice da ihu da murna,wasu da gudu suka fada cikin gida wajen Su Mummy gashi anyi sa'a yau Saturday duk suna gida,Mummy suka ji ihu ana Oga Na'im a gigice suka Mike gaba daya,Securities suna Haki suka bada labari gasu can da Salma da wasu dattijai tare da yarinya sa'ar Salma wai Zainura,Mummy bata San Sanda tayi sujjada ba ta nuna farin ciki,haka su Irfan ma,sai kuwa ga Na'im ya shigo da sallama,sai Salma,sai Malam da Umma,Zainura tana baya sai kalle kalle takeyi ta rasa inda zata kalla ma,
Tana shigowa ciki ta fara taka kafar a hankali tana sanda kamar barauniya harda dukawa,tana lallabawa,Hunaif dariyar Zainura ta kamashi kamar tana taka wata Kwalaba tana gudu karta yanketa,Mummy baki har kunne tana ku shigo dan Allah,nan ta rungume Na'im da karfi tana Hawaye sosai shima Na'im haka sun dade a haka,sai Su Irfanma suka rungumeshi ana ta murna da Hawaye,Aisha ce ta karshe tace Bro mun shiga wani Hali na rashinka we missed u so Much,Mummy kullum sai tayi kuka,Malam yace to Alhmdllh komai ya zo karshe,Mummy sai lokacin tace kuyi hakuri dan Allah ku zauna,Zainura tana tsaye taki zama sai kalle kalle takeyi bata gajiya,Na'im ya kalli Zainura yace to Zauna mana,
Zainura ta fashe da Kukan Dadi haka kawai aka ji tana kuka,kowa saida yayi tunanin wani abu ne ya sameta,Salma tace lfy Zainura?Zainura tana goge hawaye tace ni ya zanyi Allah yana sona ta kara zubo da Hawaye tare da cewa badan ikon Allah ba ya zanyi nazo garin nan har cikin wannan Aljannar duniyar haka cikin turawa,ni iya haka ma ya isheni darasi a duniya,ta kalli Na'im ta goge hawaye tace ni wlh na fasa auren Kanin naka kunnensa yayi ja da yawa gasu nan irinku daya ni jansa yayi min yawa yasin.
Hhhhhhhh gaba daya palon suka dinga dariya kamar me,Umma tace ke dalla zauna sarkin surutun jarabar tsiya ke ko ina bakya kasa magana? Zauna mana cewar Mummy tana dariyar Maganar Zainura,ta zauna kusa da Hunaif ta tashi ta dawo Kusa da Irfan nan ma ta mike ta dawo wajen Na'im tace alquran mijin Salma yafi fuskar Rahma.
Akayi dariya nan ma ta dawo wajen Malam tace ga na gida wanda na sani.
Mummy tace ya kamata kuci abinci ku huta kuyi wanka sai a zauna ayi maganar.
Salma ke da kike yar gida ki dauki Umma da Malam din ki kaisu dakin dake kasa yafi girma za sufi sakewa a can,Aisha ke ku tafi da Zainura dakinki ki koya mata komai ta shirya.
Salma ga dakinki nan dama ba wanda ke shiga gyarawa kawai akeyi,kaima Na'im haka,kuje ku fito aci abinci.Salma ta raka Malam da Umma dama Malam da Umma su wayayyu ne suna mu'amula da yan birni sun iya amfani dasu duk da cewa na gidan su Na'im basu taba ganin irinsa ba saida Salma ta nuna musu, ta wuce dakinta,Na'im tuni yaga yanda Bedroom nasa ya koma kamar wata Aljannar duniya,ya fada wanka,kayansu tuni guards sun kaiwa kowa dakinsa.
