Showing 30001 words to 33000 words out of 104561 words
har su na hada baki wajen cewa " Ku na nufin ta dinga zuwa ta na yi mishi magana ? dan ni fa ban gane ba "
wani cool murmushi Asheem ya yi kafin ya ce " kar ku damu , kawai ku ce mata ta dinga zuwa ta na yi mishi magana , everything will be okay in sha Allah "
cikin sanyin murya MALIKAT INAS ta ce " Shikenan , na gode Doctor , please duk wani sauyi da a ka samu ka dinga fada mana "
gyada mata kai Doctor ya yi ba tare da ya ce komai ba
a tare su ka sauke ajiyar zuciya kafin MALIKAT AL'UMU ta mike ta na fadin " INAS , mu je don Allah na gan shi , ina son ganin yaro na , na San in ban gan shi ba ba zan iya barci ba "
gyada mata kai MALIKAT INAS ta yi kafin ta mike ta riko hannun ta kamar wasu abokai su ka yi wa Doctor sallama sannan su ka baro office din shi
kai tsaye room din da a ka kontar da Malik , da sallama a bakin su su ka shigo dakin
daya bayan daya sojojin nan su ka fara sara musu su na yi musu barka da wannan lokacin da ga haka su ka fara fita dakin daya bayan daya su ka ba su waje
su na fita MALIKAT AL'UMU ta karaso bakin gadon ta kai hannu saman face din shi ta shafa a hankali , sannan ta matso da face din ta kusan tashi , murya kassa kassa ta ce mishi " Na san ka na jin abun da na ke fada maka , in sha Allah ba abun da zai same ka , nan gaba kadan za ka bude idanu , na yi maka alkawari ni da kai na zan fitar da kai da ga cikin wannan kangin , na san burin su kawai su raba ni da kai , amma ba zan ba su dama ma , Na san kun shirya tafiya US Honey Moon , na sa a shirya muku gidan da za ku sauka , da duk wani abu da za ku bukata , jira kawai na ke ka tashi ba za ka kwana cikin Daular nan ba , Ina matukar son ka ka sani ko ? na san yanzu ka na son kasancewa da MALIKAT din ka , za ta dawo nan da jimawa , ni ma zan tafi amma zan dawo , ka kula min da kan ka/ka ji ko my baby ? , I love you " ta na gama fadar haka ta kai lips din ta saman forehead din shi ta manna mishi kiss , sannan ta shiga karanto mishi addu'o'in tsari ta tofa mishi sannan ta mike ta riko hannun MALIKAT INAS ta na hawaye ta ce mata " mu tafi yanzu "
a hankali MALIKAT INAS ta kai hannu ta goge mata hawayen ta , cikin sanyin murya ta ce mata " kar ki damu ba abun da zai samu yaron mu in sha Allah zai tashi "
gyada mata kai kawai MALIKAT AL'UMU ta yi ta na yi mata wani dan karamin murmushin karfin hali kafin su fara takawa a tare su ka baro dakin
su na fitowa MALIKAT AL'UMU ta tsaya gaban sojojin nan ta ce musu " bayan ni , MALIKAT INAS , MALIKAT Inaya , Tesnim , RIANNA , Diya , Doctor Asheem & Mike sai ku shiddan nan , ban yarda kowa ya shiga dakin nan ba , ko da kuwa nurse ce ta zo da sunnan Doctor ya aiko ta kar ku bari ta shiga , sannan ka tura a karo sojojin da za su tsare da ga wajen , da fatan kun fahimce ni ? " ta fada cikin ba da umarni
a tare duk su ka daga kafa su na Sara mata sannan shugaban su ya ce " an gama ran ki shi dade "
gyada mishi kai kawai MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ci gaba da takawar ta , su ka bar wajen tare da MALIKAT INAS
su na barin wajen sojojin nan su ka koma cikin dakin su ka tsatsaya su na ci gaba da bawa Malik kariya
