Showing 57001 words to 60000 words out of 104561 words

Chapter 20 - Exiled Prince Book 3 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

406

nan ya janyo su

har zai saka su cikin motar da ke baya , Malik ya ce ya saka a cikin motar tsakiya dan da mota guda zai tafi , ba musu Azim ya dawo wajen motar tsakiya ya bude bayan ta ya saka trolley din

Malik kuwa da kan shi ya budewa Inaya gidan gaba ya ce ta shiga , ba musu ta shiga sannan ya rufe kofar

har ya nufi wajen driver Diya ya riko hannun shi ya na fadin " yanzu da gaske tafiya za ka yi ka bar familyn ka , ka bar ni ? " ya fada ya na marairaice fuska

a hankali Malik ya dawo gaban shi ya tsaya ya na fadin " dama na fada maka , ba zan zauna cikin kassar nan ba , ya kamata na tafi tun wani abu bai sake faruwa ba "

cikin nitsuwa Diya ya katse shi da cewa " kujerar Malik fa , ya ka ke so mu yi da ita ? wa zai ci gaba da kula da kassar Saudiya , please kar ka tafi kowane problem ya na da solution , amma guduwa ba ita ba ce solution din ka ba "

" no Diya , ba guduwa na yi ba , ka gan ta ko ? " ya fada ya na nuna mishi Inaya ta cikin glass din motar
sannan ya ce " idan wani abu ya same ta ta dalilin wannan kujerar ba zan iya yahewa kai na ba , su je na bar musu gadon mahaifina , duk wanda ya ke so ya hau na ba shi izini ko da kuwa kai ne , da ga wannan ranar ku manta da wani Malik mai sunan Nawfel a cikin kassar nan dan ba zan sake dawowa cikin ta ba "

da sauri Diya ya fada jikin shi ya rungume shi ya na fadin " don Allah kar ka tafi , at least ka bari har takwaran la ya shigo duniya ka gan shi kafin ka tafi please ko dan saboda ni kar ka tafi " ya fada kamar zai yi kuka

dan bubuga bayan shi Malik ya yi ya na fadin " I'm sorry Diya , but i can't stay here , rayuwarta ta fiye min wannan dukiyar da Mulkin , dole na tafi ko dan na ci gaba da ganin ta a raye ba tsakanin rai da mutuwa ba "

a hankali Diya ya dago da ga jikin shi ya kai hannu ya na goge hawayenshi , tun kafin ya ce wani abu Malik ya ce mishi " sai watarana " ya raba ta geffen shi ya nufi mazaunin driver , ya shiga sannan driver ya ba shi key din motar ya tada ta
da kan shi ya tukka motar ya bar wajen da mugun gudu

ya na barin wajen shi ma Diya ya juya ya nufi part din shi kamar zai yi kuka

sai da su ka nufi hanyar fita masarautar sannan Inaya ta ce mishi " baby , uncle na yi maka magana "

ba tare da ya juyo ba ya ce " uhm me ya ke cewa ? "

" tabbas ka tafi , amma za ka dawo , dan wannan kujerar a rubuce take cikin tarihin rayuwar ka , ka gudu amma ba ka tsira ba dan yaki yanzu ka fara yin shi , nan ba da jimawa za ka dawo "

ba tare da ya kalle ta ba ya ce " i'm sorry Dad , but ba abun da zai medo ni cikin wannan masarautar , zan sauya tarihin rayuwa ta , kuma za ka gani "

dai'dai lokacin da motar shi za ta bi ta kofar fita masarautar Inaya ta ce mishi " za ka dawo , ni na fada maka "
bai ce mata komai ba ya ci gaba da tukin shi ya nufi hanyar airport , ga shi kuma glass din motar bakake ne ba wanda ya san wa ke cikin motar

