Showing 36001 words to 39000 words out of 104561 words

Chapter 13 - Exiled Prince Book 3 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

396

ta dauki wayoyin
ta Inaya ta fara kunnawa , ta ga wallpaper din ta pic din Malik ne a sama , daya da ga cikin pics din da RIANNA ta turo mata
a hankali ta saki wani dan karamin murmushi kafin ta kunna wayar Malik , shi ma wallpaper din shi pic din Inaya ne , ta na konce saman gado , ta na sanye da wasu kananan kayan barcin pink color , gashin nan nata duk a tirje ta na barcin ta cikin konciyar hankali har wani dan karamin murmushi ta saki gwanin burgewa

wani cool murmushi Tesnim ta saki , ta na ci gaba da latsa wayar Malik amma sai ta ga ta na da Password ba dan ta so ba ta meda ta saman bedside drawer ta ajiye , sannan ta shiga latsa ta Inaya ta shiga messenger din ta , ta fara karanto Text din da Malik ya turo mata
sai da ta yi zaune ta karance su tsab sannan ta kashe wayar ta ajiye saman bedside drawer
sannan ta juyo ta kali Inaya ta saki wani cool murmushi murya kassa kassa ta ce " Gaskiya , yayana ya na matsanancin son ki , na san da ya son ki , amma ban taba tunanin soyayyar da ya ke miki ta kai haka ba , kamata ya yi a kira ku da Romeo & juliet , Allah ya sa ni ma wanda na ke so ya so ni haka , fiye da rayuwarshi "
ta na gama fadar haka ta tashi ta shiga toilet


▪AYMANE


" why ? why ? why ? why bai mutu ba ? ta ya a ka yi ma ya tashi wannan banzan Malik " Aymane ya ke fada cike da bacin rai

wani dan karamin tsaki Rouksar ta yi kafin ta ce " ka na tambaya ta , yo ni sani na yi , ko ni Tesnim da RIANNA na ji su na maganar , na zo shiga part din MALIKAT INAS ne na ji RIANNA ta na cewa Tesnim wai Malik ya bude idanu "

" na san wacen banzar yarinyar ce ta ta tashe shi , sai da na ce miki ki kashe ta , ki kashe ta , ki kashe ta amma kin kassa , yanzu ya ki ke so na yi , Rouksar duk abun da ya faru laifin ki ne " ya fada ya na nuna ta da yatsa

hannu Rouksar ta kai ta buge hannun shi ta na kallon shi cikin ido ta ce " no , laifin ka ne , lokacin da Hakim ke shirin harbin Nawfel , kai ka juya kwakwolwar shi ya harbi Malik , why ba ka kyale shi ba ya harbe shi , da yanzu wannan ba ta faru ba , ba ka tunani kafin ka aiwatar , Malik da ka ke ganin shi ya fi mahaifin shi wayo , da tun farko shi ka bari Hakim ya kashe da yanzu kai ne a kan kujerar Malik , yanzu Ruhin MALIKAT AL'UMU da ka sa na boye cikin bishiyar nan da me zai anfane ka ? a sani na ba MALIKAT AL'UMU za ta nadda ka a matsayin Malik , son da ka ke wa mulkin Saudiya ya sa ka daina anfani da kwakwolwar ka , ka ce min idan na yi abun da ka ke so za kyale ni , na yi abun ka ke so dan haka da ga yanzu kar ka sake nema ta " ta na gama fadar haka ta bace bat

ta na barin wajen ya saki wata yar karamar kara ya na fadin " Ba zan hakura ba , dole mulkin Saudiya ya dawo hannu na , dole Saudiya ta dawo cikin hannun Aymane bin Abdoul Mujeeb " ya na gama fadar haka ya bace bat
ni dai sai dai na ce Allah ya tsare Malik da ga sharin Aymane , dan da ga gani ba abun da ba zai iya yi ba dan hawa kujerar Malik



