Showing 6001 words to 9000 words out of 104561 words
saman lips din ta ya manna mata kiss
maimakon ya yi barci kawai sai ya tsaya ya zuba mata wadanan hazel eyes din nashi , kamar ya meda ta cikin jikin shi ya ke ji
ya na a haka kawai ya ga ta saki wani cool murmushi murya kassa kassa ta ce " baby kallon ya isa haka , rufe idanun ka ka yi barci "
dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta ya ce " dama ba barci ki ke ba ? "
shiru ta yi ba ta amsa mishi ba ,
da allamu dai aljanun nata ne su ka yi mishi magana π€£π€£π€£π€£
a hankali ya lumshe idanun shi , ba jimawa barci ya yi gaba da shi
βͺMISALIN KARFE 2 NA DARE
a hankali ya fara jiyo wayar shi ta na ringing
slowly ya ware idanun shi ya na karanto adu'ar tashi da ga barci
ya na bude idanun shi sai cikin nata , ba karamar razana ya yi ba , bare kuma cikin bacin nasu ya juya da ita ta dawo saman shi ko ni ce sai na ji tsoro
" wayar ka " ta fada mishi cikin sanyin murya
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai hannun shi ya dauki wayar shi ya kali screen din
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ko sallama bai yi ba ya ce " General why za ka kira ni a irin wannan lokacin , ba za ka bari safiya ta yi ba ? "
shiru ya yi ya na sauraron abun da General ke fada mishi
sannan ya ce mishi " General ka na jin abun da ka ke fada , yanzu fa ? "
yanzu ma shiru ya yi ya na sauraron abun da General ke fada mishi sannan ya amsa mishi da cewa " Okay i'm coming " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran sannan ya latsa wayar na dan dakikai sannan ya kashe ta ya ajiye gefe
a hankali ya juyo ya kali Inaya , cikin sanyin murya ya ce " Cutie ? "
" uhm " ta fada ba tare da ta dago kan ta ba
" zan fita amma ba zan jima zan dawo " ya fada ya na kai hannu saman bayan ta ya na shafawa a hankali
da sauri ta dago kan ta da ga saman Chest din shi kamar za ta yi kuka ta ce mishi " Baby , yanzu fa ? ni gaskiya babu inda za ka je " ta kai karshen ta na meda kan ta saman chest din shi ta kankame shi da kyau
cikin sigar rarrashi ya ce mata " please Cutie , ki bari na je wlh ana jira na "
girgiza mishi kai ta yi ta na cewa " ni gaskiya babu inda za ka je cikin daren nan "
" Shikenan tashi mu tafi tare "
a hankali ta dago kan ta, ta ce mishi " da gaske ? "
gyada mata kai kawai ya yi kafin ya ce " sauka yanzu "
ba musu ta sauka da ga saman jikin shi ta koma gefe ta zauna
ta na sauka ya mike ya fara takawa ya nufi corridor ya bar ta nan zaune
jim kadan ya fito Sanye da jallabiya Fara kal mai dogayen hannuwa
hannun shi kuma ya na rike da wata Abaya Fara kal ita ma , da veil din ta
wajen ta ya karaso , ya mika mata hannu
ba musu ta daura hannun ta saman nashi ta mike tsaye
ta na mikewa ya bude abayar hannun shi ya saka mata ita , sannan ya yafa mata veil din ya riko hannun ta su ka nufi lift a tare
kai tsaye part din su ka baro
su na fitowa sai saman wata dankareriar mota baka kirin , Azim na tsaye wajen motar ya na jiran Malik
Da sauri Azim ya bude mishi gidan baya , a hankali Inaya ta daga kafa ta shiga cikin motar sannan shi ma ya shiga Azim ya rufe musu kofar ya yi sauri ya shiga wajen mai zaman banza
ya na shiga Driver ya tada motar su ka bar wajen
