Showing 45001 words to 48000 words out of 104561 words
, kullum ni ce fada da yaran mutane har na ji musu ciwo , kullum sai sun kai kara ta wajen mahaifina shi kuma ya yi min fada wani lokaci ya cilas ta min na je na bawa yaran hakuri , har ya kai ya daina bari na fita kullum ina cikin gida gudun kar na janyo wani fadan , wata rana ina tsaka da barci na kawai na ji hannun mutum a jiki na , ina bude idanuna su ka sauka kan yaron matar mahaifina , dama ta taba yin aure har da yaron ta guda wanda ya ba ni kusan shekara biyar haka , cikin tsoro na mike ina tambayar shi me ya kawo shi daki na , kawai ya shiga ce min wai na bashi hadin kai ya biya bukatar shi da ni dan ya jima da wannan burin a ran shi , ni kuma na ki yarda , hakan ko ba karamin bata mishi ya yi ba kawai sai ya yi kokarin cin zarafina , ni kai na ban san ya hakan ta faru ba kawai sai bude idanu na yi na ga gawar shi konce a gefe na babu kai a jikin shi , lokaci guda na fita cikin hayacina dan abun ba karamin tsorata ni ya yi ba , lokacin da matar mahaifina ta shigo dakina dan ta tashe ni kawai sai ta ga yaron ta konce ba kai , nan take ta shiga kira na da mayya wai na kashe mata yaron ta , ko tsayawa ba ta yi ba ta fice gidan ta kiran mayya mayya ta kashe mata yaron ta , a haka har mutane su ka fara taruwa cikin gidan , duk irin magiyar da na yi musu ina cewa ni ban san abun da ya faru ba amma su ka ki yarda , sa'a ta guda kora ta su ka yi da ga cikin kauyen ba su kashe ni ba , bayan sun kore ni mahaifina ya biyo baya na ba tare da sanin kowa ba ya kai ni wajen wani dan uwan shi da ke zaune a kaduna , bayan ya kai Kaduna ne na hadu da Abban Abdoul , da sannu sannu har mu ka fara soyayya mu ka zo mu ka yi aure , na san ka abun da ya faru lokacin da ka karbi budurcin ta , to ni ma hakan ce ta faru , ba karamar razana Abban Abdoul ya yi , shi a tunanin shi aljana ce ma ni , ni kuma ban ma san maganar me ya ke min ba , sai dai kawai na yi zaune na yi ta yi mishi kuka , da ya ga kukan nawa ya fara yin yawa zan iya cutar da kai na , kawai ya hakura ya danne abun da ke cikin zuciyar shi ya dinga rarrashi na , a haka har na samu cikin Abdoul , lokaci guda na haife shi ko nakuda ban yi ba , haka zalika Nesrine , amma na Inaya , sai da na yi kamar zan mutu dan har suma na dinga yi kafin ta shigo duniya , lokacin da ta fara tasowa irin jarabar ta , kawai ta ke jan Nesrine fada kuma ta ba ta kashi duk da ita ce karama , ta sa sha Nesrine kuka ba dalili , bayan kuma wani lokaci ta daina kamar ba ta taba yi ba , kawai ta shiga yin wasu abubuwa kamar mara hankali , bayan Abban Abdoul ya bude makarantar islamiya ne kawai mu ka samu saukin abun da ke damun ta , na san ka sha yin mamakin yadda ta ke wasu abubuwa wanda ba dai'dai shekarun ta ba ne , ba ita ba ce aljanun da ke jikin ta ne su ke birkita mata kwakwolwa , duk cikin yarana ita kadai ce ta yi gadon aljanuna Abyad da Aswad , idan sun ga dama su sakin min kwakwolwa idan kuma su ka so su rufe ta na manta komai na rayuwata ta baya , ni ko yanzu na yi mamakin yadda a ka yi na ba ka wannan labarin " ta na gama fadar haka ta ja wani dogon nunfashi
shi dai Malik shiru ya yi ya na sauraron ta ya kassa cewa komai
sai da su ka share good ten minutes a haka kafin ya bude baki a hankali ya ce " it means da aljanu a jikin ta ? "
gyada mishi kai mama ta yi ta fadin " Eh da aljanu a jikin ta , lokacin da ka......... to a lokacin su ka tashi , kar ka ji tsoro ba abun da za su yi maka sai ma ba ka kariya da za su yi saboda kai da ita kun zama abu guda yanzu , Abyad ita ce me kula da lafiyar ta duk wani ciwo da zai iya shiga jikin ta sai ta kawar da shi shi ya sa da ta ci poison din nan ba abun da ya same ta , Aswad kuma gaskiya ban sani ba , sai dai nan gaba idan ta fito ka ga nata aikin , amma zan ba ka shawara , duk abun da za ta fada maka ka yarda da ita dan ba za ta iya fadin kariya ba , idan kuma ta ce maka ka yi abu kawai ka yi ita ta san dalilin ta na yin hakan "
dan lumshe idanun shi a hankali Malik ya yi ya ma rasa abun da zai ce , shi dama ya san akwai abun da ke damun babyn shi amma bai yi tunanin haka abun ya ke ba
ya na haka kawai ya ji hannun mama saman cinyar shi
slowly ya bude idanun shi ya na kallon ta hannun ta kafin ya dago kai ya kale ta
wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " Zayd , ka san za ka iya fadamin abun da ke damun ka ko ? "
gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya juya ya sunkuyar da kai ya na kallon hannayan shi
" shikenan fada min to , ko dai abun da na fada maka ne ya tada maka hankali ? don Allah ka kontar da hankalin ka , har yanzu Inayar ka ce b....... "
cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " a'a mama , ni ba wannan abun ke tada min hankali ba , har ga Allah ina son na dauke ta mu bar wajen nan , mu tafi inda babu wanda zai yi kokarin rabani da ita , zama na a nan wlh babban hatsari ne ga rayuwar baki daya , yanzu ni kawai jira na ke momyna ta tashi na dauke ta mu bar wajen nan , amma doctor ya ce min shi bai san abun da ke damun ta ba , na rasa ya zan yi " ya kai karshen ya daura hannun saman forehead din shi
shiru mama ta yi ba tare da ta ce komai ba , da ga gani ka san ya na cikin matsananciyar damuwa , amma ya shanye kayan shi kar ya takurawa mutanan da ke zagaye da shi
wani dogon nunfashi mama ta ja kafin ta ce " na tambaye ka ? Inaya ta yi maka wata magana a kan ita momyn taka ? "
shiru Malik ya yi kamar mai tunanin wani abu
cen kuma sai ya ce mata " ta ce min kamar ba ruhi a jikin ta , ni ban gane abun da ta ke nufi shi ya sa na share kawai "
" ina ga tun da ta fadi hakan , to tabbas babu ruhi a jikin ta ....... "
cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " ban gane ba ? " ya kai karshen ya na dago kai ya kalli mama
dan jinkirtawa ta yi ta na shirin magana ta ja wani dogon nunfashi har sai da kirjin ta ya yi sama , idanunta su ka koma farare kal har wani haske su ke yi kamar torch
a hankali ta bude baki ta fara magana da wata murya ta daban mai amo ta na fadin " kamar yadda ta ce babu ruhi a jikin ta , sai ka yi hankali dan wanda ya yi mata hakan ba karamin hatsari ne da shi ba , za ku fuskanci babban tashin hankali idan ku ka fitar da ruhin ta da ga wajen da ga su ka boye shi "
ta na gama fadar haka idanun ta su ka dawo dai'dai ta fadi konce saman gadon ta nunfashi sama Sama
a hankali Malik ya ce mata " are you okay ? "
a hankali mama ta sauke ajiyar zuciya kafin ta mike zaune ta na yi mishi wani irin kallo ta ce " Zayd , tun yaushe ka ke nan ? Allah ya sa ba wani abu autar tawa ta yi maka ? "
cak Malik ya tsaya ya na kallon ta cike da rudu
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya girgiza mata kai ya na cewa " ba komai "
wani dan karamin murmushi mama ta saki ta na cewa " shikenan , ka na dai lafiya ko ? "
gyada mata kai ya yi ya na fadin " zan tafi , idan na samu lokaci zan dawo " ya kai karshen ya na kokarin tashi
da sauri Mama ta ce mishi " don Allah idan za ka dawo ka taho min da Auta ina son ganin ta "
" in sha Allah " ya fada a takaice ba tare da ya juyo ba , ya na cire button din kofar ya cire security ya bude kofar ya sa kafa ya fita ya bar mama nan zaune
bangaran Malik kuwa kai tsaye part din ya baro , ko da ya fito a na shirye shiryen kirayen Sallar Azahar , kai tsaye Mosque ya wuce , ko da ya kammala Sallat ya nufi likita wajen MALIKAT AL'UMU
▪TESNIM
zaune ta ke cikin garden saman ciyayi ta na cirar flowers ta na wakar ta , da allamun yau ta na cikin annashuwa
ta na a haka ta ga an miko mata rose ta bayan ta
cak ta tsaya da wakar ta , ta na bin rose din da kallo , kafin ta juya
nan ta ga Abdoul tsugunne a bayanta ya saki wani cool murmushi
a hankali ta kai hannu ta karbi rose din ta na yi mishi godiya
a hankali ya dawo gabanta shi ma ya zauna a kassa ya ce mata " da allamun yau ki na cikin farin ciki ? "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai ba tare da ta ce komai ba
" ko zan iya sannin dalilin ? " ya fada ya na daga mata gera guda
ba tare da ta dago kai ba ta ce mishi " ai ka fi kowa sani "
murmushi mai dan sauti ya yi ya ce mata " shikenan , tashi mu koma ciki "
noke mishi kafada ta yi ta na fadin " ni na fi jin dadin zama a nan , yanayin garin yau akwai dadi "
" hmmm shi ya sa ki ka taho ki ka bar ni , sai da na bude ido na ga baki kusana "
" sorry ba na son na tashe ka ne " ta fada cikin sanyin murya
a hankali ya mike tsaye , sannan ya mika mata hannu ya na fadin " tashi mu koma , na shirya miki wani abu "
" da gaske ? " ta fada ta na dago kai ta kalle shi
gyada mata kai ya yi ya na sakin mata wani kyawatencen murmushi
a hankali ta daura hannunta saman nashi ta mike tsaye a hankali