( 🤓🤓 kai gaskiya Mulki da dadi , ko da kuwa na kamun Fara ne 🤣🤣🤣 wlh ya na da dadi , ku dubi don Allah mutumin da ke konce bai ma san inda kan shi ba ya ke , wai shi ne za a bawa kariya , 😭😭😭😭 don Allah ku kai ni gidan Sarautar nan , ko da kuwa dan Sarkin Fawa ne ina so 😭🤣 )
▪INAYA
konce ta ke cikin parlourn MALIKAT INAS , ta tada kai da cinyar RIANNA ta daura hannu saman kan ta ta na shafawa a hankali
su na a haka MALIKAT INAS ta shigo parlourn ta na sallama ,
a hankali RIANNA ta dago kai ta kali Saitin kofar ta na amsa sallamar
sai da MALIKAT INAS ta karaso cikin parlourn ta zauna saman sofa one seater sannan RIANNA ta ce mata " Ammie me doctor ya ce muku ? "
wani cool murmushi MALIKAT INAS ta yi ta na kallon Inaya ta ce " har ta yi barci ? "
dawo da kallon ta RIANNA ta yi kan Inaya sannan ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " Eh , tun fitar ku , na san ta gaji , Ammie wai ba ki lura ba yadda ta sauya kwana biyu ? "
cikin rudu MALIKAT INAS ta ce mata " sauyawa kuma kamar ya ke ? "
a hankali ta juyo ta dawo da kallon ta kan MALIKAT INAS ta ce " Ammie , i think she is Pregnant , ba ki ga yadda ta dan yi haske ba kwana biyu "
dan zaro idanu MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " ke rufa min asiri kin fi kowa sanin Malik bai shirya samun baby yanzu ba , dan haka ki cire wannan tunanin da ga cikin kan ki , kawai dai mijinta na kula da ita yadda ya dace , dan haka ki ba ta lafiya , ina baby ta kai daukar ciki " ta na gama fadar haka ta mike ta fara takawa cikin nitsuwa ta nufi corridor
da sauri RIANNA ta ce mata " Ammie kenan ba ki son ganin baby's din Malik ? "
" ina so , amma ba yanzu ba " Fadin MALIKAT INAS da dan karfi dai'dai lokacin da ta bude kofar bedroom din ta ta shiga
wata yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta dawo da kallon ta kan Inaya da ke faman barcin ta cikin konciyar hankali
▪MISALIN KARFE 2 NA DARE
▪ HOSPITAL
a hankali wata nurse ta nufi room din Malik ta na rike da wani farin box kamar A box haka
ta na isa bakin kofar dakin sojojin da ke tsaye bakin kofar su ka tsayar da ita
tun kafin su tambaye ta ta ce musu " Doctor Asheem ne ya turo ni duba jikin mai girma Malik "
cikin nitsuwa sojan ya ce mata " je ki cewa Doctor ya zo da kan shi "
da sauri ta ce mishi " ba shi lokacin zuwa da kan shi , that's why ya turo ni , please ku ban wuri na je na yi aiki na , kun ga , ga box din nan za ku iya dubawa "
cikin bacin rai daya da ke tsaye daya geffen kofar ya ce " ke fice min da ga nan , babu inda za ki shiga , ki je ki cewa doctor ya taho da kan shi "
" amma....... " ba ta kai karshen maganar ta ba ya daka mata tsawa ya na fadin " za ki fita da ga nan ko sai na tataka ki a nan ? " ya kai karshen ya na zaro mata idanu da kyau
ba karamar razana ta yi ba , ai ba shiri ta juya ta na rike da box din ta ta bar wajen
sai da ta bar wajen sannan wanda ya yi mata magana da farko ya saki wata yar karamar dariya ya ce " ko ni sai da ka ban tsoro wlh "
" na ga kamar ta na son ta raina min hankali , da tun farko tsawar ka yi mata da ba ta bata mana lokaci ba haka " ya fada ya na kauda kai
murmushi mai dan sauti Sojan ya yi kafin ya kauda kanshi shi ma
