Showing 75001 words to 78000 words out of 104561 words
............ 24 🌹🕊}
▪SRORY 🔥
A hankali Malik ya mike ya na fadin " ki kontar da hankalinki , ina nan zuwa gobe " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran
haka ya ci gaba da latsa wayar shi , ya dan jima kafin ya kai wayar a kunne babu ko sallama ya ce " ina jiran ka Saudiya gobe , tare da Familyna " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran ya mike tsaye
kai tsaye stair ya nufa ya Haye ya koma bedroom din su
ko da ya shiga dressing room ya wuce , ya shirya kayan su cikin trolley guda babba , ya fiddo ta ya ajiye bakin kofar
sannan ya nufi bed din su ya haye ya na sauke ajiyar zuciya , ya lumshe idanunshi
ya na a haka ya jiyo Muryar ta ta na fadin " yaya Zayd , gida za mu koma ? "
ba tare da ya bude idanunshi ba ya ce " No , ke a nan za ki zauna , ni ma ba zan jima zan dawo "
" what ? me ya sa ? ni gaskiya tare za mu tafi , ina so na ga su Ammie " ta fada kamar za ta yi kuka
a hankali ya ware idanunshi ya juya su na fuskantar juna ya ce " ki yi hakuri Cutie ki zauna a nan , wlh idan ki ka bi ba zan samu nitsuwar yin aikin da ya mayar da ni , idan ki na nan hankali na zai fi konciya , ba zan so wani abu ya same ki tare da babyn mu ba "
" ni gaskiya yaya Zayd tare za mu tafi , ka bukata ta a kusa da kai , ni wlh ko ka tafi ka bar ni sai na bi bayan ka , in ya so na bace saman hanyar "
" please my Cutie , kar ki raba min hankali gida biyu , kin ga ko kwana biyu ba zan yi ba zan dawo "
a hankali ta juyo ta ba shi baya , kawai sai ta sakin mishi kuka ba tare da ta ce komai ba
" ya salam !" ya furta cen kassan makoshi
a hankali ya kai hannu ya janyo ta jikin shi ya hade bayan ta da kirjin shi ya ce " shikenan , rigimamiya kawai, mu tafi , amma wlh ba za ki fito bedroom din ki ba "
wata yar karamar dariya ta yi dama ba kukan ta ke ba kawai dai ta san duk lokacin da ta ke mishi kuka ya na yi mata abun da ta ke so
▪BAYAN SALLAR ASUBA ⛅
tsaye Malik ya ke bakin kofar shiga parlourn , ya na sanye da wandon jeans black color , da T-shirt red color , ya daura wata jacket black color da ga sama , ya na tsaye sai faman duba watch din hannun shi ya ke
ya na tsaye a haka Inaya ta fara sauko stair , ta na sanye da wata Abaya pink color , sai dan karamin hijab din ta white color dai'dai kirji , ga katon cikinta ya yi tsaye
a hankali ta ke sauko stair din ,
tun da ta fara saukowa ya tsare ta da ido babu ko kiftawa
har sai da ta karaso gaban shi ta tsaya , ta na shagwabe fuska , ta na faman turo bakin nan nata kamar ya ce zai yi mata kiss
matse gera ya yi ya na nuna mata hanyar fita parlourn ya ce " wuce mu tafi , da wani katon cikinki kamar ball "
murguna mishi baki ta yi ta na yi mishi hararrar kassa ido kafin ta daga kafa ta fice
sai da ya kashe duk lamps din parlourn , sannan ya bi bayan ta su ka fita
kai tsaye get din fita gidan su ka nufa , ta na gaba ya na bayan ta
su na fitowa gidan ta ga motar shi bakin kofar an yi parking din ta , ga gateman nan tsaye geffen ta
su na fitowa Malik ya bude mata kofar motar ta shiga a hankali , sannan ya juya ya yi wa gateman magana kafin ya juya ya nufi wajen driver ya shiga ya tada motar kai tsaye ya nufi airport
