Showing 66001 words to 69000 words out of 104561 words
diner "
ba tare da ya juyo ba ya ce mata " ba na jin yunwa "
ya na gama fadar haka ya tura kofar ya shiga sannan ya turo kofar ya rufe ya jingina bayan shi a jikin ta ya daga kai sama ya lumshe idanu , ya sauke ajiyar zuciya
Inaya kuwa ta na ganin ya rufe kofar ta juya a hankali ta koma bedroom din da ta fito ta haye saman gadon ta konta ta dauki pillow ta rungume tsab ta na hawaye
a haka har barci ya yi gaba da ita ba ta sani ba
😴😴😴😴bari dai mu dan takaice labarin
▪AFTER SOME MONTHS
( 🤣🤣🤣yeah months na ce ba week or day ba )
da wassa² cikin Inaya har ya kai wata hudu , kullum ciwon ciki ta ke kamar wanda ke shirin nakuda , duk ta rame har wani duhu ta yi , ta daina cin abincin sai zallar fruits , ga shi in cikin nata ya tada masifar shi wata rana har sumewa ta ke ba ta da labari ta kwana ta ini a haka , sai ta dawo cikin hayacinta ita kadai
na san za ku tambaye ni ina Malik ?
ya na nan shi ma , sai dai yanzu ya daina kula ta sam , cikin gida guda su ke amma ko taku gaishe shi sama sama ya ke amsa mata , asali ma tun karfe biyar na asuba ya ke barin gidan ya dawo karfe daya na dare , saboda ba zai iya jure ganin ta cikin wannan halin ba , duk yin duniyar nan da ya yi da ita a kan su zubar da cikin ta ki yarda , haka ya sa mata ido ya kyale ta da abunta , amma shi dai ya daina kula da ita ya bar kwana bedroom guda da ita , amma kawo Maid cikin gidan wanda za su dinga kula da ita da yi mata girki , shi kuma ya bar gidan , ko ya bar gidan babu inda ya ke tafiya , sai in ya ji yunwa ya tafi restaurant , idan ya gama ya koma cikin motar shi ya zauna har tsakiyar dare sannan ya koma
amma wani abu kuma , duk lokacin da ya koma sai ya fara shiga bedroom din ta ya ga halin da ta ke ciki , idan kuma ya tardo ta na barci ya tsaya ya na kallon ta kamar bakuwar shi
ya na son ya rungumi babyn shi amma son kai ya hana shi
▪MALIK
a hankali ka tafiya cikin wani kyawatencen park cike da mutane musaman yara ko wane ya na sha'anin shi
Malik kuwa ya na tafe ya na kallon gaban shi amma da ga gani ka san hankalinshi ba ya tare da shi kawai dai tafiya ya ke
ya na tsaka da tafiyar shi kawai ya ji ya bugi mutun har sai da ya yi gaba da zai fadi
da sauri mutumin nan ya sa hannu ya taro shi , sannan ya janyo shi baya ya mikar da shi tsaye
wata yar karamar Ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya kalli mutumin nan ya na yi mishi godiya
mutumin fari ne kal jinin larabawa , ya na da sexy blue eyes ma daukar hankali da dogon hanci kamar pencil ga lips din shi pink color , ya na da curly hair kamar na Malik sai dai na shi ya fi cizawa ya daure shi a baya , a shekaru zai kai 38 years
ya na sanye da wani jeans baki da t-shirt T-shirt navy blue , hannayan shi cikin wasu gloves black color
cikin sanyin murya ya cewa Malik " are you okay ? ka na tafiya ko gaban ka ba ka kallo ? "
gyada mishi kai kawai Malik ya yi ya na shirin magana kawai ya ga mutumin nan ya duka ya dauki wayar shi da ta fadi kassa