motar na barin wajen Inaya ta konta da kan ta saman shoulder din ta ce " Baby ina kuma za mu je ? "
" nowhere " ya fada a takaice
da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har sai da su ka karaso Word rooms din masarautar
su na isowa tun kafin Azim ya sauko ya bude mishi kofar ya bude ta da kan shi ya sauko ya yi gaba
da sauri ita ma Inaya ta sauko ta bi bayan shi
ya na shigowa word room din ya ga wasu sojojin biyu tsatsaye a bakin kofar , su na ganin shi su ka sara mishi
bai bi ta kan su ba ya karaso cikin dakin , nan ya ga Hakim Konce saman gado an yi mishi bandeji a kai da hannun daman shi , dayan hannun ya na sanye da catheter a na yi mishi karin jini
cikin rudu Malik ya dago kai ya kali General da ke tsaye dayan geffen gadon ya ce " How ? Ta ya hakan ta faru ne ? "
General na shirin magana Inaya ta shigo dakin , da sauri ta kama Hannun Malik ta kontar da kan ta saman damtsen shi ta na boye Fuskar ta
wani cool murmushi General ya saki kafin ya sara mata
sannan ya kali Malik ya ce " wani ne ya kai mishi hari a cikin cell din shi "
" He is Die ? " Malik ya tambaye shi
General bai ce mishi komai ba ya kai hannu ya daga mishi rigar shi , nan ya ga wani bandejin a cikin shi da allamun wuka a ka caka mishi
" i'm sorry Sir , he is Die " General ya fada ya na janye hannun shi ya meda shi a baya ya rike su
cike da takaici Malik ya ce " How ku na zaman me da har za a kai mishi hari cikin cell har a kashe shi , zaman me ku ke ? General Abdallah Tell me ya ka ke so na........ "
bai kai karshen maganar shi ba Inaya ta katse shi da cewa " baby kontar da hankalin ka , bai fa mutu ba "
ba shiri General da ya sunkuyar da kai tun lokacin da Malik magana ya dago shi ya na kallon Inaya , shi ba katse Malik da ta yi ba ya sa shi dago kai , babyn da ta ce mishi tsakani da Allah shi da ita wa za a ce ma baby
ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " please Cutie keep quiet "
marairaice mishi fuska ta yi ta na cewa " Please baby ka tsaya ka ji mana "
dan karamin tsaki Malik ya yi ya na kauda kai gefe cikin bacin rai , yanzun hanyar shi guda da zai kamo wanda ya saka a kashe Malik ta mutu ya zai yi
ya na a haka kawai ya ji Inaya ta janye hannun ta da ga cikin nashi
slowly ya juyo ya kale ta irin kallon nan na me za ki yi
cikin girmamawa ta ce " na ce maka bai mutu ba , Ka ba ni izini ranka shi dade na gwada maka "
a hankali ya gyada mata kai allamun ya ba ta izini
wani cool murmushi ta saki kafin ta tako a hankali ta karaso gaban gadon Hakim ta tsaya ta na kallon shi na dan dakikai
nan take idanun ta su ka koma Farare kal ko digon baki babu a ciki har wani haske su ke kamar torch
Dum General ya ji zuciyar shi ta buga har wani baya ya yi ya na karanto kalmar shahada ya na dafe saitin zuciyar shi kamar dan shi ya ke fuskantar ta
cikin rudu Malik ya ce mishi " General Lafiya ? "
Ina fa General babu bakin magana zuciyar shi sai duka uku uku ta ke yi ya na kallon Inaya babu ko kiftawa
a hankali ta dago hannun ta , ta daura saman cikin Hakim inda a ka yi mishi Dressing ta dan danna kadan ta lumshe idanun ta
wani irin dogon nunfashi Hakim ya ja har sai da kirjin shi ya yi sama kafin ya koma ya shiga yin nunfashi da karfi ya bude idanun shi slowly
