Showing 78001 words to 81000 words out of 104561 words
musu dogarin nan ya tako gadan² ya na zaro takobi wai cire kan Malik
lokaci guda Malik ya kai hannu baya ya fido gun ya juya ya harbe dogarin nan tsakiyar kai , nan take ya fadi kassa matace
ba karamar razana Aymane da mutanan fadar su ka yi ba
a hankali Malik ya juyo , ya saita kan Aymane ya na fadin " idan na ga dama , move guda zan yi na aika inda ka aika mahaifina , amma zan ba ka damar ci gaba da rayuwa , ka sauka da ga kujerar nan "
cikin bacin rai Aymane ya mike tsaye ya na fadin " ba ka da ikon ce min na sauka da ga saman kujerar nan , kai da kanka ka bar ta , kowa ya na shaidar ka hakura da kujerar nan a bisa tsarin masarautar nan , duk Malik din da ya hakura da kujerar shi , ba shi da izinin komowa da sunnan zai koma saman kujerar shi , dan haka ba ka da ikon ce min na sauka "
ya na gama rufe bakin shi ya ga Rafik ya shigo cikin fadar ya na fadin " as a direct descendant of Malik HACHIM bin JAABAR, he has every right to claim the tron of his late father, even if he renounced him "
" Gaskiya Rafik ya fada , dan haka malam ka tattara kayanka ka yi gaba " Fadin Diya ya na karasowa geffen Malik ya tsaya ya na sakin murmushi
" No ! " Aymane ya fada da karfi ya na mikewa tsaye ya ci gaba da cewa " No , ba ka da izinin ce min na sauka , ba ka san irin famar da na sha kafin na hau saman kujerar nan , tun kafin ka shigo duniya na shirya hawa na kujerar nan ta Malik dan har yaron MALIKAT INAS na kashe , na kuma sace mahaifar ta dan kar ta samu wani babyn , amma wannan banzan uban naka ya auri kanwar Daddy , ta haife ka , tun ranar da ka shigo duniya , tawa duniyar ta ruguje , ni na sakawa part din Malik wuta shekara shidda baya kawai dan ka mutu na dawo na kashe Malik , amma wani ikon Allah dan banzan yaron nan ya rayu , okay na hakura , why za ka dawo ? me ya sa ba ka yi zaman ka a cen ba ? amma sai da ka dawo ka shiga tsakanina da burina , amma ban hakura ba ni na juya kwakwolwar Hakim ya harbi Malik saboda ya kassa kashe shi , ni na sa Rouksar zuba mata poison cikin abincinka , ni na saka ta sace ruhin MALIKAT AL'UMU , amma wacen banzar yarinyar ta ruguza shirina baki daya , why ba za ku bar ni na hau kujerar nan cikin konciyar hankali ba ? why ? , wlh ko da sama da kassa za ta nade , ba zan sauka da ga kan kujerar nan ba " ya fada cike da bacin rai da allamun fasuwar rai ta kama shi
duk mutanan wajen sai da su ka yi salati su na sauraron abun da Aymane ke fadi , bacon zai ya sa ya tonawa kan shi asiri da kan shi
shiru Malik ya yi ya na sauraron abun da Aymane ke fadi , dole ya yi mishi ta wayo dan ya samu ya sauka da ga kan kujerar nan , Idan ya ce zai ta karfi , ba zai yi nassara ba , dole shi ma ya yi tunani kamar na su na mugaye , dole ya meda kwakwolwar shi irin tasu kafin ya samu Aymane ya sauka da ga kujerar nan , dama an ce mugu shi ya san makwontar mugu , cuta ce za ta dau cuta
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya , cike da nitsuwa ya ce "as the heir of Malik HICHAM bin JAABAR I have the right to claim the throne of my late father, but since you do not want to give in passively okay, Aymane Abdoul Mujeeb Me Nawfel HICHAM bin JAABAR I provoke you in a duel, the winner will ascend the throne of Saudiya and the loser will pay with his life "
