Showing 1 words to 3000 words out of 104561 words
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH 👑🔥
BOOK ________3 ✍📚🔥
P A G E 1 🥀 ❤
▪MALIK
kai tsaye part din shi ya nufa da ita , sam bai damu da mutanan da ke cikin masarautar ba , ya san kuma su na kallon shi amma bai sauke ta ba
ya na shiga part din shi ya wuce kai tsaye floor na hudu da ita
su na shigowa parlourn ya sauke ta saman kafafun ta
ya na sauke ta ko ta yi sauri za ta bar wajen
taku daya ta yi ya damko kugun ta ya juyo ta su na fuskantar juna ya ce mata " ina kuma za ki je ? "
" Ka sake ni wanka zan je na yi " ta fada ta na matse gera
sai da ya karewa face din ta kallo da kyau sannan ya sake ta a hankali ba tare da ya ce mata komai ba
da sauri ta juya ta fara takawa ta shige corridor ta nufi bedroom din su
sai da ya ga ta shiga cikin corridor din sannan shi ba ya tako a hankali ya bi bayan ta ya shiga bedroom din su
ko da ya shiga kai tsaye Dressing room ya wuce ,
jim kadan ya fito hannun shi rike da wata yar karamar box Red color ya karaso bakin gado ya ajiye ta
sannan ya juya ya nufi toilet , a bakin kofar ya tsaya ya kai hannu ya yi mata knocking
bai jira amsar ta ba ya ce " Ga kaya nan na fido miki saman gado " ya na gama fadar haka ya juya ya fice bedroom din
sai da ta dauki wajen good 45 minutes kafin ta fito da ga cikin toilet ta na daure da towel a kirjin ta
kai tsaye gadon ta nufa har ta kai hannu za ta dauki box din ya ajiye
ta jiyo Muryar shi ya na sallama a bayan ta
slowly ta dago ta juya ta amsa mishi sallamar shi ta na murmushi
a hankali ya ke takowa cikin dakin ya na sanye da kayan barcin shi farare kal , sai tashin qamshi ya ke
gaban ta ya karaso ya tsaya ya sa hannayan shi cikin aljihun wandon shi ya ce mata " Sai yanzu ki ka yi Niyyar fitowa "
wani cool murmushi ta saki kafin ta matso kussan shi ta zagayo da hannayan ta a bayan shi ta kontar da kan ta saman chest din shi
a hankali ya sauke ajiyar zuciya har sai da ya lumshe idanun shi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ni ma na yi kewar ka sosai "
da sauri ya bude idanun shi ya sunkuyo ya kontar da kan shi saman shoulder din ta ya ce " ta ya ki ka San na yi kewar ki ? "
" Ummm na ji a jiki na " ta fada ta na lumshe idanun ta
a hankali ya kai lips din shi ya manna mata kiss saman shoulder sannan ya yi mata saman wuya
yar karamar dariya ta yi ta na neman ta janye jikin ta da ga nashi
da sauri ya fido hannayan shi , ya zagayo da su a kugun ta ya matse ta tsam a jikin shi
" baby sake ni na saka kayana , na fara jin sanyin " ta fada mishi cikin sanyin murya
a kunne ya rada mata " don't worry I'm here I'll warm you up " ya na gama fadar haka ya sa hannu ya ja towel din jikin ta da karfi ya fadi kassa
a hankali ya sa hannu ya daga ta cak ya karaso wajen gadon ya kontar ta ita , sannan ya mike ya cire kayan jikin shi ya bar short sannan ya Haye saman gadon ya mata runfa da fafadar kirjin shi
AL'AMARIN MALIK SAI INAYA , NI DAI NA KOMA DA GA GEFE HAR SU KAMALLA
▪WASHE GARI ( PRISON )
▪MALIK
Zaune ya ke a cikin Cell din Hakim saman gadon shi , ya daura laptop saman cinyoyin shi ya juyawa Hakim ita ya na kallo
sai da ya share wajen ten minutes kafin Hakim ya yi sauri ya ce " Ga ta nan , ita ce , a ranar da mu ka shigo kassar Turkey "