su na isa , su ka shiga private jet din shi , lokaci guda Jet din ya daga ya nufi kassar Saudiya
▪AFTER SOME HOURS
▪MASARAUTAR SAUDIYA ❤
Misalin karfe 9 na safe , jirgin su ya sauka a kassar Saudiya
tun da ya shigo kassar ya ga komai ya sauya mishi kamar ba Saudiyar da ya sani ba
bai gama shan mamaki ba sai da ya isa bakin kofar Daular Saudiya
a nan ya ga wasu status guda biyu na lions sun bude bakunansu , ga wasu Sword biyu gaban kawuna su , a takaice tambarin Daular Ottoman ne a kafe bakin kofar Daular Saudiya da ga gani kuma na zallar gold
a haka Malik ya danne abun cikin zuciyar shi ya shiga Daular
nan ya tabbatar da cewa Eh Aymane ba Al'heri ya ke shukawa ba , dan duk Daular ta ruguje
garden din ta ya bushe kamar ba a taba yin ciyayi a wajen ba , duk ginin sun kwararabe da ga gani ba a kula da su
a hankali Inaya ta tabo hannun shi ta na cewa " yaya Zayd , an ya nan gidan mu ne ? ba ka yi batan kai ba ? "
murya a sanyaye ya ce mata " No my Cutie , ban yi batan kai ba , in sha Allah komai zai koma kamar da farko "
ba ta ce mishi komai ba ta tsaya ta bin wajen da kallo ga jikin ta ya yi mugun sanyi
duk inda motar su ta wuce sai an tsaya a na bin ta da kallo
Malik kuwa kai tsaye part din MALIKAT HOUDA ya nufa ya yi parking din motar bakin kofar shiga part din
ya na yin parking ya kashe motar ya kalli ta cikin glass din motar
ya ga kowa ya tsaya waje guda su na kallon motar allamun su na jiran su ga wanda zai fito da ga ciki
a hankali ya sauke ajiyar zuciya , kafin ya kai hannu ya bude kofar motar ya sauko da kafar shi guda ,
sai da ya dan jinkirta kafin ya fiddo gudar kafar ya fito da ga cikin motar
duk wanda ke wajen sai da ya saki kuka lokaci guda ganin Malik ya dawo cikin masarautar
shi kan shi sai da idanunshi su ka ciko da ruwa
a hankali ya fara bin wajen da kallo , cen ya hango Azim ya tunkaro shi da mugun gudu ya na daga mishi hannu , ga idanun shi nan cike da ruwa
haka Malik ya tsaya ya na kallon shi , har sai da ya kusa kawowa wajen motar ya yi tuntunbe ya fadi
da gudu Malik ya nufe shi , ya zuwa ya Zube saman guyiwowinshi ya tallabo Azim ya na fadin " Azim , ba ka ji ciwo ba ? "
ina ko amsa mishi tambayar shi Azim bai yi ba , ya rungume shi ya na sakin kuka kamar karamin yaro
a hankali shi ma Malik ya zagayo da hannayanshi a baya a Azim ya rungumeshi , da a ce zai iya yin kuka da ya yi shima
sai da Azim ya gaji da kukan nashi sannan ya dago da ga jikin Malik ya na fadin " Ina ka shiga ranka shi dade ? ina ka tafi ka bar mu ? kai da kanka ka ce mu ne ahalinka amma shi ne ka tafi ka bar mu ? ba ka san irin kangin da mu ka shiga bayan tafiyar ka ba , na godewa Allah da ba abun da ya same ka , don Allah kar ka tafi ka sake barin mu a hannun wacen azzalumin mutum " ya fada ya na hawaye bibiyu
a hankali Malik ya mike tsaye , sannan ya taimakawa Azim ya mike tsaye shi ma
hannu ya kai ya fara gogewa Azim hawayen shi ya na fadin " kar ka damu Azim , in sha Allah babu inda zan je , ko zan tafi sai na cire ou da ga hannun wacen azzalumin "
a hankali Azim ya gyada mishi kai ya na sakin wani dan karamin murmushin da har ya manta rabon shi da ya yi murmushi
a hankali Malik ya juya ya nufi motar shi da sauri Azim ya mara mishi baya , su na isa
ya bude gidan baya ya fiddo trolley din su
