Showing 18001 words to 21000 words out of 104561 words
, da sauri mutanan wajen su ka yi kokarin tashi , sai dai ya daga musu hannu a kan su zauna , ba musu kowane ya koma ya zauna ya na kallon Malik
a hankali ya yi taku biyu sannan ya tsaya ya rike hannayan shi a baya ya ce wa Mohammed " kamar yadda na fadawa shi Miram , duk wani abu da ke faruwa cikin masarautar nan ina sane da shi , ko da kuwa gwayar zarra ce , kawai dai ina shiru ne na ga gudun ruwan ku , ko ka zata ba ni da masaniya a kan abun da ku ka shirya , na san kai ka kawo shawarar kashe Malik , da farko Miram bai yarda ba amma ka matsa mishi , tun kafin na dawo masarautar nan ku ka shirya wannan , tare auren Gimbiya RIANNA da Miram yadda da kun kashe Malik a nadda Miram matsayin Malik tun da ba na nan yadda za ku yi yadda ku ka so cikin masarautar nan , amma shirin ku ya ruguje bayan dawowa ta , duk da hakan sai da ku ka saka a kashe Malik , da ga baya ya zagayo ya kashe ni , amma General ya yi nassarar kamo Sniper din da ku ka saka aikin , bayan an kai Hakim prison , sai da ka je wajen shi ka yi mishi kashedi a kan kar ya fada min gaskiya a kan cilas ta mishi a ka yi ya kashe Malik , amma bai saurare ka ba ya fada min , bayan na yi maganar a fada , shi ne ka tsorata , ka je wajen Miram , ka ba shi shawarar ku kashe Hakim tun kafin ya bayana gaskiya , a ranar da Miram ya yi kokarin kashe shi a cell , a tare ku ke , sai dai kai , ka tsaya a bakin kofa ba ka shiga cell din ba , ta yadda ko an tashi kamawa , Miram ne za a kamawa ko ba haka a ka yi ba ? " ya kai karshen ya na dagawa Mohammed gera guda
wasu wahalalun yawu Mohammed ya hadiye , ramin da ya gina ya rumzo mishi , ta ina zai fita yanzu ?
GASKIYA MALIK KA CIKA DAN SA IDO π€£π€£ NI BAN MA SAN WANNAN LABARIN SAI DA YA FADA , GASKIYA NA SARA WA BASIRAR KA ππ
ya na a haka kawai ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Mohammed Magid , Miram bin Salman , an kama ku da laifin kisan marigayi Malik , ko ku na da abun fada kafin na yanke muku hukunci ? "
da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce " Ranka shi dade me kuma za su ce ? A yanke musu hukunci dai'dai abun da su ka aikata , dama dokar musulumci ta ce wanda ya kashe a kashe shi , hukuncin kisa ne kawai ya dace da su , dalilin su Ιiya na guda uku sun rasa mahaifin su , ni da yar uwa ta mun rasa mijin mu , wace damar magana za a ba su kawai a kashe su kamar yadda su ka kashe shi " ta kai karshen ta na sakin kuka
a hankali MALIKAT INAS ta sa hannu ta janyo ta jikin ta ta rungume dama Sofar su a kusa ta ke , Ita kan ta ba ta taba tunanin mijin yar uwarta zai raba ta da nata mijin , idan ta ce ta yi magana ta san Manisha ba za ta ji dadi , shi ya sa kawai ta yi shiru amma har cikin zuciyar ta ta na bayan maganar MALIKAT AL'UMU
Shi dai Malik shiru ya yi ya na sauraron abun da su ke fada , kawai ya tsare Mohammed da idanu babu ko kiftawa , shi dama ya na sane da kishin da Mohammed ke yi wa mahaifin shi , dan tun ya na yaro Mohammed ya sha tsangwamar shi , ya na dukan shi , har ya zagi Malik gaban idan shi , amma bai taba nunawa ba
A hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya bude baki ya ce " duk wanda ke son yin magana , na ba shi dama , ya yi maganar shi "