Aisha da Zainura suka shiga Bedroom tare,Zainura tace duk wannan dakinki ne? Aisha tayi murmushi tace ae mana Zainura tace cab yo mu a kauye ba sai mu goma mu kwana ciki ba,Kinga gidan su Zahrau kawarmu dakin kamar akurkin kaji Amma su Bakwai suke kwana daki daya,yara suyi ta tsula fitsarin kwance,Aisha tayi dariya tare da cewa mene Akurki? Zainura anyi har Jss3 tace cage na chickens hhh Aisha ta gane tace gaskiya ne,muje kiyi wanka da dare kya bani labarin kauyen naku,nan ta raka Zainura ta koya mata,Zainura ga basira har ta iya,Aisha tace Daura Towel ungo karbi,Zainura ta rufe baki da hannu tace a gabanki ki kallarmin jikina,kuma wannan guntun tawul haka ni dai bani Zani a Cikin jakata ina da abuna,Aisha ba musu ta zuge yar jakar Zainura ta dauko Zani spear har kamshi yakeyi ga brush dinta harda sabulu give guda da mudubi da Powder da jambaki ja har jagira,Aisha tace a ranta wannan a kauyen ma su daban suke gaba dayansu masu Tsabta ne jibi har tasan tazo da brush da toothpaste,harda kayan kwalliya,Nan dai ta bawa Zainura Zani ta cire kayanta tayi wanka tana gama wanka akwai botiki a toilet din ta wanke kayan da ta cire tas ta fito tace da Aisha ina zanyi shanya? Aisha ta nuna mata bayan corido nata ta shanya kayanta har pant data cire bra ce kadai kuma bata sawa.
Zainura ta fito Aisha ta kalli gashinta har kafada baki me santsi na yan fulani yasha kananan kitso sabo,Aisha tace yaushe kikayi kitson nan?tace jiya aka yi min yau sunan Kawarmu Allah yasa Malam ya taho dani nan garin,Aisha tace uhm yayi kyau,ai kema fara ce Amma kina ce mana jajaye? Zainura tace ba irinku ba ni ai bakace ko Salma ban kai haskenta ba bare ku turawa.suna ta hira har Zainura ta gama ta dauko riga da skert dinta shima na sallah ne Lace ba wani me tsada bane Amma dinkin dan dai dai ita tasa abinta harda yin acuci Maza Sabo da kitsonta shuku ne, ta yafa bakin gyalenta bayan ta shafa Powder da jambaki Amma bata Sa ko kwalli a idonta ba,ta kalli Aisha tace to ina zan Sa jakata kar ta hargitsa miki daki,ganin Zainura me tsafta ce Aisha ta karba ta sa mata a sip bari daban da bata Sa kaya,Zainura tace karki gaji dani naga kina danna waya na hau gadonki na kwanta ko shimfida zaki min? Aisha tace gadona fa kika ce? Ki tsaya a matsayinki karki ga na miki mutunci ki zake kuma zan mai dake dakin Salma ba wajena ba kina min kauyanci.
Zainura ta kalli Aisha tace toooo ikon Allah sai kice nima na fito da kalar daya halin nawa hali biyu gareki,dana mutunci dana tsiya gidan kikazo nima sune dani,kan Uba na miki kauyanci kikace gadonki din me?an fada miki bamu da gadon mu? Wlh baki Isa ki rainani ba sai dai ki raina tsohuwarki da tace nazo wajenki danma kin mun mutunci ne da farko Amma wlh da na nuna miki wace Zainura,Zainura taja tsaki,Aisha taji haushi kamarta wata yarinya karama yar kauye zata zageta dan kawai ta sakar mata fuska ita dama bata so Mummy tace yar kauye tazo mata daki ba,dama darajar Mummy taci har ta biyeta sukayi hira Amma da badan Mummy ba wlh da sai tayiwa Zainura duka a gidan.
Zainura ta fada saman gadon Aisha tana sani tace sai an hau ma a yankani,Aisha ta matsa gefe can tace ke nafa girmeki ba sa'arki bace Naga kina son rainani banza yar kauye zaki shafa min dirty,Zainura tayi banza da ita tace bazan biye miki ba mu zama daya Amma zanyi maganinki kafin na bar gidan nan,Nan Aisha ta dinga zage zage da mafisa tana ta ciwa Zainura mutunci akan yan kauye ne.