a dubu dari Rafik da Diya su ka kalli Malik su na zaro idanu , har su na hada baki wajen cewa " ka na jin abun da ke fada kuwa , hakan na nufin idan ka fadi kashe ka zai yi "
cikin kwarin guyiwa Malik ya ce " Eh , na ji abun da na fada "
ya na gama fadar haka Aymane ya bushe da wata shegiyar dariya har da tapi ya dafe ciki
shiru kowa ya yi ya kallon shi kamar wani zarrare
sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya dago ya kalli Malik ya ce " kai a ganin za ka iya kashe ni ? , ko ka kashe ni kamar ka kashe maciji ba ka cire kai ba , Okay na yarda , wane irin duel ka ke so mu yi ? "
" Sword Duel " ya fada a takaice ya na kallon Aymane
sake bushewa da dariya Aymane ya yi ya fadin " okay , na yarda , in dai ta haka ne kawai zan zauna saman wannan kujerar , na yarda , kai kuma ka shirya tarda tsohon mahaifinka , dan har yanzu ba a yi wanda zai ga bayan Aymane bin Abdoul Mujeeb , ko mutuwa tsorona na ke , bare kai ragon banza "
" All right , tun da ka yarda fine , yau ranar monday , za mu yi shi a ranar Friday , amma kafin nan , da ga kai har wadanan mutanan fadar taka , ba ku da izinin shigowa fada da sunnan aiki , har sai mun kammala duel din mu , sannan da ga yanzu ka fita da ga Malik Aymane , ka koma Aymane , har zuwa lokacin da za mu kammala , a nada wanda ya yi nassara a matsayin sabon Malik "
" okay " Aymane ya fada a takaice kafin ya sa hannu ya cire Alkyabar Malik da ke jikin shi ya ajiye saman chair din bayan shi , ya cire Rawanin kan shi ya ajiye saman Alkyabar , sannan ya juyo ya fara takawa ya karaso gaban Malik ya tsaya
sai da ya kalle shi cikin ido sannan ya ce " mu zuba mu gani , shege ka fassa , Nawfel Hicham Bin Jaabar tun yanzu ka sa a shirya kabarin ka , da ni ne kai zan ce a yi shi nesa da na mahaifina dan kar ya ga wane irin lusarin yaron da ya haifa " ya kai karshen ya sakin wata yar karamar dariya ya raba ta geffen shi ya wuce
ya na fita Malik ya saki wata yar karamar sheet da ya rike a hannun shi a baya
nan take wajen ya fara zubar da jini
a dubu dari Rafik ya riko hannun nashi ya na fadin " Inallillahi , ranka shi dade , why za ka ji wa kanka haka ? "
a hankali Malkk ya sauke ajiyar zuciya ya na fadin " dole na yi hakan , if not zuciya za ta debeni , na buge shi "
ya na gama fadar haka ya dago kai ya kalli mutanan fadar Aymane , wani mugun kallo ya wurga musu nan take su ka sha jinin jikin su
cikin ba da umarni ya ce musu " idan ku ka yi one minute a cikin wajen nan , ka tabbatar gawarku ce za su fita "
bai gama rufe bakin shi ba su ka tashi daya bayan daya da gudu su ka fice fadar , ta rage da ga Diya sai Malik sai Rafik
su na fita Shi ma Malik ya juya ya fice fadar , ya na tafiya kamar zai tashi sama hannun shi na zubar da jini , ga idanun shi duk sun yi ja da allamun ya na cikin bacin rai
kai tsaye part MALIKAT HOUDA ya nufa , babu ko sallama a bakin shi ya shigo parlourn
nan ya tardo su duk su na zaune ban da Inaya da mama da su ka shiga Bedroom
duk su na ganin shi kowane ya saki wani kyawatencen murmushi , MALIKAT INAS har da hawaye
har sun tashi za su nufe shi , su ka ga Diya ya fado mishi a baya ya rungume shi ya na fadin " ni dama na san za ka dawo , tabbas za ka dawo , ai dama damuna a lokacin da a ka fi bukatar ta ta ke samuwa , kamar wata ka ke a sararin samaniya haskenka ya na mamaye duk duniya , na ji dadin ganin ka abokina , I have really missed you "
