Showing 27001 words to 30000 words out of 104561 words
book din
Wata muguwar faduwa gaban shi ya yi , da sauri ya mike zaune ya na zaro idanu ya na kallon ta ya ce " ke , ke me ki ke yi nan " ya kai karshen ya na jan Duvet ya rufe kafafun shi har zuwa kugu
zaune ta ke bakin gadon nashi , ta na sanye da wata Abaya fara kal mai mugun kyau , ta sha wasu stone golden color , ta yafa veil din ta a kai ba ta yi Rowling din shi ba
kallon book din Tesnim ta na fadin " me ka ke karantawa "
" ba ki ba ni amsar tambaya ta ba , me ki ke yi a nan "
a hankali ta ajiye book din saman bedside drawer ta juyo ta kalle shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " ba ka ji dadin gani na ba ? "
" Tesnim please tashi fice min da ga daki , ba za ki iya jira na a parlour ba " ya fada ya na nuna mata kofar fita dakin
turo mishi dan bakin nan nata ta shagwabe fuska ta ce " haba ni da na zo yi maka Surprise shi ne za ka ce na tashi na fita "
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " shikenan , tafi parlour ki jira ni na saka kayana "
noke mishi kafada ta yi ta na cewa " uhm ni a nan za mu yi hira " ta kai karshen ta na daura dan yatsar ta saman hannun shi ta fara yi mishi tafiyar tsutsa
da sauri ya riko hannun ta ya na zaro idanu ya ce " Ke lafiyar kuwa , kin san haka ba dai'dai ba ne , please tashi ki fita "
" okay " ta fada a takaice kafin ta tashi a hankali ta nufi kofar fita
ya na ganin ta mike ya sauke ajiyar zuciya kafin ya janye duvet din jikin shi ya sauko da kafafun shi kassa ya na shirin mikewa ya ga ta tura kofar dakin ta saka mata security
wani dan karamin tsaki Abdoul ya ja , ya na marairaice murya ya ce mata " Tesnim , what are you doing ? "
a hankali ta juyo ta fara takawa ta dawo gaban shi ta tsaya ta na murmushi
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya kauda kai ya na fadin " shikenan , zauna ke ki ka sani " ya kai karshen ya na kokarin tashi
da sauri ta kai hannu ta tura shi ya koma ya zauna
a dubu dari ya dago kai ya na kallon ta a razane , " ke wai lafiyar ki kuwa ? " ya tambaye ta
" ban sani ba , me ka ce min ah ? wai ba na cikin ajin matan da za ka bude baki ka furta musu kalmar soyayya "
da sauri ya ce mata " i'm sorry , ni fa wassa na ke yi miki "
noke mishi kafada ta yi ta na cewa " ni ban yarda ba , yau sai ka fada min dalilin da ba za ka iya bude baki ka ce ka na so na ba "
marairaice mata fuska ya yi ya na cewa " please Tesnim , wlh ba na jin dadin yanayin nan da mu ke ciki , in magana ki ke son mu yi ki bari na saka kayana mu tafi garden "
noke mishi kafada ta yi ta na turo dan bakin nan nata
a hankali ya furza iska da ga bakin shi ya dafe kan shi da hannu guda murya cen kassan makoshi ya ce " na shiga uku yau ni Abdoul , yarinyar nan ta na neman ta kashe ni " ya kai karshen ya na jan tsaki kafin ya yi kokarin tashi
da sauri ta sa hannu ta tura shi ta na fadin " ba bu in da za ka je yau , sai ka ba ki amsar tambaya ta "
shiru ya yi ya na kallon ta , ya ma rasa abun da zai ce mata dan fa hakurin nashi ya kusa karewa
cikin zafin nama ya mike tsaye lokaci guda , ya riko hannun ta ya na kallon ta cikin ido ya ce " Get out ! "
marairaice mishi fuska ta yi ta na sakin kukan shagwaba kamar Inaya har da bubuga kafafu a kassa , har da wasu hawaye ke zubo mata
da sauri ya sake ta ya na fadin " please stop , wai me na yi miki ne ki na son ki takurawa nitsuwa ta wlh " ya fada ya na marairaice mata murya
a hankali ta daina kukan shagwabar ta , ta na turo mishi baki ta ce " kenan da gaske ba ka so na ? "
a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce mata " Tesnim Ina son ki mana , ki na son takura min dayawa , dubi cikin halin da ki ka saka ni yanzu , duk duniyar nan bayan Inaya da Nesrine ba taba kai hannu na taba wata macen ba , yanzu ga shi sai da ki ka sa na taba ki , why za ki min haka "
da sauri ta katse shi da cewa " because you are mine , and I love you "
a hankali ya koma ya zauna ya dafe kan shi da hannu ya ma rasa abun da zai ce mata wlh
ya na a haka kawai ya ji ta zauna geffen shi
slowly ya juyo ya kale ta cikin sanyin murya ya ce mata " Tesnim , wlh ba na jin dadin zaman ki a nan , dubi ko kaya ba bu a jikina "
cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " so when we'll get marry ba za ka iya zama kusa na ba bare har " ta kai karshen ta na daga mishi gera guda
wani cool murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ke dai wlh so ki ke ki kashe ni yau , na ji shikenan mu zauna a hakan amma wlh kar ki taba ni , in kuma ki ka taba ni sai na yi miki ihu kwartuwa "
bai gama rufe bakin shi ba Tesnim ta bushe mishi da dariya har da tapi
sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce " hayya bismillah yi mu gani , Ka ce fyade na zo yi maka "
hararrar wassa ya wurga mata ya na tsuke fuska ya ce " Lafiyar ki kuwa ? "
hararrar wassa ita ma ta yi mishi kafin ta ce " me ka gani ? "
daga mata kafadu ya yi allamun bai sani ba
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta mike ta dawo gaban shi ta tsaya sannan ta mika mishi hannun ta
kallon hannun nata ya yi na dan lokaci kafin ya dago nashi a hankali ya riko nata ya na kallon cikin idanun ta
" Na tafi , amma fa zan dawo , dan ban gama da kai ba " ta kai karshen ta na janye hannun ta ta juya a hankali ta fara takawa ta nufi kofar ta cire security , sannan ta bude ta
har ta daga kafa za ta fita ta jiyo Muryar shi ya na kiran sunan ta
a hankali ta juyo ta na murmushi ta daga mishi gera guda allamun minene
wani dan karamin murmushi shi ma ya sakin mata kafin ya ce " murmushi na yi miki kyau "
kara fadada murmushin ta ta yi sannan ta ce mishi " kai ma haka " ta na gama fadar hakan ta juya ta fice abun ta
wani kyawatencen murmushi ya saki ya na kallon har ta fita sannan ya kai hannu saman bedside drawer ya dauki book din shi , ya koma ya konta ya ci gaba da karatun shi
▪AFTER SOME HOURS
▪INAYA
a hankali ta turo kofar dakin da a ka kontar da Malik ta shigo ta na sallama
dakin babu kowa sai wasu sojoji guda Shidda ko wane rike da gun su na tsare da shi
su na ganin ta duk su ka shiga sara mata cikin girmamawa , sannan daya bayan daya su ka fara takawa su ka fice dakin , su ka tsaya a bakin kofar dakin
su na fita Inaya ta karaso a hankali ta janyo Chair ta zauna bakin gadon Malik , ta kai hannu a hankali ta riko nashi hannun
har yanzu dai jikinshi da sanyi , abun kamar kara sanyi ma ya ke yi
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Baby , na fada maka wani abu ? " Sai ta yi shiru na dan dakikai kamar ya amsa ta
a hankali ta matso da bakin ta wajen kunnen shi ta ce mishi " ka kusa zama uncle , Nesi is Pregnant " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya
da ga haka ta turo dan bakin nan nata ta na cewa " uhm ni ma ina son mu samu baby , kyakyawan baby boy or baby Girl , mai kama da kai , har wadanan idanun naka , na san ba karamin kyau zai yi ba , na ga Text din da ka tura a waya ta , Hmm dama haka ka iya zuba kalaman soyayya , sai da na tambayi kai na anya yaya Zayd di na ya rubuta su , Please ka tashi mana , ba ka ce honey moon za mu tafi ba , shi ne za ka konta ciwo ? wlh ban yarda ba , sai ka tashi mun tafi honey moon , ni fa har na fara tunanin wajajen da za mu tafi , ka ga ina son mu tafi shan ice cream , mu tafi cinema , Mu tafi Shopping , kuma ina son mu tafi beach kamar yadda masoyya su ke yi a film " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya
a hankali ta kai bakin ta saman kumatun shi ta manna mishi kiss , sannan ta ce " shikenan ya isa haka , ba zan cika ka da surutu ba , dama ka ce ina da surutu kamar parrot , Ina son ka sosai yaya Zayd di na , I love you Mr Inaya " ta kai karshen ta na sake yin wata yar karamar dariya
sai da ta gama dariyar ta sannan ta mike a hankali ta kai lips din ta saman forehead din shi ta manna mishi kiss , sannan ta sauko saman kumatun shi dukka biyu ta yi mishi kiss , sannan ta sauko saman lips din shi ta yi mishi kiss kafin ta janye
murya kassa kassa ta ce mishi " zan tafi dare ya yi , amma gobe zan dawo , ka kula min da kan ka my baby , I love you "
ta na gama fadar haka ta juya ta fara takawa cikin nitsuwa ta fice dakin , ta na fita ko sojojin nan su ka shigo daya bayan daya , dai-dai lokacin da wasu hawaye su ka zubo da ga cikin idanun Malik
duk sojojin wajen sai da su ka yi mamakin Hawayen da su ka gani a face din shi , cikin nitsuwa daya da ga cikin su ya juya ya fita ya nufi office din doctor , dan MALIKAT AL'UMU ta ba su umarni ko nunfashi da karfi Malik ya yi a je a kira Doctor ya duba shi
