Showing 60001 words to 63000 words out of 104561 words

Chapter 21 - Exiled Prince Book 3 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

391

ji a na yi mishi knocking
ba tare da ya motsa ba ya bada izinin shigowa

a hankali a ka turo kofar wata kyakyawar baturiya fara kal ta shigo dakin ta na sanye da wata faral vest irin ta doctor hannu ta rike da wata farar box , ta karaso bakin gadon

da sauri Malik ya sauka da ga saman gadon ya na fadin " doctor , please ki duba tun zuwan mu ta ke ce min cikinta na ciwo , ga shi kuma har da fever ta ke "

cikin nitsuwa doctor ta ce mishi " calm down please , ko za ka iya ban wuri na duba ta "

" okay " ya fada a takaice kafin ya nufi kofar fita dakin ya janyo mata kofa
kai tsaye parlourn kassa ya sauko ya zauna saman sofa ya dafe kan shi da hannayan shi biyu

sannu sannu har ya share one hour zaune a haka , ya ma rasa tunanin me zai yi

ya na zaune a haka ya ji an fara tako stair
a hankali ya dago kan shi ya na kallon ta har ta karaso cikin parlourn sannan ya nuna mata sofar da ke geffen tashi a kan ta zauna

ba musu ta karaso wajen sofar ta zauna ta ajiye box din ta geffen kafafun ta
sai da ta zauna sannan ya ce mata " ya jikin nata ? "

wani dan karamin murmushi Doctor ta saki kafin ta ce " ku kontar da hankalin ku , na yi mata allurar barci , yanzu haka ma ta na cen ta na barci "

" maganar ciwon cikinta kuma fa ? "

dan jinkirtawa doctor ta yi kafin ta ce " ban san yadda zan fada muku haka ba , it's a good and a bad news "

cikin rudu Malik ya ce mata " ban gane ba good and bad new ? "

" she is Pregnant " Doctor ta fada kai tsaye

wani irin sanyi ne lokaci guda cikin zuciyar ta , ya na sauke wata nanauyar ajiyar zuciya har sai da doctor ta dan zaro idanu ta na kallon shi

cikin sanyin murya doctor ta ce " amma kuma...... "

ba ta kai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " amma kuma me ? "

dan jinkirtawa doctor ta yi kafin ta ce " amma her pregnancy is so dare "

" risk ? how ? ban gane ba ta na cikin hatsari ? " ya fada duk a rude

" ban san ya zan kwatanta muku ba , but akwai wasu matan su na fuskantar hatsari lokacin da su ka samu ciki , mafi yawwancin lokaci hakan ya na samun nasaba ne da ga shekarun su , ina ga madam ba ta yi three months da ta fara period ta samun cikin , it's normal , wasu su na iya fuskantar hatsari wasu kuma abun ya zo musu normal "

cikin nitsuwa Malik ya katse ta da cewa " please ki kwatanta min yadda zan gane " ya fada dan ya fara gajiya da wannan dogon surutun

wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " ya kamata ku zubar da ciki tun kafin ya girma , idan ba haka ba za ta samu matsala , za kuma ta iya rasa rayuwarta lokacin haihuwar , at least 83% over 17% chance din ta na ta rayu idan ta ce za ta haife shi "

wata irin muguwar faduwa ce gaban shi ya yi , har sai da idanun shi su ka ciko da ruwa lokaci guda
da sauri ya lumshe idanun shi ya kauda kai gefe

a hankali doctor ta mike ta na fadin " i'm sorry , idan kun shirya zubar da cikin , za ku iya kira na na kawo maganin da zai zubar mata da cikin ba tare da ya cutar da ita ba , ni zan tafi sai da safe " ta kai karshen ta na nufar hanyar fita parlourn

shi dai Malik ya kassa bude idanun shi , ya na cikin tsaka mai wuya yanzu , ba ya jin zai iya kashe first baby din shi , Idan kuma ya bar shi ita zai rasa har abada , dole ya hakura da babyn dan ba zai iya rayuwa babu ita ba , bai matsu ba ko nan da shekara goma ne kafin su samu wani babyn


❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊




【BOOK ________3 👑✌】





______________________⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘___________________




{ P A G E ………19 🌹🕊}





a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya mike ya koma bedroom din su
ya na shigowa ya sa hannu ya cire jallabiyar jikin shi ya ajiye saman bedside drawer sannan ya Haye gadon ya na kallon ta , sai barci ta ke cikin konciyar hankali ta daura hannu guda saman cikinta

a hankali ya kai hannu saman cikinta shi ma
murya kassa kassa ya ce " i'm sorry but , ba za ka ci gaba da zama a nan ba , rayuwarta ta fiye min komai a duniya , kar ka damu nan da five years za ka dawo " ya na gama fadar haka ya kai bakin shi saman cikinta ya manna mata kiss sannan ya konta geffen ta ya sa hannu ya janyo ta jikinsa ya karanto musu adu'ar barci sannan ya lumshe idanunshi


▪WASHE GARI ⛅


▪MALIK



zaune ya ke saman sofa a parlourn kassa , ya na sanye da trouser white color da Shirt sky blue , ya saki wannan lalawsan gashin kan shi ya zubo mishi har saman shoulder

ya sunkuyar da kai ya na latsa wayarshi cikin konciyar hankali
ya dauki wajen good ten minutes a haka kafin ya kai wayar a kunne ya na sallama cen kassan makoshi

a daya bangaran amsa mishi sallamar shi MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " yanzu baby tafiya za ka yi ka bar ni ? " ta fada kamar za ta yi kuka

cikin sigar rarrashi ya ce " please Ammie kar ki yi min kuka , in sha Allah zan dawo nan da dan lokaci "

" shikenan , Ya ku ke ? fatan kun isa lafiya ? "

" Fine Ammie , i'm sorry ban samu na yi miki bankwana ba "

wani cool murmushi MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " hmmmm , ka yi sa'a ka ban hakuri da yanzu na kashe kiran na yi fushi da kai "

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " na san ba za ki iya yin fushi da babyn ki ba "

wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " hmmm kai dai , zan sa baby ta yi maganin ka , yanzu fada min ina ta ke ma ? ina son na mata magana "

" ta na barci " ya fada a takaice

" ka na ji , please ka yi mata pregnancy test , momyn ka ta ce min wai ta ga allamun ciki ne da ita , ina son na tabbatar da maganar hankalina ya konta " ta kai karshen ta na marairaice murya

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya bude baki murya kassa kassa ya ce " na yi mata "

wani kyawatencen murmushi MALIKAT INAS ta saki ta na fadin " da gaske ? please tell me , me ya bada ? na matsu na ji wlh "

shiru ya yi bai ce mata komai ba , shi ya ma yi nadamar fada mata , yanzu dole ya fada mata gaskiya
ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ji Muryar ta ta na fadin " Nawfel ka yi shiru ka kyale ni "

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " Ammie , ban san ya zan yi ba "
cikin sanyin murya MALIKAT INAS ta ce mishi " Nawfel kontar da hankalin ka ka fada min abun da ke faruwa "

ba musu ya shiga ba ta labarin abun da ya faru daren jiya da abun da doctor ta fada mishi
sannan ya daura da cewa " ban san ya zan yi ba Ammie , duk shawarar da zan yanke dole na rasa guda cikin su , amma gaskiya ban shirya rasa ta ba , zan iya hakuri da babyn na san Allah zai ba mu wani idan lokaci ya yi amma ba zan taba samun ta biyun ta ba that's why na yanke shawarar zubar da cikin kawai tun kafin ya yi mata illa "

a hankali MALIKAT INAS ta sauke ajiyar zuciya
kamar da ga sama ya jiyo Muryar MALIKAT AL'UMU ta na fadin " my baby , ka yi abun da zuciyarka ke fada maka , ba mu matsu da ganin yaran ka ba , farin cikinka mu ke so yanzu , idan kuma ita ce farin cikinka , duk abun da zai faru kar ka bari ka rasa ta ,in sha Allah za ku samu wani babyn nan gaba "