🤧🤧🤧🤧 shikenan yanzu Malik ya bar Daular Saudiya ? ya bar kujerar Malik har abada ? yanzu wa zai hau kujerar ? shikenan Aymane ya samu abun da ya ke so
duk masarautar babu wanda bai samu labarin Malik ya yi hijira da matar shi , lokacin da RIANNA ta ji labarin sai da ta samu , sai da ta yi kamar ran ta zai fita , ita kan ta MALIKAT INAS ta sha kuka , shikenan yanzu ta rasa yaronta guda da ya yi mata saura
bangaran Aymane kuwa Meli na kawo mishi labarin Malik ya yi hijira , Garin ciki wajen shi kamar zai tsuntsuwa ya tashi sama , shikenan burin shi na zama Malik ya cika , dama Malik ne ya hana burin shi cika yanzu kuma ba ya nan ba wanda zai iya shiga tsakanin shi da kujerar Malik

bangaran su Malik kuwa , kai tsaye Airport ya nufa
ya na isa ya shiga private jet din shi , sun yi good 30 minutes a na shirya tashin jirgin , kafin ma ya tashi Inaya barci ya dauke ta , a haka har jirgin su ya daga ba ta da labari su ka bar kassar Saudiya
SAI DAI NA CE ALLAH YA TSARE KU , ALLAH YA KARE KASSAR SAUDIYA DA GA SHAIRIN AYMANE 🤧🤧



❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊




【BOOK ________3 👑✌】





______________________⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘___________________




{ P A G E ………18 🌹🕊}





▪UNITED STATES OF AMERICA ( U.S.A )


▪WASHINGTON DC


▪INAYA



a hankali ta fara motsi ta na karanto addu'ar tashi da ga barci , a hankali ta ware idanunta ta na kallon ceiling , a hankali ta mike zaune ta na bin wajen da kallo

wani kyawatencen bedroom ne mai mugun girma , gadon da ta ke sama ya na fuskantar wasu doors guda biyu allamun dressing room da toilet ne , a geffen dama kuma akwai wasu sofas guda uku , guda three seaters , sai biyu one seater su na fuskantar juna duk white color , da ga tsakiyar su akwai wata yar table ta glass an daura wasu decorations a sama

a hankali ta juya ta kalli saitin hagun ta , nan ta ga wall din wajen duk na glass ne ka na iya ganin garin , duk duhu da allamun dare ya yi ba ta sani ba
nan ta gan shi tsaye gaban wall din nan ya na sanye da short sai wata T-shirt , ya nade hanayan shi a kirji ya na kallon yanayin garin

wani cool murmushi ta saki kafin ta sauko da kafafunta kassa ta mike tsaye , a hankali ta fara takawa ta nufe shi

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi kawai ya ji ta rungumo shi ta baya
wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " sai yanzu ki ka tashi ? "
turo dan bakin nan nata ta yi ta na fadin " baby ciki na ke min ciwo "
a hankali ya sa hannu ya zagayo da ita gaban shi ya daura hannun shi saman wuyan ta ya ji jikinta ya yi zafi allamun fever ne da ita

janye hannunshi ya yi ya na fadin " da allamun mun baro lafiyar Daular Saudiya "

cike da shagwaba ta ce " baby da gaske cikina ke min ciwo , kamar ana murde min shi "

" don't worry my Cutie , ina ga period ne za ki yi , yanzu ki je ki yi wanka ki yi Alwalla tun kafin ya zo ki yi sallat , ki zo mu ci diner sai mun konta mu yi barci , gobe kuma , za mu fita mu ga garin "

wani cool murmushi ta saki ta na fadin " da gaske baby ? "
a hankali ya gyada mata kai allamun Eh
da sauri ta sake shi ta nufi door din toilet da gudu ta shige