▪WASHE GARI ⛅



a hankali Inaya ta turo kofar dakin Malik ta shigo ta na sallama kassa , ta na sanye da wata Abaya mai hawa biyu , ta ciki white color ta saman kuma kamar Alkyaba ta ke sky blue color , ta yi Rowling veil din ta white color shi ma sai tashin qamshi ta ke
ta na shigowa duk sojojin wajen su ka sara mata kafin su fice dakin daya bayan daya

su na fita ta saki wani kyawatencen murmushi ta na kallon Malik da ke zaune ya gama bayan shi da bango ya lumshe idanunshi

a hankali ta karaso bakin gadon ta tsaya ta na kallon shi wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta cije lips din ta na kassa a hankali ta juya ta zauna saman cinyoyinshi ta na sakin wata yar karamar dariya

a hankali ta kai hannayan ta ta sakalo wuyan shi ta na kallon face din shi ta turo wannan dan karamin bakin ta ta ce " baby , ce wa Nesi na yi wai ta bar ni na taba babyn da ke cikin ta , amma ta hana ni , ni ma lokacin da zan samu nawa babyn ba zan bari ta taba shi ba , na fada maka wani abu ? kwana biyun nan da ka yi har ka fara yin gemu , kum gaskiya ya na yi maka kyau " ta kai karshen ta na daura hannun ta saman face din shi

sai da ta gama shafar face din shi sannan ta sauko hannun ta saman chest din shi , kamar za ta yi kuka ta ce " baby wai yaushe za ka tashi ne ? don Allah ka tashi ina kewar ka sosai , ba na jin dadin kwana in har ba na tare da kai , ba ka ce honey moon za mu tafi ba ? shi ne ka ki tashi dan kar mu tafi ko ? ni ka tashi na hakura da tafiyar ma , ni kawai so na ke ka tashi mu bar wajen nan , mu komawar mu Nigeria , na san in mu ka zauna a nan sai sun raba ni da kai , ni kuma ba zan iya rayuwa babu kai ba , please baby ka tashi don Allah , ko dan saboda ni don Allah " ta kai karshen ta na sakin wani dan karamin kuka ta kontar da kan ta saman chest din shi ta na ci gaba da kukan ta

ita ba ta san tun shigowar ta dakin ya san da ita , duk abun da ta ke fada mishi ya na jin ta dama ba barci ya ke ba , tun lokacin da ya farka ya ke jiran ta dan ita kadai ce ya ke muradin gani

a hankali ya dago hannayan shi ya rungume ta a jikin shi
wata irin muguwar bugawa ce da zuciyar ta ta yi lokacin da ta ji saukar hannayan shi a bayan ta , ba shiri ta ware idanun ta ta na kallon hannayan shi

slowly ta dago da kanta , zuciyar ta na duka uku uku ta na kallon face din shi ta bude baki ta na son ta yi magana amma ta ki fitowa

a hankali ya ware idanun shi , ba su sauka ko ina ba sai cikin nata
daga mata gera guda ya yi ya na cewa " lafiya ki na min irin wannan kallon ? kar ki cinye ni " ya fada murya cen kassan makoshi da kyair ma ta iya jiyo sautin abun da ya ce ga shi kuma duk ta disashe

ba ta san lokacin ta saki wata yar karamar kara ta fada jikin shi ta rungume shi tsam ta na sakin kuka mai karfi har da hadiyar zuciya ta ke
bai yi kokarin hana ta ba , sai ma kara matse ta da ya yi a jikinshi ya lumshe idanunshi , ji ya ke kamar ya yi kuka

sai da ta gaji da kukan ta sannan ta dago kan ta , ta kai hannayan ta dukka biyu saman face din shi ta na cewa " baby , da gaske kai ne ? ba mafarki na ke ba ? ni ko mafarkin ne ma ba na son a tashe ni , na ji matukar kewar ka baby na , ji na yi kwanan da na yi babu kai kamar shekaru ne , kowace dakika ji na ke kamar awanni ne , don Allah kar ka sake tafiya ka bar ni ba zan iya jure rashin ka ba "