" Momy ! " ya fada murya kassa kassa , ashe dama a tare su ke duk abun da ya fada MALIKAT AL'UMU ta ji shi , kawai ta yi shiru ne

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " yanzu tashi ka je ka duba ta , may be ta tashi ta na neman ka ba ka sani ba "

" i love you " ya fada cikin sanyin murya

a tare MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka amsa mishi da cewa " ni ma ina son ka "

da ga haka su ka yi sallama ya sauko wayar ya dan latsa na mintoci kafin ya mike ya sa wayar a aljihun shi sannan ya nufi hanyar stair
bai kai ga hawa stair din ba idanun shi su ka sauka saman ta , ta na tsaye bakin stair din ta daura hannu saman cikinta , sai hawaye ta ke bibiyu

" Cutie " ya fada a razane dan bai yi tunanin ta na nan ba , shi ko bai san tun lokacin da ya fara bawa MALIKAT INAS labarin abun da doctor ta fada mishi , ta ke tsaye wajen , duk abun da fada ta ji shi

da sauri ya fara taka stair din sai dai kafin ma ya iso tsakiya ta juya da sauri ta koma bedroom din su
da gudu ya bi bayan ta ya kiran sunan ta
ya na shigowa bedroom din su ya gan ta zaune tsakiyar gadon ta juyawa kofar baya ta na kuka

a hankali ya karaso bakin gadon murya kassa kassa ya ce " Cutie , why did you cry ? "
ba tare da ta juyo ba ta ce " na ji abun da ka fadawa Ammie , ka na son ka kashe babyn mu "

" ya salam " ya furta cen kassan makoshi sannan ya zauna bakin gadon ya kai hannu ya janyo ta kusan shi
cikin sanyin murya ya ce mata " Cutie , please ki yi hakuri ki daina kukan please , kin fi kowa sanin ba na son ganin kukan ki "

girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " ni ka kyale ki , ni babu wanda zai raba ni da babyna "

" Cutie , please listen to me , ni ma fa babyna ne "

da sauri ta katse shi da cewa " kuma shi ne za ka ce mu zubar da shi ? ni gaskiya a bar mun babyna "

a hankali ya sa hannu ya juyo ta su na fuskantar juna , ya ce mata " Cutie , duk fa ciwon cikin nan da ki ke yi saboda shi ne , kuma haka zai ci gaba ba zai daina ba , kuma doctor ta ce za ki iya rasa rayuwarki idan ki ka ce za ki haife shi , yanzu doctor za ta kawo miki maganin da za ki sha ya Zube ba tare da kin cutu ba "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " baby don Allah kar ka raba ni da shi , wlh zan iya jurewa , kuma ai ba lalle na mutu ba , in lokacin haihuwar ya zo , a na iya cire shi ba tare da na yi nakuda ba , please baby wlh ina son shi , kuma ai kai da kanka ka ce ka na son mu samu baby , gashi kuma yanzu mun samu ka na neman ka kashe shi , a ka je mu kassa samun wani bayan shi kuma fa ? "

hannu ya kai saman kumatunta , sannan ya matso a hankali ya daura forehead dinshi saman nata murya kassa kassa ya ce " ba zan so abun da zai taba ni da ke My Cutie , amma tun da kin ce ki na son babyn , za mu shawo kan matsalar tare "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta fada jikin shi ta rungume shi ta na fadin " na gode sosai babyna "

kiss ya yi mata saman forehead kafin ya ce " shikenan yanzu tashi ki je ki yi wanka , sai ki sauko mu yi breakfast "

da to kawai ta amsa mishi kafin ta raba jikinta da nashi ta tashi a hankali ta nufi toilet ta shige
da kallo ya raka ta har sai da ta shiga sannan ya mike ya fito bedroom din