Malik kuwa ya nufi geffen Inaya , ya bude mata kofar , sannan ya mika mata hannu
ba musu ta daura hannun ta saman nashi , sannan ta sauko a hankali
Azim na ganin cikin Inaya ya saki wani kyawatencen murmushi ya na yi wa Allah godiya cikin zuciyar
cikin sanyin murya ya ce mata " ki shiga ina zuwa , su Ammie duk su na ciki "
gyada mishi kai kawai ta yi , da ga haka ya manna mata kiss saman forehead ya raba ta geffen ta ya shiga cikin motar shi
A hankali ta daga kafa ta fara takawa ta shiga part din MALIKAT HOUDA , Azim na biye da bayan ta janye da trolley
bakin ta da Sallama ta shigo parlourn MALIKAT HOUDA , nan ta tardo MALIKAT INAS , MALIKAT AL'UMU , mama , Tesnim , Nesrine , har ita kan ta MALIKAT HOUDA
Nesrine da mama na ganin ta su ka tashi da gudu su ka nufe ta , su ka rungume , su na sakin kuka
wata yar karamar dariya Inaya ta yi ta na fadin " Ashhhhhh , kar ka ku ji wa babyna , ciwo "
a tare mama da Nesrine su ka daga da ga jikin Inaya su na kallon katon cikinta
Godiya mama ta shiga yi wa Allah cikin zuciyar ta , Nesrine ma haka sai sakin murmushi ta ke
wani kyawatencen murmushi Inaya ta saki , ta nufi MALIKAT INAS da sauri ta na fadin " Ammie "
da sauri MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka mike su na fadin " yi a hankali baby "
cak ta tsaya ta na murmushi har su ka karaso wajen ta , su ka rungume ta sannan su ka shiga tambayar ta ya jiki , ya hanya
gyada musu kai kawai ta ke ta na murmushi
cen cikin hannun MALIKAT HOUDA ta hango wani baby , ya na barci sai jijiga shi ta ki
washe baki Inaya ta yi ta nufi MALIKAT HOUDA ta na fadin " la mamie , baby ki ka samu ? "
a tare duk su ka yi wata yar karamar dariya sannan MALIKAT HOUDA ta ce mata " ba na son shirme , na Nesrine ne "
dan zaro idanu Ta yi kafin ta juya ta kali Nesrine , da ke tsaye ta na hawaye , irin kallon nan na tambaya
a hankali Nesrine ta gyada mata kai ta na murmushi allamun Eh
zama geffen MALIKAT HOUDA ta yi ta na fadin " mamie ba ni shi na rike " ta fada na mika mata hannu
cikin zolaya Tesnim ta ce mata " wannan katon cikin naki zai bari ki dauke shi ? "
" ni dai sai na dauki babyn Nesi " ta fada cike da shagwaba har da turo baki
" karbi , ba za mu iya rigimar ki ba , ai dama dole ta ce sai ta rike shi , ba mijin ta ba ne " MALIKAT HOUDA ta fada ta na daura Baby saman hannayan Inaya
da sauri Nesrine ta ce mata " yi a hankali kar ki murde min kan baby "
hararrar ta Inaya ta yi ta na fadin " to ina ruwan ki , ai ni ma na kusa samun nawa babyn " ta kai karshen ta na murguna mata baki
a hankali Nesrine ta karaso wajen ta , ta na fadin " ban babyna tun da haka ne " ta kai karshen ta na mika mata hannu
da sauri Mama ta ce mata " Nesrine wai biye mata za ki yi , kin fi san halin ta "
hararrar Inaya Nesrine ta yi kafin ta koma gefe ta zauna ta na tsuke fuska
a tare kowa ya koma ya zauna kafin MALIKAT INAS ta ce " baby , ina mijinki ya yi ? ba tare ku ka zo ba ? "
a hankali Inaya ta dago kai ta kalli MALIKAT INAS ta ce " a tare muku Ammie , ya ce akwai inda zai je yanzu ya dawo "
a tare duk su ka yi hamdallah , sannan MALIKAT AL'UMU ta ce " baby , ya kamata ki je ki huta ko ? "
noke mata kafada ta yi ta na fadin " ni tare da babyna zan tafi "