a tare su ka fara takawa ba tare da ya ce mata komai ba har su karaso part din shi
kai tsaye bedroom din shi su ka wuce ya na rike da hannunta
sai da su ka shigo tsakiyar dakin sannan ya saki hannun ta
cikin rudu ta ce mishi " ina abun da ka shirya min ? " ta fada dan ita ba ta ga komai ba cikin dakin
a hankali ya zagayo da hannayan shi saman cikin ta ya rungume ta ta baya ya kontar da kan shi saman shoulder din ta
cikin nitsuwa ya ce mata " wa ya ba ki izinin fita ? "
" hmmm dama dan ka yi min fada ne ka sa na dawo ? " ta fada ta na daura hannayan ta saman nashi
a hankali ya girgiza mata kai ya na cewa " no , kawai dai ban ji dadi ba na bude ido ban gan ki ba , please ki daina tafiya ki bar ni "
a hankali ta juyo ta rungume shi ta kontar da kan ta saman kirjin shi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " sorry my baby , kawai dai ba na jin dadin jikin na , shi ya sa na fita na sha iska "
" da gaske ? " ya fada ya na dago kai da ga saman shoulder dinta
a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh
" shikenan , mu ja na yi miki tausa "
da sauri ta dago da ga jikin shi ta na fadin " Tausa kuma ? "
gyada mata kai ya yi ya na kai hannun ya zame Alkyabar jikin ta , ya tila saman sofa , sannan ya riko zip din rigar ta ya fara yin kassa da shi
da sauri ta raba jikin ta da nashi ta na zaro idanu ta ce " me ka ke shirin yi haka ? "
" tausa zan yi miki mana "
tsuke fuska ta yi ta na kallon shi ta ce " tausa kuma shi ne ka ke kokarin cire min riga ta ? "
wani cool murmushi ya sakin mata ya na daga mata gera allamun Eh
da sauri ta girgiza mishi kai ta na cewa " no , ni ba na so , na ma tafi wanka zan yi "
" mu je na yi miki " ya fada ya kashe mata ido guda
wata muguwar harara ta wurga mishi ta na fadin " ni yarinya ce da za ka yi min wanka ?
a hankali ya girgiza mata kai ya na fadin " no ke ba yarinya ba ce , shikenan tafiyar ki " ya kai karshen ya na takowa bakin gadon shi ya zauna ya fido wayar shi da ga cikin aljihu ya fara latsawa
tsayawa ta yi ta na kallon shi ta na sakin wani cool murmushi
a hankali ta kai hannu ta ida zuge zip din rigar ta , sannan ta yi kassa da ita ta fida ta , sai underwear kadai a jikin ta
a hankali ta tako bakin gadon ita ma ta zauna geffen shi , ta zagayo da hannayan ta a kugun shi , ta rungume shi ta lumshe idanun ta
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya daura hannun shi saman bayan ta ya kai lips din shi saman forehead din ta ya manna kiss ya na fadin " kin fasa yin wankan ? "
girgiza mishi kai ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce " ni kai za ka min "
" yanzu fa ki ka ce ba ki so na yi miki ? " ya fada ya na kai hannu saman bedside drawer ya ajiye wayar shi
" to ai yanzu kuma na ce ina so , kuma dole ka min ko kuma na yi maka kuka " ta fada cike da shagwaba
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ba sai an yi haka ba , tashi mu tafi "
wani murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta dago da ga jikin shi
a hankali ya mike tsaye kafin ya juya ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya fara takawa ya nufi toilet ya na fadin " ya na ji kin kara nauyi ? "
murguna mishi baki ta yi ta na kauda kai gefe ba tare da ta ce mishi komai ba dai'dai lokacin da ya shiga toilet da ita ya sa kafa ya medo kofar
a tom ni bari na juya tun da hakane abun
❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
BOOK ________3 👑✌
______________________⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘___________________
{ P A G E ………15 🌹🕊}
▪INAYA
a hankali ta ke tafiyar ta cikin masarautar , ta na sanye da wata Abaya pink color ta yi Rowling veil din ta a kai ta na tafiya cike da nitsuwa
ta na a haka kawai ta ji ta buge mutum har sai da su ka yi wani dan baya a tare
wani dan karamin tsaki Rouksar ta ja ta na fadin " wai ke don Allah kullum sai kin buge ni , ba ki gani ne ko kuwa ? "
shiru Inaya ta yi ta na bin ta da ido babu ko kiftawa
hararrar ta Rouksar ta yi kafin ta raba ta geffen ta za ta wuce
cak Inaya ta riko hannun ta , ta medo ta baya da karfi
a razane Rouksar ta ce mata " ke lafiyar ki kuwa ? "
cikin sanyin murya Inaya ta ce mata " ina ki ka boye shi ? "
Duk Rouksar ta ji gaban ta ya fadi , murya na kerma ta ce mata " me me ki ke magana a kai ? "
" kar ki ce za ki raina min hankali , ki fada min ina ki ka