a hankali ya dago hannu ya daura saman kumatun ta a hankali ya fara goge mata hawayen ta ya na cewa " ba abun da zai raba ni da ke sai mutuwa , cikin daren nan za mu bar musu kassar su , za mu tafi US honey Moon , da ga nan ba za mu sake dawowa ba , a cen za mu yi rayuwar mu , yadda babu wanda zai sake kokarin raba ni da ke "

wani dan karamin murmushi ta saki ta na fadin " da gaske ka ke baby ? "

gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya ce mata " matso ki ji wani abu "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta matso da face din ta , ta na ce mishi " shikenan gani , me za ka fada min ? "

bai ce mata komai ba ya tsaya kawai ya na kallon ta
sai da ya gaji da kallon ta sannan ya dan sunkuyo a hankali ya sauke lips din shi saman nata ya manna mata kiss dai'dai lokacin da RIANNA ta turo kofar dakin ta shigo ta na sallama Tesnim na biye da bayan ta

da sauri Inaya ta zaro idanu , ta yi kokarin sauka da saman cinyoyin shi
da sauri RIANNA ta ce mishi " a'a koma zauna , bari mu tafi har ku gama mun dawo " ta na gama fadar haka ta riko hannun Tesnim su ka juya dan ta ga Allamun dan uwan nata bai gama debe kewar matar shi ba

su na fita Inaya ta juya ta kalli Malik ta na yi mishi hararrar wassa ta ce mishi " dubi yanzu ka sa sun tafi "

" ni na ce su zo min a wannan lokacin ? " ya fada cike da izza

" shikenan ni ma na tafi " ta fada ta na kokarin sauka da ga saman cinyoyin shi
da sauri ya riko ta ya na fadin " har kin gaji da gani na kenan ? "
turo mishi dan bakin nan nata ta yi ta na cewa " ni ban ce na gaji da ganin ka ba "
" why ki ke son tafiya to ? please kar ki tafi , wlh duk duniya ke kadai na ke bukata a kusa da ni a yanzu idan ki ka tafi may be na koma inda na fito " ya fada mata cikin sanyi murya

a hankali ta saki wani cool murmushi ta kontar da kan ta saman chest din shi ta ce " baby ni fa wassa na ke yi maka "

" da gaske ? " ya fada ya na daga mata gera guda kamar ta na ganin shi
a hankali ta dago kai ta ce mishi " baby wai na fada maka ka kusa zama uncle , Nes...... "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " na sani kin fada min , har yanzu ba ki daina wannan uban surutun naki ba , mutum dai kamar parrot "

kukan shagwaba ta fara yi mishi ta na harba kafafun ta ta ce " ni ka daina ce min parrot , kuma ai ni ban da surutu , kai ne kawai ke cewa hakan "

a hankali ya kai hannu ya ja mata kumatu ya na cewa " wannan dan bakin naki bai iya zama a rufe ba , amma a haka na ke son shi "

wani cool murmushi ta saki ta na shirin magana kawai ya cabko lips din ta ya fara kissing din ta cikin konciyar hankali ya na sauke ajiyar zuciya a jere ya zagayo da hannayan shi a bayan ta
a hankali ta kai hannu ta sakalo wuyanshi , ta na mayar mishi da martani , da ga gani ka san sun yi missing din junan su
a hankali ya kai hannu ya cire button din abayar ta ta sama , sannan ya riko zip din ta kassa ya fara yin kassa da shi sai dai zip din a iya kirji ya tsaya

a hankali ya zame bakin shi da ga cikin nata ya fido tongue din shi ya fara yi mata tafiyar tsutsa tun saman wuyan ta har tsakiyar boobs din ta

da sauri ta kai hannu ta riko shoulder din shi ta na cewa " baby , yi hakuri kar wani ya shigo mana "

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya dago kanshi ya na kallon ta sai wani lumshe idanu ta ke yi da allamun ya fara kashe mata jiki

" Tashi mu tafi " ya fada mata ya na ci gaba da kallon face din ta
daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " ina kuma za mu je kai da ba ka samu sauki ba ? , ka bari doctor ya zo ya sallama ka "