da sauri Inaya ta bude idanun ta sun koma dai'dai , ta ja da baya ta na dafe saitin zuciyar ta ita ma ta na bugawa da karfi
da sauri Malik ya taro ta ya na cewa " Cutie are you okay ? "
a hankali ta juyo ta kale shi kafin ta gyada mishi kai da ga haka ta fada jikin shi ta rungume shi
sunkuyar da kan shi ya yi ya manna mata kiss saman forehead din ta sannan ya dago ya kali General ya ce " ku ba shi kulawar da ta dace , Idan wani abu ya same shi a wannan karan kai zan tuhuma , Mu hadu a fada Gobe tare da Azzam " ya na gama fadar haka ya sa hannayan shi biyu ya dauki Inaya cak kamar baby ya juya ya fice word room din
su ka bar General nan tsaye ya na faman zaro idanu ya kassa tantance abun da ya faru anya gaskiya ne ko dai mafarki ne ya ke bai sani ba
β€β EXILED PRINCE ββ€
(LOVE MEETS POWER ) ππ₯
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : MEERAH ππ₯
BOOK ________3 βππ₯
P A G E 3 π₯ β€
bangaran su Malik kuwa , kai tsaye motar su ya nufa da ita su ka koma part din su
ko da su ka koma part din su maimakon su koma barcin su , kawai su ka shiga sabon aiki , ni dai ina da ga gefe ina kallon su , su ka murji junan su da kyau
sai da ya fara jiyo kiran Sallar asubahi sannan ya hakura ya kyale ta sannan su ka shiga wanka a tare , su ka fito su ka shirya shi ya kama hanyar mosque ita kuma ta yi sallar ta cikin dakin
Malik kuwa ko da su ka Kamala Sallat sai da ya wuce wajen Momyn shi da Ammie
sai wajen karfe 7 ya koma part din shi , ko da ya shigo part din su ya tardo ta konce saman gado ta na barci
bai bi ta kan ta ba ya shiga toilet ya yi wanka sannan ya fito ya shirya cikin manyan kayan shi na Malik sannan ya bar dakin , amma kafin ya fita sai da ya manna mata kiss a saman forehead din ta sannan ya tafiyar shi Fada
Bakin shi da sallama cen kassan makoshi ya shigo fadar
su na ganin shi duk su ka mike tsatsaye su na sunkuyar da kai cikin girmamawa
bai bi ta kan su ba ya nufi Chair din shi ya zauna ba tare da ya ce musu komai ba
a hankali kowane ya koma ya zauna
su na zama ko Inaya ta shigo fadar ta na sallama , ta na sanye da wata muguwar gown pink color har kassa ta daura Alkyabar MALIKAT AL'UMU da ya daura mata ranar naddin shi sai qamshi ta ke saki
a tare duk mutanan Fadar su ka yi mamakin ganin ta har shi kan shi Malik , wadda ya bari yanzu ta na kwana ya a ka yi ta samu lokacin yin wannan uban shirin da ga gani kuma wannan shirin ba na mintina ba ne
a hankali ta daga kafa ta fara takowa cikin Fadar
a hankali duk wanda ke zaune ya mike ya na kallon ta cike da tambaya
ba ta bi ta kan su ba ta nufi Chair din MALIKAT ta zauna cikin nitsuwa
ta na zama ko wane ya koma ya zauna ya na bin ta da kallo wajen ya yi tsit
kamar ko Malik ya san abun da su ke tunanin cikin nitsuwa ya ce musu " Why ku ka tsare ta da idanu haka , ba ku taba ganin MALIKAT ta shigo fada ba ? "
a tare duk su ka saki murmushi su ka kauda kai cikin girmamawa Diya ya sunkuyo ya ce mishi " ba komai ran ka shi dade , bare kuma ina ga za mu bukaci ra'ayin mace a tare da mu dan wannan karar ta shafe ta , Azim za ka iya shigo da su "
Gyada mishi kai Azim ya yi kafin ya juya ya fice fadar
ya na fita ya dan matso da kan shi kusan Inaya ya ce mata " me ki ke yi a nan ? "
ba tare da ta kale shi ba ta ce " Why za ka tafi ka kyale ni ? "