a hankali Miram ya dago kai ya ce " ranka shi dade , ko cell za a saka mu kar a hada ni da shi "
" kar ka damu kowane za a saka shi cikin ta shi cell din " Malik ya fada cikin nitsuwa
da sauri Mohammed ya kali Miram ya ce " maciya Amana kawai "
wani murmushi mai dan sauti Miram ya yi kafin ya ce " Ai kai ne wanda za a kira da maciya amana , kai da kashe mijin kanwar matar ka , sannan ka yi wa yarinyar mutane fyade , ko kunyar shekarun ka ba ka ji ba "
da sauri Najoua ta ce " bai yi nassara ba "
wani dan karamin murmushi Miram ya yi kafin ya dago kai ya kale ta ya ce " ai ni ba a kan ki na ke magana ba "
da sauri Mohammed ya ce mishi " kai Miram kar ka yi min Kazafi dan kwatar kan ka "
hararrar shi Miram ya yi kafin ya juya ya kali Malik ya ce " ranka shi dade , mai girma Rafik , Mohammed shi ya kashe maka yarinyar ka , Tun da lokacin tonan asiri ne , ba zan kyale ka ba "
a dubu dari Rafik ya mike ya na fadin " Miram , ka na nufin Mohammed shi ya kashe Rhalida ? "
gyada mishi kai Miram ya yi ya na fadin " shi ya kashe ta , har school din su ya je ya dauke ta da sunnan zai kai ta gida , da ga nan ya wuce da ita gida na da ke Riyadh ya yi mata fyade , da ya ga ta mutu , ya bunne gawar ta a cen , yadda babu wanda zai samo ta "
cikin bacin rai Rafik ya nufi Mohammed a zafafe ya na isa ya wanka mishi wani gigitacen mari har sai da ya bidi faduwa
ya na shirin magana ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Rafik ! "
wani mugun kallo Rafik ya wurga mishi cike da takaici , ba tare da ya ce komai ba ya koma saman sofar shi idanun shi na cikowa da ruwa gaskiya Mohammed bai kyauta mishi ba , inda ya fada mishi ya na son yarinyar shi da ba abun da zai hana shi ba shi auren ta , amma yanzu ga shi yayi sanadiyar mutuwar ta ko gawar ta bai gani ba tsawan shekara biyar har yanzu su na jimamin rasuwar ta
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya yi wa Hakim allamun ya karaso da hannu
ba musu Hakim ya saki Najoua , ya fara takawa a hankali ya karaso gaban Malik
har zai zubewa saman guyiwowin shi Malik ya taro shi , ya koma ya tsaya ya na kallon Malik
a hankali ya tako ya zo dab da shi ya kai hannu ya riko hannun Hakim , sannan ya zagayo da dayan hannun a bayan shi ya fido gun ya daura saman Hannun Hakim
sannan ya kai bakin shi saitin kunnen shi ya ce " Duk duniya babu laifin da ya kai cin zarafin mace , ba zan kama ka da laifin kisan Malik ko ni ne zan iya yin fin hakan for my Cutie dan haka na ba ka dama , ka karbawa matar ka hakin ta "
ya na gama fadar haka ya yi taku biyu baya ya tsaya ya rike hannayan shi a baya ya na kallon Hakim
kallon gun din Hakim ya yi kafin ya dago ya kali Malik da ya tsare shi da idanu
a hankali ya gyada mishi kai allamun ya yi abun da ke cikin zuciyar shi
dawo da kallon shi Hakim ya yi kan gun din ya yi charging din ta ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanun shi a hankali kafin ya sake bude su cikin na Malik , cikin dakikan da ba su kai biyar ba , ya yi wata irin juyowa ya saita zuciyar Mohammed ya harbe shi , sannan ya sauko ya saita Miram a kai ya harbe shi
kowa cikin Fadar sai da zuciyar shi ta buga dan ba karamar razana su ka yi ba
Hafsat kuwa har da Sakin kara ta tashi da gudu ta nufi Mohammed ta na kuka
