Showing 99001 words to 102000 words out of 104561 words

Chapter 34 - Exiled Prince Book 3 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

405


bai ce mata komai ba har sai da ya raba ta da bra din ta ya ajiye gefe sannan ya ce " it's a surprise "

har ta bude baki za ta yi magana kawai ta ji ya sauke lips din shi saman nata
a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta lumshe idanunta ta fara biye mishi ita ma


▪AFTER SOME HOURS



a zaune duk su ke a dining room din part din Malik su na yin diner , MALIKAT AL'UMU , MALIKAT INAS , mama , Diya , RIANNA , Tesnim , Nesrine , Junior , Inaya , Abdoul , Yarinyar wajen Tesnim da shi kan shi Malik duk su na zaune saman dining room sai cin abincin su su ke su na hira su na dariya gwanin burgewa

cen na hango Prince konce saman Sofa , ya na rike da phone din Inaya ya na latsawa
a hankali ya sauko da kafafun shi ya mike tsaye ya fara takawa cike da izza ya karaso wajen Malik , ya kai hannu ya dan bubuga cinyar shi

a hankali Malik ya juyo ya kalle shi ya na fadin " what happening my Prince ? "

" Daddy , wannan lion na ke son ka saya min " ya fada ya na nuna mishi screen din wayar hannunshi

da murmushi a face din ta MALIKAT INAS ta ce " My prince , me za ka yi da lion kuma ? ba ka tsoron ya ji maka ciwo ? ko dai Teddy ne ? "

tsuke fuska Prince ya yi cike da dakiya ya ce " ba Teddy ne ba , Lion din gaske ne kuma sai an saya min "

a hankali Inaya ta daura hannun saman kan shi ta na fadin " Prince , ba fa lion din gaske ba ne Teddy ne , ba ka gani da kyau ba "

" to momy ai ni lion din gaske na ce ina so , ba Teddy ba , Daddy ka fada mata mana " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan Malik

da sauri yarinyar da ke zaune saman cinyar Tesnim ta ce " Uncle , ni ina son Teddyn "
wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " ke dai princess , duk Teddyn da gare ki ba su ishe ki ba "

ta na gama rufe bakin ta Prince ya marairaice fuska kamar zai yi kuka ya na kallon Malik ya ce " Daddy "
a hankali Malik ya kai hannu ya dauki Prince ya daura saman cinyar shi , ya na fadin " da ka tashi dauko rigimar momynka sai da ka fita , me za ka yi da lion don Allah ? kuma lion ba ya cikin dabobin cikin gida , bari zan sayo maka Dog or cat wane ka fi so ? "

" Lion " ya fada a takaice

" ya salam " Malik ya furta a hankali cikin zuciyar shi kafin ya ce " okay , zan siya maka , kafin mu koma US , shikenan ? "

da sauri Prince ya girgiza mishi kai ya na fadin " Yeah , that's why i love you more than momy "

da sauri Malik ya rufe mishi baki ya na fadin " yi shiru kar ta ji "
ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " na ji ai , kuma na yi fushi da kai kar ka sake min magana " ta na gama fadar haka ta tashi ta nufi corridor

sai da ta shiga sannan Malik ya bude bakin Prince ya na fadin " ka gani ko ? to ai yanzu sai ka tashi ka je ka bata hakuri tun da ka bata rai "

ba musu prince ya sauko ya bi bayan momyn shi
da ga haka su ka ci gaba da cin abincinsu , su na hira har sai da su ka kammala sannan kowa ya tashi ya nufi part din shi

Malik da Diya kuma su ka zauna a parlour

sai da Diya ya tashi ya na yi wa Malik sai da safe ya tsayar da shi ya na cewa " please ka sa a shirya min Helicopter gobe wajen karfe 10 ko 12 haka "

cikin rudu Diya ya ce mishi " Helicopter kuma ? akwai inda za ka je ne ? wai kai ba ka iya zama waje guda ? ka san sunan da a ke kiran ka da shi ? THE EXILED PRINCE , babu wanda bai san wannan sunnan ba cikin Saudiya "