da sauri Malik ya juyo da laptop din gaban shi , ya na kallon Hall din Airport din , cike ta ke da mutane amma ya iya gano Hakim , ya na tare da wata budurwa da a shekaru ba za ta wuce 20 years ba ta na sanye da Abaya blue color ta yafa veil din ta a kai
slowly Malik ya dago kai ya kali hakim ya ce " ka tabbata two weeks ku ka yi a Turkey ? "
da sauri hakim ya ce mishi " i'm sure "
" yanzu babu wata hanya yadda za ka iya tantance wanda ya saka wannan aikin ? "
" ranka shi dade da na sani da tun da ga farko na fada maka duk lokacin da mu ke haduwa fuskar shi a rufe ta ke " ya fada kamar zai yi kuka
gyada kan shi Malik ya yi kafin ya mike ya ce mishi " Shikenan zan dawo gare ka , an jima " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya nufi hanyar fita cell din
har ya kai bakin kofar Hakim ya yi sauri ya ce mishi " ranka shi dade , Muryar shi ina iya gane Muryar shi "
slowly Malik ya juyo ya ce mishi " Za ka iya gane Muryar shi ka tabbata "
gyada mishi kai Hakim ya yi kafin ya ce " na tabbata ranka shi dade , sannan akwai wani bracelet da na taba gani a cikin hannun shi , Bracelet din kamar dai Zanen da ke saman wuyan ka kuma na Gold ne sau biyu ina ganin shi sanye da bracelet din nan "
dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Shikenan " a takaice sannan ya juya ya fice cell din
kai tsaye Prison din ya baro , ya na fitowa sai saman motocin shi da Diya tsaye a gaban su
ya na isowa Diya ya bude mishi gidan baya ya shiga sannan shi ma ya shiga ya rufo kofar , Driver ya tada motar su ka bar wajen
cikin nitsuwa Malik ya ce ma Diya " Mu je Fada "
gyada mishi kai Diya ya yi kafin ya ce ma Driver ya kai su Fada
ba musu Driver ya juya kan motar su ka nufi hanyar Fada
Fadar ko ta na cike a lokacin duk wanda ke cikin fadar ya na a wajen har Rafik da Aymane wannan karan , Sai surutu su ke
cikin Izza Malik ya shigo Fadar ya na sallama cen kassan makoshi yadda shi kadai ya ji abu ne
su na ganin shi su ka yi tsit su ka mike tsatsaye da sauri su na sunkuyar da kai cikin girmamawa
bai bi ta kan su ya wuce kai tsaye wajen kujerar shi , ya zauna Diya ya koma geffen shi ya tsaya
sai da ya zauna sannan dukkan su su ka zauna su na kallon shi
bai bata lokaci ba ya bude laptop din da ke cikin hannun shi , ya kunna sannan sai saman video din nan da ya gwada wa Hakim
a hankali ya juya laptop din yadda kowa na cikin fadar ke iya gani bai Ce musu komai ba
kowa ya yi shiru ya na kallon Laptop din irin kallon nan na karin bayani
kamar ko Malik ya sani sai ya ce " A cikin video din nan za ku ga saurayin da General Abdallah ya kamo wanda ya harbe Malik , sannan za ku ga Wata Mata a tare da shi "
ya na gama fadar haka ya kashe laptop din ya rufe ta
cikin rudu Hussein ya ce " amma ranka shi dade , me ya kawo zancen wannan videon "
dan jinkirtawa Malik ya yi cikin nitsuwa ya ce " wannan Videon ta na daya da ga cikin abun da zai tabbatar da gaskiyar saurayin nan "
da sauri Mohammed ya mike ya ce " wace gaskiya kuma ran ka shi dade , General Abdallah kai da kan ka , ka kawo saurayin nan ka ce shi ya kashe Malik ko dai batan kai ku ka yi ? "