Malik kuwa bai bi ta kan su ba ya juya ya sa hannayan shi biyu ya dauki Inaya cak kamar baby , sannan ya dawo da kallon shi kan Hakim ya ce " Diya , ka sa a shirya jirgi nan da one hour a mayar da Hakim da matar sa Marocco "
ya na gama fadar haka ya fara takawa bai bi ta kan kowa ba ya sa kafa ya fice fadar da Inaya
wata nanauyar ajiyar zuciya Hakim ya sauke jin an ce a meda su Marocco ba tare da an yanke mishi wani hukunci ba , har lumshe idanun shi ya yi ya na sakin wani dan karamin murmushi
ya na a haka ya ji Najoua ta rungumo shi ta baya , a hankali ya juyo ya rungumo ta ya na sumbatar forehead din ta π€§ kai soyayya dadi
WAI KU TSAYA NI KADAI NA LURA BABU ROUKSAR A WAJEN NAN KO KUWA ? π€π€
ALLAH YA SA BA DAI WATA TA KULA BA , GASKIYA BAN YARDA DA SHIRUN NAN NATA BA YA KAMATA MU LEKO TA
βͺ ROUKSAR
a tsaye ta ke cikin kitchen na part din MALIKAT AL'UMU , ta na rera wata waka ta na rawa da kugun ta da allamun ta na cikin annashuwa
yankar Fruits ta ke cikin konciyar hankali ta gyara su saman wani tray gwanin burgewa
sai da ta Kamala yankar fruits din nan tsab , sannan ta saki wani makirin murmushi ta lumshe idanun ta , a hankali ta fara motsa lips din ta allamun wani abu ta ke karantawa
a hankali daya da ga cikin jelar gashin ta , ta fara yin kwarri ta goma green , scales irin na maciji su ka fara fitowa , nan take jelar ta koma wani dankareren maciji , ya na fido Tongue din shi waje ya na kukan macizai
wani kyawatencen murmushi Rouksar ta saki kafin ta ware idanun ta da su ka koma tamkar na macijin nan da ke cikin jelar gashin ta
a hankali ta kai hannu saitin kan macijin nan
nan take ya fito da ga cikin jelar gashin ta , ya nade a saman hannun ta , ya daura kan shi tsakanin yatsun ta biyu
a hankali ta matso macijin nan saitin face din ta ta ce " My baby , yau ina ji a jiki na ranar nassara ce , Burin mu zai cika , kar ka gaji da ni ka san abun da na ke bukata a wajen ka "
ta na gama fadar haka macijin nan ya yi wani kuka ya na fiddo tongue din shi , kafin ya juya
a hankali ta matso da hannun ta ta kai shi sama kadan da tray din fruits din
bude bakin shi Snake din na ya yi , nan take poison din shi ya fara fitowa da ga cikin hakwaren shi , ya fara zagaye Tray din nan duk fruits din da ke a sama sai da ya zuba musu poison
sai da ya gama sannan ya rufe bakin shi ya na kukan macizai
wani kyawatencen murmushi Rouksar ta saki kafin ta matso da Snake din nan ta kai saitin bakin ta ta manna mishi kiss a saman jikin shi ta na cewa " na gode baby na , za ka iya komawa ka huta "
wani dan karamin kuka ya yi mata kafin ya yi wata irin burra ya koma cikin jelar gashin ta nan take ya bace a ciki
ya na bacewa Rouksar ta juya ta nufi kofar fita kitchen ta na karasowa bakin kofar glass din ya zuge sai ga wasu mata hudu tsatsaye geffen door din
a hankali ta daga kafa ta fito , ta karaso gaban matan nan ta tsaya ta ce musu " ga Fruits cen Tesnim ta Shirya wa Malik , ku dauka cikin abincin da za ku kai wa part din shi , yanzu nan kafin su Kamala zaman fada " ta na gama fadar haka ta yi gaba abun ta ta na taku kamar ita ce Malik
ba musu matan su ka shiga kitchen su ka fara shirya abincin da za su kai wa part din Malik su ka hada da tray din nan na fruits da Rouksar ta shirya sannan su ka tafi
βͺMALIK