" yeah I'M AN EXILED PRINCE , I bought the island of Palawan in the Philippines three years ago , ina son mu tafi ni da ita , ta ga gidan da na yi mana a cen "

dan zaro idanu Diya ya yi ya na fadin " noooo , you're serious , yanzu Islande guda sukutum ka saya ? "

gyada mishi kai Malik ya yi ya na fadin " yeah , har da gidaje ma a sama dan yanzu haka a na cikin gina na ukun , ni dai ka yi abun da na sa ka please , kar ya wuce kar ya wuce karfe 12 please "

" nawa ka saye ta ? a sani na Island din Palawan ita ce No 1 a cikin jerin wajajen Tourism , ta ya a ka yi ka saye ta ? "

" five hundred millions of American dollars na yi cinikin ta , that's why su ka yarda , akwai kuma wata private Island a Thailand cikin archipelago din Koh Samui da a ka saka a kasuwa last year , ita ma na saye ta "

shi dai Diya ya tsaya kawai ya na kallon shi , ya ma rasa abun da zai ce wa Malik

" okay , zan sa a shirya muku duk abun da ya dace , Allah ya kiyaye hanya , Hope dai ba za ku jima ba ? "

mikewa tsaye Malik ya yi ya na fadin " don't worry , just one week ne za mu yi mu dawo , kar ka fadawa kowa maganar tafiyar nan please "

" okay , sai da safe "

" sai da safe " Malik ya fada ya na nufar corridor , Diya kuma ya nufi lift

kai tsaye bedroom din su Malik ya koma , ya shiga ya ga Inaya konce tare da Prince har sun yi barci
wani cool murmushi ya saki kafin ya taka ya shiga toilet ya yi wanka sannan ya fito ya shirya cikin kayan barcin shi kafin ya nufi bed din ya haye a haka har barci ya yi gaba da shi shi ma



▪WASHE GARI ⛅⛅


A hankali ta ware idanunta ta na karanto addu'ar tashi da ga barci
ta na gama karantawa ko ta jiyo Muryarshi ya na fadin " sarauniyar barci , sai yanzu a ka tashi ? "

wani cool murmushi ta saki kafin ta mike zaune ta kontar da kan ta saman bayan shi ta na fadin " barka da safiya baby "

" barka , yanzu tashi ki je ki yi wanka ki zo ina jiran ki yi sauri please "

da to kawai ta amsa mishi kafin ta mike ta sauko da kafafun ta kassa ta nufi toilet ta shige
jim kadan ta fito sanye da bathrobe
har ta nufi dressing room ta jiyo Muryar shi ya na fadin " ga su na fiddo miki "

ba musu ta nufo shi , har ta kai hannu za ta dauki kayan , ya taro ta ya na fadin ta bari zai saka mata da kan shi
ba ta yi mishi musu ta tsaya ya saka mata kayan kamar wata baby , ya feshe ta perfume sannan ya kai hannu saman bedside drawer ya dauki bowl din fruits salad din da ya hada mata da kan shi ya ba ta

wani cool murmushi ta saki ta na fadin " na gode sosai baby , kamar ko ka san abun da ke cikin rai na "

daga mata gera guda ya yi ya na fadin " da Gaske ? "
a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh
" shikenan , cinye ina zuwa " ya fada ya na tashi ya fice dakin
ba musu ta fara shan fruits salad din nan , sai da ta shanye dukka sannan ta ajiye bowl din saman bedside drawer

ta haye saman bed din ta konta , kamar ba yanzu ba ta tashi da ga barci
ten minutes bayan konciyar ta Malik ya dawo cikin dakin
ya na ganin ta konce ya saki wani cool murmushi ya karaso bakin gadon ya zauna ya kai dan bakin shi saman forehead din ta ya manna mata kiss



▪AFTER SOME HOURS ( misalin karfe 6 na yamma )