ya na gama rufe bakin shi , Malik ya kai hannu cikin zafin nama ya medo Diya gaban shi , ya dunkule hannu ya kai mishi wani mugun bugu a face har sai da ya fadi kassa
a tare duk ka razana , Nesrine har da sakin kara , lokaci guda babyn ta ya saki kuka kamar ya san abun da ke faruwa
cike da bacin rai Malik ya ce mishi " ka na sane da abun da ke faruwa amma ka ki fada min , why ba za ka kire ni ka fada min halin da ahalina su ke cike tun kafin abun ya tsananta ? why Diya ? da yanzu RIANNA ba ta kire ta fada min ba shikenan haka Saudiya za ta dongwama hannun wacen azzalumin dan uwan naka "
a hankali Diya ya dago kai ya mike tsaye , ya na fadin " lokacin da na samu labarin abun da ke faruwa , sai da na kira ka , amma ba ka dauki wayata ba , na tura maka text a na bukatar ka a Saudiya , amma ba ka min reply ba , asali ma blocked di na ka yi , shi ya sa na ja bakina , na yi shiru ba kyale ka , na tattare familyn ka na tafi da su Qatar , duk abun da ya faru laifin ka ne , da tun farko ba ka tafi ba da duk wannan ba ta faru ba " ya fada cikin bacin rai shi ma
gaskiya Diya ya fada , duk abun da ya faru laifinshi ne , da tun farko ya tsaya , ya yaki Aymane da duk wannan abun ba ta faru ba
ya na gama fadar haka ya fara jiyo kukan baby
wani dan karamin tsaki Diya ya ja ya na fadin " dubi don Allah ka saka shi kuka " ya kai karshen ya na juyawa ya nufi Nesrine , ya kai hannu ya karbi babynshi , sannan ya juyo ya dawo gaban Malik
ya shiga jijiga shi ya na fadin " Shiiiiiiiiii , calm down my baby ba abun da ya faru "
a hankali ya dago kai ya kalli Malik ya na murmushi ya ce " tun kafin a rigani , bari na gabatar maka da Nawfel bin Abdoul Mujeeb , my baby "
lokaci guda idanun Malik su ka ciko da ruwa , har wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na kallon babyn babu ko kiftawa
Diya na jin yadda ya sauke ajiyar zuciya , ya saki wani kyawatencen murmushi ya ce " ba za ka rike shi ba ? " ya fada ya na mika mishi babyn
a hankali Malik ya dago hannayanshi har kerma su ke yi ya kai zai karbi babyn
kamar wanda ya tuno wani abu , lokaci guda ya juya ya fita da gudu
a tare su ka kalle shi har ya fita sannan Diya ya kalli babyn hannun shi ya ce " Oh sorry my baby , yanzu ya dawo kai da takwaran ka guda , duk gudun ruwanshi sai ya dawo ya dauke ka " sa ga haka ya juya ya koma geffen Nesrine ya zauna su ka shiga rarrashin babyn su
haka kowa ma ya koma ya zauna , ya yi zugum sun rasa abun yi , wannan tashin hankali da me ya yi kama , su dan ba su ma ji abun da Aymane ya fada da sai sun dinga sumewa
▪AYMANE
cike da bacin rai ya nufi part din Malik , kai tsaye a floor na biyu ya nufa dan a nan RIANNA ta ke , shi kuma tare da Hafsat a floor na uku , dan tun zuwan shi part din bai taba hawa floor na hudu ba , dan ya na rufe kuma babu wanda ya San ta yadda a ka rufe shi bare a bude shi
babu ko sallama ya shigo parlourn ya kwallawa RIANNA kira kamar murya shi za ta fado
da gudu RIANNA ta fito da ga Corridor , ta na tafe ta na ingishi da allamun kafar ta na ciwo , ga fuskar ta duk ta yi ja , ta na sanye da wata gown pink color ko veil ba ta da a kanta
kai tsaye gabanshi ta karaso murya har kerma ta ke ta ce " ga ni , ka na bukatar wani abu ? "