bangaran Nurse din nan kuma , kai tsaye Hospital din ta fito , amma ta kofar baya ta fito , babu kowa a wajen ko haske sosai ma ba bu
ta na fitowa ta tila box din hannun ta gefe cen cikin ciyayi
ta ja tsaki ta na fadin " why za su hana ni shiga ? gaskiya sai na zage damtse dan ganin na kashe Malik , dole na san abun yi game da wannan lamarin tun kafin ya tashi da ga saman gadon nan , ko kuma wacen sakarar yarinyar ta riga ni aiwatarwa , You just won a battle but the war has just begun "
ta na gama fadar haka ta ja wani siririn tsaki ta bace bat a wajen
▪WASHE GARI ⛅⛅⛅
a hankali Inaya ta ke tafiya cikin likita , ta na rike da wani basket a hannun ta , ta na sakin wani cool murmushi
ta na karasowa bakin dakin da Malik ke ciki duk sojojin da ke tsaye bakin kofar sai da su ka sara mata
da fara'a a fuskar ta ta ce musu " zan iya shiga ? "
a hankali guda cikin su ya kai hannu ya bude mata kofar ba tare da ya ce komai
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi ta na yi mishi godiya kafin ta daga kafa a hankali ta shiga dakin ta na sallama
yanzu ma sai da sojojin wajen su ka sara mata cikin girmamawa sannan daya bayan daya su ka fice dakin
su na fita ta karaso a hankali bakin gadon shi ta janyo chair ta zauna bakin gadon ta na bin shi da kallo ta na murmushi , yanayin Skin din shi ya koma kamar yadda ya ke , ta rage wannan farin
a hankali ta dago hannun ta ta daura saman face din shi , nan ta ji jikinshi ya rage sanyin da gareshi jiya
wani kyawatencen murmushi ta saki ta na janye hannun ta ta ce " Baby , da ga gani ka na samun sauki , na fada maka wani abu ? Gaskiya ba na jin dadin kwana idan ba ka nan " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata
a hankali ta juya ta kai hannu ta bude basket din da ke geffen ta , ta ciro wani dan karamin bowl da spoon , sannan ta cire Plate din da ke rufe da bowl din ta meda cikin basket din kafin ta juyo ta na kallon shi ta fara shan Fruit salad din da ke cikin bowl din , ta na ci ta na yi mishi hira , har wani dan jinkirtawa ta ke kamar ya na amsa mata
sannu sannu sai da ta share yinin ranar a cikin dakin shi ta na zuba mishi surutu , sai wajen kiran sallar Azahar sannan ta tashi ta ce mishi za ta dawo da yamma sannan ta baro dakin
▪ROUKSAR
zaune ta ke kassan bishiyar nan , Aymane na zaune geffen ta wannan karan bai rufe fuskar shi ba
ta yi irin zaman bokaye , ta na sanye da wasu kaya bakake da veil baki ta rufe fuskar ta shi
ga wasu kwallaye gaban ta sai hayaki ke fitowa da ga cikin su
a hankali wani wata guguwa ta fara tashi ta mamaye ta , har veil din ta ya fadi gashin ta ya fara tashi sama
sai motsa lips din ta ke yi da sauri sauri idanun ta sun koma farare kal
a hankali ta daga hannu sama , ta na haka kawai wata ball fara kal kamar lamps ta fado cikin hannun ta
lokaci guda ta juya da hannun ta daura shi saman bishiyar bayan ta , nan take Ball din nan ta shige cikin bishiyar
da sauri Rouksar janye hannun ta , ta yi baya ta na sauke nunfashi da karfi har da dafe saitin zuciyar ta da hannu guda
wata yar iskar dariya Aymane ya bushe da ita ya na fadin " Good job , kin yi aiki mai kyau "
wata nanauyar ajiyar zuciya Rouksar ta sauke kafin ta ce " Aymane , wlh idan wani abu ya same ni ba zan yahe maka ba , maci amana kawai "