▪DAULAR SAUDIYA 👑🔥



a zaune MALIKAT AL'UMU , MALIKAT INAS da Rafik su ke cikin garden
cikin nitsuwa MALIKAT AL'UMU ta fara magana kamar haka " Rafik , na san ka na da labarin barin kujerar Malik da Nawfel ya yi ? "

cikin girmamawa Rafik ya ce " Eh ran ki shi dade na sani , kuma gaskiya ban ji dadin hakan ba "

" babu yadda za mu yi , ya tafi yanzu , mu kan mu ba mu san inda ya tafi ba , ya na da niyar dawowa ko ba shi da ? " Fadin MALIKAT INAS

dan jinkirtawa Rafik ya yi kafin ya ce " shikenan , Allah ya tsare shi ko a ina ya ke , amma Saudiya ta rasa babban shugaba , dan zuciyar yaron ku mai kyau ce , da a ce ya zauna kan kujerar ba karamin aiki zai yi ba cikin Saudiya "

" dama a kan maganar Saudiya ne mu ka kira ka " MALIKAT AL'UMU ta fada
sannan MALIKAT INAS ta daura da cewa " tun da Nawfel ya sauka da ga kujerar , yanzu babu kowa a saman ta , shi ne na ce ya kamata mu nada wani Malik , wanda zai dace da kujerar dan ci gaba da kula da masarautar Saudiya "

gyada kan shi a hankali Rafik ya yi kafin ya ce " Eh haka ne ranki shi dade , yanzu wa ku ke tunanin zai dace da kujerar mai girma Malik "

dan jinkirtawa MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " why ba za a nada Aymane ba ? ka ga shi ma dan sarki ne , ya san yadda a ke kula da masarauta , da wasu harkokin cikinta , ina ga zai dace , bare kuma shi ya ke aure babbar yarinyar marigayi Malik , ina ga ba matsala idan a ka nada shi a matsayin Malik ko kuwa ? "

" to , ranki shi dade , a nawa tunanin why ba za a nada na hannun daman Malik ba ? wato Diya , ina ga zai fi dacewa da kujerar , kin ga shi ne na hannun daman Malik , ya yarda da shi fiye da rayuwarshi , kuma duk wata shawara da Malik ya yanke tare da Diya ya yanke ta , ina ga gaskiya zai fi dacewa fiye da Aymane , kun ga Aymane ba wani sanin kirki mu ka yi mishi ba "

gyada mishi kai MALIKAT INAS ta yi kafin ya ce " ni ma haka na gani , amma Rafik ka sani sai wanda ya ke da hadi da Daular Saudiya a ke iya nadawa a matsayin Malik , Diya kuma ba shi da hadi da Daular Saudiya , ka ga ba zai iya hawa ba "

" kin yi gaskiya ranki shi dade , ai zai iya auren Gimbiya Tesnim , Idan hakan bai bata muku ba ranka shi dade " ya fada ya dan sunkuyar da kai

murmushi mai dan sauti MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " Rafik , a ranar da a ka yi auren RIANNA da Aymane , a ranar a ka yi auren Tesnim da babban yayan MALIKAT INAYA "

dan zaro idanu Rafik ya yi dan shi sam ba shi da masaniya a kan auren Tesnim , dan a lokacin da a ka tafi mosque daura auren , an kira shi a gida ya koma bai ziyarci auren ba

a hankali ya furza iska da ga bakin shi kafin ya ce " shikenan ranki shi dade , a nada Aymane din , Allah ya sa shi ya fi al'heri "

a tare MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS su ka amsa da Ameen
sannan MALIKAT INAS ta ce " a fara shirye shiryen , ban da sati guda sai a nada shi a matsayin Malik "

" an gama ranki shi dade " Rafik ya fada
da ga haka su ka ci gaba da tattaunawar su a kan abun da ya shafi masarautar



▪NESRINE


zaune ta ke cikin parlourn su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login