tsaya wa ya yi ya na kallon ta babu ko kiftawa
sai da ya dauki one minute ya na kallon ta kafin ya daga hannu ya wanke ta da wani gigitacen mari har sai da ta saki kara ta fadi kassa
cikin bacin rai ya tsuguna ya kai hannu ya shako wuyan ta ya na fadin " bayan ke na san babu wanda zai yi wannan aikin , why ? azabar da na ke miki ba ta ishe ki ba sai da ki ka yi abun da zai sani na kashe ki ? why za ki sa dan banzan dan uwanki ya dawo , har ya yi kokarin kwace min kujerar Malik ? "
tattara duk karfin ta RIANNA ta yi , ta sa hannayan ta dukka biyu ta ture shi ya fadi baya
da sauri ta mike tsaye ta na sakin murmushi ta na fadin " Akhie ya dawo ? " ta kai karshen hawaye na zubo mata
ta na gama fadar haka ta ji hannun Aymane ya damko wuyanta ya na fadin " ya dawo , amma ba za ki samu ganin shi ba , da ga nan gawar ki ce za ta fita da ga part din nan , duk wanda ya yi kokarin shiga tsakanina da kujerar Malik , sai na ga bayan shi , ki jira shi ma dan uwan naki , zai tarda ki ranar Friday "
" ka sake ni " ta fada murya a disashe dan a rarrabe ma ta fiddo hariffan
ya na shirin magana ya ga an riko hannun shi
a hankali ya juya ya ga ko wanene , kai tsaye cikin idanun Malik nashi su ka sauka
ba karamar razana ya yi ba ganin wadanan hazel eyes din nashi , ga shi sun yi jazir dan bacin rai , har sai da Aymane ya saki wuyan RIANNA bai shirya ba
ya na ganin ya sake ta ya yarfa hannu shi da karfi kassa , ya riko hannun RIANNA zai bar wajen da ita
da sauri Aymane ya riko hannunta ya na fadin " she is my wife , ba ka da ikon tafiya da ita "
Malik bai ce mishi komai ba , ya sa kafa ya tura shi har sai da ya fadi kassa
ya na faduwa ya juya ya nufi lift ya na rike da hannun RIANNA , sai da su ka yi ido hudu da Aymane kafin kofar lift din ta rufe
kai tsaye part din su ka baro , ya na janye da hannun RIANNA , ita ko ko gaban ta ba ta gani , kawai ta tsare shi da ido babu ko kiftawa ta na hawaye
sai da su ka shigo parlourn MALIKAT HOUDA ba ta sani ba , kawai sai ganin ta yi ya saki hannun ta ya nufi corridor
da sauri ta riko hannunshi , da karfi ya kwace shi ya nufi corridor
ba ta hakura ba sai da ta sake kai hannu ta riko nashi ta na fadin " Akhie "
ba ta gama rufe bakinta ba , ya juyo ya daka mata wata gigitaciyar tsawa ya na fadin " I say let me ! " da ga haka ya nufi corridor ya shige ya bar ta ta yi sumar tsaye
da sauri MALIKAT INAS ta tasso ta rungume yarinyarta ta na sakin kuka
a hankali RIANNA ta bude baki ta ce " Ammie , cewa ya yi na kyale shi " ta fada hawaye na zubo mata
da sauri Diya ya ce mata " RIANNA , gwara ki kyale shi , dan yanzu bacin ran da ya ke ciki ko da marigayi Malik ne a gaban shi , zai iya yi mishi fiye da tsawan , dan idanunshi a rufe su ke , ba ku san abun da Aymane ya fada mishi ba a fada , dan haka ku kyale shi har ya sauko "
da sauri RIANNA ta shige jikin MALIKAT INAS ta na sakin kuka har da zubewa saman guyiwowinta , ta na kuka
bangaran Malik , kai tsaye corridor ya nufa , har ya wuce bedroom din da Inaya ke ciki ya jiyo Muryar ta , ta na fadin " Ashhhhhhh "
cak ya tsaya , ko tunani bai tsaya yi ba ya tura kofar ya shiga babu ko sallama
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】
【 BOOK ________3 📚✍💌 】
_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________
{ P A G