cikin nitsuwa General Abdallah ya ce mishi " Please Sarkin bayi ka zauna ka ji abun da zai fada "
bai gama rufe bakin shi ba Mohammed ya ce " ka yi hakuri General amma ba zan iya yin shiru ba , yaron nan shi ya kashe Malik me a ke jira har yanzu ba a yanke mishi hukuncin ba , Ku sa baki Jama'a "
ya na gama fadar haka kowane ya shiga fadin Albarkacin bakin shi wasu na cewa a kara bincike wasu kuma su ka goyi bayan Mohammed na cewa a yanke mishi hukuncin yanzu ba sai an jima ba
shi dai Malik shiru ya yi ya lumshe idanun shi ya na sauraron su
cikin bacin rai ya bude idanun shi ya ce " Silence !! " ya fada da karfi duk sai da su ka razana ba shiri kowane ya ja bakin shi ya yi shiru ba
a hankali ya dago kai ya kali Diya
da sauri Diya ya sunkuyo da kan shi ya na sauraron abun da Malik ya rada mishi
gyada mishi kai kawai ya yi kafin ya koma ya tsaya
juyowa Malik ya yi ya kale su ya ce " ku na shaida a ranar da na hau kujerar nan , na yi Alkawari kwatarwa duk wanda ya kawo min kukan shi hakin shi ko da kuwa mai laifi ne , kamar yadda a ka kamo shi da sunnan ya kashe Malik , haka shi ma ya kawo min kukan shi domin na ceci Matar shi , bai kamata mu yanke mishi hukuncin ba tare da mun saurare shi , ba tare da mun ji dalilin shi na kashe Malik , abu guda zan fada muku , Abdoul Hakim ya fada min gaskiyar abun da ya faru , ya kuma fada min dalilin shi na kashe Malik , na yi muku alkawari duk wanda ya saka shi yin wannan aikin sai na kamo shi na yanke mishi hukunci dai'dai abun da ya aikata , na farko na saka shi kashe Malik , na biyu kuma Matar shi da ya sace , ko wanene idan na kamo shi zai fuskanci hukunci ba ruwa na da matsayin shi a waje na ko a cikin masarautar nan "
ya na gama fadar haka ya tashi ya fara takawa cike da Izza ya fice fadar , da sauri Diya ya bi bayan shi su ka bar wajen
kowane dai kallon shi ya ke , sun kassa cewa komai amma da ga gani ga tsoro nan konce saman fuskokin su , Ba karya General ya yi ba , yanzu duk wanda ya saka Hakim yin wannan aikin sai shiga tayi tayin shi , a nan ne wajen ceton kan shi zai yi mistake har a kama shi
bangaran Malik kuwa su na fitowa ya mika wa Diya Laptop din shi ya ce ya sa a kai shi part din shi , zai wuce wajen MALIKAT INAS
ba musu Diya ya karbi laptop din ya juya
har sun yi hannun riga Malik ya juyo ya ce mishi " Diya ya jikin Nesrine ? ta samu sauki ? "
juyowa shi ma Diya ya yi ya na murmushi ya ce mishi " don't worry , kawai Fever ce ta ke amma yanzu ta samu sauki "
gyada kan shi kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba ya juya ya ci gaba da takawar shi
kai tsaye part din MALIKAT INAS ya nufa dan ya san ita kadai ce za ta iya ba shi amsar tambayar shi
Bakin shi da Sallama ya shigo parlourn ta
nan ya tardo ta zaune tare da RIANNA su na hira fuskokin su dauke da murmushi
MALIKAT INAS na ganin shi ta tsuke fuska ta kauda kai gefe
sai da ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofa geffen RIANNA sannan ya ce " Ina kwana Ammie "
" lafiya " ta fada a takaice ba tare da ta juyo ba
yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta dafa shoulder din shi ta ce " Akhie ina ga Ammie fushi ta ke da kai "
" Da gaske Ammie ? " ya fada cikin sanyin murya
tsuke fuska ta yi ta na kara kauda kai gefe