jim kadan ya dawo cikin room din , Doctor Asheem na biye da bayan shi
karasowa cikin dakin Doctor ya yi , ya nufi Machines din da ke bayan gadon Malik ya shiga dubawa , sai da ya dauki wajen good five minutes a haka kafin ya ciro stethoscope din wuyan shi ya daura saman kirjin shi saitin zuciyar shi ya na sauraro
sai da ya dauki wajen two minutes a haka kafin ya ji zuciyar shi ta yi bugu guda , duk da haka bai janye ba ya tsaya , sai da ya sake two minutes kafin ya sake jiyo zuciyar shi ta yi bugu guda yanzu ma
slowly ya janye Stethoscope din , ya juyo ya kali Sojojin wajen ya ce " wani ya shigo wajen nan ? "
" yeah , His MALIKAT " sojan da ya je ya kirawo shi ya fada
❤⚘ E X I L E D ⚘❤ P R I N C E ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
BOOK ________3 👑✌
P A G E 10 🌹🕊
wani kyawatencen murmushi Doctor ya saki kafin ya ce " please ku yi min magana da MALIKAT INAS & MALIKAT AL'UMU , su same ni a office "
" okay " sojan ya fada kafin ya fice dakin , a hankali doctor ya daga kafa ya bi bayan shi ya fita amma office din shi ya koma
ko da ya koma ya tardo Doctor Mike zaune saman Sofa ya na rike da wani File
a hankali Mike ya dago kai ya kali Asheem ya ce " what happening ? "
Asheem bai ce mishi komai ba har sai da ya karaso cikin Office din ya nufi chair din shi ya zauna sannan ya ce " File din minene a hannun ka ? "
rufe File din Mike ya yi , ya Ajiye saman table din gaban shi ya ce " na mai girma Malik , ina son mu gano wane irin poison ne a jikin shi , tun kafin ya mu kai ga yi mishi wankin jini , you know , it's not sure ya rayu idan a ka yi mishi wankin jini "
" kar ka damu ba san mu kai ga wankin jini ba , mun yi kokari mu cire ragowar poison din da ke a jikin shi "
" Why ? ka na ganin wannan ita ce solution , ba dan na ce it's not sure ya rayu ba , za mu ce mu kyale shi , a ka je lokacin bai yi ba , ni gaskiya ina ga fitar da shi is the best solution "
" Mike , da a ce lokacin shi ya yi da yanzu sai dai a yi maganar wani ba dai shi ba , in dai lokacin shi bai yi ba ko ba a yi mishi wankin jini ba zai tashi , saboda mutum guda , ko dan saboda ita ba zai daina yaki da wannan poison da ke a jikin shi , kuma za ka gani ita ce za ta yi sanadiyar tashin shi ba sai mun kai ga tafiya US ba "
cikin rudu Doctor Mike ya ce " Who ? "
har Asheem ya bude baki MALIKAT INAS ta turo kofar office din ta shigo ta na sallama MALIKAT AL'UMU na bayan ta
cikin nitsuwa Doctor Mike , da Doctor Asheem su ka mike tsatsaye su na gaishe su cikin girmamawa , sannan Asheem ya ce musu bismillah su zauna
ba musu su ka karaso bakin office din su ka janyo chair su ka zauna a tare su na kallon doctor babu wanda ta ce komai amma da ga ganin yanayin su ka san sun yi sanyi kamar a tsorace su ke
wani dan karamin murmushi Doctor ya saki kafin ya ce " dama a kan Malik ne na ke son mu yi magana "
da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce " me ya same shi ? wai me ku ke jira har yanzu bai tashi ba , ko so ku ke sai ya mutu baki daya na rasa shi ? " ta kai karshen kamar za ta yi kuka
cikin nitsuwa MALIKAT INAS ta ce mata " please ki kontar da hankalin ki , ki ji abun da zai fada "
murmushi mai dan sauti Doctor ya yi kafin ya ce " MALIKAT karama ta zo wajen shi yanzu da jimawa , ina ga kuma ta yi mishi hira , bayan fitar ta ne daya da ga cikin guard ya zo ya na ce min wai na zo na gani Malik ya na hawaye , da na je na duba shi na ga Zuciyar shi ta fara bugawa , har jini ya na ci gaba yawo a jikin shi "
da sauri MALIKAT INAS ta ce mishi " ka na nufin bai mutu ba , zai iya tashi ? "
gyada mata kai Doctor ya yi kafin ya ce " zai tashi ma in Allah ya yarda , na lura kamar maganar nan ce da MALIKAT ta yi mishi , ya ji ta a jikin shi , da za ku bi shawara ta , ta dinga zuwa ta na yi mishi magana , idan har ya na jin Muryar ta na san zuciyar shi za ta dawo dai'dai , mu kuma za mu kokarin cire sauran poison din da ke jikin shi , ta yadda ba sai an yi mishi wankin jini ba , ni fa ban yarda da irin wadanan abubuwan ba , amma wannan karan zan iya cewa soyayyar ta ita ce antidote din da zai tayar da mai girma Malik "
kallon juna MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka yi kafin su juya su kali Doctor