▪DAULAR SAUDIYA 👑🔥



zaune MALIKAT INAS ta ke cikin parlourn ta yi zugum waje guda sai hawaye ta ke yi , tun safe ta ke kiran layin Malik amma a kashe babu yadda ta iya ta hakura ta sakawa sarautar Allah ido

ta na a haka MALIKAT AL'UMU ta shigo parlourn ta na sallama
sam MALIKAT INAS ba ta san da shigowar MALIKAT AL'UMU ba kawai sai jin ta yi an dafa shoulder din ta
a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta juya ta kalli MALIKAT AL'UMU

cikin sanyin murya MALIKAT AL'UMU ta ce " ina kuma tunanin ki ya tafi haka , na yi sallama ba ki amsa min ba ? "

kamar za ta yi kuka MALIKAT INAS ta ce " Moussina , ki na da labarin yaron mu ya tafi ? "

gyada mata kai MALIKAT AL'UMU ta yi ta na dan karamin murmushi ta ce " Eh ina da labarin , ni na ba shi izinin tafiya "

da sauri MALIKAT INAS ta katse ta da cewa " ke ki ba shi izini ? why ? Moussina yanzu kin bar yaron mu tilo tafiya "

" Eh na sani , amma babu yadda zan yi , yaron ki ya na son tafiya na isa na hana shi ? ni hakan ya fi yi min dadi , ko ba komai sun bar shi da ranshi , ko kin fi son ganin shi konce rai hannun Allah ? "

a hankali MALIKAT INAS ta girgiza mata kai allamun a'a

wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " shikenan , yanzu ki kontar da hankalin ki yaron mu ya na cikin koshin lafiya tare da matar shi , addu'a kawai za mu yi musu , mu jira jikokin mu dan ina ga fa baby ciki ne da ita "

dan zaro idanu MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " Ciki ? haka RIANNA ta fada min , amma gaskiya ba na tunanin Malik zai bari ta samu ciki da karancin shekarun ta , shi da kan shi ya ce bai shirya haihuwa yanzu ba , ko zancen babyn ba ya son yi "

wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " kin san fa yadda yanayin mace mai ciki ya ke , kallo guda na yi mata na tabbatar da ba ita kadai ba ce "

ba ta san lokacin da MALIKAT INAS ta saki wani kyawatencen murmushi kamar dariya ta na fadin " kin ga aikin yaron ki ko ? shi ya sa ya ke son ya tsere dan kar a cutar mishi da babys din shi , kin ga mai wayo ? "

wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " kin ga ki kyale min yarona da matar shi "

" shikenan , yanzu ina su ka tafi ? "

" gaskiya ban sani ba , amma duk in da ya ke na san zai kira mu idan ya huta "

dan jinkirtawa MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " shikenan , yanzu batun kujerar Malik kuma fa ? ya za mu yi da ita ? "

dan jinkirtawa ita ma MALIKAT AL'UMU ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce " why ba za mu nada Aymane ba ? "

" Aymane ? , ki na ganin zai dace da kujerar Malik , ba wani sanin kirki mu ka yi mishi ba , ni da za a bi shawara ta a daura Diya , tun da kun ga shi ne babban aminin Malik , kuma na hannun daman shi , an ce abokin barawo , barawo ne , na san duk yadda a ka yi Diya ya dauko halayen Malik "

" matsalar Diya ba shi da gami da masarautar Saudiya , da a ce Tesnim ya ke aure da hakan zai iya faruwa , amma ba zai iya hawa ba , kin sani ? yanzu Rafik ya kamata mu yi wa wannan maganar mu ji abun da zai ce "

a hankali MALIKAT INAS ta gyada kan ta , ta na fadin " shikenan yadda ki ka ce haka za a yi "

wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " na dawo nan da zama , tun da yaran namu sun tafi sun bar mu , ni gaskiya ba zan iya kwana ni daya ba "

wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " ashe ba banza Malik ke ce miki matsoraciya "

hararrar ta MALIKAT AL'UMU ta yi ta na kauda kai gefe ta ce " wlh ku daina ce min matsoraciya "

" hmmm , na ji shikenan ke ba matsoraciya ce ba "
" yawwa " MALIKAT AL'UMU ta fada ta na kara kauda kai


▪US ( WASHINGTON DC )