sannan ya mike ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya ce " sorry , ni ma ba na kallon gaba na ne "
ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar wata mata a bayan shi ta na fadin " na kamo ka " ta kai karshen ta na riko hannayan shi duka biyu a baya
matar kyakyawa ce , fara kal da ita da ga gani ta na samun hutu , a shekaru za ta kai 23 haka
ta na sanye da wata Abaya navy blue mai mugun kyau ta yi Rowling veil din ta black color
ga wani katon ciki da ya yi mata tsaye , da allamun juna biyu ne da ita kuma zai kai wata bakwai ko takwas
wata yar karamar kara mutumin nan ya saki ya na fadin " please ki sake ki mana , ba ki ga ina magana da mutum ne ? "
" Ah da Aljani ka ke magana , Abban Ummi , kai fa ka ce na shirya mu tafi park , yanzu kuma mun zo ka ka ce mu koma gida , ni wlh babu inda zan je , mu tafi plush na ke so " ta kai karshen cikin shagwaba
kallon ta kawai Malik ya ke , yanayin da ta yi shagwabar ta ya yi mugun tuno mishi Cutie din shi
a hankali mutumin nan ya dago kai ya ga irin kallon da Malik ke yi wa matar shi
bai ce mishi komai ba ya kwace hannayan shi da ya juya a hankali ya ce mata " Mrs Aylan , tafi ina zuwa , bari na gama magana da shi "
cike da shagwaba ta ce mishi " da gaske za ka ciwo min plush ? "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " bayan wadda ke cikin cikinki ? in bai ishe ki ba zan ba ki wani " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda
turo dan bakin ta ta yi ta na fadin " ni dai plush na ke so , kuma dole ka amso min yawwa "
wata yar karamar dariya ya yi ya na fadin " yanzu dai bari na yi mishi magana , in ya so ko me plush din ne ma za ki samu "
wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta koma inda ta fito
ta na barin wajen ya juyo ya zo gaban Malik ya tsaya ya ce " lafiya ka tsare ta da ido ? , she is my wife "
cikin sanyin murya Malik ya ce mishi " i'm sorry " ya kai karshen ya na shirin rabawa ta geffen shi zai wuce
da sauri ya riko hannun shi ya na fadin " ta yi maka kama da wata ce ? "
a hankali Malik ya bude baki ya ce " Cutie "
wani dan karamin murmushi mutumin nan ya saki kafin ya ce " hmm , ka ga, ga banci cen , mu je ka fada min wacece wanan Cutie , zan so na ji labarin soyayyar ku in ya fi namu dadi , let's go ? " ya kai karshen ya na daga mishi gera allamun ya sunan shi
" Nawfel " Malik ya fada a takaice
gyada kan shi mutumin nan ya yi kafin ya ce mishi " General Aylan " ya kai karshen ya na mika mishi hannu
ba musu Malik ya riko hannunshi , su ka yi musbaha , sannan Aylan ya ja shi su ka nufi wani hanci su ka zauna ya na cewa " tell me now , wacece Cutie ? "
" My wife " Malik ya fada ya na kallon hannayanshi
" waw , we are maried , yaran ku nawa ? , ni ina da Twins , na uku na kan hanya " ya kai karshen ya na wata yar karamar dariya
ba tare da ya dago kan shi ba Malik ya ce " ko guda , ina ga kuma ba za mu taba samu ba " ya kai karshen a sanyaye kamar ya na shirin kuka
" oh , i'm sorry , what happened ? we are sick ? a kassar US fa ku ke , in matsalar haihuwa gare ku za ku iya samun solution , cikin sauki ma kuwa " .