▪ISLAND OF PALAWAN


▪INAYA



konce ta ke tsakiyar wani lafiyayen gado mai mugun laushi , ya na shinfide da wata bedsheet white color , ta na sanye da wata bathrobe pink color

a hankali ya motsi ta na kokarin tashi , da kalmar shahada a bakinta ta farka kafin ta ware idanunta a hankali
slowly ta mike zaune ta na bin wajen da kallo , gaskia bedroom din ya hasu ba kadan ba , a cen geffen hagunta , kawai sai ta ga teku , ya yi wani blue mai mugun kyau , ga rana ta zo faduwa , kun dai san yadda yanayin sky ya ke idan rana ta zo faduwa , musaman wajen su karfe 8 din nan abun ya na da matukar kyau , ga wani dan balcony nan , an saka mishi wasu chair gwanin burgewa , sai wata yar karamar chair kamar table karamar stair makale da karyar balconyn

sai a lokacin ta fara jiyo wata music mai dadi na tashi cikin bedroom din
ta na tsaka da juye juyen ta kawai sai ta ga wall din glass da ke fuskantar bed din ya rabu gida biyu , ya zuge kan shi gefe da gefe
sai ga Malik a tsaye ya na kallon ta ya riko hannayanshi a baya da ga shi sai short

ta na ganin shi ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauko da gudu da ga saman gadon ta nufe shi ta fada jikinshi ta na fadin " da farko na zata mafarki na ke , amma da na gan ka na tabbatar ba mafarki na ke ba "

wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " mafarkin ki ne ya zama gaskiya "
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta dago da ga jikin shi ta na bin wajen da kallo , tamkar gidan da a ka fiddo da ga cikin film haka ya ke dan musaman duk walls din gidan na glass ne , ga wasu tsadadun fournitures farare kal da a ka kawata shi da su

a hankali ta dawo da kallon ta gare shi , kafin ta yi magana ya yi sauri kai hannu saman lips din ta ya na fadin " mu je ki gani "

ba musu ta bi bayan shi su ka iso saman balconyn nan
murmushi mai dan sauti ta yi ta na fadin " baby , it's so beautiful , don Allah ko cikin film mu ke ne ? "

" ba film ne ba zahiri ne , wannan shi ne gift din da na yi miki alkawari last five years "

dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi , ita ko a lokacin da ta fada mishi hakan cikin wassa ne , ba ta yi tunanin zai dauki abun serious ba , bare ya yi abun da ta ce , ita ba ta ma san gift din minene ya ba ta , kawai ya tambaye ta wane irin gift ta ke so ta ba shi amsa

ta yi nisa duniyar tunaninta kawai ta ji ya raba ta da bathrobe din jikin ta , ya bar mata underwear kadai , ya ajiye bathrobe din saman chair a gefe
, da sauri ta ce mishi " baby , ba ka tsoron wani ya gan mu a haka ? "

a hankali ya sa hannu ya dago ta , da sauri ta zagayo da kafafun ta a kugunshi , hannayanta kuma a wuyan shi ,
murya kassa kassa ya ce mata " babu kowa a wajen nan da ga ni sai ke , sai Allah , sai wacen mai idanun mage da ta tsare mu da ido "

wata yar karamar dariya Ta yi ta na fadin " baby , where is prince ? "
" ya na wajen Ammie da RIANNA , babu kowa a wajen nan da ga ni sai ke "
" to yanzu me za mu yi " ta fada ta na daga mishi gera guda

a hankali ya fara takawa ya nufi yar table din nan kamar stair a bakin kariyar balconyn ya haye sannan ya ce mata " close your eyes "
ba musu ta lumshe idanunta ta na sakin murmushi
" kin shirya ? " ya fada cikin sanyin murya
" na shirya " ta fada duk da ba ta san abun ya ke shirin yi ba

ta na gama fadar haka kawai ta ji sun yi sama , wata kara ta saki ta ware idanunta dai'dai lokacin da su ka tsunduma a cikin ruwan Tekun

a tare su ka dago ta na janye kafafun ta da ga saman kugun shi , amma ba ta janye na wuyan shi ba ta wata yar karamar dariya , shi kuma ya zagayo da hannayanshi a kugunta

" ya ? da dadi ? " ya fada ya na daga mata gera guda

wata yar karamar dariya ta yi ta na gyada mishi kai , kafin ta juya ta kalli rana har ta shige kadan a ke iya gani , da murmushi a face din ta ta ce " it's so beautiful "

ta na gama rufe bakin ta ya daura da cewa "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login