▪MALIK

konce ya ke saman bed din su , da ga shi sai short ya na fuskantar ceiling , ya daura hannunshi guda saman forehead ya lumshe idanunshi

ya na a haka kawai ya ji ta konto mishi a jiki ta na fadin " baby , barci ka ke ? "

ba tare da ya bude idanun shi ya ce " Eh , amma kin tashe ni "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kai lips din ta saman chest din shi ta fara yi mishi kiss har ta kai saman wuyan shi

da sauri ya ce mata " ke malama sauka da ga sama na "
a hankali ta dago kai ta kalle shi ta ce " why ? "
" ki na ji ? yi hakuri ki sauka ban shirya shiga hannu yanzu ba , please "

ya na gama rufe bakin shi ya ji saukar lips din ta saman nipple din shi ta fara sucked din shi
a dubu ya ware idanunshi , ya daura hannun saman bayan ta ya ce " please ki yi hakuri , i'm not feel well now please "

a hankali ta dauke bakin ta da ga saman nipple din shi ta matso da face din ta kusan tashi ta ce " baby , me ya faru ? me ya ke damun ka ? "

hannu ya daura saman kumatun ta , cikin sanyin murya ya ce mata " nothing my Cutie , just na gaji , ina son na huta please "

wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta sauka da ga saman shi , ta koma gefe ta konta sannan ta rungume shi ta lumshe idanun ta
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya zagayo da hannunshi a bayan ta ya rungume ta shi ma , sannan ya lumshe idanunshi

sun dauki wajen good ten minutes a haka kafin ta ware idanun ta a hankali ta daura hannu saman cikinta , ta na dan shafawa a hankali

a hankali ya ware idanun shi dan dama ba barci ya ke ba , a hankali ya daura hannun shi saman cikinta ya na fadin " me ya faru ? "

" baby ciki na ciwo ya ke min " ta fada murya kassa kassa
a hankali ya mike zaune ya na fadin " wai wane irin ciwon ciki ne wannan , tun kafin mu baro gida ki ke ce min cikin ki na ciwo , bayan na konta ciwo ba ki yi period ba ? "

girgiza mishi kai ta yi a hankali ta na fadin " a'a ban yi ba "
shiru ya yi ya tsaya ya na kallon ta , In haka ne kenan last period din ta sati daya kafin a yi nadin shi Malik , kenan wajen one month har da kwanaki , hakan na nufin tun lokacin da ya yi dis virgin din ta cikin ya samu ?
" she is Pregnant ? " ya fada cikin zuciyar shi

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi kawai ya jiyo kukan ta
a rude ya dawo cikin hayacin shi ya na fadin " Cutie , what's wrong ? "

cikin kukan nata ta ke ce mishi " baby , cikina ciwo ya ke min sosai "
da sauri ya sa hannu ya janyo ta jikin shi ya na fadin " i'm sorry , zai daina kin ji ? "
a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " baby ba zai daina ba , zafi ya ke min sosai "

" shikenan , me ki ke so na yi miki yanzu ? "
" ni mu tafi likita su ban magani ko kuma ya kashe ni " ta fada ta na kara sautin kukan ta

bai ce mata komai ba ya sake ta a hankali sannan ya ce " shikenan konta kin ji yanzu doctor ta zo ta duba ki "

ba musu ta konta ta hannayan ta saman cikin ta ta na kuka kamar wata baby
ya na gani ta konta ya kai hannu saman bedside drawer ya dauki wayar shi ya fara latsawa sannan ya meda saman bedside drawer kafin ya tashi ya shiga dressing room

jim kadan ya fito sanye da jallabiya fara kal mai dogayen hannu
kai tsaye bed din su ya nufa ya haye , ya riko hannun ta ya na fadin " i'm sorry my Cutie , yanzu doctor ta zo ta duba ki "

ba ta ce mishi komai ba sai kuka kassa kassa ta ke yi
haka ya ci gaba da rarrashin ta
sun dauki wajen good ten minutes kafin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login