girgiza mishi kai Malik ya yi a hankali ya na fadin " ba matsalar haihuwa gare mu , we are okay "
cikin rudu Aylan ya ce mishi " and ? why ka ce ba za ku taba samu ba ? ko ba ka son samun baby ? ni ma da farko haka na ke , ko mace ba na so kusa da ni , amma lokaci guda ta shigo rayuwa ta , kuma ba na fatan ta fita "
cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " ni ma ba na son ta tafi , i don't know what to do , ba ta jin magana ta , na ce mata ta zubar da cikin amma ta ki , sai illa ya ke yi mata ya kokarin raba ni da ita amma ta kassa gani , i can't live without her " ya kai karshen a sanyaye
" okay , calm down now , ina ga wani abun na damun ka , tell me , may be i can help you "
girgiza mishi kai Malik ya yi ya na cewa " ko na fada maka ba abun da za ka iya yi min "
" just tell me , za ka gani "
ba musu Malik ya ce mishi " she is Pregnant , but her pregnancy is risked za ta iya rasa rayuwarta wajen haihuwa , ko yanzu ba karamar illa ya ke yi mata ba , bayan fruits ba ta iya saka komai a cikin ta , imagine two months da fruits kawai ta rayu , Idan ya fara yi mata ciwo har sai ta fita hayacinta ba ta sani ba , duk doctor din da na yi wa maganar , ce min ya ke wai mu zubar da cikin , ko kuma a cire mata yaron idan ya kai wata bakwai ko takwas , shi ma it's not sure baby ya rayu , na ce mata mu zubar da cikin amma ta ki yarda , she just want to leave me , i can't live without her , i can't " ya kai karshen idanun shi na cikowa da ruwa
da sauri ya lumshe su ya na kauda kai gefe
ya na a haka ya ji Aylan ya dafe shoulder din shi cikin sigar rarrashi ya ce mishi " bari na fada maka , lokacin da ta haife min Twins di na a ranar mutuwa kawai a ba ta yi ba , ba zan taba manta wannan ranar saboda a ranar na ji tsoron da ban taba ji ba a rayuwa ta , ga shi yanzu har sun girma sai shegantaka kala kala , ita kanta ta manta da wannan ranar kamar komai bai faru ba , yanzu a ka je wajen haihuwa ba ta mutu kuma fa ? ya za ka yi ? me za ka ce mata ? "
shiru Malik ya yi ya na tunanin abun da ya ke fada mishi
dan jinkirtawa Aylan ya yi kafin ya ce " kamata ya yi a ce ka na tare da ita a wannan lokacin , ko da shi ne last time din ta a duniya , ku yi shi a tare , yanzu ka sa kan ka cikin damuwa , ka saka ta cikin damuwa , hakan ko ba karamin hatsari ba ne ga mace mai karamin ciki , ka na neman ka kashe ta da kanka , shawara guda zan ba ka , ka je ka rungumi matar ka da babynku , why za ka juya mata baya a lokacin da ta fi bukatar ka a kusa da ita ? kai a ganin ka ka yi mata adalci ? kar ka bari son zuciya ya raba ka da ita tun kafin mutuwa ta raba ku "
slowly Malik ya dago kai ya kalle shi , cikin sanyin murya ya ce " i'm afraid , ba zan so na rasa ta ba , ita kadai ta yi min saura a duniya "
" in sha Allah ba abun da zai faru da ita , kamar dai ba ka san ikon Allah ba , ka kai kukanka gare shi , in sha Allah zai warware maka matsalar ka , bare kuma wannan dan karamin abu , mata nawa ne ke rasa rayukan su wajen haihuwa without her pregnancy was dared ? kawai lokacin su ne ya yi , idan lokacin ka bai yi ba ko cikin bakin lion ka ke ba za ka mutu ba , may be ita ma nata lokacin ba wajen haihuwa zai zo ba , kawai ka sakawa kan ka tsoro ne "
a hankali Malik ya sunkuyar da kai ya na kallon hannayanshi
murmushi mai dan sauti Aylan ya yi ya na fadin " na cika surutu ko ? "