" ba dawowa zan yi ba ? "
" hmmm irin na jiya ko ? "
har ya bude baki zai yi magana Azim ya shigo fadar
a hankali Malik ya gyara zaman shi dai'dai lokacin da wani namiji ya shigo fadar da mata a bayan shi su na sallama
a tare su ka karaso tsakiyar Fadar sannan su ka zube saman guyiwowin su kai a sunkuye su ka gaishe da Malik cikin girmamawa
gyada musu kai kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba
sai da su ka Kamala gaisuwar su sannan Diya ya ce " Ranka shi dade , wannan sunnan shi Hadi Ahmed , wannan kuma matar shi ce Zulaihat , shekaran jiya ta kawo karar ta na rokon mai martaba Malik ya shiga tsakanin su ya raba auren "
ya na gama rufe bakin shi Rafik ya ce " Yarinya , why za ki ce a raba auren ku , wani laifi ya yi miki ko kuma ba ki son shi ? "
shiru Zulaihat ta yi ba ta ce komai ba , sai ma kuka da ta fara yi kassa kassa
cikin sigar rarrashi Diya ya ce mata " Zulaihat , ba kuka za ki yi ki , ki bude baki ki fada mana dalilin ki na cewa a raba auren ku , kin san ba karamin abu ba ne raba aure "
a hankali Zulaihat ta fara girgiza kai cikin kukan nata ta ke cewa " Don Allah ku raba da shi , wlh ba na son shi "
" ba ki son shi ki ka yarda ki ka aure shi , ko kuma cilas ta miki a ka yi ? " Diya ya fada
A hankali ta girgiza musu kai allamun a'a
cikin Tsawa Mohammed ya ce mata " ki bude baki ki yi magana ba shiru za ki yi ba , ki na son ki batawa Mai martaba lokaci "
ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Inaya ta na cewa " Ba tsawa za ka yi mata ba , Kamata ya yi ku bi ta a hankali " ta na gama fadar haka ta mike a hankali ta fara takawa kowa na kallon ta ya na jiran ya ga abun da za ta yi
a hankali ta karaso gaban Zulaihat ta Zube saman guyiwowin ta da murmushi a fuskar ta ta ce " yar uwa , kar ki ji tsoro ki fadi abun da ke cikin ran ki , kin ji ko ? "
gyada mata kai kawai Zulaihat ta yi ba tare da ta ce komai ba
wani cool murmushi Inaya ta saki sannan ta ce " Shikenan yanzu fada min ba ki son shi ? "
girgiza mata kai ta yi ta na cewa " da ba na son shi ba zan yarda na aure shi ba "
" to minene matsalar , why za ki ce a raba auren ku bayan ki na son mijin ki "
" Ina son shi amma gaskiya ba zan iya zama tare da shi ba , ba zan iya zama da mutumin da zai iya daga hannu ya dake ni , wanda zai iya halaka ni babu ko tsoron Allah a idanun shi ni gaskiya a raba auren nan "
" Inallillahi , ki na nufin Dukan ki ya ke ? "
gyada mata kai Zulaihat ta yi kafin ta ce " kullum sai ya sa hannu ya dake ni , ko da ban yi mishi laifi ba , har ya kai na rasa cikin shi da ke a jiki na saboda Dukan da ya ke min , Idan na fadawa yan gidan mu , sai su ce na yi hakuri mu rufawa juna asiri , ko karar nan da na kawo babu wanda ke da labarin ta saboda na san za su yi kokarin hana ni , Don Allah ina rokon ki , ki yi wa adalin shugaban mu magana ya raba ni da shi , duba ki gani irin azabar da ya ke min "
ta kai karshen ta na sa hannu ta warware veil din da ke a kan ta
ga shaidar belt nan konce a kan fatar ta , saman shoulder , saman wuya har a kirji , sun ni jazir kamar jini zai fito
cike da takaici Inaya ta ce mata " ki yi hakuri na yi miki Alkawari ba ke ba shi a yau , kuma zai fuskanci hukunci dai'dai abun da ya yi miki "