kai tsaye part din shi ya koma ya Inaya , amma a floor na Uku ya tsaya , a parlour
zaunar da ita ya yi saman sofa sannan ya zauna geffen ta ya ce " my Cutie are you okay ? "
marairaice mishi fuska ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce mishi " baby ina ga fa yunwa na ke ji "
a hankali ya kai hannu ya ja mata kumatu ya na fadin " sai da na ce miki ki tsaya mu yi breakfast amma ki ka ce no , ba ga shi ba yanzu wa gari ya waya ? "
kukan shagwaba ta fara yi mishi ta na fadin " uhm uhm ni baby yunwa na ke ji '
da sauri ya ce mata " Shikenan , shikenan Me za ki ci na kawo miki a nan "
cike da shagwaba ta ce mishi " ni fruits ma sun ishe ni "
" an gama ran ki shi dade " ya fada ya na kokarin tashi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " I love you my baby "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " i love you my Cutie " ya fada dai'dai lokacin da ya shiga dining room
tsaya wa ya yi ya na bin table din da kallo
cen ya ga wani bowl da ga tsakiya cike da fruits , kusan shi kuma wani tray ne shake da fruits an yan'yanka su
a hankali ya kai hannu ya dauki Fork guda biyu , ya daura saman tray din sannan ya dauke shi ya juya ya dawo cikin parlour
gaban ta ya karaso ya ajiye tray din a kassa sannan ya zauna ya ce mata " To Sarauniya ta , sauko mu ci ko ? "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta sauko kassa ta zauna su na fuskantar juna sannan ta kai hannu ta karbi fork din da ya miko mata ta na yi mishi godiya
a tare su ka kai fork din su cikin tray din , ita ta dauki Apple shi kuma ya dauki Strawberry , su ka kai baki a tare
a hankali ta fara taunawa , ta na kallon shi
cak ta tsaya ta na zaro idanu , da sauri ta hadiye Apple din bakin ta ta ce mishi " baby kar ka hadiye , kar ka hadiye "
tsayawa ya yi ya na kallon ta , ita ba ta san tun kafin ta fara magana ya hadiye
β€β E X I L E D ββ€ P R I N C E ββ€
(LOVE MEETS POWER ) ππ₯
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ
BOOK ________3 πβ
P A G E 7 πΉπ
a hankali ya bude baki ya ce " Me ya faru ? " ya kai karshen ya na daga mata gera guda
marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " sai da na ce maka kar ka hadiye "
har ya bude baki zai yi magana kawai sai ya shiga cough , idanun shi su ka koma jazir
a rude Inaya ta koma geffen shi ta na fadin " baby lafiya , me ya faru ? "
a hankali ya bude baki murya a disashe ya ce mata " take me water "
bai gama rufe bakin shi ba ta tashi da gudu ta nufi dining room , ta na isa bakin dining table ta kai hannu ta dauki glass da jug din ruwa , ta zuba ruwan cikin glass sannan ta juya da Sauri ta dawo cikin parlourn
tun kafin ta karaso gare shi ya saki glass din ya fadi kassa , wata razananiyar kara ta saki kafin ta nufe shi da gudu har sai da ta taga glass din ba ta sani ba
da gudu ta Zube saman guyiwowin ta ta talabo kan shi ta na bubuga kumatun shi ta na fadin " baby , baby me ya same ka , ka bude idanun ka don Allah , baby ! " ta kai karshen da karfi
ina ko jin ta ba ya yi idanun shi su na rufe , jikin shi ya yi zafi , sai wata rawa ya ke , ga wata zufa da ta karayo mishi a Fuska kamar an watsa mishi ruwa
ta na a haka kawai ta ga wani fari abu kamar kunfa haka ta na fitowa da ga bakin shi
dan zaro idanu ta yi ta na kallon shi , ba ta san lokacin da