da sauri Nesrine ta ce mata " wane babyn ? kam , wlh tun wuri ki sauke idanun ki da ga saman babyna , in ba haka ba na yi miki duka kawo ruwa "
cikin nitsuwa Tesnim ta ce mata " Malik ko ya cire miki kai , gwara ki bi ta cikin ruwan sanyi ku rabu lafiya , dan ita ta na son babyn nan ko mutuwa za ki ba abun da zai raba ta da shi "
marairaice fuska Nesrine ta yi ta na shirin magana , ta ga Inaya ta miko mata babyn ta na fadin " amshi , barci na ke ji "
da sauri Nesrine ta kai hannu ta karbi babynta
ta na karba Inaya ta mike tsaye a hankali , ta na dafe da cikinta , ta ce " mama , barci na ke ji " ta kai karshen cike da shagwaba
wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon ta , yau dia ga autar ta da ciki har ya kai watan haihuwa , ga kuma Nesrine da babynta , saura na Abdoul kadai ta ga burin ta ya cika
a hankali ta mike ta nufi Inaya ta riko hannunta , ta na fadin " mu je ki yi wanka ki konta ki huta , Nesrine kawo kayanta bedroom di na "
" bari zan kai " Tesnim ta fada , ta na mikewa ta nufi trolley din da Azim ya ajiye a wajen ta bi bayan su mama da su ka shiga corridor
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】
【 BOOK ________3 📚✍💌 】
_______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________
{ P A G E ________ 25 ✍💕🔥}
▪MALIK AYMANE
zaune ya ke saman kujerar shi ta Gold
ya na rike da wayar shi ya na latsa , haka zalika duk mutanan wajen kowa na harkar gaban shi , sai hira su ke yi su na dariya
su na a haka Meli ya shigo da gudu babu ko sallama
ya nufi Aymane da gudu , kai tsaye wajen kunnen Aymane ya nufa ya yi mishi rada
a dubu dari Aymane ya mike tsaye har sai da ya saki wayar shi ta fadi kassa
a tare duk kowa ya juyo ya na kallon Aymane da ke faman zaro idanu baki sake har su na hada baki su na tambayar shi lafiya
ba su kai ga gama rufe bakunansu ba , su ka ga Aymane ya kai hannu ya damko wuyan Meli ya na fadin " karya ka ke , ba zai taba dawowa ba "
murya a disashe Meli ya ke fadin " ranka shi dade , ba karya na ke ba , da ido na na gan shi zai shiga part din MALIKAT HOUDA "
cikin bacin rai Aymane ya tura Meli baya har sai da ya fadi
ya na shirin magana idanun shi su ka sauka cikin na Malik , ya na tsaye bakin kofar shigowa Fadar ya rike hannayan shi a baya
a tare kowa ya mike tsaye ya na kallon Malik baki sake , wasu zuciyoyin su na bugawa
cikin bacin rai Aymane ya ce mishi " me ka ke yi a nan ? "
a hankali Malik ya daga kafa ya fara takawa ya karaso tsakiyar fadar ya na fadin " na zo karbar abu na , dama aro ne na ba ka "
wata shegiyar dariya Aymane ya yi kafin ya koma saman kujerar Malik ya zauna , irin zaman nan na qasaita ya ce " ko da HICHAM BIN JAABAR ne zai fito da ga cikin kassa , ba isa ya sauke ni da ga saman kujerar nan ba , bare kai ragon banza "
cikin bacin rai Malik ya ce mishi " kar ka kuskura ka kira sunan mahaifina "
" na kira , na kira me za ka yi ? ,ko ba ka son na fadi sunan wanda ya haifi lusarin namiji kamar ka ? tun kafin na sa a cire maka kai , ka fice min da ga fada "
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " Aymane , tun ina yi maka cikin ruwan sanyi , ka sauka da ga kujerar nan "
wani makirin murmushin geffen fuska Aymane ya saki , kafin ya juya ya kalli wani dogari da ke tsaye bakin kofar fadar , da hannu ya mishi allamun ya cirewa Malik kai
ba