a hankali ya mike da ga saman sofar shi , ya tako ya dawo gaban ta ya zauna saman carpet ya kai hannu ya fara murza mata kafa ya na fadin " duk da ban san laifin da na yi ba , amma ina neman afuwar ki , Kin san ba na son ganin ki cikin fushi please Ammie kar ki ce za ki yi min fushi , wlh ba zan ji dadi ba "
a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " Nawfel , ni fa wassa na ke yi maka ba fushi na ke ba "
a hankali ya kontar da kan shi saman cinyar ta ya ce " na sani , ai ba karamin abu zai sa Ammie na ta yi fushi "
" duk da hakan ina fushi da kai , tsakani da Allah yanzu Nawfel yaushe rabon da ka zo waje na ? ko da gaisuwar tsaye ya ce ? " ta fada ta na marairaice murya
dan lumshe idanun shi ya yi kamar mai jin barci ya ce " I'm sorry Ammie , ke ma yanzu kin san aikin da ya karun min "
cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " Kar ka damu , na sani Allah ya taya ka riko bisa gaskiya kamar yadda mahaifin ka ya yi "
a tare shi da RIANNA su ka amsa mata da Ameen
sannan RIANNA ta ce " Akhie wai , ina baby ta yi ne na yi kwana biyu ban gan ta ba "
" wace baby ? wlh Ukhtie na lura duk ke ki ka bata yarinyar nan , sai ta kashe ni sannan ki huta "
dariya sosai RIANNA ta yi har ita kan ta MALIKAT INAS
sai da ta gama dariyar ta sannan ta ce " Nawfel fadi gaskiya ko dai kai ne ka ke takurawa babyn ta mu , na ji an ce har yaji ta yi maka "
da sauri ya dago kan shi fuska cike da mamaki ya ce " How do you know that ? "
yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " Nawfel , ai labarin masarautar nan ba ya boyyiwa "
a hankali ya koma ya kontar da kan shi saman cinyar ta ya ce " to babu ruwan ku dai "
" Akhie , Fadi gaskiya me ka yi wa baby " RIANNA ta fada
lumshe idanun shi ya yi sannan ya ce mata " da ya ke ita yar aljanna ce ba ta laifi , sai na ma kara aure na huta da rigimar ta "
ya na gama fadar haka ya ji MALIKAT INAS ta sa hannu ta murde mishi kunne
kamar karamin yaro ya dago kai ya na cewa " Ammie , sake min kunne na da zafi fa "
" yi min shiru mara kunya kawai , yanzu baby tawa za ka yi wa kishiya ? A hir din ka wlh ban yarda da haka ba "
" Ammie ni fa wassa na ke miki "
a hankali MALIKAT INAS ta sakin mishi kunne , sannan RIANNA ta ce " Akhie , wlh duk ranar da ka yi wa baby kishiya ni da kai mun yi hannun riga , me ta yi maka haka kawai ? "
meda kan shi ya yi saman cinyar MALIKAT INAS cikin sanyin murya ya ce " in da a ce ina da Niyyar kara aure da lokacin da Mohammed ya ba ni auren Hafsat ba zan ce a'a ba , Ukhtie har ga Allah ba na tunanin zan iya zama da wata matar bayan Cutie , Ita kadai ta san sirri na ita kadai ke iya saka ni cikin nitsuwa , ita kadai ke iya saka ni cikin farin ciki kuma har duniya ta nadde ba za a samu ta biyu ta a waje na , kamar yadda ta ba ni ragamar rayuwar ta na yi yadda na ke so ita , haka ni ma na ba ta ragamar rayuwa ta ta yi yadda ta so da ita "
wani kyawatencen murmushi RIANNA ta saki ta na cewa " iyeeeee , Ammie ki na ji ko , yaron ki fa ya fada tarkon soyayya "
lumshe idanun shi Malik ya yi kafin ya ce " Ai ni dama na jima da fadawa "
murmushi mai dan sauti MALIKAT INAS ta yi ta kai hannu saman kan shi ta fara shafawa a hankali ta ce " Ka ce mu fara shirya