" za ki iya fadin duk abun da ki ke so , ni dai ba zan ja da baya ba a kan kudiri na , na gode da taimakon ni , idan kuma ki ka ce za ki yi wani abu against me , kar ki manta da hannu kadai zan iya kawo karshen ki " ya kai karshen ya na dafe bishiyar bayan shi da hannu ya na sakin mata wani makirin murmushi kafin ya bace ya bar ta a wajen
wata yar karamar kara Rouksar ta saki kamar za ta yi kuka kafin ta bace ita ma , dama an ce macuci shi ya san makontar macuci , yanzu Aymane ya saka rayuwar Rouksar a hatsari , dan ko da kuwa branch guda ce ta bishiyar nan ta fado , to sai Rouksar ta ji a jikin ta bare a ce za a cire bishiyar baki daya , Allah ne kadai ya san abun da zai faru , amma ni dai na san ba al'heri ne su ka aikata ba
▪BAYAN SALLAR ISHA
a hankali Inaya ta ke fitowa da ga cikin corridor ta na sanye da wata Abaya Pink color me mugun kyau , ta yafa veil din a kai ba ta yi Rowling din shi ba ,
❤⚘ E X I L E D ⚘❤ P R I N C E ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊
BOOK ________3 👑✌
P A G E 11 🌹🕊
ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali da murmushi a fuskar ta
bakin ta da sallama ta shigo parlourn nan ta tardo RIANNA rungume da Tesnim da ke kuka kassa kassa
a rude Inaya ta karaso wajen ta na fadin " Aunty Tesnim me ya faru ki ke kuka ? "
cikin nitsuwa RIANNA ta ce mata " kar ki damu baby , momy ce a ka kai likita jinin ta ya hau saboda halin da Malik ke ciki , amma kar ki damu za ki iya tafiya wajen Malik "
a hankali Inaya ta karaso ta dafa shoulder din Tesnim ta na cewa " ki yi hakuri kin ji Aunty Tesnim ? ba abun da zai samu momy in sha Allah "
wani murmushin karfin hali ta na gyada mata kai ba tare da ta ce komai ba
kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Abdoul ya shigo wajen ya na sallama
Tesnim na ganin shi ta tashi da gudu ta nufe shi ta fada jikin shi ta na sauke ajiyar zuciya
a tare Inaya da RIANNA su ka saki wani dan karamin murmushi , kafin Inaya ta tako a hankali ta raba ta geffen Abdoul ba tare da ta ce komai ba ta fice abun ta dan ita ma yanzu ta na da burin kasancewa da nata masoyin
a haka ita ma RIANNA ta mike ta bi bayan Inaya amma ita wajen MALIKAT AL'UMU za ta je
su na fita Abdoul ya dago Tesnim da ga jikin shi ya ce " To rigimamiya , sake ni kare ki karaya min baya "
noke mishi kafada ta yi ta na turo dan bakin nan nata ba tare da ta ce komai ba
a hankali ya rage sautin Muryar shi ya ce mata " mu tafi garden to ? "
da sauri ta gyada mishi kai kafin ta sake shi a hankali ta na sunkuyar da kai
hannu ya kai ya riko hannun ta kafin ya juya su ka bar part din a tare
😂😂😂✌KU BARI NA BI BAYAN SU TUKUNNA , MUN NEMI INAYA DA GA BAYA 🤣🤣🤣
a tare su ka baro part din MALIKAT INAS su ka nufi garden
su na shigowa ya ce mata " me ya faru ki ka ce ki na son ganina ? " ya fada ba tare da ya kale ta ba su na ci gaba da tafiyar su
cikin sanyin murya ta ce mishi " kawai ina son kasancewa tare da kai "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " hmmm fada min gaskiya dai , da ga gani akwai abun da ke damun ki , za ki iya fadamin kin sani ko ? "
dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce mishi " ban