" shikenan tashi da ga sama na ni na tafi tun da ba za ki bi ni ba "
ba musu ta sauka da ga saman shi , ta yi tsaye bakin gadon ta na kallon shi
a hankali ya sauko da kafafun shi kassa , ya mike tsaye
nan take jiri ya debe shi ya yi baya zai fadi
da sauri Inaya ta riko hannun shi ta na fadin " ka gani ko ? please ka bari har doctor ya zo ya duba ka "

bai ce mata komai ba ya sake mikewa tsaye sai dai wannan karan ya zagayo da hannun shi a wuyan ta , sannan ya riko hannun ta ya zagayo a kugunshi ya ce mata " mu tafi "

babu yadda ta iya haka su ka fara takawa a tare ta na rike da shi , shi kuma sai sake mata nauyin shi ya ke
a haka har su ka fito dakin , guards na ganin shi su ka nufe shi da sauri za su taimaka mishi
a hankali ya daga musu hannu ya na cewa " ina a ka kontar da MALIKAT AL'UMU ? "
daya da ga cikin su ne ya yi gaba ya karaso bakin kofar dakin MALIKAT AL'UMU kawai ya tsaya

kallon Inaya Malik ya yi ya na cewa " Mu tafi ko ? "
gyada mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba , ita fa ta fara gajiya rikon nan da ta yi mishi , ga shi shi kuma sai kara sakin mata nauyin shi ya ke
babu yadda ta iya haka su ka daga kafa har su ka karaso dakin MALIKAT AL'UMU
a hankali ya kai hannu ya tura su ka shiga ya na sallama cen kassan makoshi

Tesnim na ganin shi ta taso da gudu ta fada jikin shi ta rungume shi
a hankali ya zagayo gudan hannun shi a bayan ta ya bubuga a hankali
a hankali Tesnim ta dago da ga jikin shi ta na cewa " Akhie , na yi kewar ka over "
" ni ma na yi kewar ki " ya fada ya na daura hannun shi saman kumatun ta

juyawa ya yi ya Kalli Inaya ya ce mata " zan iya tafiya yanzu , na gode "
" okay " ta fada a takaice ta na janye hannun ta da ga saman kugunshi , sannan ya janye hannun shi da ke saman wuyan ta ya fara takawa a hankali ya nufi gadon MALIKAT AL'UMU

baki sake Inaya ke kallon shi ya na tafiyar shi cikin nitsuwa , kenan dama zai iya tafiya da kan shi , shi ne ya sauke mata nauyi ga shi yanzu har wuyan ta ya fara yi mata ciwo

a hankali ya karaso bakin gadon MALIKAT AL'UMU , da sauri RIANNA ta mika mishi chair , ya zauna saman ta , kafin ya juya ya kali Inaya
daga mata gera guda ya yi ganin irin kallon da ta ke yi mishi
ta na ganin ya juyo gare ta ta kauda kai gefe ta na turo dan bakin nan nata
bai ce mata komai ba ya juya ya kali MALIKAT AL'UMU da ke konce kamar gawa
a hankali ya dago hannun shi ya daura saman kumatun ta ya na cewa " me ya same ta haka ? "

da sauri Tesnim ta ce mishi " Akhie ni ma ban sani ba , kawai mu zaune na ga ta fadi , da mu ka kawo ta likita shi ne doctor ya ke ce mana wai jinin ta ne ya hau saboda damuwar da ta ke ciki "

" Shi ne kawai zai sa ta shiga doguwar suma ? ku kira min doctor " ya fada cikin ba da umarni
da sauri Tesnim ta fita ta yi wa daya da ga cikin guard magana a kan ya kira doctor sannan ta dawo cikin dakin ta nufi Malik ta rungume shi ta na cewa " Akhie , ka ce mishi ya tada momy kar ta tafi ta bar ni "

" don't worry ba abun da zai same ta " ya fada cikin sigar rarrashi
a hankali MALIKAT INAS da ke zaune a bayan su ta karaso geffen Malik
ta na isowa ta sauke lips din ta saman forehead din shi ta manna mishi kiss ta na fadin " na godewa Allah da ba abun da ya same ka babyna , don Allah ka shirya ku bar wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login