Mummy ce ta shigo ta dauka hira sukeyi ta kirki tsakanin Aisha da Zainura,tace ku fito aci abinci,Sun fito a hanya Aisha ta bangaje Zainura,haka Zainura ta kyaleta kawai.
Malam,Umma,Salma,Zainura,Aisha,Mummy,Irfan,Hunaif, Dada Babar Mummy, Na'im kadai ake jira,idan kuka ga wankan da Salma tasha sai ku rantse daga Misira tazo shigar larabawa tayi.
Abinci aka jera iri iri a palo ba a dining ba Katon carpet aka Sa wajen.
Kamshi ne ya cika wajen wanda yasa kowa kallon inda ake tahowa ba kowa bane face Na'im ya dau wanka cikin tsadajjiyar shadda fara yana kyalli da sheki,Malam da Umma kallonsa kawai sukeyi Kamar ba Muhd dinsu ba Sam ya manta dasu ko tunasu baiyi,haka Salma saida gabanta ya fadi Sabo da kyan da yayi,Mummy farin ciki sosai dasu Irfan da gani Na'im ba wahala yasha a inda yake ba,domin jikinsa hutu da jin dadi ya nuna ba wahala ba.
Kusa da Salma ya zauna tare da dan bugunta kadan a baya irin na tsokana murmushi kawai tayi cike da kunya Sabo da Mummy dasu Malam sun gani,Abinci aka baje kowa ya fara cin abinda yake so,Zainura ce kadai take ta ruwan ido ta rasa wanda zata fara da shi,Salma tace kici mana,Zainura tace ni dai a zabar min,Hunaif ya maka mata harara ya dauke kai, Dada tace yau naga yarinya da tsiya sai an zabar miki ma? Nan Zainura ta fara ci itama har suka gama ci kowa ya koshi
Malam ne yayi bismillah tare da Budewa da addua sannan ya fara bayani akan abinda ke tafe dasu,kowa yayi shuru yana sauraro.
Malam ya basu labari tun a inda ya tsinci Na'im sai Salma,da kuma irin zaman da sukayi cikin jin dadi da kaunar juna har dalilin da yasa ya daurawa Salma da Na'im aure tare da gabatar da shedu masu karfi,har littafin da aka rubuta da shedu ya basu Suka karanta,Mummy da Sauran mutanen wajen murna,farin ciki tare da jinjina sukewa Malam,godiya suke musu ba adadi,tare da fadawa Malam ba matsala dama can Saurayi da budurwa ne kamar yanda Na'im ya fada musu a kauye haka ma su Mummy suka basu labari.
Dada harda Kukan Dadi da tausayi,haka Mummy ma,bayan Malam ya gama bayaninsa ya sanar musu gobe zasu koma kauye,Mummy dasu Dada suka ce sai sunyi sati suna ta rokonsu da kyar suka yarda zasuyi kwana Uku sunki yarda da Sati dayan.
Mummy tace yanzu basu tuna wacce rayuwa sukayi daku ba Malam ina so in ba damuwa a bar mana Zainura a nan zuwa wani dan kwanaki tana tuna musu rayuwarsu ta baya da sukayi a kauye ko Allah zai sa Memory nasu na baya ya dawo gaba daya,idan zuwa wani lokaci bai dawo ba da kaina zan dawo da Zainura gida,Zainura Zaraf tace Allah Baffana bazai yarda ba sai dai idan Malam ne ya masa bayani,ni dai nafi son kauyenmu Yasin kina gani yanda wannan Aisha take min rashin mutunci a dakinta idan ana so na zauna sai dai a hada mu daki daya da Salma idan ba haka ba Alquran kauyenmu zan tafi nima ina da iyaye suna sona ko bamu da kudi na rungumi talaucinmu bana maitar abin duniya.
Na'im yace sai dai a baki Room ke kadai dai