" hmmmm , ai kai na ba ka ce komai ba , idan Cutie na magana sai ka ce an kunna radio sam ba ta gajiya da surutu "
wata yar karamar dariya ya yi ya na fadin " haka matan nan su ke da mugun surutu , ga shi yanzu ta koya min har ya kai ba na iya rufe baki na " ya kai karshen ya na wani dan karamin tsaki ya kauda kai gefe
shi dai Malik bai ce mishi komai ba ya tafi duniyar tunanin shi , har sai da Aylan ya tashi ya bar wajen bai sani ba
sai da ya share wajen ten minutes a haka kafin ya dago kan shi , ya na shirin magana ya ga wajen babu kowa
ya kalli dama ya kalli hagu , amma bai gan shi ba
kawai ya tambayi kanshi ko dai da aljani ne ya yi magana bai sani ba
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya jingina bayan shi a jikin bancin ya daga kai sama ya lumshe idanu , har ga Allah ya na matukar kewar Cutie din shi , specially wannan yar shagwabar ta , da wannan dan bakin surutun nata , ya na kewar komai nata , wajen two months ya kwaurace mata baki daya , sai yanzu ya ke nadamar biyewa son zuciyar shi , da yanzu tare da ita zai zowa park din nan , shi ma katari ne a ka yi ya zo wucewa kawai ya ga wajen ya burge shi shi ne ya shigo , ya San ita ma zai mugun burge ta , gaskiya zuciya ba ta yi mishi adalci ba , gashi yanzu ta na neman ta raba shi da abun kaunar shi guda , shi kan shi bai san ya a ka yi ya jure tsawan watanni ba ta kusan shi , bare kuma ita da ta fi bukatar shi fiye da komai , bisa hallacin da ta yi mishi , ta so shi a lokacin da ba shi da komai , kowa na yi mishi kallon makaho da kurma amma a haka ta so ta zauna tare da shi gaskiya bai kyauta mata ba
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】
【 BOOK ________3 📚✍💌 】
______________________🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸___________________
{ P A G E ♡♡♡ 22 🌹🕊}
▪MISALIN KARFE 1 NA DARE
a hankali ya ke haura stair jiki a mace , ya sunkuyar da kai hannun shi rike da wata yar leda kamar ta restaurant
kai tsaye bedroom din shi ya nufa
har zai shiga ya jiyo Muryar ta kassa kassa kamar ta na gama
a hankali ya juya ya nufi bakin kofar bedroom din ta ya tsaya ya na sauraron abun da ta ke fada
zaune ta ke tsakiyar gadon ta yi irin zaman cin ruwa , ta na rike da waya a kunne ta na hawaye
sai da ya yi wajen one minute a haka kafin ya jiyo Muryarta ta na fadin " shikenan Ammie zan yi yadda ya ke so "
dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce " sai da safe Ammie " ta na gama fadar haka ta sauko wayar ta ajiye gaban ta , ta saki kuka kamar ran ta zai fita
har cikin zuciyar shi ba ya jin dadin wannan kukan nata , yau ga shi kuma ta kuka saboda shi gaskiya bai ji dadin haka ba
ta na tsaka da kukan nata ta ji cikin ta ya murda
a hankali ta ce " Ashhhhhh , za ka fara ko ? "
a rude Ya tsaya ya na tambayar kanshi da wa kuma ta ke magana
ya na a haka ya sake jiyo Muryar ta ta na fadin " ka yi hakuri babyna , amma ba yadda zan yi dole na rabu da kai , ba dan Daddyn ka ba ya son ka ba , kawai bai shirya haihuwa yanzu ba , amma ya na son ka , sosai ma fiye da yadda na ke son ka , ba zan iya jure ganin fushin shi ba ko wace safiya , ka na gani ya daina min magana , ko kallo na ba ya yi , hakan ya na min zafi , ka yi hakuri amma ba za ka ci gaba da zama ba , Washhhh " ta fada da dan karfi ta na komawa ta konta ta takure waje guda ta rungume pillow ta na kuka kassa kassa
duk abun da ta fada ya ji ta , ya na